Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 2/1 pp. 13-17
  • Ka Yi Koyi Da Haƙurin Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Koyi Da Haƙurin Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi La’akari da Haƙurin Jehobah
  • Ka Yi Koyi da Haƙurin Annabawa
  • “Jimrewar Ayuba”
  • ‘Ranar Jehobah Za Ta Zo’
  • Ka Koyi Darasi Daga Haƙurin Jehobah Da Na Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Ci Gaba da Zama Mai Hakuri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Muna Bukatar Haƙuri a Hidimarmu
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Haƙuri Yana Sa Mu Kasance da Bege
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 2/1 pp. 13-17

Ka Yi Koyi Da Haƙurin Jehobah

“Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zancen alkawarinsa . . . amma mai-haƙuri ne.”—2 BITRUS 3:9.

1. Wace kyauta ce da babu na biyunta Jehobah ya ba ’yan adam?

JEHOBAH ya ba mu abin da ba wanda zai iya ba mu. Abu ne mai kyau ƙwarai da kuma tamani, duk da haka ba za a iya sayensa ba. Kyautar rai madawwami ne yake bayarwa, wato rayuwa marar iyaka a cikin aljanna a duniya. (Yohanna 3:16) Wannan abin farin ciki ne! Abubuwa da ke kawo baƙin ciki, jayayya, mugunta, talauci, aikata laifi, ciwo, har da mutuwa ba za su ƙara kasancewa ba. Mutane za su yi rayuwa cikin cikakkiyar salama da haɗin kai a ƙarƙashin Mulkin Allah da ke sarauta cikin ƙauna. Muna begen wannan Aljannar ƙwarai!—Ishaya 9:6, 7; Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.

2. Me ya sa Jehobah tukuna bai kawar da zamanin Shaiɗan ba?

2 Jehobah shi ma yana sauraron lokacin da zai kafa Aljanna a duniya. Ballantana ma, yana ƙaunar adalci da gaskiya. (Zabura 33:5) Ba ya jin daɗin ganin duniya da ba ta bin mizanansa na adalci, duniya da ke ƙin ikonsa da kuma tsananta wa mutanensa. Duk da haka, da dalilai masu kyau da ya sa bai aikata ba tukuna don ya kawar da tsarin Shaiɗan. Waɗannan dalilai sun ƙunshi batun ɗabi’a game da ikon mallakarsa. Don ya sasanta waɗannan batutuwa, Jehobah ya nuna hali mai kyau, da mutane da yawa a yau ba sa nunawa, wato, haƙuri.

3. (a) Menene kalmomin Helenanci da na Ibrananci da aka fassara “haƙuri” a cikin Littafi Mai Tsarki suke nufi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika yanzu?

3 Da akwai kalmar Helenanci da aka fassara sau uku “haƙuri” a cikin New World Translation. A zahiri tana nufin “dogon ruhu” da haka sau da yawa ana fassara ta “tsawon jimrewa” sau ɗaya kuma “haƙuri.” Kalmomin Helenanci da Ibrananci da aka fassara “haƙuri” sun ƙunshi jimiri da jinkirin fushi. Ta yaya muke amfana don haƙurin Jehobah? Waɗanne darussa za mu koya daga haƙuri da kuma jimirin Jehobah da na bayinsa masu aminci? Ta yaya muka sani cewa haƙurin Jehobah ba shi da iyaka? Bari mu bincika batun.

Ka Yi La’akari da Haƙurin Jehobah

4. Menene manzo Bitrus ya rubuta game da haƙurin Jehobah?

4 Game da haƙurin Jehobah manzo Bitrus ya rubuta: “Ƙaunatattu, kada ku manta da wannan abu guda, rana ɗaya a wurin Ubangiji kamar shekara dubu ce, shekara dubu kuma kamar rana ɗaya ne. Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zancen alkawarinsa, yadda waɗansu mutane su ke aza jinkiri; amma mai-haƙuri ne zuwa gareku, ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.” (2 Bitrus 3:8, 9) Don Allah ka lura da darussa biyu da aka nuna a nan da zai iya taimaka mana mu fahimci haƙurin Jehobah.

5. Ta yaya yadda Jehobah yake ɗaukan lokaci ya shafi ayyukansa?

5 Darassi na farko shi ne cewa Jehobah ba ya ɗaukan lokaci yadda muke yi. Shekara dubu rana ɗaya ce a gare shi wanda ke raye har abada abadin. Lokaci ba ya ƙure masa ko kuma hana shi yin abu, kuma ba ya jinkirin yin wani abu. Da yake mai hikima ne marar iyaka, Jehobah ya san lokacin da ya fi kyau ya aikata don amfanin dukan waɗanda abin ya shafa, kuma ta yin haƙuri yana jiran lokacin ya kai. Amma, bai kamata mu kammala cewa Jehobah ba ya damuwa da kowace wahala da bayinsa suke fuskanta a yanzu ba. Allah ne mai “jinƙai mai-taushi,” shi ƙauna ne. (Luka 1:78; 1 Yohanna 4:8) Yana iya kawar da kowane lahani da wannan wahalar da ya ƙyale na ɗan lokaci ya kawo gabaki ɗaya da kuma dindindin.—Zabura 37:10.

6. Menene bai kamata mu kammala ba game da Allah, kuma me ya sa?

6 Hakika ba shi da sauƙi mutum ya jira abin da yake begensa. (Misalai 13:12) Shi ya sa sa’ad da mutane ba su cika alkawarinsu da sauri ba, wasu suna iya kammala cewa ba su da niyyar yin abin. Bai kamata mu yi tunani cewa Allah zai yi hakan ba! Idan muna tunanin cewa Allah yana jinkiri domin haƙurinsa, shigewar lokaci zai sa mu yi shakka da kuma sanyin gwiwa, kuma wannan zai sa mu yi rashin ƙwazo a ruhaniya. Mafi muni ma, masu ba’a da marasa bangaskiya da Bitrus ya yi mana gargaɗi da farko game da su suna iya yaudararmu. Irin waɗannan suna ba’a suna cewa: “Ina alkawarin tafowassa? gama, tun daga randa ubanni suka kwanta barci, dukan al’amura suna nan kamar yadda su ke tun farkon halitta.”—2 Bitrus 3:4.

7. Ta yaya haƙurin Jehobah yake da nasaba da son mutane su tuba?

7 Darassi na biyu da za mu koya daga kalmomin Bitrus shi ne cewa Jehobah yana haƙuri domin yana son dukan mutane su tuba. Jehobah zai halaka waɗanda suka ƙi barin mugayen hanyoyinsu. Amma Allah ba ya jin daɗin mutuwar mugu. Maimakon haka, yana jin daɗin ganin mutane sun tuba, sun bar mugayen hanyoyinsu, kuma su ci gaba da rayuwa. (Ezekiel 33:11) Shi ya sa yake haƙuri, yana sa a yi shelar bishara a dukan duniya don mutane su sami zarafin rayuwa.

8. Menene za mu koya game da haƙurin Allah ta wajen bincika sha’aninsa da al’ummar Isra’ila?

8 Za mu iya koya game da haƙurin Allah a sha’aninsa da al’ummar Isra’ila na dā. Ƙarnuka da yawa, ya jimre da rashin biyayyarsu. Sau da yawa, ya aririce su ta wurin annabawansa: “Ku juyo ga barin miyagun ayyukanku, ku kiyaye dokokina da farillaina, bisa ga dukan shari’a da na umurci ubanninku, shari’a kuma da na aika maku da ita ta hannun bayina annabawa.” Menene sakamakon? Abin baƙin ciki, mutanen “suka ƙi ji.”—2 Sarakuna 17:13, 14.

9. Ta yaya Yesu ya nuna haƙuri kamar Ubansa?

9 A ƙarshe Jehobah ya aiko da Ɗansa wanda ya ci gaba da roƙon Yahudawa su sulhunta da Allah. Yesu ya yi haƙuri kamar Ubansa. Da yake ya san cewa ba da daɗewa ba za a kashe shi, Yesu ya ce: “Ya Urushalima, Urushalima, wanda ki ke kisan annabawa, kina jejjefe waɗanda an aiko a gareki! So nawa ina so in tattara ’ya’yanki, kamar yadda kaza ta kan tattara ’yan tsākinta ƙarƙashin fikafikanta, amma ba ku yarda ba!” (Matta 23:37) Alƙali marar tausayi da yake neman ya hukunta wani ba zai furta waɗannan kalmomi masu ban tausayi ba amma sai aboki mai ƙauna da yake haƙuri da mutane. Kamar Ubansa a sama, Yesu yana son mutane su tuba kuma su tsira wa hukunci mai tsanani. Wasu sun yi biyayya da gargaɗin Yesu kuma suka tsira wa hukunci da aka yi wa Urushalima a shekara ta 70 A.Z.—Luka 21:20-22.

10. Ta yaya muka amfana da haƙurin Allah?

10 Hakika haƙurin Allah abin ban mamaki ne. Duk da yawan rashin biyayyar ’yan adam, Jehobah ya ba mu zarafi mu san shi kuma mu sami begen ceto tare da sauran mutane biliyoyi. Bitrus ya rubuta wa Kiristoci ’yan’uwa: “Ku maida jimrewar Ubangijinmu ceto.” (2 Bitrus 3:15) Bai kamata mu yi godiya ba cewa haƙurin Jehobah ya ba mu zarafin samun ceto? Ba ma yin addu’a cewa Jehobah ya ci gaba da haƙuri da mu yayin da muka ci gaba da bauta masa kowace rana?—Matta 6:12.

11. Idan mun fahimci haƙurin Jehobah menene wannan zai motsa mu mu yi?

11 Sa’ad da muka fahimci dalilin da ya sa Jehobah ke haƙuri, wannan zai taimake mu mu jira ceto da zai kawo cikin haƙuri, ba za mu kammala ba cewa yana jinkirin cika alkawarinsa. (Makoki 3:26) Yayin da muka ci gaba da yin addu’a Mulkin Allah ya zo, mun gaskata cewa Allah ya san lokacin da ya fi kyau ya amsa wannan addu’a. Bugu da ƙari, za mu motsa mu yi koyi da Jehobah ta wajen nuna haƙurinsa a sha’aninmu da ’yan’uwanmu da kuma waɗanda muke wa wa’azi. Mu ma ba ma son a hallaka kowa amma za mu so mu ga mutane sun tuba kuma kamar mu su sami begen rai madawwami.—1 Timothawus 2:3, 4.

Ka Yi Koyi da Haƙurin Annabawa

12, 13. Ta yaya annabi Ishaya ya yi nasara wajen yin haƙuri?

12 Ta wajen yin la’akari da haƙurin Jehobah, an taimake mu mu san amfanin wannan halin kuma mu koyi nuna shi. Ba shi da sauƙi ’yan adam ajizai su yi haƙuri, amma za a iya yin hakan. Za mu iya koya daga bayin Allah na dā. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “ ’Yan’uwa, ku lura da annabawa waɗanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, su zama gurbi gareku na shan wahala da na haƙuri.” (Yaƙub 5:10) Yana sanyaya zuciya da kuma ban ƙarfafa idan muka san cewa wasu sun sha kan matsaloli kamar waɗanda muke fuskanta.

13 Alal misali, annabi Ishaya ya bukaci ya yi haƙuri a aikinsa. Jehobah ya nuna wannan sa’ad da ya gaya masa: “Je ka, ka faɗa ma al’umman nan, Sai ku ji, ku dosa ji, amma kada ku fahimta; sai ku gani ku riƙa gani, amma kada ku gāne. Ka sa zuciyar al’umman nan ta yi kitse, a nawaitadda kunnuwansu, a rufe idanunsu; domin kada su gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su gane da zuciyarsu, su juyo, su warke kuma.” (Ishaya 6:9, 10) Duk da taurin kan mutanen, Ishaya da haƙuri ya sanar da su saƙon gargaɗi na Jehobah, har tsawon shekara 46! Hakanan ma, haƙuri zai taimake mu mu jimre a aikinmu na wa’azin bishara, ko da mutane da yawa ba sa saurarawa.

14, 15. Menene ya taimaki Irmiya ya jimre da wahala da sanyin gwiwa?

14 Hakika, sa’ad da annabawan suke yin hidimarsu, sun jimre wa rashin saurarawa kuma an tsananta musu. An saka Irmiya cikin turu, an sa shi cikin “kurkuku,” kuma aka jefa shi cikin rami. (Irmiya 20:2; 37:15; 38:6) Mutanen da yake son ya taimake su, su suka sa shi cikin wannan wahalar. Duk da haka, Irmiya bai yi baƙin ciki ba, ko kuma ya rama. Ya jimre shekaru da yawa.

15 Tsanantawa da ba’a ba su sa Irmiya ya daina aikinsa ba, kuma ba za su sa mu daina a yau ba. Hakika, a wani lokaci muna iya yin sanyin gwiwa. Irmiya ya yi sanyin gwiwa. Ya rubuta: “An maida maganar Ubangiji abin zargi ne, abin reni ne a kaina, dukan yini. Idan kuwa na ce, ba ni ambatonsa, ba ni ƙara faɗin magana cikin sunansa.” Menene ya faru? Irmiya ya daina wa’azi ne? Ya ci gaba: “Sai cikin zuciyata [kalmar Allah] in ji kamar wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwana, in gaji kuma da haƙuri, in kasa jimrewa.” (Irmiya 20:8, 9) Ka lura cewa sa’ad da ya mai da hankali game da ba’ar mutane, ya yi rashin farin cikinsa. Sa’ad da ya mai da hankalinsa ga kyan saƙon da kuma muhimmancinsa, sai ya sabonta farin cikinsa. Ƙari ga haka, Jehobah yana tare da Irmiya “ƙaƙarfa ne mai-ban tsoro,” yana ƙarfafa shi ya yi shelar kalmar Allah da himma da kuma gaba gaɗi.—Irmiya 20:11.

16. Ta yaya za mu ci gaba da farin ciki a aikinmu na yin wa’azin bishara?

16 Annabi Irmiya ya yi farin ciki ne a aikinsa? Babu shakka! Ya ce wa Jehobah: “Aka iske maganarka, na kuwa ci su: zantattukanka sun zama mani murna da farinciki na zuciyata: gama an kira ni da sunanka, ya Ubangiji.” (Irmiya 15:16) Irmiya ya yi farin ciki da gatarsa na wakiltar Allah na gaskiya da kuma wa’azin kalmarsa. Mu ma za mu iya farin ciki. Ballantana ma, muna farin ciki kamar mala’iku a sama cewa a dukan duniya mutane da yawa sun saurari saƙon Mulki, sun tuba kuma suna kan hanyar samun rai madawwami.—Luka 15:10.

“Jimrewar Ayuba”

17, 18. Ta yaya Ayuba ya jimre, menene sakamakon?

17 Bayan ya yi maganar annabawa na dā, almajiri Yaƙub ya rubuta: “Kun ji labarin jimrewar Ayuba, kun ga ƙarkon Ubangiji kuma, Ubangiji da shi ke cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.” (Yaƙub 5:11) Kalmar Helenanci da aka fassara “jimrewa” a nan tana nufin “haƙuri,” wadda ta yi daidai da kalmar da Yaƙub ya yi amfani da ita a cikin ayar da ta gabata. Da yake nuna bambanci tsakanin kalmomin biyu, wani manazarci ya rubuta: “Ɗayan haƙuri ne sa’ad da mutum ya zage mu, ɗayan kuma jimrewa ne sa’ad da muke cikin yanayi mai wuya.”

18 Ayuba ya fuskanci wahala sosai. Ya yi rashin dukiyarsa, rashin yaransa, ya yi mugun ciwo. Ya jimre wa zargin ƙarya cewa Jehobah ne yake yi masa horo. Ayuba bai yi shuru ba sa’ad da yake wahala; ya yi baƙin cikin yanayinsa har da ma cewa ya fi Allah adalci. (Ayuba 35:2) Amma, bai yi rashin bangaskiya, ko kuwa ya karya amincinsa ba. Bai zagi Allah ba yadda Shaiɗan ya ce zai yi. (Ayuba 1:11, 21) Menene sakamakon? Jehobah “ya albarci ƙarshen Ayuba, har ya fi farkonsa.” (Ayuba 42:12) Jehobah ya warkar da Ayuba, ya ninka dukiyarsa, ya albarkace shi da cikakkiyar rayuwa na farin ciki da ƙaunatattunsa. Ayuba ya fahimci Jehobah sosai domin ya jimre cikin aminci.

19. Menene muka koya daga jimirin Ayuba?

19 Menene muka koya daga jimirin Ayuba? Kamar Ayuba, muna iya yin ciwo ko mu fuskanci wasu matsaloli. Mai yiwuwa ba za mu fahimci abin da ya sa Jehobah ya ƙyale mu muna wahalar wani gwaji ba. Duk da haka, mun tabbata da abu ɗaya: Idan mun kasance da aminci zai albarkace mu. Jehobah ba ya fasa saka wa waɗanda suke nemansa. (Ibraniyawa 11:6) Yesu ya ce: “Wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.”—Matta 10:22; 24:13.

‘Ranar Jehobah Za Ta Zo’

20. Me ya sa muka tabbata cewa ranar Jehobah za ta zo?

20 Ko da Jehobah mai haƙuri ne, shi adali ne kuma ba zai bar mugunta har abada ba. Haƙurinsa yana da iyaka. Bitrus ya rubuta: “[Allah] ba ya kuwa keɓe duniya ta dā ba.” Ko da an ceci Nuhu da iyalinsa, an kawo rigyawa bisa wannan duniya ta masu fajirci. Jehobah ya kuma zartar da hukunci a kan Saduma da Gwamrata, ya mai da su toka. An mai da waɗannan hukunci abin “nuni ga waɗanda za su yi zaman fajirci.” Mun tabbata cewa: ‘ranar Jehobah . . . za ta zo.’—2 Bitrus 2:5, 6; 3:10.

21. Ta yaya za mu nuna haƙuri da jimiri, wane batu ne za mu bincika a talifi na gaba?

21 Bari mu yi koyi da haƙurin Jehobah ta wajen taimakon wasu su tuba domin a cece su. Bari mu yi koyi da annabawa ta yin shelar bishara cikin haƙuri ko da wasu cikin waɗanda muke wa wa’azi ba za su saurara ba. Bugu da ƙari, idan kamar Ayuba mun jimre wa gwaji, mu tabbata cewa Jehobah zai albarkace mu sosai idan mun kasance da aminci. Muna da dalilin yin farin ciki a hidimarmu idan muka lura da yadda Jehobah yake yi wa mutanensa albarka a ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na yin wa’azi a dukan duniya. Za mu ga wannan a talifi na gaba.

Ka Tuna?

• Me ya sa Jehobah yake haƙuri?

• Menene muka koya daga haƙurin annabawa?

• Ta yaya Ayuba ya nuna jimiri, menene sakamakon?

• Ta yaya muka sani cewa haƙurin Jehobah yana da iyaka?

[Hoto a shafi na 14]

Yesu ya nuna haƙurin Ubansa sosai

[Hotuna a shafi na 16]

Ta yaya Jehobah ya yi wa Irmiya albarka don haƙurinsa?

[Hotuna a shafi na 17]

Ta yaya Jehobah ya saka wa Ayuba don jimirinsa?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba