Ka Kara Mana Bangaskiya”
“Ka taimake ni in kasance da bangaskiya!”—MAR. 9:24, New World Translation.
WAKOKI: 81, 135
1. Ta yaya bangaskiya take da muhimmanci? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
KA TAƁA tambayar kanka ‘Shin Jehobah zai so ya ceci ni a lokacin kunci mai girma kuma ya sa in shiga cikin sabuwar duniya?’ Hakika, samun wannan ceton ya kunshi abubuwa da yawa, amma mafi muhimmanci shi ne abin da manzo Bulus ya ce: “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe shi [Allah] ba sai tare da bangaskiya.” (Ibran. 11:6) Hakan zai iya kasancewa da sauki, amma gaskiyar ita ce “ba duka ke da imani ba.” (2 Tas. 3:2) Waɗannan ayoyin sun taimaka mana mu fahimci cewa yana da muhimmanci mu kasance da bangaskiya sosai.
2, 3. (a) Ta yaya Bitrus ya koya mana cewa bangaskiya tana da muhimmanci? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna yanzu?
2 Manzo Bitrus ya nuna cewa bangaskiya tana da muhimmanci sosai sa’ad da ya yi magana game da tabbatacciyar bangaskiya wadda “ta kai zuwa yabo da daraja da girma a kan bayyanuwar Yesu Kristi.” (Karanta 1 Bitrus 1:7.) Tun da yake kunci mai girma yana nan tafe, muna son mu tabbata cewa mun kasance da bangaskiya da za ta sa mu zama cikin waɗanda Yesu Kristi zai albarkace su sa’ad da ya bayyana a matsayinsa na Sarki mai ɗaukaka. Hakika, muna so mu zama “cikin waɗanda suke da bangaskiya zuwa ceton rai.” (Ibran. 10:39) Saboda haka, bari mu yi roko kamar wani mutumin da ya ce: “Ka taimake ni in kasance da bangaskiya.” (Mar. 9:24, NW) Ko kuma mu ce kamar manzannin Yesu: “Ka kara mana bangaskiya.”—Luk. 17:5.
3 A wannan talifin za mu tattauna wasu tambayoyi game da bangaskiya. Ta yaya za mu karfafa bangaskiyarmu? Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya? Wane tabbaci muke da shi cewa idan muka roki Allah, zai kara mana bangaskiya?
ALLAH YANA SON MU KARFAFA BANGASKIYARMU
4. Waɗanne misalai ne za su sa mu karfafa bangaskiyarmu?
4 Za mu iya koyan darussa daga mutane da yawa da suka kafa misali mai kyau da ke cikin Littafi mai Tsarki, tun da yake ‘iyakar abin da aka rubuta a dā an rubuta su domin koyarwarmu’ ne. (Rom. 15:4) Karanta labaran mutane kamar Ibrahim da Saratu da Ishaku da Yakubu da Musa da Rahab da Gidiyon da Barak da dai sauransu zai sa mu bincika kanmu ko muna da bangaskiya sosai. (Ibran. 11:32-35) Kari ga haka, za mu yi iya kokarinmu mu karfafa bangaskiyarmu idan muka karanta labaran ’yan’uwa maza da mata masu bangaskiya sosai a zamaninmu.a
5. Ta yaya Iliya ya nuna cewa ya gaskata sosai da Jehobah, kuma wace tambaya ce ya kamata mu yi wa kanmu?
5 Wani misali da ke cikin Littafi Mai Tsarki shi ne na annabi Iliya. Ka yi tunani a kan wasu abubuwan da suka faru da suka nuna cewa ya dogara sosai ga Jehobah. Sa’ad da Iliya ya gaya wa Sarki Ahab cewa Jehobah zai hana ruwan sama a kasar, ya yi hakan da gaba gaɗi kuma ya ce: “Na rantse da Ubangiji, Allah . . . ba za a yi raɓa ko ruwan sama . . . sai da faɗata.” (1 Sar. 17:1) Iliya ya gaskata cewa Jehobah zai biya bukatunsa da na wasu a lokacin fāri. (1 Sar. 17:4, 5, 13, 14) Ya kasance da aminci cewa Jehobah zai ta da wani yaro daga mutuwa. (1 Sar. 17:21) Bai yi shakka ba cewa Jehobah zai aiko da wuta ta cinye hadayarsa a Dutsen Karmel. (1 Sar. 18:24, 37) Sa’ad da lokaci ya yi da Jehobah zai kawo karshen farin, kafin a ga alama cewa za a yi ruwa, Iliya ya gaya wa Ahab: “Ka hau, ka ci, ka sha; gama da motsin ruwan sama mai-yawa.” (1 Sar. 18:41) Karanta waɗannan labaran zai sa mu bincika kanmu ko muna da bangaskiya sosai.
MENE NE ZA MU YI DON MU KARFAFA BANGASKIYARMU?
6. Mene ne muke bukatar Jehobah ya ba mu don mu karfafa bangaskiyarmu?
6 Tun da yake ba za mu iya karfafa bangaskiyarmu da kanmu ba, muna bukatar mu roki Allah ya ba mu ruhunsa mai tsarki. Me ya sa? Domin bangaskiya tana cikin halayen da ruhu mai tsarki yake bayarwa. (Gal. 5:22) Saboda haka, ya dace mu bi shawarar Yesu kuma mu roki Allah ya ci gaba da ba mu ruhu mai tsarki domin Yesu ya tabbatar mana cewa Uban ‘za ya ba da Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke rokonsa.’—Luk. 11:13.
7. Ka kwatanta yadda za mu ci gaba da karfafa bangaskiyarmu.
7 Muddin mun ba da gaskiya ga Allah, wajibi ne mu ci gaba da karfafa bangaskiyarmu. Muna iya gwada bangaskiya da wuta. Idan muka cinna wuta, zai rika ci sosai. Idan aka kyale wutar, zai zama garwashi, daga baya ya zama toka. Amma, idan kana saka itace a kai a kai, wutar ba zai mutu ba. Hakazalika, za mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya idan muka ci gaba da karanta da kuma nazarin Kalmar Allah a kai a kai. Hakan zai sa mu kaunaci Jehobah sosai da kuma kalmarsa. Ta yin hakan za mu karfafa bangaskiyarmu sosai.
8. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da karfafa bangaskiyarmu?
8 Mene ne kuma za ka kara yi don ka ci gaba da karfafa bangaskiyarka? Ka ci gaba da koyan abubuwa da za su karfafa bangaskiyarka bayan ka yi baftisma. (Ibran. 6:1, 2) Alal misali, za ka iya ci gaba da nazarin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika domin za su taimaka maka ka ci gaba da karfafa bangaskiyarka. Kari ga haka, za ka iya yin amfani da Kalmar Allah don ka bincika kanka ko kana da bangaskiya sosai.—Karanta Yakub 1:25; 2:24, 26.
9, 10. Ta yaya muke karfafa bangaskiyarmu ta: (a) yin tarayya da abokan kirki? (b) halartan taron ikilisiya? (c) yin wa’azin bishara?
9 Manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci cewa za su iya ‘karfafa juna ta bangaskiyarsu.’ (Rom. 1:12, Littafi Mai Tsarki) Yayin da muke cuɗanya da ’yan’uwa, za mu iya karfafa bangaskiyar juna musamman a lokacin da muke tare da waɗanda sun riga sun karfafa bangaskiyarsu sosai. (Yak. 1:3) Tarayya da abokan banza tana haddasa rashin bangaskiya, amma yin cuɗanya da abokan kirki zai karfafa bangaskiyarmu sosai. (1 Kor. 15:33) Shi ya sa aka ba mu shawara cewa kada mu rika “fasa” taro, amma mu ci gaba da “gargaɗar da juna.” (Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.) Wani dalili kuma shi ne cewa abubuwan da muke koya a taron ikilisiya suna karfafa bangaskiyarmu. Hakan ya jitu da abin da Bulus ya faɗa: “Bangaskiya fa daga wurin ji ne.” (Rom. 10:17) Saboda haka, ka tambayi kanka, Shin ina cuɗanya da ’yan’uwa sa’ad da na halarci taro?
10 Idan muna wa’azi da kuma koya wa wasu Littafi Mai Tsarki, hakan zai karfafa bangaskiyarmu. Kamar Kiristoci na farko, mun ba da gaskiya sosai ga Jehobah kuma muna magana gabanmu gaɗi a duk yanayin da muka samu kanmu.—A. M. 4:17-20; 13:46.
11. Me ya sa Kaleb da Joshua suka kasance da bangaskiya sosai, kuma ta yaya za mu yi koyi da su?
11 Muna karfafa bangaskiyarmu ga Jehobah sa’ad da muka ga yadda yake taimaka mana da kuma yadda yake amsa addu’o’inmu. Abin da ya faru da Kaleb da Joshua ke nan. Sun dogara ga Jehobah sa’ad da suka je leken asirin Kasar Alkawari. Amma, da shigewar lokaci sun kasance da bangaskiya sosai yayin da suka shaida yadda Jehobah ya taimaka musu. Shi ya sa Joshua ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku.” Daga baya ya daɗa cewa: “Ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa cikin sahihanci da cikin gaskiya . . . Da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.” (Josh. 23:14; 24:14, 15) Idan muka dogara ga Jehobah kuma muka lura da yadda yake taimaka mana, za mu karfafa bangaskiyarmu sosai.—Zab. 34:8.
YADDA ZA MU NUNA BANGASKIYARMU
12. Mene ne Yakub ya nuna cewa yana da muhimmanci idan za mu kasance da bangaskiya?
12 Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya sosai? Almajiri Yakub ya amsa wannan tambayar ta wurin cewa: “Ni kuwa ta wurin ayyukana in nuna maka bangaskiyata.” (Yak. 2:18) Abubuwan da muke yi za su nuna cewa muna da bangaskiya sosai. Bari mu bincika wasu misalai.
Waɗanda suka kasance da kwazo a yin wa’azin bishara sun nuna cewa suna da bangaskiya sosai (Ka duba sakin layi na 13)
13. Ta yaya yin wa’azi a hanyoyi dabam-dabam ya nuna cewa muna da bangaskiya?
13 Yin wa’azin bishara, hanya ce mafi kyau da za mu nuna cewa muna da bangaskiya sosai. Me ya sa? Domin sa’ad da muke wa’azi, muna nuna mun gaskata cewa karshen ya kusa kuma ba zai “yi jinkiri ba.” (Hab. 2:3) Hanya ɗaya da za mu san ko muna da bangaskiya sosai ita ce ta wurin bincika ko muna a shirye mu yi wa’azi da kwazo. Shin muna yin iya kokarinmu a yin wa’azi da kwazo? Shin muna neman sababin hanyoyi na yin wa’azi kuwa? (2 Kor. 13:5) Hakika, yin wa’azin bishara ga mutane don su sami ceto hanya ɗaya ce mai muhimmanci da za mu nuna cewa muna da bangaskiya sosai.—Karanta Romawa 10:10.
14, 15. (a) Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya a rayuwarmu ta yau da kullum? (b) Ka bayyana yadda wasu suka nuna cewa sun dogara ga Jehobah.
14 Sa’ad da muka jure da kalubale na yau da kullum, za mu kuma nuna cewa mun dogara ga Jehobah sosai. Muna da tabbaci cewa Jehobah da Ɗansa za su “taimake mu a kan kari” a lokacin da muke rashin lafiya ko sanyin gwiwa ko fama da talauci ko kuma wasu matsaloli. (Ibran. 4:16, LMT) Sa’ad da muka roki Jehobah ya taimake mu, muna dogara gare shi. Yesu ya ce muna iya yin addu’a don Jehobah ya biya bukatunmu, kuma hakan ya haɗa da “abincin yini.” (Luk. 11:3) Labaran Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Jehobah zai iya ba mu kome da muke bukata. Alal misali, a lokacin da ake fāri a kasar Isra’ila, Jehobah ya ba Iliya abinci da ruwa ta wajen aika ‘hankaki kuwa su kawo masa gurasa da nama da safe, gurasa da nama kuwa da yamma: ya kuwa sha daga cikin rafin.’ (1 Sar. 17:3-6) Muna da bangaskiya cewa Jehobah zai iya biyan bukatunmu.
Muna nuna bangaskiya idan muna yin iya kokarinmu duk da kalubalen da muke fuskanta (Ka duba sakin layi na 14)
15 Mun tabbata cewa bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu ciyar da iyalinmu. Rebecca, wata ’yar’uwa a Asiya ta shaida hakan a iyalinta. Sun bi ka’idar da ke Matta 6:33 da Misalai 10:4, wato sun saka ibadarsu ga Jehobah kan gaba a rayuwarsu kuma suna aiki da kwazo. Rebecca ta ce a wani lokaci mijinta ya ga cewa aikinsa zai ɓata dangantakarsu da Jehobah, sai ya bar aikin. Amma suna da yara huɗu da za su kula da su. Rebecca ta ci gaba da cewa: “Muka soma sayar da abinci, kuma mun yi shekara da yawa muna wannan sana’ar, mun shaida cewa Jehobah bai yi watsi da mu ba. Ba mu taɓa kwana da yunwa ba.” Shin ka gaskata cewa Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ja-gora mafi amfani a yau?
16. Mene ne zai faru idan muka dogara ga Allah?
16 Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa idan muka bi ja-gorar Allah, zai taimaka mana. Sa’ad da Bulus yake kaulin Habakkuk, ya ce: “Mai-adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.” (Gal. 3:11; Hab. 2:4) Saboda haka, yana da muhimmanci mu ba da gaskiya ga Mai taimakonmu da gaske. Bulus ya tuna mana cewa Allah ne “wanda yake da iko shi aikata kwarai da gaske gaba da dukan abin da muke roko ko tsammani, bisa ga ikon da ke aikawa a cikinmu.” (Afis. 3:20) Bayin Jehobah suna iya kokarinsu don su yi nufin Allah, amma suna dogara ga Jehobah don sun san cewa suna da kasawa. Babu shakka muna godiya cewa Allah yana yi mana albarka saboda kokarin da muke yi.
AN AMSA ADDU’ARSU GAME DA BANGASKIYA
17. (a) Ta yaya aka amsa rokon manzannin? (b) Me ya sa muke da tabbaci cewa Allah zai amsa rokonmu na karin bangaskiya?
17 Abin da muka tattauna a wannan talifin zai iya sa mu soma tunani cewa muna bukatar bangaskiya kamar manzannin Yesu da suka gaya masa cewa: “Ka kara mana bangaskiya.” (Luk. 17:5) An amsa rokonsu, musamman ma a ranar Fentakos ta shekara ta 33, sa’ad da aka ba su ruhu mai tsarki kuma suka kara fahimta nufin Allah, kuma hakan ya karfafa bangaskiyarsu. A sakamako, suka soma yin wa’azi bishara sosai a lokacin. (Kol. 1:23) Hakazalika, idan muka roki Allah ya kara mana bangaskiya, zai amsa addu’armu. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa za mu iya yin haka sa’ad da “mun roki kome daidai da nufinsa.”—1 Yoh. 5:14.
18. Ta yaya Jehobah yake albarkar waɗanda suka ba da gaskiya?
18 Hakika, idan muka dogara ga Jehobah, za mu sa shi farin ciki. Jehobah zai amsa rokonmu na karin bangaskiya. Kari ga haka, za mu kasance da bangaskiya sosai, kuma za mu zama waɗanda suka “cancanta ga Mulkin Allah.”—2 Tas. 1:3, 5.
a Don ka ga wasu misalai, ka duba tarihin Lillian Gobitas Klose (Awake! na 22 ga Yuli, 1993), Feliks Borys (Awake! na 22 ga Fabrairu, 1994), and Josephine Elias (Awake! na Satumba 2009).