Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 6/15 pp. 12-16
  • “Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DALILIN DA YA SA ZA MU IYA ƘAUNAR ALLAH
  • ABIN DA ƘAUNAR ALLAH YA ƘUNSA
  • DALILIN DA YA SA ZA MU ƘAUNACI JEHOBAH
  • YADDA ZA MU NUNA CEWA MUNA ƘAUNAR ALLAH
  • KA CI GABA DA KYAUTATA ƘAUNARKA GA ALLAH
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Kada Ku Bar Ƙaunar da Kuke wa Juna ta yi Sanyi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 6/15 pp. 12-16

Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka

“Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.”—MAT. 22:37.

MECE CE AMSARKA?

  • Mece ce ƙaunar Allah ta ƙunsa?

  • Me ya sa ya kamata mu ƙaunaci Jehobah?

  • Ta yaya za mu iya nuna ƙaunarmu ga Jehobah Allah?

1. Ta yaya dangantakar da ke tsakanin Yesu da Ubansa ta daɗa sa su ƙaunar juna?

YESU ya kwatanta dangantakarsa da Jehobah sa’ad da ya ce: “Ina ƙaunar Uba.” (Yoh. 14:31) Ya ƙara da cewa: “Uban yana ƙaunar Ɗan.” (Yoh. 5:20) Shin hakan abin mamaki ne? A’a. Me ya sa? Domin Yesu ya rayu a sama a matsayin “gwanin mai-aiki” na Allah shekaru da yawa kafin ya zo duniya. (Mis. 8:30) Da yake Yesu da Jehobah sun yi aiki tare, ya koyi halayen Uban kuma hakan ya sa ya daɗa ƙaunarsa. Hakika, dangantakarsu ta kud da kud ta sa sun daɗa ƙaunar juna.

2. (a) Mece ce ƙauna ta ƙunsa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

2 Idan kana ƙaunar wani, kana son mutumin sosai. Dauda, marubucin zabura ya ce: “Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.” (Zab. 18:1) Kamar marubucin zabura, ya kamata mu ƙaunaci Allah, da yake yana ƙaunarmu sosai. Idan muka yi masa biyayya, zai ƙaunace mu. (Karanta Kubawar Shari’a 7:12, 13.) Amma zai yiwu mu ƙaunaci Allah ne da yake ba ma ganinsa? Mene ne ƙaunar Allah ya ƙunsa? Me ya sa za mu ƙaunace shi? Kuma ta yaya za mu nuna muna ƙaunar Allah?

DALILIN DA YA SA ZA MU IYA ƘAUNAR ALLAH

3, 4. Me ya sa zai yiwu mu iya ƙaunar Jehobah?

3 Da yake “Allah ruhu ne,” ba za mu iya ganinsa ba. (Yoh. 4:24) Duk da haka, za mu iya ƙaunar Allah don Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi hakan. Alal misali, Musa ya gaya wa Isra’ilawa: ‘Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.’ —K. Sha 6:5.

4 Me ya sa za mu iya ƙaunar Allah sosai? Domin Allah ya halicce mu a hanyar da za mu riƙa son Kalmarsa da kuma ƙaunar mutane. Sa’ad da muka san Allah da kyau, ƙaunarmu za ta daɗa ƙaruwa kuma hakan zai sa mu farin ciki sosai. Yesu ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah, domin za su gāji mulkin sama.” (Mat. 5:3, New World Translation) Littafin nan mai suna Man Does Not Stand Alone ya ce: “Abin mamaki ne ka ga cewa mutane a faɗin duniya a kullum suna nema da kuma son su gaskata da Allah.” Mutane da yawa suna kamar wannan marubucin domin sun fahimci cewa an halicce mutane don su bauta wa Allah.

5. Ta yaya muka gane cewa za mu iya sanin Allah?

5 Zai yiwu ne mu san Allah? E zai yiwu don yana son mu kasance da dangantaka mai kyau da shi. Manzo Bulus ya bayyana cewa hakan zai yiwu a lokacin da yake magana da wasu mutane a birnin Atina. Da yawa daga cikinsu sun yi tsammani cewa zai dace su je haikali don su bauta wa allahiyar Atina. Amma Bulus ya gaya musu cewa za su iya samun Allah na gaskiya “wanda ya yi duniya da abin da ke ciki duka.” Ya bayyana cewa Allah ba ya zama a haikalin da aka yi da hannuwa. Kuma mutanen da suke nemansa za su iya samunsa ko da a ina suke da zama. Sai daga baya ya ce: Allah “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.” (A. M. 17:24-27) Hakika, zai yiwu mu san Allah. Shaidun Jehobah fiye da miliyan ɗaya da rabi sun “same shi” kuma suna ƙaunarsa da gaske.

ABIN DA ƘAUNAR ALLAH YA ƘUNSA

6. Wace doka ce “babbar doka” kuma ta fari?

6 Ƙaunar da muke yi wa Allah ya kamata ya zama da zuciya ɗaya. Yesu ya bayyana wannan sa’ad da wani Ba-Farisi ya tambaye shi: “Malam, wace ce babbar doka a cikin Attaurat?” Yesu ya gaya masa: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari.”—Mat. 22:34-38.

7. Me yake nufi mu ƙaunaci Allah da (a) ‘dukan zuciyarmu’? (b) ‘dukan ranmu.’ (c) ‘dukan azancinmu’?

7 Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce mu ƙaunaci Allah da ‘dukan zuciyarmu’? Yana nufin cewa mu ƙaunaci Jehobah da zuciya ɗaya, wato da sha’awarmu da tunaninmu da motsin ranmu. Wajibi ne mu ƙaunace shi da ‘dukan ranmu,’ wato da dukan ƙarfinmu. Ƙari ga haka, ya kamata mu ƙaunace shi da ‘dukan azancinmu.’ Ma’ana, ana son mu bauta wa Jehobah babu fashi.

8. Ta yaya za mu nuna muna ƙaunar Allah?

8 Idan muna ƙaunar Allah da dukan zuciyarmu da ranmu da kuma azancinmu, za mu riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ƙwazo. Ƙari ga haka, za mu bauta masa da zuciya ɗaya kuma za mu yi wa’azin bishara ta Mulkin da himma. (Mat. 24:14; Rom. 12:1, 2) Za mu kusaci Jehobah idan muna ƙaunarsa da gaske. (Yaƙ. 4:8) Hakika, ba zai yiwu mu lissafta dukan dalilan da muke da su na bauta wa Allah ba. To, bari mu bincika wasu daga cikin waɗannan dalilan.

DALILIN DA YA SA ZA MU ƘAUNACI JEHOBAH

9. Me ya sa muke ƙaunar Jehobah a matsayin Mahaliccinmu da kuma Mai mana tanadi?

9 Jehobah ne mahaliccinmu kuma shi ne mai mana tanadi. Bulus ya ce: “Gama cikinsa mu ke rayuwa, mu ke motsi, mu ke zamanmu.” (A. M. 17:28) Jehobah ne ya tanadar mana da duniya mai kyau da muke rayuwa a ciki. (Zab. 115:16) Yana yi mana tanadin abinci da wasu abubuwan da muke bukata a rayuwa. Saboda haka, Bulus ya gaya wa mutanen Listra cewa “Allah mai-rai, . . . ba ya bar kansa babu shaida ba, da shi ke yana yin alheri, yana ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi, yana cika zukatanku da abinci da farin ciki.” (A. M. 14:15-17) Wannan dalili ne ya sa muke ƙaunar Mahaliccinmu wanda ke yi mana tanadi, ko ba haka ba?—M. Wa. 12:1.

10. Mene ne ya kamata mu yi don tanadin da Allah ya yi mana na kawar da zunubi da kuma mutuwa?

10 Allah ya yi tanadi don kawar da zunubi da mutuwa da muka gāda daga Adamu. (Rom. 5:12, 8) Hakika, “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da yake, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:12, 8) Babu shakka, idan muka tuba da gaske kuma muka ba da gaskiya ga fansar, Allah zai gafarta mana zunubanmu. Muna ƙaunar Allah sosai don shi ne ya aiko da Ɗansa ya mutu domin mu.—Yoh. 3:16.

11, 12. Wane bege ne Jehobah ya saka a gabanmu?

11 Jehobah na ba da begen da ke sa mu “farin ciki da salama.” (Rom. 15:13, Littafi Mai Tsarki) Begen da Allah ya sa gabanmu yana sa mu jimre gwajin bangaskiyarmu. Za a ba shafaffun da suka kasance da ‘aminci har mutuwa, rawanin rai’ a sama. (R. Yoh. 2:10) Waɗanda suke da begen zama a duniya da suka kasance da aminci za su more rayuwa a Aljannar da Allah ya yi alkawarin ta. (Luk 23:43) Yaya muke ji game da wannan begen da aka saka a gabanmu? Wannan begen yana sa mu kasance da farin ciki da salama kuma yana sa mu ƙaunaci Wanda yake ba da “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta.”—Yaƙ. 1:17.

12 Allah ya yi mana alkawarin tashin matattu. (A. M. 24:15) Ko da yake muna baƙin ciki sosai sa’ad da wani wanda muke ƙauna ya mutu, begen tashin matattu yana sa ba ma “baƙinciki, kamar sauran mutane, waɗanda ba su da bege.” (1 Tas. 4:13) Domin ƙaunar da Allah Jehobah yake mana, zai ta da waɗanda suka mutu musamman ma masu aminci kamar Ayuba. (Ayu. 14:15) Za mu yi farin ciki sosai sa’ad da aka ta da matattu don su yi rayuwa a nan duniya. Muna ƙaunar Ubanmu na sama sosai saboda begen tashin matattun da ya ba mu!

13. Wane tabbaci muke da shi cewa Jehobah yana kula da mu da gaske?

13 Jehobah yana kula da mu da gaske. (Karanta Zabura 34:6, 18, 19; 1 Bitrus 5:6, 7.) Da yake mun san cewa Allah yana ƙaunarmu kuma yana son taimaka wa mutanen da suke da aminci a gare shi, ba ma tsoron kome don mu ‘tumakin garkensa’ ne. (Zab. 79:13) Ƙari ga haka, Allah zai bayyana ƙaunarsa ta wurin abubuwan da Mulkin Almasihun zai cim ma. Bayan Yesu Kristi ya kawo ƙarshen mugunta da zalunci da kuma aika laifi, mutane masu biyayya za su yi zaman lafiya da ni’ima. (Zab. 72:7, 12-14, 16) Idan muka yi bimbini a kan waɗannan alkawuran, hakan zai sa mu ƙaunaci Allah da dukan zuciyarmu da ranmu da kuma azancinmu, ko ba haka ba?—Luk 10:27.

14. Wane babban gata ne Jehobah ya ba mu?

14 Jehobah ya ba mu babban gata na zama Shaidunsa. (Isha. 43:10-12) Muna ƙaunar Allah don damar da ya ba mu na goyon bayan sarautarsa da kuma taimaka wa mutanen wannan muguwar duniyar su kasance da bege na ainihi. Ƙari ga haka, za mu iya yin wa’azi da gaba gaɗi don muna shelar bisharar Kalmar Allah wanda a kullum yana sa alkawuransa su tabbata. (Karanta Joshua 21:45; 23:14.) Hakika, ba za mu iya ƙirga dalilai masu yawa da muke da su na ƙaunar Jehobah ba. Amma ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunarsa da gaske?

YADDA ZA MU NUNA CEWA MUNA ƘAUNAR ALLAH

15. Ta yaya nazari da kuma bin Kalmar Allah zai taimake mu?

15 Ka riƙa yin nazarin Kalmar Allah a koyaushe kuma ka yi amfani abin da ka koya. Yin hakan zai nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma muna son Kalmarsa ta zama ‘haske ga tafarkinmu.’ (Zab. 119:105) Idan muna cikin wata matsala, kalaman nan za su iya ƙarfafa mu: “Karyayyar zuciya mai-tuba ba za ka rena ta ba, ya Allah.” “Jinƙanka ya tagaje ni, ya Ubangiji. A cikin yawan tunani da ke cikina ta’aziyyanka suna ji wa raina daɗi.” (Zab. 51:17; 94:18, 19) Jehobah da Yesu suna nuna jin ƙai wa mutanen da suke shan wahala. (Isha. 49:13; Mat. 15:32) Idan muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, za mu fahimce yadda Jehobah yake ƙaunarmu kuma hakan zai sa mu ƙaunace shi.

16. Ta yaya yin addu’a zai sa mu daɗa ƙaunar Allah?

16 Ka yi addu’a a kai a kai. Idan muka yi addu’a ga Jehobah kuma muka ga cewa ya amsa addu’armu, hakan zai sa mu ƙaunace shi sosai. (Zab. 65:2) Alal misali, mun sani cewa ba zai bari mu fuskanci gwajin da ya fi ƙarfinmu ba. (1 Kor. 10:13) Idan muna da damuwa kuma muka yi addu’a ga Jehobah, za mu kasance da “salama kuwa ta Allah.” (Filib. 4:6, 7) A wasu lokatai, za mu iya yin addu’a a zuciyarmu kamar yadda Nehemiya ya yi kuma Allah ya amsa addu’ar. (Neh. 2:1-6) Idan muka “lizima cikin addu’a,” kuma muka fahimci cewa Allah yana jin addu’o’inmu, hakan zai sa mu ƙaunace shi sosai kuma za mu kasance da tabbaci cewa zai taimaka mana mu jimre da gwajin da za mu fuskanta a nan gaba.—Rom. 12:12.

17. Yaya za mu ɗauki zuwa taro idan muna ƙaunar Allah da gaske?

17 Ka riƙa halartan taron ikilisiya da manyan taro a kai a kai. (Ibran. 10:24, 25) Isra’ilawa sun taru don su saurara kuma su koyi abubuwa game da Jehobah domin hakan zai sa su bauta masa kuma su bi Dokarsa. (K. Sha 31:12) Idan muna ƙaunar Jehobah sosai, za mu riƙa halartan taro a kai a kai. (Karanta 1 Yohanna 5:3.) Saboda haka, kada mu yarda wani abu ya sa mu daina ɗaukan zuwa taro da muhimmanci. Wajibi ne mu ci gaba da kasancewa da ƙaunar da muke da shi ga Jehobah tun farko.—R. Yoh. 2:4.

18. Mene ne ƙaunar Allah zai motsa mu mu yi?

18 Ka riƙa yi wa mutane wa’azin “gaskiyar bishara.” (Gal. 2:5) Ƙaunarmu ga Allah ne yake motsa mu mu yi wa’azin Mulkin Almasihu wanda zai yi “hawan ɗaukaka” don ya “tsare gaskiya” a Armageddon. (Zab. 45:4; R. Yoh. 16:14, 16) Idan muka yi almajirai kuma muka taimaka wa mutane su san ƙaunar Allah da kuma alkawarin sabuwar duniya da ya yi mana, za mu yi farin ciki matuƙa.—Mat. 28:19, 20.

19. Me ya sa ya kamata mu gode wa Jehobah saboda tanadin dattawa?

19 Ka nuna godiyarka ga Allah saboda tanadin dattawa. (A. M. 20:28) A kullum, Jehobah yana kula da mu shi ya sa ya yi mana tanadin dattawan ikilisiya. Dattawa suna kama da “maɓoya daga iska, makāri kuma daga hadarin ruwa; kamar koguna cikin ƙeƙasashiyar ƙasa, kamar inuwar babban dutse cikin ƙasa mai-agazari.” (Isha. 32:1, 2) Babu shakka, wurin fakewa mai kyau yana kāre mu daga ruwan sama ko zafin rana! Wannan kwatancin ya taimaka mana mu fahimci yadda dattawa suke taimaka mana da kuma ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta wa Jehobah duk da matsalolin da muke fuskanta. Yin biyayya ga waɗannan suke ja-gora a ikilisiya zai nuna cewa muna daraja waɗannan “kyautai ga mutane” sosai. Ƙari ga haka, yin hakan zai nuna cewa muna ƙaunar Allah da kuma Kristi wanda shi ne Shugaban ikilisiya.—Afis. 4:8; 5:23; Ibran. 13:17.

KA CI GABA DA KYAUTATA ƘAUNARKA GA ALLAH

20. Idan kana ƙaunar Allah, ta yaya za ka bi umurnin da ke Yaƙub 1:22-25?

20 Idan kana da dangantaka mai kyau da Jehobah, za ka kasance ‘mai-aika magana ba mai-ji kaɗai ba.’ (Karanta Yaƙub 1:22-25.) ‘Mai-aika magana’ yana da irin bangaskiyar da ke sa mu kasance da ƙwazo a wa’azi da kuma halartan taron Kirista. Idan kana ƙaunar Allah sosai, za ka bi “cikakkiyar shari’a,” wato dukan abubuwan da Allah yake bukata a gare mu.—Zab. 19:7-11.

21. Da me za ka iya kwatanta addu’o’in da kake yi daga zuciya?

21 Ƙaunar Jehobah Allah zai sa ka riƙa addu’a daga zuciya. Marubucin zabura Dauda ya kwatanta addu’arsa da turaren hayaƙi da Firist yake ƙonawa kullum a zamanin Isra’ila ta dā sa’ad da ya ce: “Ka bari addu’ata ta miƙu a gabanka kamar turaren ƙonawa; ta da hannuwana kuma kamar hadaya ta maraice.” (Zab. 141:2; Fit. 30:7, 8) Jehobah ya ji addu’o’in Dauda. Hakazalika, idan addu’o’inka da roƙe-roƙenka suna ƙunshe da furucin yabo da godiya daga zuciyarka, za su zama kamar turaren ƙonawa mai ƙamshi da ke faranta wa Jehobah rai.—R. Yoh. 5:8.

22. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

22 Yesu ya ce wajibi ne mu ƙaunaci Allah da kuma maƙwabtanmu. (Mat. 22:37-39) Idan muka ƙaunaci Jehobah da kuma dokokinsa, hakan zai sa mu ƙaunaci maƙwabtanmu. Za mu tattauna abin da ƙaunar maƙwabtanmu take nufi a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba