Da Gaske Ka Ba Da Gaskiya Ga Bisharar?
“Mulkin Allah kuwa yana nan: ku tuba ku bada gaskiya ga bisharar.”—MARKUS 1:15.
1, 2. Ta yaya za ka yi bayani a kan Markus 1:14, 15?
SHEKARA ta 30 ce A.Z. Yesu Kristi ya riga ya fara muhimmiyar hidimarsa a Galili. Yana wa’azin “bishara ta Allah,” furcinsa ya motsa Galiliyawa da yawa: “Zamani ya cika, mulkin Allah kuwa yana nan: ku tuba ku bada gaskiya ga bisharar.”—Markus 1:14, 15.
2 “Zamani” ya zo da Yesu zai fara hidimarsa domin mutane su yi shawarar da za ta kawo musu albarkar Allah. (Luka 12:54-56) ‘Mulkin Allah ta yi kusa’ domin Yesu wanda za a ba shi Sarauta yana wurin. Aikinsa na wa’azi ya motsa mutane masu zukatan kirki su tuba. Amma ta yaya suka nuna cewa suna da ‘bangaskiya ga bisharar,’ kuma ta yaya za mu ba da gaskiya a gare ta?
3. Ta wajen yin menene mutane suka nuna cewa suna da bangaskiya ga bisharar?
3 Kamar Yesu, manzo Bitrus ya aririci mutane su tuba. Da yake magana da Yahudawa a Urushalima a Fentakos ta 33 A.Z., Bitrus ya ce: “Ku tuba, a yi ma kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi zuwa gafarar zunubanku; za ku karɓi Ruhu Mai-tsarki kyauta kuma.” Dubbai suka tuba, aka yi musu baftisma suka zama mabiyan Yesu. (Ayukan Manzanni 2:38, 41; 4:4) A shekara ta 36 A.Z., mutanen al’ummai da suka tuba su ma sun ɗauki matakan nan. (Ayukan Manzanni 10:1-48) A zamaninmu, bangaskiya ga bishara tana motsa dubban mutane su tuba daga zunubansu, su keɓe kansu ga Allah, kuma su yi baftisma. Sun yi imani da bishara ta ceto kuma suna nuna bangaskiyarsu ga fansar Yesu. Bugu da ƙari, suna ayyukan adalci kuma suka zaɓi Mulkin Allah.
4. Mecece bangaskiya?
4 Amma mecece bangaskiya? Manzo Bulus ya rubuta: “Bangaskiya fa ainin abin da mu ke begensa ne, tabbatawar al’amuran da ba a gani ba.” (Ibraniyawa 11:1) Bangaskiyarmu tana ba mu tabbacin cewa dukan abin da Allah ya yi alkawari a cikin Kalmarsa sa tabbata. Kamar muna da takardar sayan wani kaya ne. Bangaskiya kuma “tabbatarwar al’amura” ce, game da abin da ba mu gani ba. Fahiminmu da kuma zuciyarmu da ta cika da godiya suna tabbatar mana cewa waɗannan abubuwa gaskiya ne, ko da yake ba mu gansu ba.—2 Korinthiyawa 5:7; Afisawa 1:18.
Muna Bukatar Bangaskiya!
5. Me ya sa bangaskiya take da muhimmanci haka?
5 An haife mu da bukata ta ruhaniya amma ba da bangaskiya ba. Hakika, “ba duka ke da [bangaskiya] ba.” (2 Tassalunikawa 3:2) Duk da haka, dole ne Kirista ya kasance da bangaskiya domin ya gaji alkawuran Allah. (Ibraniyawa 6:12) Bayan ya kawo misalai masu yawa na bangaskiya, Bulus ya rubuta: “Da shi ke taron shaidu mai-girma haka yana kewaye da mu, bari mu tuɓe kowane abin nauwaitawa, da zunubin da ke manne mamu, tare da haƙuri kuma mu yi tseren da an sa gabanmu, muna zuba ido ga Yesu shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta.” (Ibraniyawa 12:1, 2) Menene ne “zunubin da ke manne mamu”? Rashin bangaskiya ne har ma hasarar bangaskiya da dā ake da ita. Domin mu ci gaba da bangaskiya mai ƙarfi, dole ne mu ‘zuba ido ga Yesu’ kuma mu bi misalansa. Kuma muna bukatar mu guji lalata, mu yi kokawa da ayyuka na jiki, kuma mu guje wa son abin duniya, ussan ilimi na duniya, da kuma al’adu da suka saɓa wa Nassosi. (Galatiyawa 5:19-21; Kolossiyawa 2:8; 1 Timothawus 6:9, 10; Yahuda 3, 4) Bugu da ƙari, dole ne mu gaskata cewa Allah yana tare da mu, kuma gargaɗin da yake Kalmarsa yana da amfani.
6, 7. Me ya sa yake da kyau mu yi addu’a domin bangaskiya?
6 Ba za mu iya ƙago bangaskiya ba da kanmu ta namu ƙwazo. Bangaskiya tana cikin ’ya’yan ruhu mai tsarki na Allah, ko kuma ikon aiki. (Galatiyawa 5:22, 23) To, yaya idan bangaskiya tana bukatar a ƙarfafa ta? Yesu ya ce: “Idan ku fa . . . , kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Luka 11:13) Hakika, mu yi roƙo domin ruhu mai tsarki, domin zai haifa ’ya’ya a cikinmu da ake bukata domin a yi nufin Allah har a lokacin gwaji mai tsanani.—Afisawa 3:20.
7 Yana da kyau mu yi addu’a domin ƙarin bangaskiya. Sa’ad da Yesu yake so ya kori aljanu daga wani ɗan yaro, baban yaron ya yi roƙo: “Ina bada gaskiya; ka taimake ni da rashin bangaskiyata”! (Markus 9:24) “Ka ƙara mana bangaskiya” in ji almajiran Yesu. (Luka 17:5) Saboda haka, mu yi addu’a domin bangaskiya, da cikakken tabbaci cewa Allah zai amsa irin addu’o’in nan.—1 Yohanna 5:14.
Bangaskiya ga Kalmar Allah Tana da Muhimmanci
8. Ta yaya bangaskiya ga Kalmar Allah za ta taimake mu?
8 Ba da daɗewa ba kafin mutuwarsa ta hadaya, Yesu ya gaya wa manzanninsa: “Kada zuciyarku ta ɓaci; kuna bada gaskiya ga Allah, ku bada gaskiya gareni kuma.” (Yohanna 14:1) Mu Kiristoci muna da bangaskiya ga Allah da kuma ɗansa. Amma Kalmar Allah fa? Za ta rinjayi rayukanmu mu amfana idan muka yi nazarinta kuma muka yi amfani da ita da tabbaci cewa tana ba da gargaɗi mafi kyau da kuma ja-gora mai kyau a gare mu.—Ibraniyawa 4:12.
9, 10. Ta yaya za ka yi bayanin abin da aka faɗa game da bangaskiya a Yaƙub 1:5-8?
9 Mu mutane ajizai rayuwarmu ta cika da matsaloli. Duk da haka, bangaskiya ga Kalmar Allah hakika za ta yi taimako. (Ayuba 14:1) Alal misali, a ce ba mu san yadda za mu magance wani gwaji ba. Kalmar Allah ta ba mu wannan gargaɗin: “Idan kowanne a cikinku ya rasa hikima, bari shi yi roƙo ga Allah, wanda ya ke bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi. Amma bari shi yi roƙo da bangaskiya, ba da shakkar kome ba: gama mai-shakka yana kama da raƙumin teku, wanda iska yana korarsa, yana jijigarsa kuma. Gama kada wannan mutum shi yi tsammani za shi karɓi kome daga wurin Ubangiji; mutum mai-zuciya biyu ke nan, marar-tsayawa a cikin dukan al’amuransa.”—Yaƙub 1:5-8.
10 Jehovah Allah ba zai kunyata mu ba domin ba mu da hikima kuma muna yin addu’a dominta. Maimakon haka, zai taimaka mana mu bi da gwajin yadda ya kamata. ’Yan’uwa masu bi za su iya tunasar mana da Nassosi da za su yi taimako ko kuma mu gansu sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki. Ko kuma ruhu mai tsarki na Jehovah ya yi mana ja-gora a wata hanya. Ubanmu na samaniya zai ba mu hikima mu jure wa gwaji idan muna “roƙo da bangaskiya, ba da shakkar kome ba.” Amma idan muna kama da taguwar teku da iska ta ke jujjuya ta, ba za mu yi tsammanin samun wani abu ba daga wurin Allah. Me ya sa? Domin wannan zai nuna cewa muna da zuciya biyu kuma ba mu kahu ba a addu’armu ko kuma a wasu hanyoyi—hakika, har a wajen nuna bangaskiyarmu ma. Muna bukatar mu kasance da bangaskiya da ta kahu a Kalmar Allah da kuma ja-gorar da take bayarwa. Bari mu yi la’akari da wasu misalai na yadda ta ba da taimako kuma ta yi ja-gora.
Bangaskiya da Abinci
11. Bangaskiya ga Kalmar Allah tana ba mu wane tabbaci ne game da bukatunmu na kullum?
11 To, idan yanzu muna wahala domin rashin abinci ko kuma talauci fa? Bangaskiya ta ba mu tabbacin cewa Jehovah zai biya bukatunmu na kullum kuma daga baya zai ba da abinci a yalwace ga waɗanda suke ƙaunarsa. (Zabura 72:16; Luka 11:2, 3) Za mu ƙarfafa idan muka yi tunani game da yadda Jehovah ya yi tanadin abinci ga annabi Iliya a lokacin fari. Daga baya, cikin mu’ujiza Jehovah ya sa gari da mai ba su ƙare ba suka ciyar da mace da ɗanta, da kuma Iliya. (1 Sarakuna 17:2-16) Haka nan Jehovah ya yi wa annabi Irmiya tanadi a lokacin da Babila ta yi wa Urushalima kwanton ɓauna. (Irmiya 37:21) Ko da yake Irmiya da Iliya ba su da abinci da yawa, Jehovah ya kula da su. Yana yin haka ma ga waɗanda suke ba da gaskiya a gare shi a yau.—Matta 6:11, 25-34.
12. Ta yaya bangaskiya za ta taimake mu mu sami abin biyan bukata?
12 Bangaskiya tare da amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki ba za su azurta mu da abin duniya ba, amma za su taimake mu mu samu na biyan bukata. Alal misali: Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi cewa ya kamata mu zama masu gaskiya, masu ƙwazo. (Misalai 22:29; Mai-Wa’azi 5:18, 19; 2 Korinthiyawa 8:21) Ya kamata mu ga muhimmancin kasance da suna mai kyau wajen aiki. Har a wuraren da ayyuka masu kyau suke wuya, ma’aikata masu gaskiya, gwanaye, masu ƙwazo sun fi samun albarka. Ko da yake waɗannan ma’aikata wataƙila ba su da abin duniya mai yawa, suna da biyan bukatar rayuwa da kuma gamsuwa na cin abincin da su da kansu suka nema.—2 Tassalunikawa 3:11, 12.
Bangaskiya Tana Taimakonmu mu Jimre Baƙin Ciki
13, 14. Ta yaya bangaskiya take taimaka mana mu jimre baƙin ciki?
13 Kalmar Allah ta nuna cewa daidai ne mutum ya yi baƙin ciki sa’ad da wanda ake ƙauna ya mutu. Uban iyali mai adalci, Ibrahim ya yi makoki sa’ad da matarsa da yake ƙauna, Saratu ta mutu. (Farawa 23:2) Dauda ya yi baƙin ciki ƙwarai sa’ad da aka gaya masa cewa ɗansa Absalom ya mutu. (2 Samu’ila 18:33) Har ma kamilin mutum Yesu ya yi kuka sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu. (Yohanna 11:35, 36) Sa’ad da wanda ake ƙauna ya mutu, za mu yi baƙin ciki ƙwarai da gaske, amma bangaskiya ga alkawuran da suke cikin Kalmar Allah za su taimake mu mu jimre wa irin wannan baƙin ciki.
14 ‘Ina da bege ga Allah,’ in ji Bulus, ‘cewa za a yi tashin matattu, na masu adalci da na marasa adalci.’ (Ayukan Manzanni 24:15) Muna da bukatar mu kasance da bangaskiya ga shiri da Allah ya yi cewa zai tashi mutane da yawa zuwa rai. (Yohanna 5:28, 29) Cikinsu su Ibrahim ne da Saratu, Ishaƙu, Rifkatu, Yakubu da Lai’atu—dukansu yanzu suna barci cikin mutuwa suna jiran su tashi cikin sabuwar duniya ta Allah. (Farawa 49:29-32) Za a yi farin ciki ƙwarai sa’ad da aka tashi matattu daga barci su rayu a duniya! (Ru’ya ta Yohanna 20:11-15) A yanzu, bangaskiya ba za ta kawar da dukan baƙin ciki ba, amma za ta sa mu kasance kusa da Allah, wanda yake taimakon mu mu jimre makoki.—Zabura 121:1-3; 2 Korinthiyawa 1:3.
Bangaskiya Tana Ƙarfafa Waɗanda Suka Raunana a Zuci
15, 16. (a) Me ya sa za mu ce raunanar zuci ba farda ba ce a tsakanin waɗanda suka ba da gaskiya? (b) Menene za a iya yi a magance raunanar zuci?
15 Kalmar Allah kuma ta nuna cewa har waɗanda suka ba da gaskiya za su iya raunana a zuci. Sa’ad da yake fuskantar gwaji mai tsanani, Ayuba ya ji kamar Allah ya yasar da shi. (Ayuba 29:2-5) Yanayin taƙaici na garun Urushalima ya sa Nehemiah ya yi baƙin ciki. (Nehemiah 2:1-3) Bitrus ya yi baƙin ciki ƙwarai bayan ya yi musun sanin Yesu domin wannan “ya yi kuka mai-zafi.” (Luka 22:62) Kuma Bulus ya aririci ’yan’uwa masu bi a ikilisiya ta Tassalunika su “ƙarfafa masu-raunanan zukata.” (1 Tassalunikawa 5:14) Saboda haka, raunanar zuciya ga waɗanda suka ba da gaskiya ba farda ba ce. To, me za mu yi mu jimre wa raunanar zuciya?
16 Wataƙila mu raunana a zuci domin muna fuskantar matsaloli masu tsanani. Maimakon mu ɗauka cewa masifa ce mai girma, za mu iya magance su a hankali ta wajen amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki. Wannan zai taimaka a sauƙaƙa raunanarmu. Ayyuka madaidaici da kuma hutu da ya dace zai yi taimako. Bangaskiya ga Allah da kuma Kalmarsa tana kyautata lafiya ta ruhaniya kuma tana ƙarfafa tabbacinmu cewa da gaske ya damu da mu.
17. Ta yaya muka sani cewa Jehovah yana kula da mu?
17 Bitrus ya yi mana wannan tabbacin mai ban ƙarfafa: “Ku ƙasƙantarda kanku . . . ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah, domin shi ɗaukaka ku loton da ya zama daidai; kuna zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:6, 7) Mai Zabura ya rera: “Ubangiji yana tallafan dukan waɗanda su ke faɗuwa, yana tada dukan tanƙwararru. (Zabura 145:14) Ya kamata mu gaskata wannan tabbacin, domin an same su ne daga Kalmar Allah. Ko da yake raunanar zuci ta iya ta ci gaba, yana ƙarfafa bangaskiya mu sani cewa za mu iya zuba dukan matsalolinmu bisa Ubanmu na samaniya mai ƙauna!
Bangaskiya da Kuma Wasu Gwaji
18, 19. Ta yaya bangaskiya take taimakonmu mu jimre wa cuta da kuma ƙarfafa ’yan’uwa majiyyata?
18 Wataƙila mu fuskanci gwaji mai tsanani na bangaskiyarmu sa’ad da wanda muke ƙauna yake ciwo mai tsanani. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai ba da rahoton warkewa ta mu’ujiza ba ga Kiristoci kamarsu Abafroditus, Timothawus, Turufimus, babu shakka Jehovah ya taimake su su jimre. (Filibbiyawa 2:25-30; 1 Timothawus 5:23; 2 Timothawus 4:20) Bugu da ƙari, game da “wanda ya kula da matalauta,” mai Zabura ya rera: “Ubangiji za ya toƙara shi a bisa shimfiɗarsa ta rashin lafiya: kana gyarta masa shimfiɗa cikin cutarsa.” (Zabura 41:1-3) Ta yaya kalmomin Mai Zabura za su taimaka mana mu ƙarfafa ’yan’uwa majiyyata?
19 Hanya ɗaya ta ba da taimako a ruhaniya ita ce ta yin addu’a domin waɗanda suke jinya da yin addu’a kuma tare da su. Ko da yake ba ma roƙon warkarwa ta mu’ujiza a yau, za mu iya roƙon Allah ya ba su ƙarfi su jimre wa wahalarsu da kuma ƙarfi na ruhaniya da suke bukata domin su jimre wa wannan lokacin raunana. Jehovah zai kula da su, kuma bangaskiyarsu za ta ƙarfafa ta wajen zuba ido ga lokacin da “wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) Yana da ƙarfafa ƙwarai da gaske sanin cewa ta wajen tashin Yesu daga matattu da kuma Mulkin Allah, mutane masu biyayya za su kuɓuta daga zunubi, cuta, da mutuwa dindindin! Domin wannan bege mai girma, muna yi wa Jehovah godiya, ‘mai warkar da dukan cututtukanmu.’—Zabura 103:1-3; Ru’ya ta Yohanna 21:1-5.
20. Me ya sa za a ce bangaskiya za ta taimaka mana mu jimre “miyagun kwanaki” na tsufa?
20 Bangaskiya kuma za ta taimake mu mu jimre wa “miyagun kwanaki” na tsufa, sa’ad da lafiya da ƙarfi suka ƙare. (Mai-Wa’azi 12:1-7) Saboda haka, tsofaffi a tsakaninmu za su iya yin addu’a kamar yadda mai Zabura ya rera waƙa: “Kai ne begena, ya Ubangiji Yahweh: . . . Kada ka yashe ni cikin kwanakin tsufa; kada ka yarfarda ni lokacin da ƙarfina ya ƙare.” (Zabura 71:5, 9) Mai Zabura ya ga yana bukatar taimakon Jehovah, kamar yawancin ’yan’uwa Kiristoci waɗanda suka tsufa a bauta wa Allah. Domin bangaskiyarsu, za su iya tabbata cewa Jehovah zai taimaka musu ba fasawa.—Kubawar Shari’a 33:27.
Ka Ci Gaba da Gaskata Kalmar Allah
21, 22. Idan muna da bangaskiya, ta yaya wannan yake shafan dangantakarmu da Allah?
21 Bangaskiya ga bishara da kuma dukan Kalmar Allah tana taimaka mana mu kusaci Jehovah. (Yaƙub 4:8) Hakika, shi ne Maɗaukakin Sarki, shi ne Mahaliccinmu kuma Ubanmu. (Ishaya 64:8; Matta 6:9; Ayukan Manzanni 4:24) “Za ya kira gareni, Kai ne Ubana, Allahna, da fa na cetona,” in ji rerawar mai Zabura. (Zabura 89:26) Idan muka ba da gaskiya ga Jehovah da kuma hurarriyar Kalmarsa, mu ma za mu ɗauke shi ‘fa, mai cetonmu.’ Lallai gata ce mai daɗaɗa rai!
22 Jehovah ne Uban Kiristoci shafaffu da kuma abokanansu da suke da begen zama a duniya. (Romawa 8:15) Kuma bangaskiya ga Ubanmu na samaniya ba zai kai ga baƙin ciki ba. Dauda ya ce: “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni.” (Zabura 27:10) Bugu da ƙari, muna da wannan tabbacin: “Ubangiji ba za ya yarda jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma.”—1 Samu’ila 12:22.
23. Menene ake bukata a gare mu idan za mu more dangantaka ta dindindin da Jehovah?
23 Domin mu more dangantaka ta dindindin da Jehovah, hakika, dole ne mu kasance da bangaskiya a bishara kuma mu amince da Nassosi kamar yadda suke da gaske—Kalmar Allah. (1 Tassalunikawa 2:13) Dole ne mu kasance da cikakkiyar bangaskiya ga Jehovah kuma ƙyale Kalmarsa ta haskaka tafarkinmu. (Zabura 119:105; Misalai 3:5, 6) Bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi sa’ad da muka yi addu’a da tabbaci, zai tausaya mana, zai ji ƙanmu, kuma zai tallafa mana.
24. Wane tunani ne mai ta’azantarwa aka gabatar a Romawa 14:8?
24 Bangaskiya ce take motsa mu mu keɓe kanmu ga Allah cikin dukan dawwama. Da bangaskiya mai ƙarfi, ko mun mutu, mu bayinsa ne waɗanda suka keɓe kai da begen tashin matattu. Hakika, “ko mu rayu fa, ko mu mutu, na Ubangiji mu ke.” (Romawa 14:8) Bari mu riƙe waɗannan kalmomin masu ƙarfafawa a zuciyarmu sa’ad da muka kasance da tabbaci ga Kalmar Allah da kuma bangaskiya ga bishara.
Yaya Za Ka Amsa?
• Mecece bangaskiya, kuma me ya sa muke bukatar ta?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da bangaskiya ga bishara da kuma Kalmar Allah gabaki ɗaya?
• Ta yaya bege zai taimake mu mu fuskanci gwaji iri iri?
• Menene zai taimake mu mu kasance da bangaskiya?
[Hotuna a shafi na 6]
Jehovah ya rayar da Irmiya da Iliya domin suna da bangaskiya
[Hotuna a shafi na 7]
Ayuba, Bitrus, da kuma Nehemiah sun kasance da bangaskiya mai ƙarfi
[Hotuna a shafi na 9]
Domin mu more dangantaka ta dindindin da Jehovah, dole ne mu kasance da bangaskiya ga bishara