Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Maris pp. 26-31
  • Hannun Jehobah ba Zai Taɓa Kasawa Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hannun Jehobah ba Zai Taɓa Kasawa Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA ZA MU KOYA DAGA HALIN MUSA DA ISRAꞌILAWA
  • IDAN MUNA BUKATAN KUƊI
  • YADDA ZA MU KULA DA KANMU IDAN MUKA TSUFA
  • Shawara ta Karshe da Maza Masu Aminci Suka Bayar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Maris pp. 26-31

TALIFIN NAZARI NA 13

WAƘA TA 4 “Jehobah Makiyayina Ne”

Hannun Jehobah ba Zai Taɓa Kasawa Ba

“Hannun Yahweh ya kasa ne?”—L. ƘID. 11:23.

ABIN DA ZA MU KOYA

Wannan talifin zai taimaka mana mu ƙara gaskata cewa Jehobah zai tanadar mana da abubuwan da muke bukata na yau da kullum.

1. Ta yaya Musa ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah saꞌad da ya taimaka wa Israꞌilawa su bar Masar?

LITTAFIN Ibraniyawa ya ambata mutane da yawa da suke da bangaskiya. Ɗaya daga cikinsu shi ne Musa kuma shi mutum ne mai bangaskiya sosai. (Ibran. 3:​2-5; 11:​23-25) Ya nuna bangaskiya a lokacin da ya taimaka wa Israꞌilawa su bar Masar. Bai ji tsoron Firꞌauna da sojojinsa ba. Ya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa kuma ya ci-gaba da yi musu ja-goranci har suka wuce ta Jar Teku da kuma lokacin da suke daji. (Ibran. 11:​27-29) Yawancin Israꞌilawa sun soma ganin kamar Jehobah ba zai iya ba su abin da suke bukata ba, amma Musa ya ci-gaba da dogara ga Jehobah. Kuma bai sha kunya ba. Jehobah ya yi wa Israꞌilawan tanadin abinci da ruwa a dajin da ba abubuwan nan da yawa.a—Fit. 15:​22-25; Zab. 78:​23-25.

2. Me ya sa Allah ya tambayi Musa cewa: “Hannun Yahweh ya kasa ne”? (Littafin Ƙidaya 11:​21-23)

2 Duk da cewa Musa yana da bangaskiya sosai, wajen shekara ɗaya bayan Jehobah ya cece su daga Masar, Musa ya soma shakka ko Jehobah zai iya ba su nama kamar yadda ya ce zai yi. Mutanen suna da yawa sosai kuma akwai ƙarancin abinci a dajin. Ta yaya Jehobah zai iya ba wa mutanen naman da zai ishe su? Jehobah da kansa ya tambayi Musa cewa: “Hannun Yahweh ya kasa ne?” (Karanta Littafin Ƙidaya 11:​21-23.) Furucin nan “hannun Yahweh” yana nufin ruhu mai tsarki ko kuma ikon da Jehobah yake amfani da shi wajen yin abubuwa. A taƙaice, abin da Jehobah yake gaya wa Musa shi ne, ‘Ina da ikon yin duk abin da nake so in yi.’

3. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tunani a kan abin da ya faru da Musa da kuma Israꞌilawa?

3 Ka taɓa yin shakka ko Jehobah zai iya tanadar wa kai da iyalinka abin da kuke bukata? Ko mun taɓa yi ko aꞌa, za mu ga abin da ya sa Musa da Israꞌilawa suka yi shakka cewa Jehobah zai ba su abin da suke bukata. Kuma za mu ga ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su sa mu gaskata cewa hannun Jehobah ba zai taɓa kasawa ba.

ABIN DA ZA MU KOYA DAGA HALIN MUSA DA ISRAꞌILAWA

4. Me ya sa Israꞌilawa da yawa suka soma shakka ko Jehobah zai iya tanadar musu da abin da suke bukata?

4 Me ya sa Israꞌilawa da yawa suka soma shakka ko Jehobah zai iya tanadar musu da abin da suke bukata? Abin ya soma ne a lokacin da Israꞌilawa, da “mutane masu yawa waɗanda su ba Israꞌilawa ba” sun bar Masar tare, suna tafiya a daji zuwa Ƙasar Alkawari. (Fit. 12:38; M. Sha. 8:15) Mutanen da ba Israꞌilawa ba sun gaji da cin manna, sai suka soma gunaguni kuma Israꞌilawa da yawa ma sun bi su. (L. Ƙid. 11:​4-6) Mutanen sun tuna da irin abincin da suke ci a Masar. Da Musa ya ga haka, sai ya ɗauka cewa hakkinsa ne ya tanadar musu abin da suke bukata.—L. Ƙid. 11:​13, 14.

5-6. Me za mu iya koya daga yadda halin mutanen da ba Israꞌilawa ba ya shafi Israꞌilawa?

5 Mutanen nan da ba Israꞌilawa ba, ba su nuna godiya don abin da Jehobah ya tanadar musu ba kuma Israꞌilawa da yawa sun bi halinsu. Mu ma za mu iya zama marasa godiya idan muka bi halin mutane a yau da ba sa godiya. Kuma hakan zai iya sa mu soma rena abin da Jehobah yake tanadar mana. Ƙari ga haka, za mu iya soma tuna da abubuwan da muke da su a dā ko kuma mu soma ƙishin wasu don abubuwan da suke da shi. Amma za mu fi yin farin ciki idan muka gamsu da abin da muke da shi ko da kaɗan ne.

6 Israꞌilawan sun manta da alkawarin da Allah ya yi musu. Ya tabbatar musu cewa sai sun isa Ƙasar Alkawari ne za su sami duk abin da suke so, ba a daji ba. Mu ma a yau, ya kamata mu mai da hankali ga abubuwan da Jehobah ya ce zai ba mu a aljanna, maimakon abubuwan da ba mu da su yanzu. Kuma za mu iya yin tunani a kan nassosin da za su taimaka mana mu ƙara dogara ga Jehobah.

7. Me ya tabbatar mana cewa Jehobah zai iya taimaka mana a koyaushe?

7 Saꞌad da Jehobah ya yi wa Musa tambayar da ke Littafin Ƙidaya 11:​23, wataƙila ya so Musa ya yi tunani a kan abubuwa biyu ne: (1) Yadda ikonsa bai da iyaka. (2) Zai iya yin amfani da ikonsa a koꞌina. Saboda haka, ko da yake Israꞌilawan suna cikin daji, Jehobah zai iya ba su nama da yawa. Kuma ya yi amfani da hannunsa “mai iko,” ya nuna musu abin da zai iya yi. (Zab. 136:​11, 12) Don haka, idan muna fama da wata matsala, mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai iya taimaka mana a duk inda muke.—Zab. 138:​6, 7.

8. Me zai taimaka mana kada mu yi irin kuskuren da Israꞌilawa da yawa suka yi a daji? (Ka kuma duba hoton.)

8 Jehobah ya cika alkawarinsa, kuma ya turo musu kajin-daji masu yawan gaske. Amma Israꞌilawan ba su yi godiya don wannan abin ban mamakin da Allah ya yi musu ba. A maimakon haka, da yawa cikinsu sun kwashe fiye da abin da suke bukata. Sun yi kwana ɗaya da rabi suna kwasa, ba dare ba rana. Jehobah ya yi fushi da “masu kwaɗayin” nan, kuma ya yi musu horo. (L. Ƙid. 11:​31-34) Mene ne hakan ya koya mana? Ya kamata mu yi hattara kada mu zama masu haɗama. Ko da mu masu arziki ne ko talakawa, zai dace mu tara wa kanmu “dukiya a sama” ta wajen ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah da kuma Yesu. (Mat. 6:​19, 20; Luk. 16:9) Idan muka yi hakan, za mu iya tabbata cewa Jehobah zai tanadar mana da abin da muke bukata.

Israꞌilawa suna tattara kajin daji da yawa har tsakan dare.

Mene me mutane da yawa suka yi da Allah ya ba su nama a daji, kuma mene ne hakan ya koya mana? (Ka duba sakin layi na 8)


9. Wane tabbaci ne ya kamata mu kasance da shi?

9 Jehobah yana shirye ya taimaka wa bayinsa a yau. Shin, hakan yana nufin cewa ba za mu taɓa samun kanmu cikin rashin kuɗi ko abinci ba? Aꞌa.b Amma Jehobah ba zai taɓa ƙyale mu ba. Zai ba mu ƙarfin da muke bukata a kullum saꞌad da muke fama da matsaloli. Ta yaya za mu nuna mun gaskata cewa Jehobah zai yi mana tanadin abubuwan da muke bukata? Bari mu yi laꞌakari da yanayoyi biyu: (1) lokacin da muke bukatan kuɗi da kuma (2) idan muna tunanin yadda za mu kula da kanmu idan muka tsufa.

IDAN MUNA BUKATAN KUƊI

10. Mene ne zai iya faruwa da zai sa mu soma neman aiki ko kuɗi?

10 Yayin da muke ƙara kusantar ƙarshen zamanin nan, matsalolin tattalin arziki za su ci-gaba da ƙaruwa. Ban da haka ma, rikicin siyasa, ko taꞌaddanci, ko balaꞌoꞌi, ko kuma ɓarkewar annoba za su iya sa mu kashe kuɗin da ba mu yi tsammani ba. Ƙari ga haka, za su iya sa mu rasa aikinmu ko dukiyarmu ko kuma gidajenmu. Kuma hakan zai iya sa mu soma neman sabon aiki ko mu yi tunanin ƙaura zuwa wani wuri tare da iyalinmu don mu iya biyan bukatunsu. Me zai taimaka mana mu tsai da shawarar da za ta nuna cewa mun dogara ga Jehobah?

11. Me zai taimaka mana mu san abin da za mu yi idan muna fama da matsalolin kuɗi? (Luka 12:​29-31)

11 Abu mafi muhimmanci da za mu yi shi ne gaya wa Jehobah game da yanayin da muke ciki. (K. Mag. 16:3) Ka roƙe shi ya taimaka maka ka yanke shawara mai kyau, ya sa ka sami kwanciyar hankali, kuma ka rage damuwa. (Karanta Luka 12:​29-31.) Ka roƙe shi ya taimaka maka ka gamsu da abin da kake da shi. (1 Tim. 6:​7, 8) Ka yi bincike a littattafanmu don ka ga abin da za ka iya yi idan kana fama da matsalolin kuɗi. Mutane da yawa da suke fama da matsalolin kuɗi, sun amfana daga talifofi da bidiyoyin da ke jw.org.

12. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka wa mutum ya zaɓi abin da zai fi taimaka wa iyalinsa?

12 Wasu sun karɓi aikin da zai sa su bar iyalinsu su je wani wuri su yi aiki, amma a kwana a tashi sun ga cewa hakan bai dace ba. Kafin ka soma yin wani aiki, kada ka yi tunani a kan albashin da za ka samu kawai, amma zai dace ka san ko aikin zai ba ka damar kusantar Jehobah tare da iyalinka. (Luk. 14:28) Ka tambayi kanka: ‘Me zai faru da aurenmu idan ni kaɗai na tafi? Zan sami damar halartar taro da fita waꞌazi da kuma yin cuɗanya da ꞌyanꞌuwa a kai a kai?’ Idan kana da yara, zai dace ka yi wa kanka wannan tambaya mai muhimmanci: ‘Ta yaya zan yi wa yarana “horo da gargaɗi ta hanyar Ubangiji” idan ba na tare da su?’ (Afis. 6:4) Saꞌad da kake so ka zaɓi abin da za ka yi, ka bi raꞌayin Jehobah, ba na ꞌyanꞌuwa da abokan arzikin da ba sa bin abin da ke Littafi Mai Tsarki ba.c Wani ɗanꞌuwa mai suna Tony, da ke zama a yammacin Asiya, ya sami damar yin aiki a wata ƙasa sau da yawa, kuma an ce za a biya shi kuɗi mai yawa. Amma bayan ya yi adduꞌa kuma ya tattauna batun da matarsa, ya ƙi dukan ayyukan, saꞌan nan suka yi ƙoƙarin rage yawan kuɗaɗen da suke kashewa. Tony ya ce: “Yanzu na sami damar taimaka wa mutane da yawa su soma bauta wa Jehobah, kuma yaranmu suna jin daɗin bauta masa. Dukanmu a iyali mun koyi cewa muddin mun bi abin da Yesu ya faɗa a Matiyu 6:​33, Jehobah zai kula da mu.”

YADDA ZA MU KULA DA KANMU IDAN MUKA TSUFA

13. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi yanzu da za su taimaka mana mu biya bukatunmu idan muka tsufa?

13 Za mu iya nuna cewa mun dogara ga Jehobah saꞌad da muke shirya yadda rayuwarmu za ta kasance idan muka tsufa. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi aiki sosai don mu iya biyan bukatunmu. (K. Mag. 6:​6-11) Idan zai yiwu, ba laifi ba ne mu ajiye kuɗin da za mu iya amfani da shi idan muka tsufa ba. Ba shakka kuɗi yana taimaka mana idan muna da bukata. (M. Wa. 7:12) Duk da haka, kada mu mai da neman kuɗi ya zama abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu.

14. Ta yaya abin da ke Ibraniyawa 13:5 zai taimaka mana kar mu damu sosai saꞌad da muke shirya yadda za mu biya bukatunmu a nan gaba?

14 Yesu ya ba da wani misali da ya nuna cewa idan mutum yana tara wa kansa kuɗi amma “a gaban Allah ba shi da arziki,” hakan wawanci ne. (Luk. 12:​16-21) Babu wanda ya san abin da zai faru gobe. (K. Mag. 23:​4, 5; Yak. 4:​13-15) Ƙari ga haka, Yesu ya ce duk wanda yake so ya zama mabiyinsa, wajibi ne ya zama a shirye ya “bar duk abin da yake da shi.” (Luk. 14:33) Abin da Kiristocin da ke Yahudiya a ƙarni na farko suka yi ke nan. Sun kasance a shirye su rasa duk abin da suka mallaka. (Ibran. 10:34) A zamaninmu ma, ꞌyanꞌuwa da yawa sun sadaukar da dukiyoyinsu domin sun ƙi su goyi bayan ƙungiyoyin siyasa. (R. Yar. 13:​16, 17) Me ya taimaka musu su yi hakan? Sun gaskata da alkawarin da Jehobah ya yi cewa: “Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.” (Karanta Ibraniyawa 13:5.) Muna iya ƙoƙarinmu mu shirya abin da muke bukata, amma idan abin da ba mu yi zato ba ya faru, muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana.

15. Wane raꞌayi ne ya kamata iyaye su kasance da shi game da yaransu? (Ka kuma duba hoton.)

15 A wasu wurare, maꞌaurata suna haifan yara ne da niyyar cewa yaran za su yi kuɗi kuma su taimaka musu idan sun tsufa. Littafi Mai Tsarki ya ce iyaye ne suke da hakkin biyan bukatun yaransu. (2 Kor. 12:14) Babu shakka, saꞌad da iyaye suka soma tsufa, za su bukaci yaransu su taimaka musu da kuɗi da kuma wasu abubuwa, kuma yara da yawa suna jin daɗin taimakawa. (1 Tim. 5:4) Amma iyaye masu dogara ga Jehobah sun san cewa abin da ya fi kawo farin ciki, shi ne taimaka wa yara su bauta wa Jehobah, ba renon su da niyyar cewa za su yi kuɗi su zo su kula da su ba.—3 Yoh. 4.

Wasu maꞌaurata suna farin ciki yayin da suna magana da ꞌyarsu da mujinta ta bidiyo. ꞌYar da mijinta suna sanye da kayan masu gini.

Maꞌauratan da suka dogara ga Jehobah suna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce saꞌad da suke tsai da shawarwari (Ka duba sakin layi na 15)d


16. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su sami kuɗin biyan bukatunsu idan suka yi girma? (Afisawa 4:28)

16 Saꞌad da kake taimaka wa yaranka su iya biyan bukatunsu, ka nuna musu cewa kai ma ka dogara ga Jehobah. Tun suna ƙanana, ka koya musu cewa yin aiki tuƙuru yana da kyau. (K. Mag. 29:21; karanta Afisawa 4:28.) Yayin da suke girma ka taimaka musu su yi iya ƙoƙarinsu a makaranta. Iyaye za su iya yin bincike don su sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa yaransu su san yawan karatun boko da za su yi. Hakan zai taimaka wa yaran su iya biyan bukatunsu kuma su sami lokacin yin waꞌazi ko kuma su yi hidimar majagaba.

17. Wane tabbaci ne muke da shi?

17 Masu dogara ga Jehobah suna da tabbaci cewa zai iya tanadar musu abubuwan da suke bukata kuma yana da niyyar yin hakan. Yayin da muke kusantar ƙarshen wannan zamanin, za mu fuskanci abubuwan da za su gwada bangaskiyarmu. Amma ko da mene ne ya faru, bari mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba mu abubuwan da muke bukata. Kuma zai ci-gaba da taimaka mana ko da a ina ne muke.

MECE CE AMSARKA?

  • Me za mu iya koya daga abin da ya faru da Musa da kuma Israꞌilawa?

  • Ta yaya za mu nuna cewa mun dogara ga Jehobah idan muna fama da matsalolin kuɗi?

  • Me zai taimaka mana saꞌad da muke shirya yadda za mu iya biyan bukatunmu idan muka tsufa?

WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto

a Ka duba, “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta Oktoba 2023.

b Ka duba, “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2014.

c Ka duba talifin nan, “Ba Wanda Zai Iya Bauta wa Iyayengiji Biyu” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2014.

d BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da matarsa suna magana da ꞌyarsu da mijinta da suke aiki a wani wurin da ake gina Majamiꞌar Mulki ta waya.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba