Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 9/15 pp. 29-31
  • Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KU “ZAUNA A FAƊAKE”
  • (1 Tas. 1:1–5:28)
  • “KU DAGE”
  • (2 Tas. 1:1–3:18)
  • “KA TSARE ABIN DA AKA DAMƘA MAKA”
  • (1 Tim. 1:1–6:21)
  • “KA YI WA’AZIN KALMA; KA YI NACIYA”
  • (2 Tim. 1:1–4:22)
  • Timothawus Yana Shirye Ya Yi Hidima
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Yi Aikin da Aka Ba Ka da Ƙwazo!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Kada Ku Yi Saurin Jijjiguwa Daga Imaninku!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Bulus da Timotawus
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 9/15 pp. 29-31

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus

SABUWAR ikilisiyar da ke Tassalunika ta fuskanci hamayya tun lokacin da aka kafa ta sa’ad da manzo Bulus ya ziyarce su. Sa’ad da Timothawus ya dawo daga Tassalunika da rahoto mai kyau lokacin da yake shekara ashirin da wani abu, hakan ya motsa Bulus ya rubuta wasiƙa ga Tassalunikawa don ya yabe su kuma ya ƙarfafa su. Wataƙila an rubuta shi a ƙarshen shekara 50 A.Z., wannan wasiƙar ita ce ta farko da aka hure Bulus ya rubuta wa Tassalunikawa. Bayan haka, sai ya rubuta musu wasiƙa ta biyu. A wannan karon ya rubuta ne don ya gyara wani ra’ayi da wasu suke da shi kuma ya ƙarfafa ’yan’uwan su tsaya da ƙarfi a ruhaniya.

Kusan shekaru goma da suka wuce, Bulus yana Makidoniya kuma Timothawus yana Afisa. Bulus ya rubuta wa Timothawus wasiƙa yana ƙarfafa shi ya tsaya a Afisas don ya ƙarfafa ’yan’uwa su riƙe dangantakarsu da Jehobah duk da cewa akwai masu koyarwar ƙarya a cikin ikilisiyar. Sa’ad da aka tsananta wa Kiristoci a lokacin da wuta ta halaka Roma a shekara ta 64 A.Z., Bulus ya rubuta wa Timothawus wasiƙarsa ta biyu. Ita ce ƙarshen hurarriyar wasiƙar da ya rubuta. A yau mu ma za mu iya amfana daga ƙarfafawa da kuma shawarar da aka ba da a waɗannan wasiƙu huɗu na Bulus.—Ibran. 4:12.

KU “ZAUNA A FAƊAKE”

(1 Tas. 1:1–5:28)

Bulus ya yaba wa Tassalunikawa don ‘aikin bangaskiyarsu da ɗawainiyar ƙaunarsu da haƙuri.’ Ya gaya musu cewa sune ‘begensa, da farin zuciyarsa, da rawanin fahariyarsa.’—1 Tas. 1:3; 2:19.

Bayan da ya shawarci Kiristoci a Tassalunika su ƙarfafa juna da bege na tashin matattu, Bulus ya ce: “Ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.” Ya shawarce su su “zauna a faɗake” kuma su natsu.—1 Tas. 4:16-18; 5:2, 6; LMT.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

4:15-17—Su waye ne aka “fyauce su zuwa cikin gizagizai su tarbi Ubangiji a sararin sama,” kuma ta yaya hakan ya faru? Waɗannan shafaffun Kiristoci ne waɗanda suke da rai a lokacin da Kristi ya soma Mulki. Sun “tarbi Ubangiji” Yesu a sararin samaniya. Kafin su shaida hakan, da farko suna bukatar su mutu kuma su tashi kamar halittu na ruhu. (Rom. 6:3-5; 1 Kor. 15:35, 44) Yesu ya riga ya soma sarauta, saboda haka shafaffun Kiristoci da suke mutuwa yau ba za su jira a kabari kuma ba. Za a “fyauce” su ko kuma a ta da su nan da nan.—1 Tas. 4:15-18; 5:2, 6.

5:23—Menene Bulus yake nufi sa’ad da ya yi addu’a ya ce a kiyaye ‘ruhu da rai da jikin’ ’yan’uwa? Bulus yana nufin ruhu, rai da kuma jikin ikilisiyar Kirista, wadda ta ƙunshi shafaffun Kiristoci na ruhu da ke Tassalunika. Maimakon ya yi addu’a don ikilisiyar ta tsira, ya yi addu’a don ‘ruhun’ da ke cikin ikilisiyar ta tsira. Ya kuma yi addu’a don “rai” da kuma “jiki,” wato, abubuwa da suka ƙunshi rukunin Kiristoci shafaffu. (1 Kor. 12:12, 13) Addu’ar ta nanata irin ƙauna da Bulus yake yi wa ikilisiya.

Darussa Dominmu:

1:3, 7; 2:13; 4:1-12; 5:15. Hanya mafi kyau da za a ba da shawara ita ce a yaba wa mutum sannan a ƙarfafa shi.

4:1, 9, 10. Ya kamata masu bauta wa Jehobah su ci gaba da ƙarfafa dangantakarsu da shi.

5:1-3, 8, 20, 21. Da yake ranar Jehobah ta kusa, ya kamata muna “yafe da sulke na bangaskiya da ƙauna; kuma da bege na ceto, kwalkwali ke nan.” Ban da haka, ya kamata mu saurari Kalmar annabci na Allah, wato, Littafi Mai Tsarki.

“KU DAGE”

(2 Tas. 1:1–3:18)

Da yake suna son su canja abin da Bulus ya faɗa a wasiƙarsa ta farko, wasu cikin ikilisiya ba su yarda ba cewa “zuwan Ubangijinmu” ya kusa ba. Don ya daidaita wannan ra’ayin, Bulus ya faɗi abin da za ta “fara zuwa.”—2 Tas. 2:1-3.

Bulus ya ba da gargaɗi: “Ku dage, ku kuma riƙi ka’idodin da muka koya muku.” Ya ba su umurni su “fita sha’anin kowane ɗan’uwa malalaci.”—2 Tas. 2:15; 3:6; LMT.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

2:3, 8—Su wanene “mutanen zunubi,” kuma yaya za a halaka su? Waɗannan “mutane” shugabanin Kiristandam ne. Yesu Kristi, wato, “Kalma” kakaki na Allah ne aka ba izini ya yi shelar hukuncin Allah a kan miyagu kuma ya ba da izini a halaka su. (Yoh. 1:1) Saboda haka, za a iya cewa Yesu zai halaka mutanen zunubi da “numfashin bakinsa [wato, ikonsa na aiki].”

2:13, 14—Ta yaya aka zaɓi shafaffu Kiristoci “tun farko zuwa ceto”? An kaddara rukunin shafaffu sa’ad da Jehobah ya ce zuriyar macen za ta ƙuje kan Shaiɗan. (Far. 3:15) Jehobah ya kuma faɗi farillai da za su cika, aikin da za su yi, da kuma gwaji da za su fuskanta. Shi ya sa ya kira su don ‘wannan makasudi.’

Darussa Dominmu:

1:6-9. Jehobah ba ya zartar da hukuncinsa a kan dukan mutane.

3:8-12. Bai kamata kusatowar ranar Jehobah ya zama dalilin ƙin yin aiki don mu biya bukatunmu ba kuma mu tallafa wa kanmu a hidima ba. Rashin aiki zai sa mu zama ragwaye kuma mu zama masu “shishigi.”—1 Bit. 4:15.

“KA TSARE ABIN DA AKA DAMƘA MAKA”

(1 Tim. 1:1–6:21)

Bulus ya gargaɗi Timothawus “ka yi yaƙi, yaƙi mai-kyau; kana riƙe da bangaskiya da managarcin lamiri.” Manzon ya tsara abin da ake bukata daga maza kafin a naɗa su a cikin ikilisiya. Bulus ya gargaɗi Timothawus ya ƙi “tatsuniyoyi na saɓo da irin na gyatumai.”—1 Tim. 1:18, 19; 3:1-10, 12, 13; 4:7.

Bulus ya rubuta: “Kada ka tsauta wa dattijo.” Ya aririce Timothawus: “Ka tsare abin da aka damƙa maka, kana bijire ma maganganu na saɓo da kuma tsayayyar ilimin da ana ce da shi hakanan a ƙaryace.”—1 Tim. 5:1; 6:20.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:18; 4:14—Wane “annabci” ne aka yi game da Timothawus? Wataƙila an yi wasu annabce-annabce game da abin da Timothawus zai yi a nan gaba, Bulus ya furta hakan da aka hure shi sa’ad da ya ziyarci Listira a ziyararsa ta wa’azi ta biyu. (A. M. 16:1, 2) Bisa waɗannan “annabci,” dattawan ikilisiya suka ‘ɗibiya hannuwa’ a kan Timothawus, sun ware shi don hidima na musamman.

2:15—Ta yaya mata “za ta tsira ta wurin haifan ’ya’ya”? Haifan yara, kula da yaranta, da kuma yin aikacen-aikacen gida, za su sa mace “ta tsira” daga ragonci kuma ba za ta zama mace mai “shishigi” ba.—1 Tim. 5:11-15.

3:16—Menene asirin ibada? Da daɗewa ba a sani ko ’yan adam za su yi biyayya sosai ga ikon mallaka na Jehobah ba. Yesu ya ba da amsar ta wajen kasancewa da aminci ga Allah har mutuwarsa.

6:15, 16—Waɗannan kalmomin na nuni ga Jehobah Allah ne ko kuwa Yesu Kristi? Waɗannan kalmomi na nuni ga wanda ake kwatantawa a nan, wato, Yesu Kristi. (1 Tim. 6:14) Idan aka gwada shi da ’yan adam da suke sarauta na sarakuna da iyayengiji, Yesu ne “Mai-iko makaɗaici” shi kaɗai ne ba ya mutuwa. (Dan. 7:14; Rom. 6:9) Tun lokacin da ya koma sama, babu ɗan adam a duniya da zai iya “ganinsa.”

Darussa Dominmu:

4:15. Ko mun zama Kirista ba da daɗewa ba ko kuma da daɗewa, ya kamata mu yi ƙoƙari mu zama masu cin gaba a ruhaniya.

6:2. Idan muna aiki a ƙarƙashin ɗan’uwa, ya kamata mu yi masa aiki sosai fiye da yadda za mu yi wa wani da ba ɗan’uwa ba.

“KA YI WA’AZIN KALMA; KA YI NACIYA”

(2 Tim. 1:1–4:22)

Don ya shirya Timothawus don lokacin wahala da ke gaba, Bulus ya rubuta: “Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko da na ƙauna da na horo.” An yi wa Timothawus gargaɗi: “Kada bawan Ubangiji kuwa shi yi husuma, amma sai shi yi nasiha ga duka, mai-sauƙin koyaswa.”—2 Tim. 1:7; 2:24.

Bulus ya yi wa Timothawus gargaɗi: “Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koyo, waɗanda ka tabbata da su kuma.” Da yake ana yaɗa koyarwar ridda, manzon ya gargaɗi Timothawus: “Ka yi wa’azin kalma; ka yi naciya . . . ka tsautar, ka kwaɓa, ka gargaɗar, da iyakacin jimrewa da koyarwa.”—2 Tim. 3:14; 4:2.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:13—Menene “kwatancin sahihiyan kalmomi”? “Sahihiyan kalmomi” “kalmomin Ubangijinmu Yesu Kristi” ne, wato, koyarwa ta gaske na Kirista. (1 Tim. 6:3) Abin da Yesu ya yi kuma ya koyar ya jitu da Kalmar Allah, saboda haka, furcin nan “sahihiyan kalmomi” wataƙila tana nufin dukan koyarwa na Littafi Mai Tsarki. Waɗannan koyarwa za su taimake mu mu san abin da Jehobah yake bukata a gare mu. Mu ci gaba da riƙe wannan kwatanci ta wajen yin abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki.

4:13—Menene “fatun nan”? Kwatancin nan “fatu” na nuni ga kayan rubutu da aka yi da fata. Wataƙila Bulus ya ce a kawo masa sashen Nassosin Ibrananci don ya yi nazarinsu sa’ad da yake kurkuku a Roma. Wasu cikin naɗaɗɗun littattafan wataƙila na ganyen papyrus ne wasu kuma na fata ne.

Darussa Dominmu:

1:5; 3:15. Ainihin dalilin da ya sa Timothawus yake da bangaskiya ga Yesu Kristi, wato, bangaskiyar da ta shafi komi da Timothawus ya yi, ita ce koyarwar Nassi da aka yi masa a gida. Yana da muhimmanci waɗanda suke cikin iyali su yi tunani sosai game da yadda suke cika wannan hakkin ga Allah da kuma yaransu!

1:16-18. Sa’ad da ’yan’uwanmu masu bi suke fuskantar gwaji, tsanantawa, ko kuma an jefa su a kurkuku, bari mu yi addu’a dominsu kuma mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu taimake su.—Mis. 3:27; 1 Tas. 5:25.

2:22. Ya kamata Kiristoci, musamman matasa kada su mai da hankali kawai ga wasan jiki, wasanni, kaɗe-kaɗe, nishaɗi, tafiye tafiye, maganganu, da sauransu, har ba su da lokacin ayyuka na ruhaniya.

[Hoto a shafi na 31]

Wane littafi ne manzo Bulus ya rubuta a ƙarshe?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba