Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 6/11 p. 1
  • Muna Bukatar Haƙuri a Hidimarmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Muna Bukatar Haƙuri a Hidimarmu
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Koyi Da Haƙurin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Koyi Darasi Daga Haƙurin Jehobah Da Na Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yadda Za Ka Zama Mai Hakuri
    Taimako don Iyali
  • Ka Ci Gaba da Zama Mai Hakuri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 6/11 p. 1

Muna Bukatar Haƙuri a Hidimarmu

1. Ta yaya Jehobah ya yi haƙuri da ’yan Adam?

1 Allah yana yin haƙuri sosai da ’yan Adam. (Fit. 34:6; Zab. 106:41-45; 2 Bit. 3:9) Misali ɗaya na musamman na haƙurinsa shi ne aikin wa’azin Mulki da ake yi a dukan duniya. Jehobah yana haƙuri da ’yan Adam kusan shekaru dubu biyu, duk da haka ya ci gaba da jawo mutane da suke son su ƙulla dangantaka da shi. (Yoh. 6:44) Ta yaya za mu iya yin koyi da haƙurin Jehobah a hidimarmu?

2. Ta yaya za mu yi haƙuri sa’ad da muke hidima a yankinmu?

2 Hidimar Gida Zuwa Gida: Muna yin koyi da haƙurin Jehobah ta wajen yin wa’azi ‘ba fasawa’ a yankin da mutane ba su so saƙon tukuna ba. (A. M. 5:42) Muna jimrewa da rashin so da ba’a da kuma hamayya a hidimarmu. (Mar. 13:12, 13) Muna kuma yin haƙuri ta wajen nacewa a ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na koma ziyara ko a lokacin da yake da wuya mu samu waɗanda suke son saƙonmu a gida.

3. Me ya sa ake bukatar haƙuri sa’ad da ake koma ziyara da kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki?

3 Nazarin Littafi Mai Tsarki: Sa shuki ya yi girma yana bukatar haƙuri. Muna iya kula da shi, amma ba za mu iya hanzarta girmansa ba. (Yaƙ. 5:7) Haka nan ma, wannan girma ta ruhaniya tana somawa da sannu-sannu kuma a lokaci dabam dabam. (Mar. 4:28) Zai iya kasance wa waɗanda muke nazari da su wuya su yi watsi da imanin ƙarya ko kuma al’adu da suka saɓa wa nassi. Bai dace mu sa ɗalibanmu su samu ci gaba ta wurin matsa musu su yi canje-canje ba. Muna bukatar haƙuri don ruhun Allah ya yi aiki a zuciyar ɗalibinmu.—1 Kor. 3:6, 7.

4. Ta yaya haƙuri zai iya taimaka mana mu ba da shaida sosai ga dangogin mu da ba masu bi ba ne?

4 Dangogin da Ba Masu Bi Ba Ne: Ko da yake muna ɗoki sosai cewa dangogin mu da ba masu bi ba ne su koyi gaskiya, muna nuna haƙuri ta jiran lokacin da ya dace don mu tattauna abin da muka gaskata da su, muna mai da hankali don kada mu cika su da bayanai da yawa. (M. Wa. 3:1, 7) Amma ya kamata mu sa halinmu ya rinjaye su kuma mu kasance a shirye mu tattauna imaninmu da su da ladabi da kuma bangirma. (1 Bit. 3:1, 15) Hakika, yin hidima cikin haƙuri zai fi ba da amfani kuma zai faranta ran Ubanmu na samaniya.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba