TALIFIN NAZARI NA 15
WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina
‘Yana da Kyau Mu Yi Kusa da Allah!’
‘Amma a gare ni, yana da kyau in yi kusa da Allah.’—ZAB. 73:28.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda za mu kusaci Jehobah da yadda yin hakan zai amfane mu.
1-2. (a) Me muke bukatar mu yi idan muna so mu ƙulla abota da wani? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
KANA da aboki na kud da kud? Me ya sa dangantakarku ta yi danƙo? Ba mamaki kuna kasancewa tare sosai, ka san abubuwa da yawa game da shi, kuma ka san abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so. Mai yiwuwa ka ga cewa yana halaye masu kyau da za ka so ka koya. Kuma hakan ya sa ka ƙaunace shi.
2 Idan kana so ka ƙulla abota da wani, wajibi ne ku kusaci juna. Haka ma yake da Allah. Idan kana so ka ƙulla dangantaka mai kyau da shi, wajibi ne ka kusace shi. A talifin nan, za mu ga yadda za mu kusaci Jehobah da yadda yin hakan zai amfane mu. Da farko, bari mu ga dalilin da ya sa ya dace mu kusaci Jehobah, abokinmu na ƙwarai.
3. Me ya sa ya kamata mu yi tunani a kan yadda za mu amfana idan muka kusaci Jehobah? Ka ba da misali.
3 Babu shakka mun san cewa ƙulla abota da Allah abu ne mai kyau. Amma yin tunani a kan yadda hakan yake da kyau sosai zai taimaka mana mu ci gaba da kusantar sa. (Zab. 63:6-8) Alal misali, cin abinci mai gina jiki, da motsa jiki, da samun isashen hutu da kuma shan ruwa sosai yana da kyau a jikinmu. Duk da haka, mutane da yawa ba su damu da abubuwan nan ba kuma suna watsi da lafiyarsu. Amma idan muna yin abubuwan da za su taimaka ma jikinmu, hakan zai sa mu kasance da koshin lafiya. Hakazalika, mun san cewa ƙulla abota da Jehobah yana da kyau, amma idan muka ci gaba da yin tunani a kan dalilin da ya sa hakan yake da kyau sosai, za mu daɗa kusantar sa.—Zab. 119:27-30.
4. Mene ne marubucin Zabura 73:28 ya ce?
4 Karanta Zabura 73:28. Marubucin Zabura 73 Balawi ne, kuma yana cikin mawaƙa da suke haikalin Jehobah. Ba mamaki ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah da aminci. Duk da haka, ya san cewa yana da muhimmanci ya riƙa tuna wa kansa da kuma wasu cewa, “yana da kyau a yi kusa da Allah.” Ta yaya za mu amfana idan mun yi hakan?
YIN “KUSA DA ALLAH” NA SA MUTUM FARIN CIKI
5. (a) Me ya sa muke farin ciki idan muka ci gaba da kusantar Jehobah? (b) Ta yaya shawarwarin da Jehobah ya yi mana tanadinsu a Kalmarsa suke kāre da kuma taimaka mana? (Karin Magana 2:6-16)
5 Idan mun ci gaba da kusantar Jehobah, hakan zai sa mu riƙa farin ciki. (Zab. 65:4) Akwai dalilai da yawa da suka nuna cewa za mu yi farin ciki. Alal misali, idan muka karanta kuma muka bi abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, za mu zama masu hikima. Abubuwan da Jehobah yake koya mana ta Kalmarsa za su iya kāre mu daga munanan abubuwa da kuma yin kurakurai masu tsanani. (Karanta Karin Magana 2:6-16.) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, wanda kuma ya sami fahimta.”—K. Mag. 3:13.
6. Me ya sa marubucin Zabura ta 73 ya daina farin ciki?
6 A wasu lokuta, bayin Jehobah ma sukan yi baƙin ciki. Abin da ya faru da marubucin Zabura ta 73 ke nan, saꞌad da ya soma tunani a kan abubuwa da yake ganin rashin adalci ne. Ya soma ƙishin mugayen mutane kuma hakan ya sa shi fushi. Ya ga kamar mugayen mutane da ba su damu da Allah ba kuma ba sa bin ƙaꞌidodinsa suna jin daɗin rayuwa. Ya ɗauka cewa masu mugunta da masu girman kai ne suke da arziki, da koshin lafiya, kuma ba sa shan wahala. (Zab. 73:3-7, 12) Rashin adalcin da yake gani ya sa ya yi tunani cewa a banza ne yake bauta wa Jehobah. Saꞌad da yake cikin baƙin ciki, ya ce: “Hakika, a banza ne na tsabtace zuciyata, na wanke hannuna in nuna rashin laifina.”—Zab. 73:13.
7. Idan muna baƙin ciki, me za mu iya yi? (Ka duba hoton.)
7 Mai zaburar bai ci gaba da baƙin ciki har ya yi sanyin gwiwa ba. A maimakon haka, ya ɗau mataki nan da nan. Ya “shiga Wuri Mai Tsarki na Allah,” kuma Jehobah ya taimaka masa ya canja tunaninsa. (Zab. 73:17-19) A duk saꞌad da muke baƙin ciki, Jehobah, abokinmu na ƙwarai yana sane da hakan. Idan mun roƙe shi, zai taimaka mana ta wajen ba mu shawarwari daga Kalmarsa. Ƙari ga haka, zai sa ꞌyanꞌuwa su ƙarfafa mu don mu ci gaba da bauta masa ko a lokacin da muke baƙin ciki. Kuma Jehobah zai taimaka mana mu sami kwanciyar hankali ko a lokacin da muke da matsaloli da yawa kuma mun ratsa abin yi.—Zab. 94:19.a
Balawin da ya rubuta Zabura ta 73, yana tsaye a “Wuri Mai Tsarki na Allah” (Ka duba sakin layi na 7)
YIN “KUSA DA ALLAH” ZAI SA MU YI RAYUWA MAI INGANCI YANZU KUMA MU ZAMA DA BEGE
8. A waɗanne hanyoyi masu muhimmanci kuma za mu amfana idan muka kusaci Allah?
8 Ga wasu hanyoyi biyu kuma masu muhimmanci da za mu amfana idan muka kusaci Allah. Na farko, yana sa mu yi rayuwa mai inganci a yanzu. Na biyu, yana sa mu kasance da tabbaci cewa za mu yi rayuwa mai kyau a nan gaba. (Irm. 29:11) Bari mu ga yadda abubuwa biyun nan za su amfane mu.
9. Ta yaya yin kusa da Jehobah yake sa mu farin ciki sosai?
9 Idan Jehobah amininmu ne, za mu yi rayuwa mai inganci. Mutane da yawa a yau da ba su yarda cewa akwai Allah ba suna ganin kamar rayuwa ba ta da maꞌana, kuma a kwana a tashi, ba wanda zai kasance a duniya. Amma mu da ke nazarin Kalmar Allah, muna da tabbaci cewa “akwai Allah kuma yana ba da lada ga duk waɗanda suke nemansa.” (Ibran. 11:6) Ƙari ga haka, Jehobah ya halicce mu don mu bauta masa ne. Don haka, idan mun bauta masa, mukan yi farin ciki sosai.—M. Sha. 10:12, 13.
10. Wane alkawari ne Jehobah ya yi ma waɗanda suka dogara gare shi? (Zabura 37:29)
10 Mutane da yawa ba su da bege. Suna zuwa aiki ne kawai, su yi aure, su haifi ꞌyaꞌya, saꞌan nan su yi ajiya don su iya kula da kansu bayan sun daina aiki. Ba su san alkawarin da Allah ya yi game da nan gaba ba. Amma mu bayin Jehobah mun san cewa Jehobah zai kula da mu. (Zab. 25:3-5; 1 Tim. 6:17) Mun ba da gaskiya ga Allahnmu da kuma Abokinmu. Kuma mun san cewa zai cika alkawarinsa. Muna da abubuwa da yawa da muna sa ran yi a nan gaba, kamar bauta masa har abada a cikin aljanna.—Karanta Zabura 37:29.
11. Me za mu samu idan muka kusaci Jehobah, kuma yaya zai ji idan muka yi hakan?
11 Har ila, akwai wasu hanyoyi kuma da yawa da za mu amfana idan muka kusaci Jehobah. Alal misali, Jehobah ya ce zai gafarta mana idan muka tuba. (Isha. 1:18) Don haka, bai kamata mu ci gaba da damuwa don wani zunubin da muka yi a dā ba. (Zab. 32:1-5) Ƙari ga haka, za mu ji daɗi idan muna yin abin da zai faranta wa Jehobah rai. (K. Mag. 23:15) Hakika, akwai albarku da yawa da za mu samu idan muka zama aminan Jehobah. Bari mu ga abin da za mu iya yi don mu ci gaba da kusantar Allah.
YADDA ZA MU CI GABA DA YIN “KUSA DA ALLAH”
12. Mene ne ka yi don ka kusaci Jehobah?
12 Kafin mu yi baftisma kuma mu zama Shaidun Jehobah, mun yi abubuwa da yawa don mu zama aminan Jehobah. Mun koyi gaskiya game da Jehobah da kuma Yesu Kristi, mun tuba daga zunubanmu, mun ba da gaskiya ga Allah, kuma mun yi iya ƙoƙarinmu don mu yi masa biyayya. Amma don mu ci gaba da kusantar Allah, muna bukatar mu ci gaba da yin abubuwan nan.—Kol. 2:6.
13. Waɗanne abubuwa uku ne za su iya taimaka mana mu ci gaba da kusantar Jehobah?
13 Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da kusantar Jehobah? (1) Wajibi ne mu ci gaba da karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki. Yayin da muke karanta Littafi Mai Tsarki, kada mu yi ƙoƙarin sanin abubuwa game da Allah sama-sama kawai. A maimakon haka, mu yi ƙoƙari mu san nufin Allah, da abin da yake so mu yi kuma mu yi rayuwa yadda yake so. (Afis. 5:15-17) (2) Wajibi ne mu ƙarfafa bangaskiyarmu ta wajen yin tunani a kan hanyoyi da yawa da Allah yake nuna wa kowannenmu ƙauna. (3) Wajibi ne mu ci gaba da ƙin abin da Jehobah ba ya so kuma mu guji mutanen da ke yin abubuwan.—Zab. 1:1; 101:3.
14. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi kowace rana don mu faranta wa Jehobah rai? (1 Korintiyawa 10:31) (Ka kuma duba hotunan.)
14 Karanta 1 Korintiyawa 10:31. Yana da muhimmanci mu riƙa yin abubuwan da mun san cewa za su faranta wa Jehobah rai. Hakan ba ya nufin fita waꞌazi da zuwa taro kawai. Ya kamata abubuwan da muke yi kullum su riƙa faranta wa Jehobah rai. Alal misali, idan muna faɗin gaskiya kuma muna bayarwa hannu sake, hakan zai sa Jehobah farin ciki. (2 Kor. 8:21; 9:7) Ƙari ga haka, yana so mu nuna cewa muna godiya sosai don rai da ya ba mu. Za mu yi hakan ta wajen mai da hankali ga yawan abubuwan da muke ci da sha, kuma mu ci gaba da yin abubuwa da za su sa mu sami koshin lafiya. Idan Jehobah ya ga cewa muna iya ƙoƙarinmu don mu faranta masa rai, hakan yana sa ya ƙaunace mu sosai.—Luk. 16:10.
Yin tuƙi da kyau, da kula da kanmu ta wajen motsa jiki, da cin abinci mai gina jiki, da kuma bayarwa hannu sake suna cikin hanyoyin da za mu faranta wa Jehobah rai (Ka duba sakin layi na 14)
15. Mene ne Jehobah yake so mu riƙa yi wa mutane? Ka bayyana.
15 Jehobah yana nuna wa kowa alheri ko da suna bauta masa ko aꞌa. (Mat. 5:45) Yana so mu ma mu nuna wa mutane alheri. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu yi ma ‘wani muguwar magana, mu zauna cikin salama, mu kasance da sauƙin kai, kuma mu yi wa kowa cikakken tawaliꞌu.’ (Tit. 3:2) Don haka, ko da a ce mutane ba su gaskata da Jehobah ba, bai kamata mu ɗauka cewa mun fi su ba. (2 Tim. 2:23-25) Za mu ci gaba da kusantar Jehobah idan muna nuna wa kowa alheri.
ZA MU IYA YIN “KUSA DA ALLAH” KO DA MUN YI KUSKURE
16. Yaya marubucin Zabura ta 73 ya soma ji bayan wasu lokuta?
16 A wasu lokuta, kana iya ji kamar kai ba aminin Jehobah ba ne don wani kuskuren da ka yi. Amma ka tuna da misalin marubucin Zabura ta 73. Ya ce: “Ƙafafuna sun yi santsi, har tafin ƙafata yana gab da faɗuwa.” (Zab. 73:2) Shi da kansa ya faɗi cewa “zuciyarsa ta ɓaci” kuma ya “zama wawa” “kamar dabba” a gaban Jehobah. (Zab. 73:21, 22) Shin, ya ɗauka cewa domin kuskurensa, Jehobah ba zai sake ƙaunarsa kuma ya gafarta masa ba?
17. (a) Mene ne marubucin zaburar ya yi har a lokacin da yake fama da baƙin ciki? (b) Wane darasi ne za mu iya koya daga labarinsa? (Ka kuma duba hotunan.)
17 Duk da cewa marubucin zaburar ya ji kamar Jehobah bai damu da shi ba, ya yi tunanin nan na ɗan lokaci ne kawai. A lokacin da yake fama da baƙin ciki, ya gane cewa kusantar Allah ne zai taimaka masa. Shi ya sa ya ce: “Duk da haka ina ta kasance kusa da kai, ka kuma riƙe ni a hannun damana. Shawararka ce take bi da ni, a ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.” (Zab. 73:23, 24) Mu ma muna bukatar mu roƙi Jehobah ya taimaka mana, musamman a lokacin da muke fama da baƙin ciki ko idan mun yi zunubi. (Zab. 73:26; 94:18) Ko da zunubin da muka yi mai tsanani ne, za mu iya komowa ga Jehobah da tabbaci cewa zai gafarta mana. (Zab. 86:5) Idan wani abu ya sa mu sanyin gwiwa sosai, yana da muhimmanci mu kusaci Allah.—Zab. 103:13, 14.
Idan muna gani ya kamata mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, zai dace mu kusace shi ta wajen yin adduꞌa sosai da kuma zuwa taro a kai a kai (Ka duba sakin layi na 17)
ZA MU IYA YIN “KUSA DA ALLAH” HAR ABADA
18. Me ya sa za mu iya ci gaba da kusantar Jehobah har abada?
18 Za mu iya ci gaba da kusantar Jehobah har abada, domin ba za mu daina koyan abubuwa game da shi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce hanyoyin Jehobah, da hikimarsa, da iliminsa, “sun wuce gaban ganewa!”—Rom. 11:33.
19. Mene ne littafin Zabura ya tabbatar mana?
19 Zabura 79:13 ta ce: “Mu jamaꞌarka kuwa, tumakin garkenka, za mu yi ta gode maka har abada, daga tsara zuwa tsara za mu lissafta yabonka.” Mu ma muna da tabbaci cewa idan mun ci gaba da kusantar Allah, zai albarkace mu har abada, kuma ba tare da shakka ba za mu ce: “Allah shi ne ƙarfin zuciyata, abin da nake da shi har abada.”—Zab. 73:26.
WAƘA TA 32 Mu Kasance da Aminci ga Jehobah!
a Wasu mutanen da suka daɗe suna fama da baƙin ciki ko damuwa mai tsanani za su bukaci su ga likita. Don samun ƙarin bayani, ka duba Hasumiyar Tsaro, Na 1 2023.