Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 2 p. 5
  • Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Magana da Kuzari
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Magana Ba Shakka
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Nuna Kauna da Tausayi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 2 p. 5

DARASI NA 2

Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa

Nassin da aka rubuta

2 Korintiyawa 2:17

ABIN DA ZA KA YI: Ka yi magana a sake yadda zai nuna cewa kana son batun da kake tattaunawa kuma ka damu da masu sauraronka.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi shiri da kyau kuma ka yi addu’a. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka don ka mai da hankali ga saƙon ba kanka ba. Ka yi ƙoƙari ka fahimci ainihin muhimman darussan da kake so ka koyar. Kada ka karanta abin da kake so ka faɗa, amma ka riƙa magana kamar kuna tattaunawa.

    Shawara mai amfani

    Idan za ka karanta wani nassi daga Littafi Mai Tsarki ko wani littafi dabam, ka yi shiri da kyau don karatun ya tafi sumul. Yayin da kake faɗin abin da wani ya faɗa, ka yi hakan kamar kana cikin yanayin mai maganar, amma ka yi amfani da muryarka.

  • Ka yi magana daga cikin zuciyarka. Ka yi tunani a kan dalilan da suka sa masu sauraronka suke bukatar saƙon. Ka mai da hankali a kansu. Tsayawarka da motsin hannayenka da jikinka da kuma yadda fuskarka take su nuna cewa abin da kake faɗa gaskiya ne.

    Shawara mai amfani

    Ka yi magana kamar kuna tattaunawa amma kada ka mai da batun wasa. Ka yi magana yadda za a gane kuma ka bi ƙa’idodin yaren domin saƙon ya kasance da daraja.

  • Ka kalli masu sauraronka. Ka kalli idanun masu sauraronka idan ana yin hakan a yankin. Yayin da kake tattaunawar, ka riƙa kallon mutane ɗaya bayan ɗaya maimakon ka riƙa jujjuyawa kana kallon kowa da kowa.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba