Lokacin Tuna Mutuwar Yesu, Zarafi Ne Mai Kyau na Ƙarin Ayyuka!
1. Waɗanne dalilai muke da su na yin ƙoƙarin ƙara ayyukanmu a hidima a watannin Maris, Afrilu, da kuma Mayu?
1 Shin za ka iya ƙara ayyukan da kake yi a hidima a lokacin Tuna Mutuwar Yesu? Wasu masu shela za su samu hutu daga aiki ko makaranta kuma za su iya yin amfani da wannan lokacin a hidima. Somawa daga ranar 2 ga watan Afrilu, za mu more yin kamfen na musamman don gayyatar waɗanda suke son saƙonmu su halarci Tuna Mutuwar Yesu tare da mu a ranar 17 ga watan Afrilu. Bayan haka, za mu yi ƙoƙarin koma ziyara wurin waɗanda suka halarci Tuna Mutuwar Yesu kuma mu gayyace su zuwa jawabi na musamman da za a ba da a makon 25 ga watan Afrilu. Hakika, akwai dalilai masu yawa na yin ƙoƙarin ƙara ayyukanmu a hidima a watannin Maris, Afrilu, da kuma Mayu.
2. Wace hanya ɗaya mai kyau ce za mu iya ƙara hidimarmu?
2 Hidimar Majagaba na Ɗan Lokaci: Hanya ɗaya mai kyau na ƙara ayyukanmu ita ce yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Tun da yake dukanmu mun taƙure da ayyuka, wannan yana bukatar yin shiri tun da wuri da kuma daidaita tsarin ayyukanmu. (Mis. 21:5) Wataƙila za ku iya tura wasu ayyuka da kuke yi a kai a kai da ba su da muhimmanci sosai zuwa watanni na gaba. (Filib. 1:9-11) Zai dace ka gaya wa wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiyarku game da muradinka na yin hidimar majagaba don ka ga ko su ma za su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci!
3. Ta yaya iyalai za su shirya don su ƙara sa hannu sosai a hidima?
3 Sa’ad da kuke Bauta ta Iyali da yamma na gaba, zai yi kyau ku tattauna maƙasudanku a matsayin iyali. (Mis. 15:22) Idan kowa a cikin iyalin ya kasance da haɗin kai, wataƙila wasu cikin iyalin za su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci na wata ɗaya ko fiye da hakan. Idan ka ga cewa wannan ba zai yiwuwa ba fa? Iyalin za ta iya shirya ta ƙara sa hannu sosai a hidima ta wurin fita hidima a wasu yamma ko kuma su jima a hidima a ƙarshen makonni.
4. Waɗanne albarka ne za mu samu idan muka ƙara sa hannu sosai a hidima a lokacin Tuna Mutuwar Yesu?
4 Jehobah yana lura da dukan abin da muke yi don mu bauta masa kuma yana godiya da sadaukarwa da muke yi. (Ibran. 6:10) Muna yin farin ciki sa’ad da muka yi baiko ga Jehobah da kuma mutane. (1 Laba. 29:9; A. M. 20:35) Shin za ka iya ƙara sa hannu sosai a hidima a lokacin Tuna Mutuwar Yesu kuma ka shaida ƙarin farin ciki da albarka da yin hakan ke kawowa?