Yaya Ƙarfin Bangaskiyarka Yake?
“Da bangaskiya ku ke tsayawa.”—2 KORINTHIYAWA 1:24.
1, 2. Ta yaya za mu sami bangaskiya, kuma ta yaya za ta yi ƙarfi?
BAYIN Jehovah sun sani cewa dole ne su zama masu bangaskiya. Hakika, ‘ba shi kuwa yiwuwa a gamsar da Allah ba sai tare da bangaskiya.’ (Ibraniyawa 11:6) Saboda haka, muna yin addu’a domin ruhu mai tsarki da kuma bangaskiya, waɗanda ’ya’yan ruhun ne da muke so. (Luka 11:13; Galatiyawa 5:22, 23) Yin koyi da bangaskiyar ’yan’uwa masu bi zai ƙarfafa wannan hali da muke da shi.—2 Timothawus 1:5; Ibraniyawa 13:7.
2 Bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi idan muka nace wajen bin tafarkin da Kalmar Allah ta kafa wa dukan Kiristoci. Za mu samu ƙarin bangaskiya daga karanta Littafi Mai Tsarki kullum da kuma kyakkyawan nazarin Nassosi da taimakon littattafai da “wakili mai-aminci” yake tanadin. (Luka 12:42-44; Joshua 1:7, 8) Muna samun ƙarfafa daga bangaskiyar wasu ta wajen halartar taron Kirista kullum, manyan taro, da kuma taron gunduma. (Romawa 1:11, 12; Ibraniyawa 10:24, 25) Bangaskiyarmu tana ƙarfafa sa’ad da muka yi magana da wasu a hidima.—Zabura 145:10-13; Romawa 10:11-15.
3. Game da bangaskiya wane taimako muke samu daga wurin dattawa masu ƙauna Kirista?
3 Ta wajen ba da gargaɗi daga Nassosi da kuma ƙarfafa, dattawa masu ƙauna Kirista suna taimakawa a gina bangaskiyarmu. Suna da zuciya irin ta manzo Bulus, wanda ya gaya wa Korantiyawa: “Mataimaka ne na farinzuciyarku: gama da bangaskiya ku ke tsayawa.” (2 Korinthiyawa 1:23, 24) Wata fassara ta ce: “Muna aiki ne tare da ku domin mu faranta muku rai, domin bangaskiyarku tana da ƙarfi.” (Contemporary English Version) Mai adalci yana rayuwa ne bisa bangaskiya. Hakika, babu wanda zai nuna bangaskiya a madadinmu ko kuma ya mai da mu amintattu. A wannan, dole ne mu ‘ɗauki kayan mu.’—Galatiyawa 3:11; 6:5.
4. Ta yaya labaran Nassosi na bayin Allah masu aminci ya taimaka wajen ƙarfafa bangaskiyarmu?
4 Nassosi suna cike da tarihin waɗanda suka ba da gaskiya. Wataƙila muna sane da fitattun abubuwa da suka yi, amma mun ga yadda suka nuna bangaskiya a rayuwarsu ta yau da kullum, wataƙila a cikin dukan kwanakin ransu? Bimbini a kan yadda suka nuna wannan hali a yanayi da suka yi daidai da namu zai taimaka wajen ƙarfafa bangaskiyarmu.
Bangaskiya Tana Ƙarfafa Mu
5. Wane tabbaci ne na Nassi muke da shi cewa bangaskiya tana ƙarfafa mu mu yi shelar kalmar Allah da gaba gaɗi?
5 Bangaskiya tana ƙarfafa mu mu yi shelar kalmar Allah da gaba gaɗi. Ahnuhu ya annabta hukuncin Allah da gaba gaɗi. “Ku duba” ya ce, “Ubangiji ya zo da rundunan tsarkakansa, garin ya hukunta shari’a bisa dukan mutane, domin shi kāda dukan masu-fajirci kuma a kan dukan ayyukansu na fajirci da suka yi cikin fajircinsu, da dukan maganganu na ɓatanci waɗanda masu-zunubi masu-fajirci suka ambace shi da su.” (Yahuda 14, 15) Da suka ji wannan maganar, abokan Ahnuhu marasa ibada suka so su kashe shi. Duk da haka, ya yi magana da gaba gaɗi cikin bangaskiya, kuma Allah “ya ɗauke shi,” zuwa mutuwa, hakika ba tare da azabar mutuwa ba. (Farawa 5:24; Ibraniyawa 11:5) Ba ma ganin irin wannan mu’ujizoji, amma Jehovah yana amsa addu’o’inmu saboda mu yi shelar kalmarsa da bangaskiya da kuma gaba gaɗi.—Ayukan Manzanni 4:24-31.
6. Ta yaya bangaskiya da Allah ya bayar da kuma gaba gaɗi ya taimaki Nuhu?
6 Ta wurin bangaskiya Nuhu “ya shirya jirgi domin ceton gidansa.” (Ibraniyawa 11:7; Farawa 6:13-22) Nuhu kuma ya kasance “mai-shelan adalci,” wanda ya yi shelar kashedi na Allah ga mutanensa. (2 Bitrus 2:5) Sun yi ba’a ga saƙonsa game da Rigyawa, kamar yadda wasu suke ba’a sa’ad da muke ba da tabbacin cewa wannan zamanin ba da daɗewa ba za a halaka ta. (2 Bitrus 3:3-12) Kamar Ahnuhu da Nuhu, mu ma za mu iya gabatar da wannan saƙon domin bangaskiya da Allah ya ba mu da kuma gaba gaɗi.
Bangaskiya Tana Sa Mu Yi Haƙuri
7. Ta yaya Ibrahim da wasu suka nuna bangaskiya da haƙuri?
7 Muna bukatar bangaskiya da haƙuri, musamman ma da muke jiran ƙarshen wannan mugun zamani. Tsakanin waɗanda ‘domin bangaskiya da haƙuri za su gaji alkawura’ uban iyali ne Ibrahim mai tsoron Allah. (Ibraniyawa 6:11, 12) Ta wurin bangaskiya ya fice daga birnin Ur, da take cike da kayan alatu, kuma ya zama baƙo a baren ƙasa da Allah ya yi masa alkawari. Ishaƙu da Yakubu su ma magāda ne na wannan alkawarin. Duk da haka, “dukan waɗannan suka mutu cikin bangaskiya, ba su rigaya sun amshi alkawura ba.” Ta wurin bangaskiya suka biɗi ‘ƙasa mafiya kyau, watau ta sama.’ Haka nan, Allah “ya tanada masu birni.” (Ibraniyawa 11:8-16) Hakika, Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu—da kuma matansu masu ibada—sun jira da haƙuri Mulkin Allah na samaniya, wanda a cikin sarautarsa za a tashe su daga matattu su rayu a duniya.
8. Duk da menene Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu suka nuna haƙuri da kuma bangaskiya?
8 Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu ba su yi rashin bangaskiya ba. Ba su mallake Ƙasar Alkawarin ba, kuma ba su ga dukan al’ummai sun albarkaci kansu ba ta wurin zuriyar Ibrahim. (Farawa 15:5-7; 22:15-18) Ko da yake ‘birnin da Allah ya gina’ ba zai kasance ba har sai ƙarnuka sun shige, waɗannan mutane sun ci gaba da nuna bangaskiya da haƙuri a dukan kwanakin ransu. Hakika ya kamata mu ma mu yi haka, musamman ma yanzu da Mulkin Almasihu ta kasance a sama.—Zabura 42:5, 11; 43:5.
Bangaskiya Tana Ba Mu Makasudai Mafi Kyau
9. Wane tasiri bangaskiya take da shi bisa makasudi?
9 Ubannin iyalai masu aminci ba su yi koyi da salon rayuwa ta ƙazanta ta Kan’aniyawa ba, domin suna da makasudai mafiya girma. Bangaskiya haka nan take ba mu makasudai na ruhaniya da suke sa mu tsayayya wa rinjaya cikin duniya da take cikin ikon mugun, Shaiɗan Iblis.—1 Yohanna 2:15-17; 5:19.
10. Ta yaya muka sani cewa Yusufu ya biɗi makasudi wanda ya fi zama babban mutum a duniya?
10 Ta wajen ja-gorar Allah, ɗan Yakubu, Yusufu ya zama mai ba da abinci a ƙasar Masar, amma ba burinsa ba ne ya zama babban mutum a wannan duniyar. Da bangaskiya cewa alkawuran Jehovah za su cika, Yusufu, mai shekara 110 ya gaya wa ’yan’uwansa: “Ina mutuwa: amma hakika Allah za ya ziyarce ku, ya fishe ku daga cikin ƙasar nan, ya kai ku cikin ƙasa wadda ya rantse ma Ibrahim, da Ishaƙu, da Yakubu.” Yusufu ya roƙi a binne shi a ƙasar alkawari. Bayan ya mutu, aka bushar da gawarsa aka saka cikin akwati a ƙasar Masar. Amma da aka ’yantar da Isra’ilawa daga hannun Masarawa, annabi Musa ya sa aka ɗauki ƙasusuwan Yusufu domin a binne a Ƙasar Alkawari. (Farawa 50:22-26; Fitowa 13:19) Bangaskiya irin ta Yusufu ya kamata ta motsa mu mu biɗi makasudai da suka fi zama babban mutum a duniya.—1 Korinthiyawa 7:29-31.
11. A wace hanya ce Musa ya nuna cewa yana da makasudi na ruhaniya?
11 Musa ‘ya gwammace a wulakanta shi tare da mutanen Allah, da ya ji daɗin nishatsin zunubi na’ ‘’yan kwanaki’ da yake mai ilimi ne ƙwarai kuma mai jinin sarauta na Masar. (Ibraniyawa 11:23-26; Ayukan Manzanni 7:20-22) Ya yasar da ɗaukaka na duniya da kuma jana’iza mai girma a cikin akwati mai adon gaske a wuri mai martaba na ƙasar Masar. Amma wane tamani wannan yake da shi idan aka gwada shi da zama “mutumin Allah,” matsakaici na Dokar alkawari, annabin Jehovah, da kuma marubucin Littafi Mai Tsarki? (Ezra 3:2) Abin da kake so ke nan ka samu ɗaukaka a duniya, ko kuma bangaskiya ta ba ka makasudi mafi girma na ruhaniya?
Bangaskiya Tana Kawo Rayuwa Mai Albarka
12. Ta yaya bangaskiya ta shafi rayuwar Rahab?
12 Bangaskiya tana ba wa mutane makasudi mafi girma da kuma rayuwa mai albarka. Rahab ta Jericho ta ga cewa rayuwarta ta karuwanci lallai ba ta da wata ma’ana. Amma, wannan ta canja sa’ad da ta ba da gaskiya! “Da shi ke ta karɓi manzannin [Isra’ila], ta sallame su kuma ta wata hanya dabam, ba ta wurin ayyuka[n] [bangaskiya] ta barata ba,” ta haka suka ɓace wa abokan gabansu Kan’aniyawa. (Yaƙub 2:24-26) Da ta fahimci cewa Jehovah shi ne Allah na gaskiya, Rahab ta nuna bangaskiya ta wurin yin watsi da rayuwarta ta karuwanci. (Joshua 2:9-11; Ibraniyawa 11:30, 31) Ta auri bawan Jehovah, ba marar bi ba ɗan Kan’ana. (Kubawar Shari’a 7:3, 4; 1 Korinthiyawa 7:39) Rahab ta sami gata mai girma ta zama kakar Almasihu. (1 Labarbaru 2:3-15; Ruth 4:20-22; Matta 1:5, 6) Kamar wasu, waɗanda suka yi watsi da rayuwa ta lalata, za ta sake samun wata lada—tashi daga matattu zuwa rayuwa a aljanna a duniya.
13. Ta yaya Dauda ya yi zunubi wurin Bath-sheba, kuma wane hali ya nuna?
13 Bayan ta yi watsi da rayuwarta ta zunubi, a bayyane yake cewa Rahab ta bi tafarkin adalci. Amma, wasu da suka keɓe wa Allah kansu da daɗewa sun yi zunubi mai tsanani. Sarki Dauda ya yi zina da Bath-sheba, kuma ya sa aka kashe mijinta a bakin daga, ya aure ta. (2 Samu’ila 11:1-27) Da yake ya tuba da baƙin ciki mai tsanani, Dauda ya roƙi Jehovah: “Kada kuma ka ɗauke mini ruhunka mai-tsarki.” Dauda bai yi rashin ruhun Allah ba. Yana da bangaskiya cewa Jehovah cikin jinƙansa ba zai raina ‘karyayyar zuciyar mai-tuba ba’ daga zunubi. (Zabura 51:11, 17; 103:10-14) Domin bangaskiyarsu, Dauda da Bath-sheba sun more wuri mai albarka cikin zuriyar Almasihu.—1 Labarbaru 3:5; Matta 1:6, 16; Luka 3:23, 31.
Bangaskiya Tana Ƙarfafa ta Wurin Tabbaci
14. Wane tabbaci ne Gidiyon ya samu, ta yaya wannan labarin zai shafi bangaskiyarmu?
14 Ko da yake muna tafiya cikin bangaskiya, wani lokaci za mu bukaci tabbaci na taimakon Allah. Haka ya kasance da Alƙali Gidiyon ɗaya daga cikin waɗanda “suka ƙasarda mulkoki ta wurin bangaskiya.” (Ibraniyawa 11:32, 33) Sa’ad da Midiyanawa da mataimakansu suka kai wa Isra’ilawa hari, ruhun Allah ya rufe Gidiyon. Da yake bukatar tabbaci daga Jehovah cewa yana tare da shi, ya yi gwaji da ya ƙunshi buzu da aka ƙyale a masussuka ya kwana. A gwaji na farko raɓa ta jika buzun, amma ƙasar a bushe take. Yanayin ya canja a gwaji na biyun. Ya ƙarfafa domin wannan tabbacin, ya mai da hankali ya yi aiki cikin bangaskiya ya yi nasara bisa magabtan Isra’ila. (Alƙalawa 6:33-40; 7:19-25) Idan muka biɗi tabbaci sa’ad da muke bukatar mu yanke shawara, ba ya nufin cewa ba mu da bangaskiya. Hakika muna nuna bangaskiya ne ta wurin tuntuɓar Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan Kirista da kuma ta wurin addu’a domin ja-gora ta ruhu mai tsarki sa’ad da muke yin shawara.—Romawa 8:26, 27.
15. Ta yaya za a taimake mu ta wajen bimbini a kan bangaskiyar Barak?
15 Bangaskiyar Barak ta ƙarfafa domin tabbaci da ya samu ta wajen ƙarfafawa. Annabiya Deborah ta ƙarfafa shi ya yi amfani da zarafin da yake da shi ya ceci Isra’ilawa daga hannun Sarki Jabin na Kan’anawa. Ta wurin bangaskiya da tabbaci na taimakon Allah, Barak ya ja-goranci maza 10,000 marasa isashen makamai zuwa yaƙi kuma ya yi nasara bisa sojojin Jabin da suka fi su da suka bi kwamandansu Sisera. An yi bikin wannan nasara da waƙa mai daɗi na Deborah da Barak. (Alƙalawa 4:1–5:31) Deborah ta ƙarfafa Barak ya kasance shugaban Isra’ilawa da Allah ya naɗa, kuma yana ɗaya daga cikin bayin Jehovah waɗanda “suka kori rundunan baƙi har suka gudu,” ta wurin bangaskiya. (Ibraniyawa 11:34) Bimbini a kan yadda Jehovah ya albarkaci Barak domin ya yi aiki cikin bangaskiya zai iya motsa mu idan muna jinkirin cika wani aiki mai ƙalubale a hidimar Jehovah.
Bangaskiya Tana Kawo Salama
16. Wane misali ne mai kyau Ibrahim ya kafa wajen biɗan salama da Lutu?
16 Kamar yadda bangaskiya take taimakonmu mu yi ayyuka masu wuya a hidimar Jehovah, haka nan take kawo salama da kwanciyar hankali. Tsoho Ibrahim ya ƙyale ɗan wansa Lutu ya zaɓi wajen kiwon mafi kyau sa’ad da matsala ta auko tsakanin makiyayansu kuma raba su ya zama dole. (Farawa 13:7-12) Ibrahim ya yi addu’a cikin bangaskiya don taimakon Allah ya warware wannan matsalar. Maimakon ya yi son kai, ya sulhunta batun cikin salama. Idan matsala ta samu tsakaninmu da ’yan’uwanmu Kiristoci, mu yi addu’a cikin bangaskiya kuma mu “biɗi salama,” mu riƙa tunawa kuma da misalin Ibrahim na yin la’akari.—1 Bitrus 3:10-12.
17. Me ya sa za mu iya cewa jayayya da ta shafi Bulus, Barnaba da kuma Markus an sulhunta ta cikin salama?
17 Ka yi la’akari da yadda yin amfani da mizanan bangaskiya zai taimaka wajen kawo salama. Sa’ad da Bulus yake so ya fara tafiyarsa ta wa’azi a ƙasashen waje, Barnaba ya yarda da shawarar su sake ziyartar ikilisiyoyi a Ƙubrus da kuma Asiya Ƙarama. Duk da haka, Barnaba yana so ya tafi da ɗan babarsa Markus. Bulus bai yarda ba domin Markus ya ja da baya a Bamfiliya. “Jayayya ta tashi” kuma wannan jayayyar ta sa suka rabu. Barnaba ya ɗauki Markus suka je Ƙubrus, Bulus kuma ya zaɓi Sila suka “ratsa Suriya da Kilikiya, yana ƙarfafa ikilisiyoyi” a wuraren. (Ayukan Manzanni 15:36-41) Da shigewar lokaci, a bayyane yake cewa an sulhunta jayayyar, domin Markus yana tare da Bulus a Roma, kuma manzon ya yaba masa ƙwarai. (Kolossiyawa 4:10; Filimon 23, 24) Sa’ad da Bulus yake kurkuku a Roma ƙila a shekara ta 65 K.Z., ya gaya wa Timothawus: “Ka ɗauko Markus, ka kawo shi tare da kai: gama yana da amfani gareni wajen hidima.” (2 Timothawus 4:11) A bayyane yake cewa Bulus ya yi addu’a cikin bangaskiya domin dangantakarsa da Barnaba da kuma Markus, kuma wannan ya sa ya sami kwanciyar rai da take da alaƙa da ‘salama ta Allah.’—Filibbiyawa 4:6, 7.
18. Menene wataƙila ya faru a batun Afodiya da Sintiki?
18 Hakika, domin ajizanci, “dukanmu mu kan yi tuntuɓe.” (Yaƙub 3:2) Matsala ta auko tsakanin mata Kiristoci biyu, da Bulus ya rubuta game da su: “Ina yi ma Afodiya gargaɗi, ina yi ma Sintiki gargaɗi, su zama da hankali ɗaya a cikin Ubangiji. . . . taimaki waɗannan mata, gama suka yi aiki tare da ni cikin bishara.” (Filibbiyawa 4:1-3) Wataƙila waɗannan mata masu ibada sun sulhunta matsalarsu cikin salama ta wajen yin amfani da gargaɗi da yake rubuce cikin Matta 5:23, 24. Amfani da mizanan Nassosi cikin bangaskiya zai taimaka wajen kawo salama a yau.
Bangaskiya Tana sa Mu Jimre
19. Wane yanayi na gwaji bai halaka bangaskiyar Ishaƙu da Rifkatu ba?
19 Ta wajen bangaskiya za mu iya jimre wa wahala. Wataƙila muna baƙin ciki domin a iyalinmu wani da ya yi baftisma ya yi rashin biyayya ga Allah ta wurin auren marar bi. (1 Korinthiyawa 7:39) Ishaƙu da Rifkatu sun wahala domin auren ɗansu Isuwa ga mata marasa ibada. Matansa ’yan Hittiyawa “suka zama abin ɓacin rai” a gare su—domin tsananin haka Rifkatu ta ce: “Na gaji da raina saboda ’yan mata na Heth: Idan fa Yakubu ya yi aure cikin ’yan mata na wannan ƙasa me raina ya daɗa mini?” (Farawa 26:34, 35; 27:46) Duk da haka, wannan yanayi na gwaji bai halaka bangaskiyar Ishaƙu da Rifkatu ba. Mu kasance da bangaskiya idan yanayi mai wuya ya zama ƙalubale a gare mu.
20. Wane misali ne na bangaskiya muka samu wajen Naomi da Ruth?
20 Gwauruwa tsohuwa Naomi ’yar Yahudiya ce kuma ta sani cewa wasu mata a Yahuda za su iya haifi ’ya’ya da za su zama kakannin Almasihu. Domin ’ya’yanta sun mutu ba su da ’ya’ya kuma ita ta riga ta shige haihuwa, yana da wuya a ce iyalinta ta iya yin gudummawa ga zuriyar Almasihu. Duk da haka, surkuwarta Ruth ta zama matar Boaz da tsoho ne, ta haifa masa ɗa, kuma ta zama kakar Yesu, Almasihu! (Farawa 49:10, 33; Ruth 1:3-5; 4:13-22; Matta 1:1, 5) Bangaskiyar Naomi da Ruth ta jimre wa wahala kuma ta kawo musu farin ciki. Za mu yi farin ciki ƙwarai mu ma idan muka kasance da bangaskiya a lokacin da muke fuskantar wahala.
21. Mecece bangaskiya take yi mana, kuma menene ya kamata mu ƙuduri aniyar yi?
21 Ko da yake ba za mu iya faɗan abin da zai faru mana ɗaiɗai ba, ta wurin bangaskiya za mu iya jimre wa ko wane irin ƙalubale. Bangaskiya tana sa mu zama masu gaba gaɗi masu haƙuri. Tana ba mu makasudai mafi girma da kuma rayuwa mai albarka. Bangaskiya tana shafar dangantakarmu da wasu kuma ta jimre wa wahala. Saboda haka, ya kamata mu zama “waɗanda su ke da bangaskiya zuwa ceton rai.” (Ibraniyawa 10:39) Cikin ƙarfin Allahnmu mai ƙauna Jehovah, kuma domin darajarsa, mu ci gaba da nuna bangaskiya mai ƙarfi.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane tabbaci ne na Nassosi muke da shi cewa bangaskiya za ta iya sa mu zama masu gaba gaɗi?
• Me ya sa za mu ce bangaskiya ta ba mu rayuwa mai albarka?
• Ta yaya bangaskiya take kawo salama?
• Wane tabbaci muke da shi cewa bangaskiya tana taimaka mana mu jimre wa wahala?
[Hotuna a shafi na 10]
Bangaskiya ta ba wa Nuhu da Ahnuhu gaba gaɗi su yi shelar saƙon Jehovah
[Hotuna a shafi na 11]
Bangaskiya irin ta Musa ta motsa mu mu biɗi makasudai na ruhaniya
[Hotuna a shafi na 12]
Tabbacin taimakon Allah ya ƙarfafa bangaskiyar Barak, Deborah, da kuma Gidiyon