Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 12/15 pp. 6-10
  • Kada Ku Yi Saurin Jijjiguwa Daga Imaninku!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ku Yi Saurin Jijjiguwa Daga Imaninku!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • GARGAƊI A KAN KARI
  • KA YI HANKALI WAJEN ZAƁAN ABOKAI
  • “KU KIYAYE DUKAN ABUBUWAN DA AKA KOYA MUKU”
  • ABIN DA ZAI SA KADA MU JIJJIGU
  • Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ku Zauna da Shiri don Ranar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • “Ku Yi Ta Gina Juna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 12/15 pp. 6-10

Kada Ku Yi Saurin Jijjiguwa Daga Imaninku!

“Muna fa roƙonku, ’yan’uwa, . . . kada ku jijjigu da sauri a cikin hankalinku.”—2 TAS. 2:1, 2.

DON BIMBINI

  • Waɗanne gargaɗin da suka dace ne wasiƙun Bulus ga Tasalonikawa suke ɗauke da su?

  • Mene ne zai taimaka mana kada mu yaudaru?

  • Ta yaya kasancewa da himma a hidima yake kāre mu?

1, 2. Me ya sa yaudara ta zama ruwan dare a yau, kuma ta yaya ake yaɗa ƙaryace-ƙaryace? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

YAUDARA da ƙaryace-ƙaryace sun zama ruwan dare a wannan duniyar. Hakan bai kamata ya zama abin mamaki a gare mu ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana a fili cewa Shaiɗan Iblis fitaccen mai yaudara ne, kuma shi ne mai mulkin wannan duniyar. (1 Tim. 2:14; 1 Yoh. 5:19) Yayin da ƙarshen wannan mugun duniyar yake gabatowa, Shaiɗan yana ƙara fushi domin “zarafinsa kaɗan ya rage.” (R. Yoh. 12:12) Saboda haka, ya kamata mu san cewa waɗanda Shaiɗan yake rinjaya za su ƙara kasancewa da rashin gaskiya, musamman ma don su yaudari masu bauta wa Jehobah.

2 A wasu lokatai, kafofin yaɗa labarai sukan baza labaran ƙarya ko kuma jita-jita game da bayin Jehobah da kuma imaninsu. Ana yaɗa labaran ƙarya ta jaridu da shirye-shiryen talabijin da kuma dandalin Intane. Saboda haka, wasu sukan ɓata rai ko kuma rikice don sun amince da waɗannan ƙaryace-ƙaryacen ba tare da sun yi bincike ba.

3. Mene ne zai taimaka mana mu kāre kanmu daga ƙaryace-ƙaryace?

3 Abin farin ciki shi ne, za mu iya kāre kanmu daga ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan don muna da tanadin Kalmar Allah “mai-amfani . . . ga kwaɓewa.” (2 Tim. 3:16) Manzo Bulus ya rubuta cewa an yaudari wasu Kiristoci da ke Tasalonika. Ya kamata mu koyi darasi daga abin da ya rubuta. Ya aririce su cewa ‘kada su jijjigu da sauri a cikin hankalinsu.’ (2 Tas. 2:1, 2) Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga gargaɗin da Bulus ya yi musu cikin ƙauna, kuma ta yaya za mu yi amfani da su?

GARGAƊI A KAN KARI

4. Ta yaya aka faɗakar da Kiristoci da ke Tasalonika game da zuwan “ranar Ubangiji,” kuma ta yaya ake mana hakan a yau?

4 A wasiƙarsa ta farko ga ikilisiyar da ke Tasalonika, Bulus ya yi musu gargaɗi game da zuwan “ranar Ubangiji.” Ba ya son ’yan’uwansa su kasance a cikin duhun kai ko kuma rashin shiri. A maimakon haka, ya ƙarfafa su cewa su “’ya’yan haske” ne, kuma ya daɗa cewa: “Mu yi zamanmu ba barci ba maye.” (Karanta 1 Tasalonikawa 5:1-6.) Yanzu, muna jiran lokacin da za a halaka Babila Babba, wato dukan addinan ƙarya. Wannan halakar ce mafarin babbar ranar Jehobah. Muna godiya cewa mun sami ƙarin haske game da yadda Jehobah zai cika nufinsa. Ƙari ga haka, a cikin ikilisiya, muna amfana daga faɗakarwa da ke taimaka mana mu kasance a shirye don zuwan ranar Ubangiji. Idan muka mai da hankali ga waɗannan faɗakarwa da muke samu a kai a kai, za mu ƙara inganta ƙudurinmu don kada ‘mu jijjigu a cikin hankalinmu,’ amma mu ci gaba da bauta wa Allah.—2 Tas. 2:2.

5, 6. (a) Mene ne Bulus ya yi magana a kai a wasiƙa ta biyu da ya rubuta ga Tasalonikawa? (b) Mene ne Allah zai yi ta hannun Yesu, kuma waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

5 Bulus ya rubuta wasiƙa ta biyu ga Kiristoci da ke Tasalonika. A cikin wasiƙar, ya rubuta game da ƙunci da ke zuwa, wato lokacin da Yesu zai idar da huƙuncin Allah a kan “waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar.” (2 Tas. 1:6-8) A sura ta biyu ta wannan wasiƙar, ya bayyana cewa hankalin wasu a cikin ikilisiyar ya “tashi,” har suka amince cewa ranar Ubangiji ta yi kusa sosai a lokacin. (Karanta 2 Tasalonikawa 2:1, 2.) Waɗannan Kiristoci na farko ba su da cikakken bayani game da yadda nufin Jehobah zai cika. Bulus ya ambata hakan sa’ad da ya rubuta daga baya cewa: “Iliminmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. Sa’ad da kuwa cikakken ya zo, sai ɗan kiman nan ya shuɗe.” (1 Kor. 13:9, 10, Littafi Mai Tsarki) Amma, za su iya kasancewa da aminci idan suka bi hurarren gargaɗin Bulus da Bitrus da kuma sauran amintattun ’yan’uwa suka rubuta.

6 Allah ya daidaita tunaninsu ta wajen hure Bulus ya bayyana cewa kafin ranar Ubangiji Jehobah, za a yi ridda sosai kuma “mutumin zunubi” zai bayyana.a Bayan haka, Ubangiji Yesu zai “halaka” dukan waɗanda suka yaudaru a lokacin da Allah ya ƙayyade. Manzo Bulus ya bayyana cewa hakan zai faru da su ne don ba sa “ƙaunar gaskiya.” (2 Tas. 2:3, 8-10) Ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Ina ƙaunar gaskiya sosai kuwa? Shin ina yin nazarin wannan mujallar da kuma sauran littattafan da ake tanadar wa mutanen Allah don sanin yadda muka fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki a yanzu?’

KA YI HANKALI WAJEN ZAƁAN ABOKAI

7, 8. (a) Waɗanne haɗarurruka ne Kiristoci na farko suka fuskanta? (b) Wane abu ne musamman ya zama haɗari ga Kiristoci a yau?

7 Abin lura shi ne, ba koyarwar ’yan ridda ne kawai za ta iya kasance da haɗari ga Kiristoci ba. Bulus ya rubuta zuwa ga Timotawus cewa “son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu.” Ya ƙara bayyana cewa “don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukan rai.” (1 Tim. 6:10, LMT) “Ayyukan jiki” ma sun ci gaba da kasancewa da haɗari ga Kiristoci.—Gal. 5:19-21.

8 Bulus ya yi wa Tasalonikawa gargaɗi sosai game da waɗanda ya kira “masu-ƙaryan manzanci.” Wasu daga cikinsu sun faɗi “karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.” (2 Kor. 11:4, 13; A. M. 20:30) Daga baya, Yesu ya yaba wa ikilisiyar da ke Afisa don sun ƙi su amince da “miyagun mutane.” Waɗannan ’yan’uwa da ke Afisa sun “auna” waɗanda suka yi da’awa cewa su manzanni ne kuma suka gano cewa manzannin jabu ne kuma su maƙaryata ne. (R. Yoh. 2:2) A wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Tasalonikawa, Bulus ya ba da wannan shawara: “Amma muna umurtanku, ’yan’uwa, cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kristi, ku ware kanku daga wajen kowane ɗan’uwa mai-tafiya da shiririta.” Ya kuma ambata cewa wasu Kiristoci ba sa son “yin aiki.” (2 Tas. 3:6, 10) Idan har an ɗauki waɗannan a matsayin masu shiririta, to, hakan ya nuna cewa yana da muhimmanci sosai su daina tarayya da waɗanda suka soma ridda. Hakika, ya dace su guji yin tarayya da irin waɗannan mutanen don hakan yana da haɗari sosai, kuma hakan ma yake a yau.—Mis. 13:20.

9. Me ya sa ya kamata mu yi hattara idan wani ya soma faɗin ra’ayinsa ko kuma yin sūkar dattawa ko wasu ’yan’uwa a ikilisiya?

9 Muna kusa da lokacin ƙunci mai girma da kuma ƙarshen wannan mugun zamanin. Saboda haka, waɗannan gargaɗin da aka ba da a ƙarni na farko yana da muhimmanci sosai a yau. Ba ma so mu “karɓi alherin Allah banza.” Idan muka yi hakan, za mu yi asarar rai na har abada ko a sama ko kuma a duniya. (2 Kor. 6:1) Wajibi ne mu yi hattara idan wani da ke halartan taron ikilisiya yana so ya sa mu faɗi ra’ayinmu game da wani batu da ba a bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki ba, ko kuma mu yi sūkar dattawa da kuma wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiya.—2 Tas. 3:13-15.

“KU KIYAYE DUKAN ABUBUWAN DA AKA KOYA MUKU”

10. Waɗanne koyarwa ne aka ƙarfafa Kiristoci da ke Tasalonika su manne musu?

10 Manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwa da ke Tasalonika cewa su “tsaya” da ƙarfi kuma su manne wa abin da suka koya. (Karanta 2 Tasalonikawa 2:15.) Waɗanne abubuwa ne aka koya musu? Waɗannan ba koyarwar addinan ƙarya ba ne. A maimakon haka, Bulus yana magana ne game da abubuwan da shi da kuma sauran Kiristoci suka koya daga wajen Yesu da kuma abubuwan da Allah ya hure manzannin su rubuta. Bulus ya yaba wa ’yan’uwa da ke Korinti domin, kamar yadda ya rubuta, “cikin dukan abu, kuna kuwa kiyaye koyarwata, kamar yadda na ba da su gare ku.” (1 Kor. 11:2) Tun da waɗannan koyarwar sun fito ne daga wurin Jehobah da kuma Ɗansa, za mu iya amincewa da su.

11. A waɗanne hanyoyi ne yaudara za ta iya shafan wasu?

11 Bulus ya ambaci hanyoyi biyu da za su iya sa Kirista ya soma rashin bangaskiya kuma ya yi rashin aminci ga Jehobah. (Karanta Ibraniyawa 2:1; 3:12.) Ya yi magana game da ‘zakuɗawa’ da kuma bauɗewa. Kwalekwale zai iya zakuɗawa daga bakin kogi da sannu-sannu kuma kafin a ankara, ya yi nesa da gaɓa. A wani ɓangare kuma, mutum zai iya tura kwalekwalen daga bakin gaɓa da gangan. Waɗannan misalai biyu suna nuna abin da zai iya faruwa da mutum idan ya yarda a yaudare shi kuma a sakamako, ya soma shakkar gaskiya.

12. Waɗanne abubuwan ne za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah?

12 Wataƙila wasu Tasalonikawa sun bari an yaudare su. Shin hakan zai iya faruwa a yau? Akwai abubuwa da yawa da za su iya ɓata lokacinmu. Ka yi tunanin awoyin da mutane suke ɓatawa a dandalin sada zumunta na Intane da karanta da kuma amsa saƙonnin Imel ko kuma yawan biɗan nishaɗi ko wasanni. Kowane ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya raba hankalin Kirista kuma ya rage ƙwazonsa a bautar Jehobah. Mene ne sakamakon? Zai soma yin addu’a da kuma nazari sama-sama kuma zai riƙa sanyin gwiwa a yin wa’azi. Shin mene ne za mu iya yi don kada mu jijjigu daga abin da aka koya mana?

ABIN DA ZAI SA KADA MU JIJJIGU

13. Wane irin hali ne mutane da yawa suke da shi kamar yadda aka annabta, kuma me zai iya sa mu kasance da bangaskiya sosai?

13 Wajibi ne mu san cewa ƙarshen zamanin nan ya ƙusa kuma haɗari ne yin tarayya da mutanen da ba su gaskata cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe” ba. Manzo Bitrus ya annabta game da wannan lokacin cewa: “Masu-ba’a za su zo da ba’a, suna bin nasu sha’awoyi, suna cewa, Ina alkawarin tafowarsa? Gama, tun daga randa ubanni suka kwanta barci, dukan al’amura suna nan kamar yadda suke tun farkon halitta.” (2 Bit. 3:3, 4) Karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana da kuma yin nazarinsa a kai a kai za su taimaka mana mu tuna cewa muna “kwanaki na ƙarshe.”’Yan ridda da aka yi annabcinsu sun soma bayyana tun da daɗewa kuma suna nan har yau. Har ila “mutumin zunubi” yana nan kuma yana gāba da bayin Allah. Saboda haka, ya kamata kada mu manta cewa ranar Ubangiji Jehobah tana nan tafe.—Zaf. 1:7.

14. Ta yaya kasancewa da himma a hidima yake kāre mu?

14 Wani abu kuma da zai taimaka mana kada mu jijjigu daga abin da aka koya mana shi ne yin wa’azin bishara a kai a kai. Sa’ad da Yesu ya umurci mabiyansa cewa su almajirtar da dukan al’ummai kuma su koya musu su kiyaye dukan abubuwan da ya koya musu, yana ba su shawara ne da za ta kāre su. (Mat. 28:19, 20) Bin wannan umurnin ya bukaci kasancewa da himma a yin wa’azi. Shin kana ganin ’yan’uwa da ke Tasalonika sun yi wa’azi da kuma koyarwa kawai ne don ya zama wajibi su yi hakan? Ka tuna cewa Bulus ya ce musu: “Kada ku ɓice Ruhu Mai-tsarki; kada ku rena annabci.” (1 Tas. 5:19, 20) Babu shakka, annabce-annabcen da muke yin nazarinsu da mutane suna da ban sha’awa sosai!

15. Waɗanne abubuwa ne za mu iya tattaunawa a ibada ta iyali?

15 Dukanmu muna so mu taimaka wa iyalanmu su inganta yadda suke wa’azin bishara. Don a cim ma wannan burin, ’yan’uwa da yawa suna amfani da sashen ibadarsu ta iyali don su inganta yadda suke wa’azi. Za ku iya tattauna yadda za ku koma ziyara wurin wani da kuka yi wa wa’azi. Wane batu ne kake so ka tattauna da shi? Mene ne za ku faɗa da zai sa mai gidan ya so ku sake dawowa? Wane lokaci ne ya fi dacewa ku koma ziyarar? ’Yan’uwa da yawa suna amfani da sashen bauta ta iyalinsu don shirya abin da za a tattauna a taro. Shin za ka iya yin haka da iyalinka? Shirya da kuma saka hannu a taro zai ƙarfafa bangaskiyarka kuma zai taimaka maka kada ka jijjigu daga abin da ka koya. (Zab. 35:18) Hakika, ibada ta iyali za ta kāre mu daga yin zaton abubuwan da ba a bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki ba da kuma yin shakkar abubuwan da Jehobah ke koya mana ta ƙungiyarsa.

16. Mene ne yake hana shafaffu jijjiguwa daga imaninsu?

16 Idan muka yi tunanin yadda Jehobah ya albarkace mutanensa da ƙarin haske a kan annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki, hakan zai sa mu kasance da gaba gaɗi cewa za mu sami lada mai kyau a nan gaba. Shafaffu suna da begen kasancewa tare da Kristi a sama. Babu shakka wannan begen yana motsa su su ƙi jijjiguwa daga imaninsu! Abin da Bulus ya rubuta ga Tasalonikawa ya shafi ’yan’uwanmu shafaffu a yau, ya ce: “Mu ba da godiya ga Allah kullum sabili da ku, ’yan’uwa ƙaunatattun Ubangiji, tun da Allah ya zaɓe ku . . . cikin tsarkakewar ruhu da ba da gaskiya ga gaskiya.”—2 Tas. 2:13.

17. Ta yaya abin da ke 2 Tasalonikawa 3:1-5 yake ƙarfafa ka?

17 Ya kamata waɗanda suke da begen yin rayuwa har abada a duniya kada su yarda su jijjigu daga imaninsu. Idan kana da begen yin rayuwa har abada a duniya, zai dace ka bi shawarar da Bulus ya rubuta wa ’yan’uwansa shafaffu a Tasalonika. (Karanta Tasalonikawa 3:1-5.) Ya kamata kowanenmu ya gode wa Allah saboda waɗannan furucin. Hakika, wasiƙun da aka rubuta zuwa ga Tasalonikawa suna ɗauke da gargaɗi masu muhimmanci game da zaton banza da ra’ayin da bai dace ba. Da yake muna rayuwa ne gab da ƙarshen wannan zamanin, ya kamata mu daraja waɗannan gargaɗin sosai.

a Bulus ya rubuta a Ayyukan Manzanni 20:29, 30 cewa: “Mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.” Da shigewar lokaci, tarihi ya nuna cewa an soma samun bambanci tsakanin waɗanda suke ja-gora da kuma sauran ’yan’uwa a cikin ikilisiya. A ƙarni na uku, ya bayyana a fili cewa wannan “mutumin zunubi” shi ne rukunin limaman Kiristendom.—Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 1990, shafuffuka na 10-14.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba