Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w24 Mayu pp. 2-7
  • Ka Amince da “Mai Shariꞌar Dukan Duniya,” Mai Jinkai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Amince da “Mai Shariꞌar Dukan Duniya,” Mai Jinkai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA BA MU SANI BA
  • ABIN DA MUKA SANI
  • “MAI SHARIꞌAR DUKAN DUNIYA” ZAI “YI SHARIꞌA DAIDAI”
  • Me Muka Sani Game da Yadda Jehobah Zai Shariꞌanta Mutane a Nan Gaba?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Shawara ta Karshe da Maza Masu Aminci Suka Bayar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
w24 Mayu pp. 2-7

TALIFIN NAZARI NA 18

WAƘA TA 1 Babu Wani Kamar Jehobah

Ka Amince da “Mai Shariꞌar Dukan Duniya,” Mai Jinƙai

“Kai da kake mai shariꞌar dukan duniya, ba za ka yi shariꞌa daidai ba?”—FAR. 18:25.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ƙara fahimtar yadda Jehobah yake yin adalci da kuma jinƙai, a batun tā da matattu marasa adalci.

1. Wane darasi mai ban ƙarfafa ne Jehobah ya koya ma Ibrahim?

TA BAKIN wani malaꞌika, Allah ya gaya wa Ibrahim cewa zai halaka birnin Saduma da Gwamarata. Wannan bawan Allah ya damu sosai. Sai ya tambayi Allah cewa: “Za ka halaka mai adalci tare da mai mugunta? . . . Kai da kake mai shariꞌar dukan duniya, ba za ka yi shariꞌa daidai ba?” Jehobah ya yi haƙuri kuma ya koya ma wannan ƙaunataccen bawansa wani darasi da zai ƙarfafa mu sosai a yau, cewa: Allah ba zai taɓa halaka masu adalci ba. Ba shakka Ibrahim bai manta da tattaunawa da suka yi ranar ba har mutuwarsa.—Far. 18:23-33.

2. Me ya tabbatar mana cewa Jehobah yana yin adalci da jinƙai a duk lokacin da yake yin shariꞌa?

2 Muna da tabbaci cewa Jehobah yakan yi adalci da jinƙai a duk lokacin da yake yin shariꞌa, don mun san cewa “yakan dubi zuciya ne.” (1 Sam. 16:7) Gaskiyar ita ce, Jehobah ya san “kowace zuciya.” (1 Tar. 28:9; 1 Sar. 8:39) Ya fi mu hikima sosai, don haka ba a koyaushe ne za mu fahimci abin da ya sa ya tsai da wata shawara ba. Shi ya sa manzo Bulus ya ce: “Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincike.”—Rom. 11:33.

3-4. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wani lokaci, kuma me za mu bincika a wannan talifi? (Yohanna 5:28, 29)

3 Duk da haka, wani lokaci tambayoyi irin na Ibrahim za su iya damin mu. Alal misali, za mu iya yin tunani cewa: ‘Shin waɗanda Jehobah ya halaka su a dā, kamar mutanen Saduma da Gwamarata, za su sake rayuwa kuwa? Zai yiwu a tā da wasu cikinsu a lokacin da “za a tā da . . . marasa adalci”?’—A. M. 24:15.

4 Bari mu bincika abin da muka sani game da yadda za a tā da matattu. Kwanan baya, mun sami ƙarin haske a kan waɗanda za su tashi “su rayu” da waɗanda za su tashi a yi musu “hukunci,” wato shariꞌa.a (Karanta Yohanna 5:28, 29.) Wannan ƙarin haske ya sa mun canja wasu abubuwa da muka yi imani da su, kuma abin da za mu tattauna a talifin nan da na gaba ke nan. Za mu fara da abin da ba mu sani ba game da yadda Jehobah yake yin shariꞌa, saꞌan nan mu bincika abin da muka sani.

ABIN DA BA MU SANI BA

5. A dā, mene ne littattafanmu suka ce a kan mutanen Saduma da Gwamarata da Jehobah ya halaka?

5 A dā littattafanmu sun ce ba za a tā da waɗanda Jehobah ya halaka ba, kamar mutanen Saduma da Gwamarata. Amma da muka ƙara yin bincike da adduꞌa game da wannan batu, sai muka ga cewa ba mu da tabbaci a kan ko Jehobah zai tā da su ko ba zai tā da su ba? Me ya sa muka ce haka?

6. Waɗanne mutane marasa adalci ne kuma Jehobah ya hukunta, kuma mene ne ba mu sani ba a kan su?

6 Ban da lokacin mutanen Saduma da Gwamarata, akwai lokuta da yawa da Jehobah ya hukunta marasa adalci. Alal misali, Jehobah ya halaka mutane a zamanin Nuhu, kuma ba mu san yawansu ba. Akwai kuma kabilu bakwai da Jehobah ya sa mutanensa su halaka su a ƙasar alkawari, da sojojin Assuriya 185,000 da malaꞌikan Jehobah ya halaka a dare ɗaya. (Far. 7:23; M. Sha. 7:1-3; Isha. 37:36, 37) Shin, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa hukunci da Jehobah ya yi wa dukansu shi ne halaka na har abada, wato ba zai tā da waninsu ba? Aꞌa. Me ya sa muka ce haka?

7. Mene ne ba mu sani ba game da mutanen da suka halaka a zamanin Nuhu da kuma a ƙasar Kanꞌana? (Ka duba hoton.)

7 Ba mu san shawarar da Jehobah ya tsai da a kan kowanne cikin mutanen nan da ya halaka ba, kuma bamu san ko kowannensu ya sami damar sanin Jehobah da yin tuba ba. Alal misali, a zamanin da aka yi ambaliya, Littafi Mai Tsarki ya ce Nuhu ya yi “waꞌazin adalci.” (2 Bit. 2:5) Amma ba a gaya mana cewa ya yi ƙoƙari ya yi ma kowanne mutum waꞌazi yayin da yake gina jirgin ba. Haka ma yake da mutanen Kanꞌana, ba mu san ko duka mugayen mutane da aka halaka sun sami damar koyo game da Jehobah don su canja halayensu ba.

Nuhu da iyalinsa suna kan gina jirgin. A kusa da inda suke ginin, akwai bishiyoyi da yawa da suka kewaye wani kauye.

Nuhu da ꞌyan iyalinsa suna gina babban jirgi. Ba mu san ko a lokacin da suke wannan ginin, Nuhu ya yi ƙoƙarin yi wa kowa a duniya waꞌazi ba. (Ka duba sakin layi na 7)


8. Mene ne ba mu sani ba game da mutanen Saduma da Gwamarata?

8 Mutanen Saduma da Gwamarata kuma fa? Lokacin Lutu yana zama a wurin kuma shi mai adalci ne. Shin, Lutu ya yi ma kowannensu waꞌazi? Ba mu sani ba. Mutanen mugaye ne kam, amma dukansu ne suka san abin da ya dace da wanda bai dace ba? Ka tuna cewa jamaꞌa daga birnin sun yi ƙoƙarin yi wa baƙi da suka zo gidan Lutu fyaɗe, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce a cikinsu akwai “matasa da tsofaffi.” Wannan ya nuna cewa tun suna ƙanana, mutanen garuruwan nan sun saba gani ana yin abubuwa marasa kyau. Kuma wataƙila ba wanda ya taɓa koya musu ƙaꞌidodin Allah. (Far. 19:4; 2 Bit. 2:7) Shin, muna da tabbaci cewa Allahnmu mai jinƙai ya yi wa kowannensu hukuncin halaka na har abada? Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa ba za a iya samun masu adalci ko guda goma a birnin ba. (Far. 18:32) Don haka su marasa adalci ne, kuma ya dace da Jehobah ya halaka su. Amma, za mu iya cewa babu waninsu da Jehobah zai tayar a lokacin da “za a tā da . . . marasa adalci?” Aꞌa, ba mu sani ba!

9. Mene ne ba mu sani ba game da Sulemanu?

9 Littafi Mai Tsarki ya kuma ba mu labarin masu adalci da daga baya suka zama marasa adalci. Sarki Sulemanu ɗaya ne daga cikinsu. Ya san Jehobah sosai, kuma ya san yadda ya kamata ya bauta masa. Ƙari ga haka, Jehobah ya yi masa albarka ba kaɗan ba. Duk da haka, Sulemanu ya juye yana bauta ma gumaka. Hakan ya ɓata ma Jehobah rai sosai kuma mutanen Israꞌila sun yi shekaru da yawa suna shan wahala don zunubansa. Mun daɗe muna zaton cewa za a tā da Sulemanu domin game da mutuwarsa, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Solomon ya yi barci tare da ubanninsa,” kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutane masu adalci kamar Sarki Dauda ke nan. (1 Sar. 11:5-9, 43, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe; 2 Sar. 23:13) Amma wannan furuci da Littafi Mai Tsarki ya yi tabbaci ne cewa Jehobah zai tā da Sulemanu? Littafi Mai Tsarki bai ce haka ba. Wataƙila wasu su ce za a tā da Sulemanu, da yake Littafi Mai Tsarki ya ce “idan mutum ya mutu, ya sami ꞌyanci daga ikon zunubi ke nan.” (Rom. 6:7) Amma hakan ba ya nufi cewa za a tā da dukan waɗanda suka mutu, sai ka ce mutuwa yana ba wa mutum damar sake rayuwa. Ba haka ba ne. Rai da Allahnmu mai ƙauna yake ba wa waɗanda suka mutu, kyauta ne daga wurinsa. Kuma waɗanda yake so ya ba su damar bauta masa har abada ne yake ba su wannan kyautar. (Ayu. 14:13, 14; Yoh. 6:44) Allah zai ba wa Sulemanu wannan kyauta? Shi ne ya sani; mu kam ba mu sani ba. Mun dai san cewa Jehobah zai yi abin da ya dace.

ABIN DA MUKA SANI

10. Mene ne raꞌayin Jehobah game da hukunta mutane? (Ezekiyel 33:11) (Ka kuma duba hoton.)

10 Karanta Ezekiyel 33:11. Jehobah ya gaya mana raꞌayinsa game da hukunta mutane. Ya sa manzo Bitrus ya maimaita abin da annabi Ezekiyel ya rubuta, cewa “Ubangiji . . . ba ya so wani ya halaka.” (2 Bit. 3:9) Kalmomin nan suna da ban ƙarfafa. Sun nuna cewa Jehobah ba ya saurin yi wa mutum hukuncin halaka ta har abada. Shi mai jinƙai ne sosai. Kuma muddin zai yiwu, zai yi wa mutum jinƙai.

Wani danꞌuwa yana koyar da wadanda aka ta da su daga mutuwa a Aljanna. Yana nuna musu hoton babban gunkin da aka ambata a Daniyel sura 2.

A lokacin da za a tā da marasa adalci, mutane iri-iri za su sami damar koyo game da Jehobah (Ka duba sakin layi na 10)


11. Su wa ba za a tā da su ba, kuma ta yaya muka san hakan?

11 Me muka sani game da waɗanda ba za a tā da su ba? Mutane ƙalila ne Littafi Mai Tsarki ya ce hakan zai faru da su.b Alal misali, Yesu ya nuna cewa ba za a tā da Yahuda Iskariyoti ba. (Mar. 14:21; ka kuma duba Yohanna 17:12.c) Yahuda ya san cewa abin da zai yi ya saɓa wa nufin Jehobah, duk da haka ya yi shi. (Ka duba Markus 3:29.d) Ban da shi, Yesu ya ce wasu malaman addini da suka ƙi shi za su mutu kuma ba za a tā da su ba. (Mat. 23:33; Ka duba Yohanna 19:11.e) Manzo Bulus ya kuma ce ba za a tā da ꞌyan ridda da suka ƙi tuba ba.—Ibran. 6:4-8; 10:29.

12. Me muka sani a kan yadda Jehobah yake yin jinƙai? Ka ba da misali.

12 A wani ɓangaren kuma, akwai abin da muka sani game da yadda Jehobah yake yin jinƙai? Alal misali, ya nuna mana cewa “ba ya so wani ya halaka.” Akwai wasu mutane da suka yi zunubi mai tsanani kuma ya yi musu jinƙai. Sarki Dauda ya yi manyan zunubai da dama, har da zina da kuma kisa. Amma Jehobah ya yi masa jinƙai kuma ya yafe masa domin ya tuba. (2 Sam. 12:1-13) Sarki Manasse ma ya yi ta yin mugunta ne a yawancin rayuwarsa. Duk da haka, da Jehobah ya ga cewa Manasse ya tuba, ya yi masa jinƙai kuma ya yafe masa. (2 Tar. 33:9-16) Misalan nan sun nuna mana cewa Jehobah yakan yi wa mutum jinƙai duk saꞌad da ya ga dalilin yin haka. Zai tā da irin mutanen nan domin sun yarda cewa sun yi manyan zunubai, kuma sun tuba.

13. (a) Me ya sa Jehobah ya yi wa mutanen Nineba jinƙai? (b) Me Yesu ya ce a kan mutanen Nineba?

13 Mun kuma san yadda Jehobah ya yi wa mutanen Nineba jinƙai. Jehobah ya ce wa Yunana: “Muguntar [mutanen Nineba] ta kai gabana.” Amma da suka tuba, Jehobah ya yafe musu cikin alherinsa. Jinƙan Jehobah ya fi na Yunana sosai, domin da Yunana ya yi fushi, Jehobah ne ya tuna masa cewa mutanen Nineba “ba su iya bambanta hannun damansu da ta hagunsa ba.” (Yona 1:1, 2; 3:10; 4:9-11, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Daga baya, Yesu ya yi amfani da labarinsu don ya koya wa mutane yadda Jehobah yake yin adalci da jinƙai. Kuma ya ce “a Ranar Shariꞌa,” mutanen Nineba da suka tuba za su tashi—Mat. 12:41.

14. Idan aka tā da mutanen Nineba, wane irin shariꞌa ne za a yi musu?

14 Me ake nufi da cewa mutanen Nineba za su tashi “a Ranar Shariꞌa”? Yesu ya ce a nan gaba, za a tā da wasu kuma a “yi musu hukunci,” wato shariꞌa. (Yoh. 5:29) A nan, Yesu yana magana ne game da lokacin da zai yi sarauta na shekara dubu. A lokacin, “za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci.” (A. M. 24:15) Za a tā da ‘marasa adalcin’ ne don a yi musu shariꞌa. Wato bayan an tā da su, Jehobah da Yesu za su lura su ga ko mutanen za su bi abubuwan da za a koya musu. Idan wani mutumin Nineba da aka tā da, ya ƙi ya bauta ma Jehobah, Jehobah ba zai bar shi ya ci-gaba da rayuwa ba. (Isha. 65:20) Amma dukan waɗanda suka zaɓa cewa za su bauta ma Jehobah da aminci, za su sami damar yin rayuwa har abada!—Dan. 12:2.

15. (a) Me ya sa bai kamata mu ce a cikin waɗanda Jehobah ya halaka a Saduma da Gwamarata, ba wanda za a tā da shi ba? (b) Mene ne Yahuda aya 7 take nufi? (Ka duba akwatin da ya ce, “Mene ne Yahuda Yake Nufi?”)

15 Yesu ya ce “a Ranar Shariꞌa,” za a tausaya ma mutanen Saduma da Gwamarata fiye da waɗanda suka ƙi shi da koyarwarsa. (Mat. 10:14, 15; 11:23, 24; Luk. 10:12) Mene ne Yesu yake nufi? Wasu za su ga kamar kwatanci ne kawai Yesu yake yi don ya nuna cewa mutanen zamaninsa sun fi mutanen Saduma da Gwamarata mugunta. Amma da alama cewa Yesu yana nufin abin da zai faru a zahiri ne. Ka tuna cewa saꞌad da Yesu ya ce “a Ranar Shariꞌa” mutanen Nineba za su tashi, yana nufin abin da zai faru ne a zahiri. Kuma “Ranar Shariꞌa” da Yesu yake zancensa a nan da “Ranar Shariꞌa” da mutanen Nineba za su tashi, duk ɗaya ne. Mutanen Saduma da Gwamarata sun yi miyagun abubuwa kamar yadda mutanen Nineba ma suka yi. Amma mutanen Nineba sun sami zarafin yin tuba. Ƙari ga haka, ka tuna abin da Yesu ya ce game da waɗanda za su tashi a yi musu shariꞌa, ya ce za su haɗa da “waɗanda sun yi mugunta.” (Yoh. 5:29, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Don haka, da alama cewa za a ta da wasu daga cikin mutanen Saduma da Gwamarata, kuma ƙila a ba mu damar koyar da su game da Jehobah da Yesu.

Mene ne Yahuda Yake Nufi?

Shekaru da yawa bayan mutuwar Yesu, ɗanꞌuwansa Yahuda ya rubuta cewa an yi wa birnin Saduma da Gwamarata da birane da ke kewaye da su “hukunci a wuta ta har abada.” (Yahu. 7) Amma abin da Yesu ya faɗa ya nuna cewa mai yiwuwa a tā da wasu daga cikinsu. (Luk. 10:12) To, mene ne Yahuda yake nufi? Maganarsa ta saɓa wa abin da Yesu ya ce game da biranen nan ne? Aꞌa. Bisa ga abin da Yesu ya ce, biranen ne da kansu aka halaka har abada, ba dukan mutane da ke cikinsu ba. Jehobah ya yi haka ne don ya ja wa mutane kunne cewa kar su yi ayyukan lalata. Abin da Yahuda ya rubuta ya yi daidai da abin da annabi Irmiya ya faɗa a kan birnin Edom da Babila da suke cike da mugunta a dā. Jehobah ya halaka biranen nan har abada, wato ba za a sake gina su ko a zauna a cikin su ba. (Irm. 49:17, 18; 50:35, 39, 40) Ƙari ga haka, Abin da Yahuda da manzo Bitrus suka rubuta ya nuna cewa mai yiwuwa Jehobah ba zai tā da wasu daga cikin mutanen nan da ya halaka ba.—2 Bit. 2:6.

16. Me muka sani a kan yadda Jehobah zai zaɓi wanda zai tayar da wanda ba zai tayar ba? (Irmiya 17:10)

16 Karanta Irmiya 17:10. Ayar nan ta bayyana abin da muka sani a kan yadda Jehobah yake yin shariꞌa, wato Jehobah yakan ‘bincika tunani, ya gwada zuciya.’ A batun tā da waɗanda suka mutu, zai “sāka wa kowane mutum gwargwadon hanyoyin rayuwarsa.” Idan da bukata, Jehobah zai yi hukunci, amma idan zai yiwu, zai yi wa mutum jinƙai. Don haka, kada mu taɓa ce ba za a tā da mutum ba, sai dai idan Littafi Mai Tsarki ne ya ce haka!

“MAI SHARIꞌAR DUKAN DUNIYA” ZAI “YI SHARIꞌA DAIDAI”

17. A nan gaba, me zai faru da waɗanda suka mutu?

17 Daga lokacin da Adamu da Hauwaꞌu suka bi Shaiɗan kuma suka yi ma Jehobah tawaye har yau, biliyoyin mutane sun rasa rayukansu. Hakika mutuwa “abokiyar gaba” ce sosai! (1 Kor. 15:26) Me zai faru da waɗannan mutanen? Za a tā da ƙalila daga cikin mabiyan Yesu kuma a ba su rai mara mutuwa a sama. Mutane da za su je sama 144,000 ne. (R. Yar. 14:1) Yawancin bayin Allah maza da mata za su tashi ne a lokacin da za a tā da “masu adalci,” kuma za su yi rayuwa har abada a duniya idan suka kasance da aminci har ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu da kuma gwaji na ƙarshe. (Dan. 12:13; Ibran. 12:1) Ƙari ga haka, a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu, za a ba wa “marasa adalci” damar canja halinsu don su bauta wa Allah. Marasa adalcin za su haɗa da waɗanda ba su taɓa bauta ma Jehobah ba, da “waɗanda sun yi mugunta.” (Luk. 23:42, 43) Amma akwai wasu mugayen mutane da suka yi niyyar ƙin yin nufin Jehobah. Sun nace da yin mugunta har Jehobah ya yanke shawara cewa ba zai tā da su ba.—Luk. 12:4, 5.

18-19. (a) Me ya sa za mu iya buga ƙirji cewa shariꞌar da Jehobah zai yi ma waɗanda suka mutu daidai ne? (Ishaya 55:8, 9) (b) Me za mu bincika a talifi na gaba?

18 Shin, za iya buga ƙirji mu ce idan har Jehobah ne ya shariꞌanta mutum, shariꞌar daidai ne? Ƙwarai kuwa! Ibrahim ya ga tabbaci cewa Jehobah, “mai shariꞌar dukan duniya” ba ya kuskure, hikimarsa babu iyaka, kuma shi mai jinƙai ne. Ya riga ya koyar da Ɗansa kuma ya ba shi hakkin yi wa kowa shariꞌa. (Yoh. 5:22) Kamar Jehobah, Yesu ma zai iya sanin abin da mutum yake tunani a zuciyarsa. (Mat. 9:4) Don haka idan suka zo shariꞌanta kowane mutum, za su “yi shariꞌa daidai”!

19 Bari mu ƙudiri niyya cewa za mu yarda da duk wata shawara da Jehobah ya yanke. Mun san ba mu cancanci mu yi shariꞌa ba, amma Jehobah ya cancanci yin hakan! (Karanta Ishaya 55:8, 9.) Don haka, mun bar dukan shariꞌa a hannun Jehobah da Ɗansa, kuma mun tabbata za su yi shariꞌar gaskiya. Tabbas, Sarkinmu Yesu zai yi koyi da adalci da kuma jinƙan Ubansa. (Isha. 11:3, 4) Amma me muka sani a kan yadda za a shariꞌanta mutane a lokacin ƙunci mai girma? Kuma me ba mu sani ba? Abin da za mu bincika a talifi na gaba ke nan.

A BATUN MARASA ADALCI DA ZA A TĀ DA SU A NAN GABA, . . .

  • mene ne ba mu sani ba?

  • me muka sani?

  • me ya sa za mu iya buga ƙirji cewa Jehobah zai yi shariꞌar gaskiya?

WAƘA TA 57 Ku Yi wa Dukan Mutane Waꞌazi

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta Satumba 2022, shafi na 14-19.

b Don bayani a kan abin da zai faru da Adamu, da Hauwaꞌu, da Kayinu, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu 2013, shafi na 12, da kuma ƙarin bayani.

c Furucin nan “ɗan halaka,” a Yohanna 17:12, yana nufin cewa mutuwar Yahuda Iskariyoti na har abada ne, ba za a tā da shi ba.

d Ka duba talifin nan da ya ce: “Mene ne Zunubin da Ba A Gafartawa?” a dandalin jw.org/ha.

e Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu 2008, shafi na 32, sakin layi na 6

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba