Ka Ci Gaba Da Yin Nagarta
“Amfanin haske yana cikin dukan nagarta da adalci da gaskiya.”—AFISAWA 5:9.
1. Ta yaya miliyoyi yanzu suke nuna cewa sun yarda da Zabura 31:19?
ABU mafi kyau da kowane mutum zai iya yi shi ne ya ɗaukaka Jehovah. A yau, miliyoyi suna yin haka ta wajen yaba wa Allah don nagartarsa. Mu Shaidun Jehovah masu aminci, da dukan zuciyarmu mun yarda da mai Zabura da ya rera waƙa yana cewa: “Ina misalin girman alherinka, wanda ka ajiye ma waɗanda ke tsoronka.”—Zabura 31:19.
2, 3. Me zai faru idan ba mu goyi bayan aikinmu na almajirantarwa da hali mai kyau ba?
2 Tsoron Jehovah na motsa mu mu yaba masa don nagartarsa. Zai kuma motsa mu mu ‘yi wa Jehovah godiya, albarkace shi, kuma mu sanar da ɗaukakar mulkinsa.’ (Zabura 145:10-13) Shi ya sa muke da himma a wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa. (Matta 24:14; 28:19, 20) Hakika, za mu goyi bayan aikinmu na wa’azi da hali mai kyau. In ba haka ba, za mu jawo kunya a kan suna mai tsarki na Jehovah.
3 Mutane da yawa suna da’awar suna bauta wa Allah, amma halinsu bai jitu da mizanai da ke cikin hurarriyar Kalmarsa ba. Game da wasu da ba sa rayuwa daidai da da’awarsu na yin abin da ke nagari, manzo Bulus ya rubuta: “Kai . . . mai-koya ma wani, ba ka koya ma kanka ba? Kai da ka ke yin wa’azi kada a yi sata, kana yin sata? Kai da ka ke faɗi kada a yi zina, kana yin zina? . . . A wurin Al’ummai ana saɓon sunan Allah saboda ku, kamar yadda an rubuta.”—Romawa 2:21, 22, 24.
4. Wane sakamako halinmu mai kyau yake da shi?
4 Maimakon mu jawo kunya ga sunan Jehovah, mu yi ƙoƙari mu ɗaukaka shi da halinmu mai kyau. Wannan zai yi tasiri mai kyau a kan waɗanda ba sa cikin ikilisiyar Kirista. Abu ɗaya shi ne, yana taimaka mana mu sa ’yan hamayya da mu su daina. (1 Bitrus 2:15) Mafi muhimmanci, halinmu mai kyau na jawo mutane zuwa ƙungiyar Jehovah, yana sa su ɗaukaka shi kuma su samu rai madawwami.—Ayukan Manzanni 13:48.
5. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika yanzu?
5 Da yake mu ajizai ne, yaya za mu guje wa hali da ba zai daraja Jehovah ba kuma ya sa masu neman gaskiya su yi tuntuɓe? Hakika, ta yaya za mu yi nasara a yin nagarta?
Amfanin Haske
6. Waɗanne ne wasu “ayyukan duhu marasa-amfani,” amma wane ’ya’ya ya kamata Kiristoci su nuna?
6 Da yake mu Kiristoci ne da muka keɓe kanmu, muna more abu da ke taimakonmu mu guje wa “ayyukan duhu marasa-amfani.” Waɗannan sun haɗa da ayyuka da ba sa daraja Allah kamarsu ƙarya, sata, baƙar magana, batsa, banzan hali, zancen wauta, da maye. (Afisawa 4:25, 28, 31; 5:3, 4, 11, 12, 18) Maimakon mu sa hannu cikin irin wannan ayyuka, mu “yi tafiya kamar ’ya’yan haske.” Manzo Bulus ya ce “amfanin haske yana cikin dukan nagarta da adalci da gaskiya.” (Afisawa 5:8, 9) Saboda haka, ta yin tafiya cikin haske ne muke iya ci gaba da yin nagarta. Amma wane irin haske ne wannan?
7. Menene dole mu yi don mu ci gaba da nuna amfanin nagarta?
7 Duk da ajizancinmu, za mu iya yin nagarta idan mun yi tafiya cikin haske na ruhaniya. Mai Zabura ya rera: “Maganarka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma a tafarkina.” (Zabura 119:105) Idan mun ci gaba da nuna “amfanin haske” ta “dukan nagarta,” dole ne koyaushe mu yi amfani da haske na ruhaniya da ke cikin Kalmar Allah, mu bincika ta a hankali a littattafan Kirista, kuma mu tattauna a kai a kai a taronmu na sujjada. (Luka 12:42; Romawa 15:4; Ibraniyawa 10:24, 25) Muna bukatar mai da hankali sosai ga misali da koyarwar Yesu Kristi, “hasken duniya” da “walƙiyar darajar [Jehovah].”—Yohanna 8:12; Ibraniyawa 1:1-3.
’Ya’yan Ruhu
8. Me ya sa za mu iya yin nagarta?
8 Haske na ruhaniya babu shakka na taimaka mana mu yi nagarta. Ƙari ga haka, muna iya nuna wannan halin domin ruhu mai tsarki, ko kuma ikon aiki na Allah na yi mana ja-gora. Nagarta sashe ne na “ɗiyan ruhu.” (Galatiyawa 5:22, 23) Idan mun yi biyayya ga ja-gorar ruhu mai tsarki na Jehovah, zai fito da ’ya’yan nagarta na ban al’ajabi a cikinmu.
9. Yaya za mu aikata daidai da kalmomin Yesu da ke rubuce a Luka 11:9-13?
9 Son mu faranta wa Jehovah rai ta nuna ’ya’yan ruhu na nagarta ya kamata ya motsa mu mu aikata daidai da kalmomin Yesu: “Ku roƙa, za a ba ku; ku nema, za ku samu; ku ƙwanƙwasa, za a buɗe muku. Gama kowane mai-roƙo yana karɓa; mai-nema kuma yana samu; wanda ya ke ƙwanƙwasawa kuma, za a buɗe masa. Wanene daga cikinku da shi ke uba, ɗansa za ya roƙi dunƙulen gurasa, shi kuwa ya ba shi dutse? ko kuwa kifi, ya ba shi kuma maciji maimakon kifi? Ko kuwa idan ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? Idan ku fa da ku ke [ajizai don haka] miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Luka 11:9-13) Bari mu bi gargaɗin Yesu ta yin addu’a don ruhun Jehovah mu ci gaba da nuna ’ya’yansa na nagarta.
‘Ka Ci Gaba da Yin Abin da Ke Nagari’
10. Waɗanne fannoni na nagartar Jehovah aka ambata a Fitowa 34:6, 7?
10 Da haske na ruhaniya daga Kalmar Allah da taimakon ruhu mai tsarki na Allah, za mu iya ‘ci gaba da yin abin da ke nagari.’ (Romawa 13:3) Ta nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, muna ƙara koyo game da yadda za mu yi koyi da nagartar Jehovah. Talifi da ya shige ya bincika fannoni na nagartar Allah da aka sanar da Musa da ke rubuce a Fitowa 34:6, 7, inda mun karanta: “Ubangiji, Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya; yana tsaron jinƙai domin dubbai, yana gafarta laifi da saɓo da zunubi: ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan.” Bincika waɗannan fannoni na nagartar Jehovah sosai zai taimake mu mu ‘ci gaba da yin abin da ke nagari.’
11. Yaya ya kamata sanin cewa Jehovah mai jinƙai ne kuma mai alheri zai shafe mu?
11 Wannan sanarwa na Allah ya nuna mana bukatar mu yi koyi da Jehovah ta zama masu jinƙai da alheri. “Masu-albarka ne masu-jinƙai,” in ji Yesu, “gama su za su sami jinƙai.” (Matta 5:7; Luka 6:36) Da yake mun sani cewa Jehovah mai alheri ne, za mu motsa mu yi alheri da hali mai kyau a yadda muke bi da wasu, haɗe da waɗanda muke musu wa’azi. Wannan ya yi daidai da gargaɗin Bulus: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.”—Kolossiyawa 4:6.
12. (a) Tun da Allah mai jinkirin fushi ne, yaya ya kamata mu bi da wasu? (b) Alherin Jehovah na motsa mu mu yi menene?
12 Tun da Allah mai jinkirin fushi ne, muradinmu mu ‘ci gaba da yin abin da ke nagari’ na sa mu iya jimre wa ƙananan kasawa na ’yan’uwa masu bi kuma mu mai da hankali ga halayensu masu kyau. (Matta 7:5; Yaƙub 1:19) Alherin Jehovah na motsa mu mu nuna ƙauna ta aminci, har ma a ƙarƙashin yanayin gwaji masu wuya. Babu shakka wannan abin ban sha’awa ne.—Misalai 19:22.
13. Yaya ya kamata mu aikata mu nuna cewa Jehovah ‘mai yalwar gaskiya ne’?
13 Tun da Ubanmu na samaniya ‘mai yalwar gaskiya ne,’ muna ‘koɗa kanmu masu-hidimarsa cikin maganar gaskiya.’ (2 Korinthiyawa 6:3-7) Cikin abubuwa bakwai da Jehovah ba ya so sune “harshe mai-ƙarya” da “mai-shaidan zur wanda ya ke furtawa da ƙarya.” (Misalai 6:16-19) Saboda haka, muradinmu na mu faranta wa Allah rai ya motsa mu mu ‘kawar da ƙarya kuma mu faɗi gaskiya.’ (Afisawa 4:25) Bari kada mu taɓa kasa nuna nagarta a wannan hanya ta musamman.
14. Me ya sa ya kamata mu riƙa gafartawa?
14 Shelar Allah ga Musa ya kamata ya motsa mu mu yi gafara, gama Jehovah yana shirye ya gafarta. (Matta 6:14, 15) Hakika, Jehovah yana ba da horo ga masu zunubi da suka ƙi su tuba. Saboda haka, dole ne mu ɗaukaka mizanansa na nagarta sa’ad da ya zo ga kasancewa da tsabta ta ruhaniya cikin ikilisiya.—Leviticus 5:1; 1 Korinthiyawa 5:11, 12; 1 Timothawus 5:22.
“Ku Mai da Hankali Ƙwarai”
15, 16. Ta yaya gargaɗin Bulus da ke rubuce a Afisawa 5:15-19 ya taimake mu mu ci gaba a yin nagarta?
15 Don mu ci gaba da yin nagarta duk da mugunta da ta kewaye mu, muna bukatar a cika mu da ruhun Allah kuma mu mai da hankali yadda muke tafiya. Bulus ya aririci Kiristoci a Afisus daidai: “Ku duba fa a hankali yadda ku ke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi, tun da shi ke miyagun kwanaki ne. Domin wannan fa kada ku zama marasa-wayo, amma ku fahimci ko menene nufin Ubangiji. Kada ku yi maye da ruwan anab kuma—cikinsa da hauka—amma ku cika da Ruhu: kuna zance da junanku cikin zabura da waƙoƙin yabo da waƙoƙi masu-ruhaniya, kuna rairawa kuna yin muzika da zuciyarku ga Ubangiji.” (Afisawa 5:15-19) Hakika wannan gargaɗi ya dace dominmu a wannan zamanin ƙarshe masu wuya ƙwarai.—2 Timothawus 3:1.
16 Idan za mu ci gaba da yin nagarta, dole mu mai da hankali ƙwarai mu yi tafiya na waɗanda suke nuna hikima ta ibada. (Yaƙub 3:17) Dole mu guje wa zunubai masu tsanani kuma dole a cika mu da ruhu mai tsarki, kuma mu ƙyale shi ya yi mana ja-gora. (Galatiyawa 5:19-25) Ta yin amfani da koyarwa ta ruhaniya da ake ba da a taron Kirista, manyan taro, da taron gunduma, za mu iya ci gaba da yin abin da ke nagari. Kalmomin Bulus ga Afisawa ya kuma tuna mana cewa a yawancin taronmu na sujjada, muna amfana daga rera “waƙoƙi masu-ruhaniya” daga zuciyarmu—yawancinsu a kan halaye na ruhaniya ne, kamar nagarta.
17. Idan yanayinsu ya hana su halartan taro a kai a kai, menene Kiristoci da suke ciwo mai tsanani za su tabbata?
17 ’Yan’uwanmu masu bi da ba sa iya zuwa taron Kirista a kai a kai domin ciwo mai tsanani fa? Ruhun yakan karye domin ba sa bauta wa Jehovah tare da ’yan’uwansu na ruhaniya maza da mata. Amma su tabbata cewa Jehovah ya san yanayinsu, zai ajiye su cikin haske, zai ba su ruhunsa mai tsarki, kuma zai taimake su su ci gaba da yin abu da ke nagari.—Ishaya 57:15.
18. Menene zai taimaka mana mu ci gaba da yin nagarta?
18 Ci gaba da yin nagarta na bukatar mu mai da hankali da waɗanda muke tarayya da su kuma mu guji “marasa-son nagarta.” (2 Timothawus 3:2-5; 1 Korinthiyawa 15:33) Yin amfani da irin wannan gargaɗin na taimaka mana mu guji “ɓata zuciyar Ruhu Mai-tsarki na Allah” ta ƙin biyayya da ja-gorarsa. (Afisawa 4:30) Bugu kan ƙari, suna taimakonmu mu yi abin da ke nagari idan muka gina tarayya ta kusa da waɗanda rayuwarsu ta nuna suna son nagarta kuma ruhu mai tsarki na Jehovah na yi musu ja-gora.—Amos 5:15; Romawa 8:14; Galatiyawa 5:18.
Nagarta na Kawo Sakamako Mai Kyau
19-21. Ka ba da labarai da sun nuna sakamakon yin nagarta.
19 Yin tafiya cikin haske na ruhaniya, bin ja-gora na ruhun Allah, da mai da hankali a yadda muke tafiya za su taimaka mana mu guje abin da ke mugu kuma mu ‘ci gaba da yin abin da ke nagari.’ Wannan zai iya kawo sakamako mai kyau. Yi la’akari da labarin Zongezile, Mashaidin Jehovah ne a Afirka ta Kudu. Da yake zuwa makaranta, wata safiya, ya duba kuɗi kaɗan da yake da su cikin banki. Takarda da ta fito daga na’urar ƙirga kuɗi cikin kuskure ta nuna ƙari R42,000 (₦670,200) a kan ainihin kuɗin da yake da shi. Wani mai gadin banki da wasu suka ce masa ya janye kuɗin ya saka a wani banki. Ma’aurata Shaidu da yake zama da su ne kawai suka yaba masa da bai janye kuɗin ba.
20 Washegari da ya je aiki, Zongezile ya nuna wa bankin kuskuren. Aka gane cewa yana da lambar bankin da ya yi daidai da na wani ɗan kasuwa mai arziki da ya yi kuskure ya ajiye kuɗi a lamba da ba ta yi daidai ba. Ya yi mamaki cewa Zongezile bai cire komi ba cikin kuɗin, ɗan kasuwan ya tambaye shi: “Wane addini ka ke yi?” Zongezile ya bayyana cewa shi Mashaidin Jehovah ne. Waɗanda suke aiki a bakin sun yaba masa sosai, suka ce: “A ce dukan mutane suna faɗar gaskiya kamar Shaidun Jehovah.” Hakika, ayyukan gaskiya da nagarta za su iya sa wasu su ɗaukaka Jehovah.—Ibraniyawa 13:18.
21 Ayyukan nagarta ba sai sun zama na musamman ba don a samu sakamako mai kyau. Alal misali: Wani Mashaidi matashi da ke hidima ta cikakken lokaci a wani tsibiri na Samoa ya je asibiti a yankin. Mutane suna jiran su ga likita, Mashaidin ya lura cewa wata tsohuwa kusa da shi tana ciwo sosai. Ya ce matar ta shiga kafin ya shiga don a yi mata jinya nan da nan. Wani lokaci, Mashaidin ya sadu da matar a kasuwa. Ta tuna abu mai kyau da ya yi a asibiti. Ta ce, “yanzu na sani cewa Shaidun Jehovah suna ƙaunar maƙwabtansu da gaske.” Ko da yake a dā ba ta sauraron saƙon Mulki, nagarta da Mashaidin ya yi mata ta samu sakamako mai kyau. Ta yarda a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da ita kuma ta soma samun sani na Kalmar Allah.
22. Wace hanya ce ɗaya ta musamman za mu ‘ci gaba da yin abin da ke nagari’?
22 Wataƙila, za ka iya ba da labarai da sun nuna amfanin yin nagarta. Wata hanya ta musamman na ‘ci gaba da yin abin da ke nagari’ shi ne sa hannu a kai a kai a shelar bishara ta Mulkin Allah. (Matta 24:14) Bari mu ci gaba da himma a sa hannu cikin wannan aikin mai tamani, mu fahimci cewa wannan hanya ɗaya ce ta yin nagarta, musamman ga waɗanda suka saurara. Mafi muhimmanci, hidimarmu da halinmu mai kyau na ɗaukaka Jehovah, tushen nagarta.—Matta 19:16, 17.
Ka Ci Gaba da “Aika Nagarta”
23. Me ya sa hidima ta Kirista aiki ne mai kyau?
23 Babu shakka hidimarmu aiki ne mai kyau. Za ta kawo mana ceto da kuma waɗanda suka saurari saƙon Littafi Mai Tsarki da haka su hau hanya da ke kai wa ga rai madawwami. (Matta 7:13, 14; 1 Timothawus 4:16) Idan za mu tsai da shawara, sha’awar yin abin da ke nagari za ta sa mu tambayi kanmu: ‘Yaya wannan shawara za ta shafi aikina na wa’azin Mulki? Abin da nake son na yi yana da kyau kuwa? Zai taimake ni na taimake wasu su karɓi “bishara ta har abada” kuma na shiga dangantaka ta kusa da Jehovah Allah?’ (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Farin ciki mafi girma zai zo daga yanke shawara da ta ɗaukaka abubuwa na Mulki.—Matta 6:33; Ayukan Manzanni 20:35.
24, 25. Waɗanne hanyoyi ne za mu yi nagarta a ikilisiya, kuma menene za mu tabbata idan muka ci gaba da yin nagarta?
24 Kada mu taɓa rena sakamako mai kyau na nagarta. Za mu iya ci gaba da nuna wannan hali ta tallafa wa ikilisiyar Kirista da kuma yin iyakacin ƙoƙarinmu mu lura da lafiyarta. Hakika muna abu da ke nagari sa’ad da muke halartar taron Kirista a kai a kai kuma muna yin furci. Kasancewarmu a wurin na ƙarfafa ’yan’uwa masu bi, kuma furci da muka shirya da kyau na ƙarfafa su a ruhaniya. Muna kuma yin abu da ke nagari idan muka yi amfani da dukiyarmu muka gyara Majami’ar Mulki da kuma sa’ad da muka taimaka wajen kula da ita da kyau. (2 Sarakuna 22:3-7; 2 Korinthiyawa 9:6, 7) Hakika, “yayinda mu ke da dama fa, bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.”—Galatiyawa 6:10.
25 Ba za mu iya sanin dukan yanayin da zai sa mu yi nagarta ba. Yayin da muke fuskantar sababbin ƙalubale, bari mu nemi wayewa daga Nassosi, mu yi addu’a don ruhu mai tsarki na Jehovah, kuma mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu nuna nagartansa da cikakken nufi. (Romawa 2:9, 10; 12:2) Za mu kasance da gaba gaɗi cewa Jehovah zai albarkace mu sosai sa’ad da muka ci gaba da yin nagarta.
Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya za mu cim ma abu mafi kyau?
• Me ya sa aka kira nagarta ‘amfanin haske’?
• Me ya sa aka kira nagarta ‘ ’yar ruhu’?
• Halinmu mai kyau na kawo wane sakamako?
[Hoto a shafi na 15]
Kalmar Allah da ruhunsa mai tsarki na taimaka mana mu yi nagarta
[Hotuna a shafi na 16]
Yin nagarta na kawo sakamako masu kyau