Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 9/15 pp. 18-22
  • Ka Koyi Darasi Daga Haƙurin Jehobah Da Na Yesu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koyi Darasi Daga Haƙurin Jehobah Da Na Yesu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ME YA SA JEHOBAH YAKE HAƘURI?
  • TA YAYA YESU YA KAFA MISALI MAI KYAU NA YIN HAƘURI?
  • TA YAYA ZAN IYA ZAMA MAI HAƘURI KAMAR ALLAH?
  • WACE ALBARKA CE KE TATTARE DA KASANCEWA DA HAƘURI?
  • Ka Ci Gaba da Zama Mai Hakuri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Yi Koyi Da Haƙurin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Muna Bukatar Haƙuri a Hidimarmu
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Haƙuri Yana Sa Mu Kasance da Bege
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 9/15 pp. 18-22

Ka Koyi Darasi Daga Haƙurin Jehobah Da Na Yesu

“Ku maida jimrewar Ubangijinmu ceto ne.”—2 BIT. 3:15.

MECE CE AMSARKA?

Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana da haƙuri?

Me ya sa Yesu ya yi haƙuri na dogon lokaci?

Mene ne za mu iya yi don mu yi koyi da haƙurin Allah?

1. Wace tambaya ce wasu amintattun bayin Jehobah suke yi?

WATA ’yar’uwa da ta bauta wa Jehobah cikin shekaru da yawa da aminci kuma ta jimre wa matsaloli da yawa ta yi tambaya ta gaba, “Zan ga ƙarshen wannan zamanin kuwa?” Wasu da suka yi shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah ma suna irin wannan tambayar. Muna ɗokin ganin ranar da Jehobah zai sabonta dukan abubuwa kuma za mu daina shan wahala. (R. Yoh. 21:5) Ko da yake mun san cewa ƙarshen wannan zamanin Shaiɗan ya kusa ainun, amma jimrewa yana iya yi mana wuya.

2. Waɗanne tambayoyi game da yin haƙuri ne za mu tattauna?

2 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wajibi ne mu kasance masu haƙuri. Kamar yadda Jehobah ya cika alkawuran da ya yi wa amintattun bayinsa a zamanin dā, hakan ma zai cika dukan alkawuran da ya yi idan mun kasance da imani da kuma jimiri. (Karanta Ibraniyawa 6:11, 12.) Jehobah ma ya daɗe yana haƙuri. Da zai kawo ƙarshe ga dukan mugunta duk sa’ad da ya ga dama, amma yana jiran lokacin da ya ƙayyade. (Rom. 9:20-24) Me ya sa yake haƙuri? Ta yaya Yesu ya yi koyi da haƙurin Ubansa kuma wane misali ne ya kafa mana? Wane sakamako ne za mu samu idan mun yi koyi da haƙurin Jehobah? Ko da za mu ji kamar Jehobah yana jinkirin kawo ƙarshen wannan zamanin, amma amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka mana mu kasance masu haƙuri da kuma masu bangaskiya sosai.

ME YA SA JEHOBAH YAKE HAƘURI?

3, 4. (a) Me ya sa Jehobah yake yin haƙuri? (b) Mene ne Jehobah ya yi bayan Adamu da Hauwa’u suka yi rashin biyayya?

3 Akwai ƙwaƙƙwarar dalilai da suka sa Jehobah yake haƙuri. Babu kowacce halitta da ta fi Jehobah iko, kuma ba ya bukatar ya yi haƙuri kafin ya kawo ƙarshe ga mugunta. Amma Jehobah ya yi haƙuri domin ya san cewa zai ɗauki lokaci kafin a amsa tambayar da Shaiɗan ya yi a gonar Adnin. Jehobah ya san abin da kowa a sama da duniya yake yi da kuma tunani, shi ya sa abubuwan da yake yi don amfaninmu ne.—Ibran. 4:13.

4 Nufin Jehobah ne cewa ’ya’yan Adamu da Hauwa’u su mamaye duniya baki ɗaya. Sa’ad da Shaiɗan ya rinjayi Hauwa’u kuma Adamu ya yi rashin biyayya, Allah bai yi watsi da ainihin manufarsa ga ’yan Adam ba. Jehobah bai yi fargaba ba ko tsai da shawara da garaje ko kuma yi watsi da ’yan Adam ba. Maimakon haka, ya yanke shawara a kan yadda zai cika nufinsa ga mutane da kuma duniya. (Isha. 55:11) Haƙurin da Jehobah ya yi zai sa ya cika nufinsa kuma ya nuna cewa shi ne ya cancanci ya Mulke halittunsa. Ya ma yi haƙuri na shekaru dubbai don ya cika wasu sassa na nufinsa a hanyar da ta dace.

5. Mene ne amfanin haƙurin da Jehobah yake yi?

5 Wani dalili kuma da ya sa Jehobah yake haƙuri shi ne don ƙarin mutane su samu rai na har abada. A yanzu, yana shirye-shirye don ya ceci “taro mai-girma.” (R. Yoh. 7:9, 14; 14:6) Jehobah yana yin amfani da aikin wa’azi don ya sa mutane su koya game da Mulkinsa da ƙa’idojinsa masu kyau. Saƙon Mulkin Allah “bishara” ne ga mutane. Hakika, labari ne mafi daɗin ji. (Mat. 24:14) Kowanne mutum da Jehobah ya jawo yana kasancewa cikin abokan gaske na ƙungiyar Jehobah da ke dukan duniya. (Yoh. 6:44-47) Allahnmu mai ƙauna yana yin dukan waɗannan abubuwan don ya taimaka wa mutane su samu amincewarsa. Ya kuma zaɓi wasu ’yan Adam su je sama don su yi sarauta a Mulkinsa. Sa’ad da suka je sama, za su taimaki ’yan Adam masu aminci su zama kamiltattu kuma su samu rai na har abada. Hakan ya nuna cewa ko da Jehobah yana haƙuri, amma yana wasu shirye-shirye don ya cika nufinsa, kuma yana hakan ne don mu amfana.

6. (a) Yaya Jehobah ya yi haƙuri a zamanin Nuhu? (b) Yaya Jehobah yake yin haƙuri a yau?

6 Ko da yake mutane da yawa suna yin munanan ayyuka don su ɓata wa Jehobah rai amma har ila Jehobah yana haƙuri. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya yi sa’ad da mugunta ta cika duniya kafin Rigyawar. Mugunta da lalata da suka cika duniya a lokacin sun “ɓata masa [Allah] zuciya ƙwarai.” (Far. 6:2-8) Ba zai ƙyale hakan ya ci gaba har abada ba, saboda haka ya ce zai halaka miyagu da rigyawa. A “lokacin da haƙurin Allah yana jinkiri a zamanin Nuhu,” Jehobah ya yi shiri don ya ceci Nuhu da iyalinsa. (1 Bit. 3:20) Jehobah ya sanar da Nuhu game da abin da yake son ya yi a lokacin da ya dace kuma ya umurce shi ya gina jirgin ruwa. (Far. 6:14-22) Bugu da ƙari, Nuhu “mai-shelan adalci” ne, kuma ya gargaɗi mutane cewa halaka tana nan tafe. (2 Bit. 2:5) Yesu ya ce zamaninmu kamar na Nuhu ne. Jehobah ya riga ya ƙayyade lokacin da zai halaka wannan mugun zamanin. Babu mutumin da ya san “ranan nan da sa’an nan” da hakan zai faru. (Mat. 24:36) A yau, Jehobah ya ce mu gargaɗi mutane kuma mu gaya musu abin da za su yi don su tsira.

7. Shin Jehobah yana jinkirin cika alkawuransa ne? Ka bayyana.

7 Hakika, haƙurin Jehobah ba ya nufin cewa yana jira ne kurum don lokacin da zai halaka miyagu ya zo. Kuma bai kamata mu yi tunani cewa ba ya kula da mu. Amma, idan mun soma tsufa ko mun sha wuya sosai a wannan mugun zamanin za mu iya soma tunani haka. Muna iya yin sanyin gwiwa ko kuma mu ji cewa Jehobah yana jinkirin cika alkawuransa. (Ibran. 10:36) Kada ka taɓa manta cewa yana da ƙwaƙƙwarar dalilin yin haƙuri kuma yana yin amfani da wannan lokacin a hanyar da za ta amfane amintattun bayinsa. (2 Bit. 2:3; 3:9) Yanzu bari mu tattauna yadda Yesu ya yi koyi da haƙurin Ubansa.

TA YAYA YESU YA KAFA MISALI MAI KYAU NA YIN HAƘURI?

8. A waɗanne irin yanayi ne Yesu ya kasance da haƙuri?

8 Yesu yana yin nufin Allah kuma ya yi hakan na tsawon shekaru da yawa. Sa’ad da Shaiɗan ya yi tawaye, Jehobah ya yanke shawara Ɗansa tilo ya zo duniya a matsayin Almasihu. Ka yi tunanin irin haƙurin da Yesu ya yi na shekaru da yawa kafin wannan lokacin ya yi. (Karanta Galatiyawa 4:4.) A lokacin, ba wai yana zaman kashe wando ba ne. Ya shagala da aikin da Ubansa ya ba shi. Kuma sa’ad da ya zo duniya, ya san cewa Shaiɗan zai sa a kashe shi kamar yadda aka annabta. (Far. 3:15; Mat. 16:21) Ya yi haƙuri sa’ad da yake shan azaba domin ya san cewa nufin Allah ne ya mutu a wannan hanyar. Babu mai aminci kamarsa. Bai yi tunanin abin da ya gamshe shi ba ko game da matsayinsa kuma za mu iya amfana daga misalinsa.—Ibran. 5:8, 9.

9, 10. (a) Mene ne Yesu yake yi yayin da yake jiran Jehobah ya ɗauki mataki? (b) Yaya za mu iya yin koyi da Yesu?

9 Bayan da Jehobah ya ta da Yesu daga matattu, ya ba shi iko bisa sama da duniya. (Mat. 28:18) Yana yin amfani da wannan ikon don ya cika nufin Jehobah kuma yana yin hakan a daidai lokacin da Jehobah ya ƙayyade. Yesu ya jira a hannun dama na Allah har shekara ta 1914 sa’ad da Jehobah ya ba shi iko bisa maƙiyansa. (Zab. 110:1, 2; Ibran. 10:12, 13) Nan ba da daɗewa ba, zai halaka zamanin Shaiɗan. Amma yayin da Yesu yake jiran wannan lokacin ya zo, yana taimaka wa mutane su bauta wa Allah kuma yana bishe su zuwa “ruwaye na rai.”—R. Yoh. 7:17.

10 Ka koya yadda za ka iya yin koyi da halin Yesu kuwa? Ya san cewa Jehobah ya ƙayyade lokacin da zai ɗauki mataki. Babu shakka, Yesu yana ɗokin yin duk abin da Ubansa ya ce ya yi, amma yana jiran lokacin ya yi. Yayin da muke jiran ƙarshen mugun zamanin Shaiɗan ya zo, muna bukatar yin haƙuri. Muna bukatar mu bi ja-gorar Jehobah kuma kada mu karaya sa’ad da muke sanyin gwiwa. Me ya kamata mu yi don mu kasance da irin wannan haƙurin?

TA YAYA ZAN IYA ZAMA MAI HAƘURI KAMAR ALLAH?

11. (a) Wace nasaba ce ke tsakanin bangaskiya da haƙuri? (b) Me ya sa muke da ƙwaƙƙwarar dalilin kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi?

11 Annabawa da wasu amintattun bayin Jehobah da suka wanzu kafin Yesu ya zo duniya sun nuna cewa zai yiwu ’yan Adam su yi haƙuri. Akwai nasaba tsakanin haƙurinsu da bangaskiyarsu. (Karanta Yaƙub 5:10, 11.) Da ba su da bangaskiya ko kuma ba su gaskata da alkawuran Jehobah ba, ba za su yi haƙuri har sai Allah ya cika alkawuransa ba. Amma sau da yawa, sun jimre da mawuyacin yanayi ko gwaje-gwaje domin suna da bangaskiya cewa Allah zai cika alkawuransa. (Ibran. 11:13, 35-40) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna da ƙwaƙƙwarar dalili na kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi a yau. Yesu ya zama ‘Mai-cika’ bangaskiyarmu. (Ibran. 12:2) Ya cika annabce-annabce da yawa kuma ya taimaka mana mu fahimci nufin Allah sosai.

12. Mene ne za mu iya yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

12 Mene ne za mu iya yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu daɗa yin haƙuri? Yana da muhimmanci mu bi umurnin Allah. Alal misali, ka yi la’akari da dalilin da ya sa yake da muhimmanci ka saka Mulkin Allah farko a rayuwarka. Za ka iya ƙoƙari sosai don ka yi biyayya da umurnin da ke littafin Matta 6:33? Wataƙila za ka iya daɗa sa’o’in da kake yi kana wa’azi ko kuma za ka iya yin canje-canje a salon rayuwarka. Jehobah yana maka albarka don ƙoƙarce-ƙoƙarcen da kake yi don ka bi umurninsa. Wataƙila ya sa ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani ko ya sa ka kasance da “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.” (Karanta Filibiyawa 4:7.) Yayin da kake mai da hankali ga albarkar da Jehobah yake maka, za ka fahimci cewa haƙurin da kake yi yana da muhimmanci.—Zab. 34:8.

13. Wane kwatanci ne ya nuna yadda bangaskiyarmu za ta iya taimaka mana mu daɗa haƙuri?

13 Kwatancin da ke gaba zai taimaka mana mu fahimci yadda bangaskiya za ta taimaka mana mu yi haƙuri. Manomi yana shuki da noma da kuma girbi. A duk lokacin da gonarsa ta yi amfani sosai, yana daɗa kasancewa da gaba gaɗi ya sake noma baɗi. Yana ma iya daɗa girman filin da yake nomewa. Zai shuka iri ko da ya san cewa zai jira har sai lokacin girbi kuma ya tabbata cewa zai samu amfani. Hakazalika, idan mun koyi dokokin Jehobah, mun bi su kuma mun samu sakamako masu kyau, za mu daɗa dogara da kuma yin imani da shi. Da hakan, zai fi kasance mana da sauƙi mu yi haƙuri kuma mu jira har sai Jehobah ya albarkace mu kamar yadda ya yi alkawari.—Karanta Yaƙub 5:7, 8.

14, 15. Wane irin ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi game da wahalar da ’yan Adam suke sha?

14 Wani abu kuma da zai taimaka mana mu daɗa yin haƙuri shi ne yin tunani a kan yadda ya kamata mu ɗauki duniyar nan da kuma yanayinmu. Ya kamata mu kasance da ra’ayin Jehobah. Alal misali, ka yi tunani a kan yadda yake ɗaukar wahalar da muke sha. Tun da daɗewa, Jehobah ya ga yadda ’yan Adam suke shan wahala kuma hakan na sa shi baƙin ciki, amma bai ƙyale hakan ya hana shi yin nagarta ba. Ya aiko da Ɗansa don “ya halaka ayyukan Shaiɗan” kuma ya cire dukan wahalar da Shaiɗan yake haddasa wa ’yan Adam. (1 Yoh. 3:8) Amma tabbas, nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai cire dukan wahalar da muke sha har abada. Saboda haka, bai kamata mu ƙyale muguntar da ke faruwa a wannan duniyar ta raunana bangaskiyarmu ba. Bai kamata mu yi rashin haƙuri a kan lokacin da Jehobah zai ɗauki mataki ba. Ya kamata mu yi imani da alkawuran Allah. Jehobah ya riga ya ƙayyade lokacin da zai cire mugunta kuma zai yi hakan idan lokacin ya kai.—Isha. 46:13; Nah. 1:9.

15 A waɗannan kwanaki na ƙarshe masu wuya sosai, za mu bukaci jimrewa da wasu gwaje-gwaje ga bangaskiyarmu. Mu ko waɗanda muke ƙauna za su iya shan wahala saboda nuna ƙarfi ko kuma wasu matsaloli. Idan hakan ya faru, bai kamata mu yi fushi ba, amma ya kamata mu duƙufa cewa za mu dogara ga Jehobah sosai. Ba shi da sauƙi mu yi hakan domin mu ajizai ne. Amma, kada ka manta da abin da littafin Matta 26:39 ya ce Yesu ya yi.—Karanta.

16. Yayin da muke jiran ƙarshe ya zo, mene ne bai kamata mu yi ba?

16 Mutumin da yake shakka cewa ƙarshe ya kusa zai iya soma samun ra’ayi marar kyau. Zai iya yin tunani cewa Jehobah zai iya kasa cika alkawuransa, kuma don hakan sai ya soma shirya wasu abubuwa da za su taimake shi idan hakan ya faru. Zai iya yin tunani cewa, ‘Bari mu ga ko Jehobah zai cika alkawuransa.’ Kuma wannan mugun ra’ayi zai iya hana shi yin haƙuri. A sakamako, zai iya ƙoƙarta don ya zama sananne a duniya ko kuma ya soma dogara ga kuɗi kuma ya daina saka Mulkin Allah farko a rayuwarsa. Ko zai iya soma makarantar jami’a don kada ya sha wahala a nan gaba. Amma, hakan rashin imani ne. Ka tuna cewa Bulus ya aririce mu mu yi koyi da waɗanda suke da “bangaskiya da haƙuri,” kuma hakan ya sa sun more albarkar da Jehobah ya yi musu alkawari. (Ibran. 6:12) Jehobah ya riga ya ce zai halaka wannan muguwar duniyar kuma ba zai fasa yin hakan ba. (Hab. 2:3) Amma kafin Jehobah ya ɗauki mataki, ya kamata mu sa ƙwazo sosai a yin ayyukansa. Ya kamata mu tuna cewa muna zaune ne a kwanaki na ƙarshe kuma hakan ya kamata ya motsa mu mu yi wa’azi da ƙwazo sosai. Wannan aikin yana sa mu farin ciki sosai a yau.—Luk 21:36.

WACE ALBARKA CE KE TATTARE DA KASANCEWA DA HAƘURI?

17, 18. (a) Wane zarafi ne muke da shi yanzu da muke jimrewa? (b) Idan mun kasance masu haƙuri, wace albarka ce za mu more?

17 Idan mun bauta wa Jehobah na ’yan watanni ko kuma mun yi shekaru da yawa muna hakan, ya kamata mu bauta masa har abada. Ko da shekaru nawa ne ya rage kafin Jehobah ya halaka wannan mugun zamanin, idan muna da haƙuri za mu iya jimrewa. A yanzu, Jehobah yana ba mu zarafin nuna cewa muna dogara ga shawarwarinsa baki ɗaya kuma za mu kasance da aminci ko da za mu sha wahala. (1 Bit. 4:13, 14) Allah yana kuma koyar da mu don mu iya jimrewa har ƙarshe kuma mu samu ceto.—1 Bit. 5:10.

18 Jehobah ya ba Yesu iko bisa sama da duniya kuma babu kome da zai iya hana shi kāre ka idan ka kasance da aminci. (Yoh. 10:28, 29) Ba ka bukatar jin tsoron mutuwa ko kuma abin da zai faru gobe. Waɗanda suka jimre har ƙarshe za su samu ceto. Saboda haka, kada mu taɓa ƙyale duniyar nan ta rinjaye mu har mu daina dogara ga Jehobah. Maimakon haka, ya kamata mu duƙufa cewa za mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu yi amfani da lokacinmu daidai wa daida.—Mat. 24:13; karanta 2 Bitrus 3:17, 18.

[Hotona a shafi na 21]

Haƙuri zai taimaka maka ka saka Mulkin Allah farko a rayuwarka kuma ka samu albarka!

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba