Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Maris pp. 14-19
  • Ka Yi Waꞌazi da Ƙwazo Kamar Yesu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Waꞌazi da Ƙwazo Kamar Yesu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YA FI SON YIN ABIN DA JEHOBAH YAKE SO YA YI
  • YA YI LAꞌAKARI DA ANNABCE-ANNABCEN DA KE LITTAFI MAI TSARKI
  • YA KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI TAIMAKA MASA
  • YA KASANCE DA TABBACI CEWA WASU ZA SU SAURARA
  • Yadda Za Ka Ƙara Jin Daɗin Yin Waꞌazi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Bari Kauna Ta Sa Ka Ci-gaba da Yin Waꞌazi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Maris pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 11

WAƘA TA 57 Ku Yi wa Dukan Mutane Waꞌazi

Ka Yi Waꞌazi da Ƙwazo Kamar Yesu

“Ubangiji ya . . . aike su biyu-biyu su yi gaba zuwa garuruwa da wuraren da shi kansa ya shirya zai je.”—LUK. 10:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga hanyoyi huɗu da za mu yi waꞌazi da ƙwazo kamar yadda Yesu ya yi.

1. Wane bambanci ne ke tsakanin bayin Jehobah da waɗanda suke daꞌawa cewa su Kiristoci ne?

ƘWAZON da bayin Jehobah suke yi a waꞌazi, yana cikin bambanci da ke tsakaninsu da waɗanda suke daꞌawa cewa su Kiristoci ne. (Tit. 2:14) Amma a wasu lokuta, za ka iya jin ƙyuyan fita waꞌazi. Mai yiwuwa kana ji kamar yadda wani dattijo da yake aiki tuƙuru ya ji saꞌad da ya ce; “A wasu lokuta, ba na marmarin fita waꞌazi.”

2. Me ya sa a wasu lokuta ba ya mana sauƙi mu yi waꞌazi da ƙwazo?

2 Mai yiwuwa mun fi jin daɗin yin wasu hidima a ƙungiyar Jehobah fiye da yin waꞌazi. Me ya sa hakan yakan faru? Domin idan muka gina sabbin Majamiꞌun Mulki ko muka yi musu kwaskwarima, ko idan muka taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu da kayan agaji ko kuma muka ƙarfafa su a wata hanya dabam, mukan ga sakamakon da wuri kuma yakan sa mu farin ciki. Ƙari ga haka, idan muna aiki da ꞌyanꞌuwanmu mukan yi hakan cikin salama da ƙauna, kuma mun san cewa ꞌyanꞌuwanmu suna jin daɗi kuma suna godiya don abin da muka yi musu. Amma za mu iya yin shekaru da yawa muna waꞌazi ba tare da samun wani sakamako mai kyau ba. Ko kuma mu haɗu da waɗanda ba sa son su ji waꞌazinmu kwatakwata. Ban da haka ma, mun san cewa yayin da ƙarshen yake gabatowa, mutane ba za su so su saurari waꞌazinmu ba. (Mat. 10:22) Me zai taimaka mana mu ci-gaba da kasancewa da ƙwazo a waꞌazi?

3. Mene ne muka koya game da Yesu daga misalin da ke Luka 13:​6-9?

3 Misalin Yesu zai taimaka mana mu kasance da ƙwazo a waꞌazi. Saꞌad da Yesu yake waꞌazi a duniya, bai bar wani abu ya hana shi yi wa mutane waꞌazi ba. Kuma ya ci-gaba da yin hakan da ƙwazo. (Karanta Luka 13:​6-9.) A wani misalin da Yesu ya bayar, ya kwatanta aikinsa da wanda yake kula da gonar ɓaure, da ya yi shekaru uku yana aiki tuƙuru amma bai samu kome ba. Yesu ma ya yi shekaru uku yana yi wa Yahudawa waꞌazi, amma yawancinsu ba su zama almajiransa ba. Duk da haka, bai gaji da yi musu waꞌazi ba. Kamar mai kula da gonar ɓauren, Yesu ya ci-gaba da sa rai cewa wata rana za a sami sakamako mai kyau. Kuma ya yi iya ƙoƙarinsa ya taimaka wa Yahudawan su amince da waꞌazin.

4. Waɗanne abubuwa huɗu ne za mu koya daga Yesu?

4 A wannan talifin, za mu ga yadda Yesu ya yi waꞌazi da ƙwazo, musamman a watanni shida na ƙarshe da ya yi a duniya. (Ka duba, “After these things” a ƙarin bayani da ke Luke 10:1 a juyin, New World Translation.) Idan muka bi abin da ya faɗa kuma muka yi abin da ya yi, za mu ci-gaba da kasancewa da ƙwazo. Bari mu ga abubuwa huɗu da za mu koya daga wurin Yesu. (1) Ya fi son yin abin da Jehobah yake so ya yi, (2) ya yi laꞌakari da annabce-annabcen da ke Littafi Mai Tsarki, (3) yana da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa, kuma (4) ya san cewa wasu za su saurare shi.

YA FI SON YIN ABIN DA JEHOBAH YAKE SO YA YI

5. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yin abin da Jehobah yake so ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa?

5 Yesu ya yi waꞌazin “labari mai daɗi na mulkin Allah” da ƙwazo, domin ya san cewa abin da Jehobah yake so ya yi ke nan. (Luk. 4:43) A gun Yesu, babu abin da ya fi yin waꞌazi muhimmanci. Har a lokacin da watanni kaɗan ne suka rage masa a duniya, ya ci-gaba da yin waꞌazi a “garuruwa da ƙauyuka,” yana koyar da mutane. (Luk. 13:22) Kuma ban da manzanninsa, ya koya ma waɗansu mutane yadda za su yi waꞌazi kamar yadda ya yi.—Luk. 10:1.

6. Wace alaƙa ce ke tsakanin waꞌazi da sauran hidima da muke yi a ƙungiyar Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

6 A yau ma, yin waꞌazi ne aiki mafi muhimmanci da Jehobah da Yesu suke so mu yi. (Mat. 24:14; 28:​19, 20) Ko da wace irin hidima ce muke yi a ƙungiyar Jehobah, tana da alaƙa da waꞌazi. Alal misali, muna gina Majamiꞌun Mulki domin waɗanda muka yi musu waꞌazi su zo su bauta wa Jehobah a ciki. Kuma ayyukan da ake yi a Ofisoshinmu da makamantansu na taimaka ma waꞌazin da muke yi. Ƙari ga haka, idan balaꞌi ya auku, mukan tabbata cewa ꞌyanꞌuwanmu sun sami abin da suke bukata don su sake soma taro da kuma yin waꞌazi. Idan muka tuna cewa yin waꞌazi ne aiki mafi muhimmanci da Jehobah yake so mu yi, hakan zai sa mu riƙa yin waꞌazi babu fashi. Wani dattijo mai suna János, a ƙasar Hungary, ya ce: “A kullum ina tuna wa kaina cewa yin waꞌazi ne aiki mafi muhimmanci da muke da shi. Babu wani aikin da muke yi wa Jehobah da ya kai yin waꞌazi.”

Hotuna: 1. Wani ɗanꞌuwan yana aiki a inda ake gine-ginenmu. 2. Wani ɗanꞌuwa yana taimaka ta wajen yin aikin Bethel daga gida. 3. Daga baya, ꞌyanꞌuwa maza biyun suna waꞌazi tare.

A yau, Yin waꞌazi ne aiki mafi muhimmanci da Jehobah da Yesu suke so mu yi (Ka duba sakin layi na 6)


7. Me ya sa Jehobah yake so mu ci-gaba da yin waꞌazi? (1 Timoti 2:​3, 4)

7 Za mu ƙara zama da ƙwazon yin waꞌazi idan muna ganin mutane yadda Jehobah yake ganinsu. Idan zai yiwu, Jehobah yana son dukan mutane su koyi gaskiya game da shi. (Karanta 1 Timoti 2:​3, 4.) Shi ya sa yake taimaka mana mu inganta yadda muke waꞌazi. Alal misali, ƙasidar nan Ƙaunar Mutane Za Ta Sa Ka Almajirtar da Su na ɗauke da shawarwari masu kyau da za su taimaka mana mu soma tattaunawa da mutane, har mu taimaka musu su soma bauta wa Jehobah. Ko da mutanen da muka yi musu waꞌazi ba su soma bauta wa Jehobah yanzu ba, za su iya samun damar yin hakan kafin ƙarshen ƙunci mai girma. Za su iya tuna da abin da muka gaya musu kuma su soma bauta wa Jehobah. Amma hakan zai yiwu ne kawai idan muka ci-gaba da yin waꞌazi.

YA YI LAꞌAKARI DA ANNABCE-ANNABCEN DA KE LITTAFI MAI TSARKI

8. Waɗanne annabce-annabce ne suka taimaka wa Yesu ya yi amfani da lokacinsa a hanyar da ta fi dacewa?

8 Yesu ya fahimci yadda annabce-annabcen da aka yi a Littafi Mai Tsarki za su cika. Ya san cewa zai yi shekaru uku da rabi ne kawai yana waꞌazi. (Dan. 9:​26, 27) Ƙari ga haka, ya kuma san annabcin da aka yi cewa zai sha wahala kuma zai mutu. (Luk. 18:​31-34) Da yake ya san waɗannan abubuwan, ya yi amfani da lokacinsa a hanyar da ta fi dacewa. Kuma hakan ya sa ya yi waꞌazi da ƙwazo sosai don ya kammala aikin da aka ba shi.

9. Ta yaya fahimtar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki, zai taimaka mana mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo?

9 Idan muka fahimci annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da kyau, hakan zai taimaka mana mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo. Alal misali, mun san cewa ƙarshen wannan zamanin ya yi kusa. Muna ganin cikar annabcin da aka yi game da abubuwan da za su faru a kwanakin ƙarshe da yadda halin mutane zai kasance. Muna ganin yadda annabcin da aka yi game da gāba da za ta kasance tsakanin sarkin kudu da sarkin arewa yake cika a wannan “kwanakin ƙarshe.” Mun gane cewa wannan gāba ce tsakanin gwamnatin Haɗin Gwiwa ta Birtaniya da Amirka, da kuma ƙasar Rasha da magoya bayanta. (Dan. 11:40) Mun kuma san cewa gwamnatin Haɗin Gwiwa ta Birtaniya da Amirka ne ke wakiltar ƙafafun gunkin da ke Daniyel 2:​43-45. Mun tabbata cewa, nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai halaka dukan gwamnatocin ꞌyan Adam. Dukan annabce-annabcen nan sun nuna cewa mun yi kusa sosai da ƙarshen wannan zamanin. Saboda haka, wajibi ne mu yi amfani da lokacinmu da kyau wajen yin waꞌazi.

10. A waɗanne hanyoyi ne kuma annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo?

10 Littafi Mai Tsarki na ɗauke da annabce-annabcen da muke marmarin gaya wa mutane. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Carrie da take hidima a Jamhuriyar Dominika ta ce, “Idan na tuna abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi alkawari zai yi mana a nan gaba, nakan yi marmarin gaya wa mutane game da su.” Ta ƙara da cewa: “Idan na ga yadda mutane suke fama a yau, nakan tuna cewa su ma suna bukatar su san game da alkawura masu kyau da Jehobah ya yi mana.” Annabce-annabcen da aka yi a Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Jehobah yana taimaka mana mu iya yin waꞌazi, kuma hakan na ƙarfafa mu mu ci-gaba da yin wannan aikin. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Leila, da ke zama a Hungary ta ce: “Abin da ke Ishaya 11:​6-9 yakan sa in yi waꞌazi har ga mutanen da babu alama cewa za su saurare ni. Na san cewa da taimakon Jehobah, ba wanda ba zai iya canjawa ba.” Wani ɗanꞌuwa kuma daga Zambiya mai suna Christopher ya ce: “Kamar yadda aka annabta a Markus 13:​10, waꞌazin labari mai daɗin nan yana yaɗuwa a dukan faɗin duniya, kuma ina jin daɗin ganin cewa ina cikin waɗanda suke taimakawa wajen cika wannan annabcin.” Kai kuma fa? Waɗanne annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki ne suke taimaka maka ka ci-gaba da yin waꞌazi?

YA KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI TAIMAKA MASA

11. Me ya sa Yesu yake bukatar ya dogara ga Jehobah don ya taimaka masa ya ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo? (Luka 12:​49, 53)

11 Yesu ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa ya ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo. Ko da yake Yesu ya yi amfani da basira wajen yin waꞌazi, ya san cewa waꞌazin Mulkin zai sa wasu mutane su yi fushi sosai kuma su yi ƙoƙarin hana yin sa. (Karanta Luka 12:​49, 53.) Shugabannin addinai ba su so yadda Yesu yake waꞌazi ba, kuma sau da yawa sun yi ƙoƙari su kashe shi. (Yoh. 8:59; 10:​31, 39) Amma Yesu bai daina yin waꞌazi ba, domin ya san cewa Jehobah yana tare da shi. Yesu ya ce: “Ba ni ne kaɗai ba, amma Ubana wanda ya aiko ni yana yi tare da ni . . . Bai bar ni ni kaɗai ba, gama kullum ina yin abin da yake so.”—Yoh. 8:​16, 29.

12. Ta yaya Yesu ya shirya almajiransa su ci-gaba da yin waꞌazi ko da ana tsananta musu?

12 Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa za su iya dogara ga Jehobah don ya taimaka musu. Ya gaya musu sau da sau cewa, Jehobah zai taimaka musu har a lokacin da ake tsananta musu. (Mat. 10:​18-20; Luk. 12:​11, 12) Da yake ya san cewa mutane da yawa ba za su so waꞌazin ba, ya gaya musu cewa su zama masu hikima. (Mat. 10:16; Luk. 10:3) Ya gaya musu cewa kada su tilasta wa mutane idan ba sa son su saurare su. (Luk. 10:​10, 11) Kuma ya gaya musu su gudu idan ana tsananta musu. (Mat. 10:23) Ko da yake Yesu ya yi waꞌazi da ƙwazo kuma ya dogara ga Jehobah, bai sa kansa cikin haɗari, ba gaira ba dalili ba.—Yoh. 11:​53, 54.

13. Me ya tabbatar mana da cewa Jehobah zai taimaka mana?

13 Mu ma muna bukatar taimakon Jehobah don mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo ko da ana tsananta mana. (R. Yar. 12:17) Me zai tabbatar mana da cewa Jehobah zai taimaka mana? Amsar na adduꞌar da Yesu ya yi a Yohanna 17. A adduꞌar, Yesu ya roƙi Jehobah ya lura da almajiransa, kuma Jehobah ya amsa adduꞌar. Littafin Ayyukan Manzanni ya bayyana yadda Jehobah ya taimaka wa manzannin don su iya yin waꞌazi da ƙwazo duk da tsanantawa. Ban da haka ma, ya kuma roƙi Jehobah ya lura da dukan waɗanda za su ba da gaskiya ga waꞌazin manzanninsa. Har da mu ma. Jehobah bai daina amsa adduꞌar nan da Yesu ya yi ba; zai taimaka mana kamar yadda ya taimaka wa manzannin Yesu.—Yoh. 17:​11, 15, 20.

14. Ta yaya muka san cewa za mu iya ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo? (Ka kuma duba hoton.)

14 Yayin da ƙarshen ke gabatowa, yin waꞌazi zai iya ƙara wuya. Amma Yesu ya tabbatar mana cewa za mu sami taimakon da muke bukata don mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo. (Luk. 21:​12-15) Kamar yadda Yesu da almajiransa suka yi, muna barin mutane su zaɓa ko za su saurare mu, kuma ba ma gardama da su. Ko a ƙasashen da an hana aikinmu, ꞌyanꞌuwanmu suna kan yin waꞌazi don sun dogara ga Jehobah ba kansu ba. Kamar yadda Jehobah ya taimaka wa bayinsa a ƙarni na farko, a yau ma yana ba mu ruhunsa mai tsarki don mu iya yin waꞌazi sosai yadda yake so. (2 Tim. 4:17) Saboda haka, idan ka dogara ga Jehobah ka tabbata cewa, zai taimaka maka ka ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo.

Ko a wuraren da aka hana aikinmu, ꞌyanꞌuwanmu sun ci-gaba da yin waꞌazi cikin basira (Ka duba sakin layi na 14)a


YA KASANCE DA TABBACI CEWA WASU ZA SU SAURARA

15. Me ya nuna cewa Yesu ya san wasu mutane za su saurari waꞌazinsa?

15 Yesu ya san cewa wasu za su saurari waꞌazinsa. Hakan ya taimaka masa ya ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo da kuma farin ciki. Alal misali, wajen shekara ɗaya saꞌad da Yesu ya soma waꞌazi, ya ga cewa mutane da yawa suna son su ji waꞌazin, shi ya sa ya ce suna kama da gonar da ta isa girbi. (Yoh. 4:35) Shekara ɗaya bayan haka, ya gaya wa almajiransa cewa: “Girbin yana da yawa.” (Mat. 9:​37, 38) Daga baya ya gaya musu cewa: “Girbin yana da yawa . . . Saboda haka, ku roƙi mai gonar ya aiko da masu aiki su yi masa girbi.” (Luk. 10:2) Yesu ya kasance da tabbaci cewa akwai waɗanda za su ba da gaskiya, kuma yana farin ciki idan suka yi hakan.—Luk. 10:21.

16. Ta yaya misalan da Yesu ya bayar suka nuna sakamako mai kyau da za mu iya samu a waꞌazi? (Luka 13:​18-21) (Ka kuma duba hoton.)

16 Yesu ya taimaka wa almajiransa su ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo ta wajen tuna musu cewa, idan sun ci-gaba za su sami sakamako mai kyau. Kuma ya fahimtar da su ta wurin misalai biyu da ya bayar. (Karanta Luka 13:​18-21.) Na ɗaya, Yesu ya ce Mulkin Allah yana kamar ƙwayar mastad wadda ta yi girma ta zama babbar bishiya. Hakan ya nuna cewa mutane da yawa za su amince da waꞌazinmu kuma babu abin da zai iya hana hakan faruwa. Na biyu, Yesu ya ce Mulkin Allah yana kama da yisti. Domin waꞌazin za ta isa wurare da yawa a faɗin duniya, kuma za ta sa mutane su yi canje-canje a rayuwarsu ko da ba ma ganin sakamakon nan take. Ta haka, Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa waꞌazinsu zai taimaka wa mutane da yawa.

ꞌYanꞌuwa mata biyu suna waꞌazi da amalanke a wurin da mutane da yawa suke tafiya. Da yawansu suna wucewa ba sa tsayawa.

Kamar Yesu, muna da tabbaci cewa wasu mutane za su saurari waꞌazinmu (Ka duba sakin layi na 16)


17. Waɗanne dalilai ne muke da su na ci-gaba da yin waꞌazi?

17 Idan muka yi laꞌakari da yadda waꞌazinmu yake taimaka wa mutane a faɗin duniya, hakan yana sa mu sami ƙarfin gwiwan ci-gaba da waꞌazi. Kowace shekara, miliyoyin mutane suna zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu kuma suna nazarin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, duban mutane suna yin baftisma kuma su soma yin waꞌazin kamar yadda muke yi. Ba mu san ko mutane nawa ne za su saurari waꞌazinmu ba, amma mun san cewa Jehobah yana tara taron jamaꞌa da za su tsira a lokacin ƙunci mai girma. (R. Yar. 7:​9, 14) Jehobah ne mai gonar, kuma yana da tabbaci cewa mutane da yawa za su saurari waꞌazin. Don haka, zai dace mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo.

18. Me za ka so mutane su sani?

18 An san mabiyan Yesu da yin waꞌazi da ƙwazo. Saꞌad da mutane suka ga yadda manzanninsa suke koyarwa, sai suka “gane cewa dā . . . suna tare da Yesu.” (A. M. 4:13) Bari mu ma mu ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo babu tsoro, ta hakan mutane za su san cewa muna koyi da Yesu.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Yesu ya nuna cewa yin waꞌazi ne ya fi muhimmanci a gare shi, kuma ta yaya za mu yi koyi da ƙwazonsa?

  • Ta yaya Yesu ya dogara ga Jehobah, kuma ta yaya za mu yi hakan?

  • Wane tabbaci ne Yesu yake da shi game da waꞌazin Mulkin Allah, kuma me hakan ya koya mana?

WAƘA TA 58 Muna Neman Mutane Masu Sauƙin Kai

a BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa yana yi ma wani mutum waꞌazi a gidan mai, cikin basira.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba