Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 2/1 pp. 8-13
  • Jehovah—Mafificin Misali Na Nagarta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehovah—Mafificin Misali Na Nagarta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Yi Mana Nagarta da ba Mu Cancance ta Ba
  • An Ɗaukaka Nagartar Jehovah
  • “Ina Roƙonka, Ka Nuna Mini Darajarka”
  • “Allah . . . Mai-Yalwar Jinƙai”
  • Jehovah—Mai Jinƙai da Alheri
  • Allah Mai Jinkirin Fushi
  • Ka Yi Koyi da Nagartar Jehovah
  • “Allah Mai Nagarta Ne da Babu Kamarsa!”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Ka Ci Gaba Da Yin Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Nagarta​—Ta Yaya Za Mu Koyi Nuna Wannan Halin?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Mu Rika Yin Alheri Kamar Allah
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 2/1 pp. 8-13

Jehovah—Mafificin Misali Na Nagarta

“A yi godiya ga Ubangiji mai-runduna, gama Ubangiji nagari ne.”—IRMIYA 33:11.

1. Me ya sa muke motsawa mu yaba wa Allah don nagartarsa?

JEHOVAH ALLAH nagari ne kamiltacce. ‘Yaya misalin yawan nagartarsa!’ in ji annabi Zechariah. (Zechariah 9:17) Hakika, nagarta ta bayyana cikin dukan abin da Allah ya yi wajen shirya duniya don mu ji daɗinta. (Farawa 1:31) Ba za mu taɓa fahimtar dukan dokoki masu wuya da Allah ya sa suna aiki yayin da ya halicci sararin samaniya ba. (Mai-Wa’azi 3:11; 8:17) Amma kaɗan da muka sani yana motsa mu mu yaba wa Allah don nagartarsa.

2. Yaya za ka ba da ma’anar nagarta?

2 Mecece nagarta? Ɗabi’a ce mai kyau, ko halin kirki. Amma, ya wuci guje wa yin abin da ba shi da kyau kawai. Nagarta, tana ɗaya daga cikin ’ya’yan ruhu, hali ne nagari. (Galatiyawa 5:22, 23) Muna yin abubuwa nagari yayin da muke aikata ayyuka da wasu za su amfana. A wannan zamani, abin da ake ɗauka nagari a wasu wurare ƙila ana ɗaukansu marasa kyau a wasu wurare. Idan za mu more salama da farin ciki, dole mu kasance da mizani ɗaya na nagarta. Waye ya dace ya kafa wannan mizani?

3. Menene Farawa 2:16, 17 ta nuna game da mizani na nagarta?

3 Allah ya kafa mizani na nagarta. A somi na tarihin ’yan Adam, Jehovah ne ya umurci mutum na farko: “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:16, 17) Hakika, ’yan Adam suna bukatar su dogara ga Mahaliccinsu a sanin nagarta da mugunta.

An Yi Mana Nagarta da ba Mu Cancance ta Ba

4. Menene Allah ya yi wa ’yan Adam tun lokacin da Adamu ya yi zunubi?

4 Begen ’yan Adam na madawwamin farin ciki cikin kamilta ya lalace sa’ad da Adamu ya yi zunubi kuma ya ƙi ya amince da ikon Allah na kafa mizanan nagarta. (Farawa 3:1-6) Amma, kafin a haifi ’ya’yan Adamu magadan zunubi da mutuwa, Allah ya annabta zuwan kamiltaccen Ɗa. Da yake magana da “tsohon macijin,” Shaiɗan Iblis, Jehovah ya ce: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; Farawa 3:15) Nufin Jehovah ne ya fanshi mutane masu zunubi. A nuna mana nagarta da ba mu cancanta ba, Jehovah ya yi wannan shirin don ceton waɗanda suka ba da gaskiya a fansar hadaya na Ɗansa da yake ƙauna.—Matta 20:28; Romawa 5:8, 12.

5. Ko da mun gaji mugun tunani, me ya sa za mu ɗan yi nagarta?

5 Domin zunubin Adamu, babu shakka mun gaji yin mugun tunani. (Farawa 8:21) Abin farin ciki, Jehovah ya taimake mu mu ɗan yi nagarta. Ci gaba cikin abubuwa da muka koya daga littattafansa masu tsarki masu tamani ba kawai sun ‘sa mu hikima zuwa ceto ba’ da ‘shirya mu da kyau domin kowane managarcin aiki’ amma sun taimaka mana mu yi abin da ke nagari a gabansa. (2 Timothawus 3:14-17) Amma, don mu amfana daga koyarwa ta Nassi kuma mu yi nagarta, dole ne mu kasance da hali na mai Zabura wanda ya rera waƙa: “[Jehovah] kai nagari ne, kana kuwa aika nagarta; ka koya mini farillanka.”—Zabura 119:68.

An Ɗaukaka Nagartar Jehovah

6. Bayan Sarki Dauda ya kawo sunduƙi na alkawari zuwa Urushalima, Lawiyawa sun rera waƙa da ke ɗauke da waɗanne kalmomi?

6 Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya yarda Allah nagari ne kuma ya nemi ja-gorarsa. “Ubangiji nagari ne mai-adalci kuma,” in ji Dauda. “Domin wannan za shi koya ma masu-zunubi a cikin tafarki.” (Zabura 25:8) Koyarwa ta Allah da aka ba Isra’ilawa ta haɗa da umurnai goma masu muhimmanci—Dokoki Goma—da aka rubuta a kan allon duwatsu biyu kuma aka ajiye a wuri mai sarki da ake kira sunduƙi na alkawari. Bayan Dauda ya kawo Sunduƙin zuwa babban birni na Isra’ila, Urushalima, Lawiyawa suka rera waƙa da ta haɗa da wannan furcin: “A yi godiya ga Ubangiji; gama nagari ne shi: gama jinƙansa ya tabbata har abada.” (1 Labarbaru 16:34, 37-41) A ji waɗannan kalmomi daga leɓunan mawaƙa Lawiyawa yana da daɗi!

7. Menene ya faru bayan aka kawo Sunduƙi cikin wuri Mafi Tsarki kuma bayan Sulemanu ya yi addu’ar keɓewa?

7 An nanata wannan kalmomin yabo lokacin da ake keɓe haikalin Jehovah da ɗan Dauda Sulemanu ya gina. Bayan an ajiye sunduƙi na alkawari a sabon wuri Mafi Tsarki na haikalin da aka gina, Lawiyawa suka soma yabon Jehovah, “nagari ne shi, gama jinƙansa ya tabbata har abada.” A wannan lokacin haikalin ya cika da gajimare ta mu’ujiza da ke alamta bayyanuwar Jehovah cikin daraja. (2 Labarbaru 5:13, 14) Bayan Sulemanu ya yi addu’ar keɓewa, “wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da sauran hadayu.” A ganin wannan, “dukan ’ya’yan Isra’ila . . . suka sunkuyadda kansu, fuskokinsu a ƙasa a kan duwatsu, suka yi sujjada, suka yi godiya ga Ubangiji, suka ce, gama shi nagari ne; gama jinƙansa yana tabbata har abada.” (2 Labarbaru 7:1-3) Bayan biki na kwana 14, Isra’ilawa suka koma gidajensu “suna murna da farin zuciya domin alherin da Ubangiji ya nuna ma Dauda, da Sulemanu da Isra’ila mutanensa.”—2 Labarbaru 7:10.

8, 9. (a) Ko da Isra’ilawa sun yabi Jehovah don nagartarsa, wane tafarki suka bi daga baya? (b) Menene Irmiya ya annabta game da Urushalima, ta yaya wannan annabci ya cika?

8 Abin baƙin ciki, Isra’ilawa ba su ci gaba ba da rayuwa cikin jituwa da waƙarsu na yabo ga Allah. Da sannu sannu, mutanen Yahuda suka shiga ‘girmama Jehovah da leɓunansu kawai.’ (Ishaya 29:13) Maimakon su bi mizanan Allah na nagarta, suka soma yin mugunta. Mecece muguntarsu ta ƙunsa? Suka soma bauta wa gumaka, suna lalata, suna zaluntar matalauta, da wasu zunubai masu tsanani! Saboda haka, aka halaka Urushalima, kuma aka kwashe mazauna Yahuda zuwa bauta a Babila a shekara ta 607 K.Z.

9 Da haka Allah ya horar da mutanensa. Amma ta annabi Irmiya, ya annabta cewa cikin Urushalima za a ji murya waɗanda suke cewa: “A yi godiya ga Ubangiji mai-runduna, gama Ubangiji nagari ne, jinƙansa ya dawwama har abada!” (Irmiya 33:10, 11) Kuma hakan ya kasance. Bayan shekara 70 da ƙasar ta kasance kango, a shekara ta 537 K.Z., raguwar Yahudawan suka koma Urushalima. (Irmiya 25:11; Daniel 9:1, 2) Suka sake gina bagadi da ke haikalin a kan Dutsen Moriah kuma suka soma miƙa hadayu a wurin. An kafa tushen haikalin a shekara ta biyu da dawowarsu. Lokaci ne na farin ciki! “Sa’anda magina suka kafa tushen haikalin Ubangiji,” in ji Ezra, “aka sa [firistoci] su tsaya cikin tufafinsu da ƙahoni, da Lawiyawa kuma ’ya’yan Asaph da kugai, su yabi Ubangiji, bisa ga ka’idar Dauda sarkin Isra’ila. Suka yi ma juna waƙa suna yabon Ubangiji suna gode masa, suka ce, Gama shi nagari ne, gama jinƙansa ya tabbata har abada zuwa ga Isra’ila.”—Ezra 3:1-11.

10. Da wane furci na musamman Zabura ta 118 ta soma kuma ta ƙare?

10 Irin wannan furci na yabo game da nagartar Jehovah ya bayyana a wurare da yawa cikin zabura. Cikinsu ita ce Zabura ta 118, iyalan Isra’ilawa ne suka rera waƙar a kammala bikin Idin Ƙetarewa. Wannan Zabura ta soma kuma ta ƙare da kalmomin nan: “A yi godiya ga Ubangiji; gama nagari ne shi: gama jinƙansa ya tabbata har abada.” (Zabura 118:1, 29) Wataƙila wannan ne kalmomi na ƙarshe na yabo da Yesu Kristi ya rera a waƙa da manzanninsa masu aminci a daren da zai mutu a shekara ta 33 A.Z.—Matta 26:30.

“Ina Roƙonka, Ka Nuna Mini Darajarka”

11, 12. Lokacin da Musa ya ɗan ga ɗaukakar Allah, wace sanarwa ce ya ji?

11 An nuna nasaba da ke tsakanin nagartar Jehovah da jinƙansa na farko ƙarnuka kafin zamanin Ezra. Ba da daɗewa ba bayan Isra’ilawa suka bauta wa maraƙi na zinariya a daji kuma aka halaka masu laifin, Musa ya roƙi Jehovah: “Ina roƙonka, ka nuna mini darajarka.” Tun da Musa ba zai iya ganin fuskarsa ba kuma ya rayu, Jehovah ya ce: “Zan sa dukan nagartata ta gibta a gabanka.”—Fitowa 33:13-20.

12 Nagartar Jehovah ta gibta a gaban Musa washegari a kan Dutsen Sinai. A wannan lokacin, Musa ya ɗan ga ɗaukakar Allah kuma ya ji wannan kirari: “Ubangiji, Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya; yana tsaron jinƙai domin dubbai, yana gafarta laifi da saɓo da zunubi: ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan; yana ziyartadda alhakin iyaye bisa ’ya’ya, bisa ’ya’yan ’ya’ya kuma, bisa tsara ta uku da ta huɗu.” (Fitowa 34:6, 7) Waɗannan kalmomi sun nuna cewa nagartar Jehovah ta danganta da jinƙansa da wasu fannoni na mutuntakarsa. Yin la’akari da waɗannan zai taimake mu mu yi nagarta. Da farko bari mu bincika hali da aka ambata sau biyu a wannan sanarwa ta nagartar Allah mai ban mamaki.

“Allah . . . Mai-Yalwar Jinƙai”

13. A sanarwa ta nagartar Allah, wane hali ne aka ambata sau biyu, me ya sa wannan ya dace?

13 “Ubangiji Allah [ne] . . . mai yalwar jinƙai . . . yana tsaron jinƙai domin dubbai.” Kalmar Ibrananci da aka fassara “jinƙai” na kuma nufin “ƙauna ta aminci.” Shi ne hali kawai da aka ambata sau biyu cikin sanarwar Allah ga Musa. Ya dace, tun da halin Jehovah na musamman ƙauna ce! (1 Yohanna 4:8) Sanannen furci na yabo ga Jehovah “gama nagari ne shi: gama jinƙansa ya tabbata har abada” ya nanata wannan halin.

14. Su wanene musamman suke more nagartar Allah da jinƙai?

14 Nuni ɗaya na nagartar Jehovah shi ne cewa “mai-yalwar jinƙai ne.” Wannan a bayyane yake musamman yadda yake kula da kyau da bayinsa masu aminci da suka keɓe kai. (1 Bitrus 5:6, 7) Yadda Shaidun Jehovah za su shaida, yana ‘ajiyar jinƙai’ ga waɗanda suke ƙaunarsa kuma na bauta masa. (Fitowa 20:6) Al’ummar Isra’ila na jiki sun daina samun jinƙai na Jehovah, ko kuma ƙauna ta aminci, domin sun ƙi Ɗansa. Amma nagartar Allah da ƙauna ta aminci ga Kiristoci masu aminci na dukan al’ummai za su tabbata har abada.—Yohanna 3:36.

Jehovah—Mai Jinƙai da Alheri

15. (a) Shela da Musa ya ji a kan Dutsen Sinai ya soma da wane furci? (b) Menene jinƙai ya ƙunsa?

15 Shela da Musa ya ji a kan Dutsen Sinai ya soma da furcin nan: ‘Jehovah, Jehovah, Allah ne cike da jinƙai, mai-alheri kuma.’ Kalmar Ibrananci da aka fassara ‘jinƙai’ na iya nufin “hanji” kuma tana da dangantaka ta kusa da kalmar “mahaifa.” Saboda haka, jinƙai ya ƙunshi mutum ya nuna juyayi mai zurfi. Amma jinƙai ya ƙunshi fiye da tausayi na gaske. Ya kamata ya motsa mu mu yi wani abu mu sauƙaƙa wahala da wasu suke sha. Alal misali, dattawa Kirista masu ƙauna suna ganin bukatar kasancewa da jinƙai ga ’yan’uwa masu bi, suna ‘nuna jinƙai da fara’a’ sa’ad da ya dace.—Romawa 12:8; Yaƙub 2:13; Yahuda 22, 23.

16. Me ya sa za a ce Jehovah mai alheri ne?

16 Nagartar Allah ta kuma bayyana cikin alherinsa. Mai alheri yana “lura da yadda wani yake ji” yana nuna ‘alheri mai daraja musamman ga talakawa.’ Jehovah ne misali mafi kyau na alheri a yadda yake bi da bayinsa masu aminci. Alal misali, ta mala’iku, Allah cikin alheri ya ƙarfafa annabi Daniel tsoho kuma ya gaya wa budurwa Maryamu game da gata da za ta samu daga haifar Yesu. (Daniel 10:19; Luka 1:26-38) Mutanen Jehovah, hakika muna godiya ga hanyarsa ta alheri da yake mana magana ta shafuffukan Littafi Mai Tsarki. Muna yaba masa a wannan nuni na nagartarsa kuma mu nemi mu kasance da alheri a sha’aninmu da wasu. Yayin da waɗanda suka ƙware a ruhaniya suke wa ɗan’uwa mai bi gyara “cikin ruhun tawali’u” suna ƙoƙari ne su kasance da taushin hali, da alheri.—Galatiyawa 6:1.

Allah Mai Jinkirin Fushi

17. Me ya sa muke godiya cewa Jehovah “mai-jinkirin fushi” ne?

17 “Allah ne . . . mai-jinkirin fushi.” Waɗannan kalmomi sun jawo hankali ga wani nuni na nagartar Jehovah. Jehovah cikin haƙuri yana jimre wa kasawarmu kuma ya ba mu lokaci mu sha kan kumammanci mai tsanani kuma mu ci gaba a ruhaniya. (Ibraniyawa 5:12–6:3; Yaƙub 5:14, 15) Haƙurin Allah kuma yana amfani waɗanda tukuna ba su zama masu bauta masa ba. Har ila suna da lokaci su saurari saƙon Mulki su tuba. (Romawa 2:4) Ko da Jehovah yana da haƙuri, nagartarsa wani lokaci na motsa shi ya nuna fushinsa, yadda ya yi sa’ad da Isra’ilawa suka bauta wa maraƙi na zinariya a kan Dutsen Sinai. Ba da daɗewa ba Allah zai nuna fushinsa a hanya mafi girma sa’ad da ya kawo ƙarshen mugun zamani na Shaiɗan.—Ezekiel 38:19, 21-23.

18. Game da gaskiya, wane bambanci yake tsakanin Jehovah da shugabanne ’yan Adam?

18 “Ubangiji, Allah ne . . . mai yalwar . . . gaskiya.” Jehovah ya bambanta da shugabanne ’yan Adam, waɗanda suke alkawari da fahariya amma ba sa cikawa! Dabam kuwa, masu bauta wa Jehovah za su iya dogara ga dukan abin da aka faɗa a hurarriyar Kalmarsa. Tun da Allah mai yalwar gaskiya ne, koyaushe za mu dogara ga alkawuransa. Cikin nagartarsa, Ubanmu na samaniya babu fasawa yana amsa addu’o’inmu don gaskiya na ruhaniya ta yin tanadinsa a yalwace.—Zabura 43:3; 65:2.

19. Wace nagarta ta musamman Jehovah ya nuna wa masu zunubi da suka tuba?

19 “Ubangiji Allah ne mai . . . gafarta laifi da saɓo da zunubi.” Don nagartarsa, Jehovah a shirye yake ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba. Hakika muna godiya cewa Ubanmu na samaniya mai ƙauna ya yi tanadi don gafara ta hadayar Yesu. (1 Yohanna 2:1, 2) Muna farin ciki, cewa duka da suka ba da gaskiya cikin fansar za su iya more dangantaka mai kyau da Jehovah, da begen rai na har abada cikin sabuwar duniya da ya yi alkawarinta. Wannan dalilai ne na musamman mu yaba wa Jehovah don yin nagarta ga mutane!—2 Bitrus 3:13.

20. Wane tabbaci muke da shi cewa Allah ba ya amincewa da mugunta?

20 “[Jehovah] ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan.” Wannan wani dalili ne na yabon Jehovah don nagartarsa. Me ya sa? Domin fanni na musamman na nagarta shi ne cewa ba ta amince da mugunta a kowacce hanya. Ƙari ga haka, a “yayin bayyanuwar Ubangiji Yesu daga sama tare da mala’iku na ikonsa,” za a kawo ramako “bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar.” Waɗannan “hukunci za su sha, madawwamiyar halaka.” (2 Tassalunikawa 1:6-9) Masu bauta wa Jehovah da suka tsira za su iya more rayuwa sosai a lokacin ba tare da mutane marasa ibada sun dame su ba, waɗanda ‘ba sa son nagarta.’—2 Timothawus 3:1-3.

Ka Yi Koyi da Nagartar Jehovah

21. Me ya sa ya kamata mu yi nagarta?

21 Babu shakka muna da dalilai masu yawa na yabon Jehovah da yi masa godiya don nagartarsa. Mu bayinsa, bai kamata ba ne mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu nuna wannan halin? Hakika, gama manzo Bulus ya aririce Kiristoci masu bi: “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” (Afisawa 5:1) Ubanmu na samaniya sau da sau yana yin nagarta, saboda haka ya kamata mu yi.

22. Menene za mu bincika a talifi na gaba?

22 Idan mun keɓe kanmu ga Jehovah da zuciyarmu, babu shakka muna so mu yi koyi da nagartarsa. Domin mu ’ya’yan Adamu mai zunubi ne, ba shi da sauƙi mu yi abin da yake nagari. Amma a talifi na gaba, za mu ga abin da ya sa zai yiwu mu yi nagarta. Za mu kuma bincika hanyoyi dabam dabam da za mu iya da kuma ya kamata mu yi koyi da Jehovah—mafificin misalin nagarta.

Yaya Za Ka Amsa?

• Mecece nagarta?

• Wane furci na Nassi ya nanata nagarta ta Allah?

• Waɗanne ne wasu nuni na nagartar Jehovah?

• Me ya sa za mu yi koyi da misalin Jehovah na nagarta?

[Hoto a shafi na 10]

Jehovah ya yi horon mutanensa na dā domin ba su yi rayuwa daidai da furcinsu na yabo ba

[Hoto a shafi na 10]

Raguwar mutane masu aminci sun dawo Urushalima

[Hoto a shafi na 11]

Musa ya ji shela mai ban mamaki na nagartar Allah

[Hoto a shafi na 13]

An ga nagartar Jehovah a hanyar da ya yi mana magana ta shafuffukan Littafi Mai Tsarki

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba