Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Afrilu pp. 14-19
  • Yana da Kyau Mu Kusaci ꞌYanꞌuwa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yana da Kyau Mu Kusaci ꞌYanꞌuwa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DALILIN DA YA SA YA KAMATA MU KUSACI JUNA
  • MU GIRMAMA JUNA
  • “KADA KU ZAUNA A RABE”
  • “KU NUNA ƘAUNARKU TA WURIN AIKATAWA DA KUMA GASKIYA”
  • Jehobah Yana Ƙaunar Ka Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • ‘Yana da Kyau Mu Yi Kusa da Allah!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Bayarwa Za Ta Sa Ka Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Afrilu pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 16

WAƘA TA 87 Ku Zo Mu Sami Ƙarfafa!

Yana da Kyau Mu Kusaci ꞌYanꞌuwa!

“Hakika, abu mai kyau ne, mai daɗi kuma ꞌyanꞌuwa su zauna tare kamar ɗaya!”—ZAB. 133:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda za mu ci gaba da kusantar ꞌyanꞌuwanmu da kuma yadda Jehobah zai yi mana albarka idan muka yi hakan.

1-2. Wani abu ne Jehobah yake ɗauka da muhimmanci sosai, kuma me yake so mu yi?

JEHOBAH yana ɗaukan yadda muke shaꞌani da mutane da muhimmanci sosai. Yesu ya ce wajibi ne mu ƙaunaci maƙwabtanmu kamar yadda muke ƙaunar kanmu. (Mat. 22:​37-39) Hakan ya nuna cewa za mu ƙaunaci kowa har da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. Idan muka yi hakan, zai nuna cewa muna koyi da Jehobah “wanda yake sa rana ta yi haske a kan masu kirki da marasa kirki ma, ya kuma aiko ruwan sama a kan masu adalci da marasa adalci.”—Mat. 5:45.

2 Duk da cewa Jehobah yana ƙaunar dukan mutane, ya fi ƙaunar waɗanda suke yi masa biyayya. (Yoh. 14:21) Kuma yana so mu yi koyi da shi. Ya umurce mu mu “ƙaunaci juna da ƙauna ta ainihi” kuma mu nuna musu “ƙauna irin ta ꞌyanꞌuwa.” (1 Bit. 4:8; Rom. 12:10) Irin ƙauna da ayoyin nan suke magana a kai shi ne irin ƙaunar da ke tsakanin abokai na kud da kud ko dangi.

3. Me ya kamata mu riƙa tunawa game da ƙauna?

3 Kamar yadda muke kula da shuke-shuken da ke lambunmu don su yi girma, muna bukatar mu sa ƙaunar da muke yi wa mutane ta ci gaba da ƙaruwa. Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci cewa: “Ku ci gaba da nuna wa junanku ƙauna irin ta ꞌyanꞌuwa.” (Ibran. 13:1) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana so mu ci gaba da ƙaunar mutane. A talifin nan, za mu tattauna dalilin da ya sa ya kamata mu kusaci ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci da kuma yadda za mu ci gaba da yin hakan.

DALILIN DA YA SA YA KAMATA MU KUSACI JUNA

4. Bisa ga Zabura 133:​1, me za mu yi don mu tabbata cewa mun ci gaba da daraja haɗin kai da ke tsakaninmu? (Ka kuma duba hotunan.)

4 Karanta Zabura 133:1. Babu shakka, raꞌayinmu ɗaya ne da mai Zabura da ya ce, yin abota da masu ƙaunar Jehobah yana da “kyau” kuma abu “mai daɗi” ne. Amma kamar yadda ido kan rena abin da yake gani kullum, idan ba mu yi hankali ba, za mu daina daraja haɗin kai da ke tsakaninmu. Da yake muna haɗuwa da ꞌyanꞌuwanmu sau da yawa kowane mako, me za mu yi don mu tabbata cewa mun ci gaba da daraja su? Ya kamata mu ɗau lokaci don mu yi tunani a kan irin amfani da ꞌyanꞌuwanmu suke da shi a ikilisiya da kuma a gare mu. Idan muka yi hakan, za mu ci gaba da ƙaunar su sosai.

Hotuna: Na 1. Wata ꞌyarꞌuwa tana kallon wani bishiya da ganyen sun canja kala. Na 2. Daga baya, ꞌyarꞌuwar ta rungumi wata ꞌyarꞌuwa a taron yanki. Wasu ꞌyanꞌuwa kuma a gefe suna taɗi suna dariya.

Kada mu daina daraja haɗin kai da ke tsakaninmu (Ka duba sakin layi na 4)


5. Idan mutane suka ga irin ƙaunar da muke nuna wa juna, me hakan yakan sa su yi?

5 Wasu da suka halarci taronmu a karo na farko sukan yi mamaki sosai don irin ƙaunar da muke nuna wa juna. Mai yiwuwa hakan yakan tabbatar musu cewa mu ne Kiristoci na gaskiya. Yesu ya ce: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yoh. 13:35) Labarin Chaithra, da take nazari da Shaidun Jehobah zai taimaka mana mu fahimci hakan. An gayyace ta wani taron yanki kuma ta amince. Bayan da ta halarci rana ta farko, sai ta gaya wa wadda take nazari da ita cewa: “Iyayena ba su taɓa rungumata ba. Amma a taronku, mutane 52 sun rungume ni a rana ɗaya kawai! Na tabbata cewa Jehobah ya yi amfani da mutanensa ne don ya nuna min yadda yake ƙauna ta. Ina so in kasance a iyalin nan.” Chaithra ta sami ci gaba har ma ta yi baftisma a 2024. Ba shakka idan mutane suka ga halayenmu masu kyau, musamman ƙauna da muke nuna wa juna, haka yakan sa su so bauta wa Jehobah.—Mat. 5:16.

6. Ta yaya kusantar ꞌyanꞌuwanmu zai iya zama mana kāriya?

6 Idan muna kusantar ꞌyanꞌuwanmu, hakan zai iya zama mana kāriya. Bulus ya gaya wa Kiristoci cewa: “Ku ɗinga ƙarfafa juna kowace rana . . . domin kada ko ɗayanku ya zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗu na zunubi.” (Ibran. 3:13) Idan muka yi sanyin gwiwa, har yin abubuwan da suka dace ya soma mana wuya, Jehobah zai iya amfani da wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ya taimaka mana. (Zab. 73:​2, 17, 23) Irin taimakon nan zai amfane mu sosai.

7. Wace alaƙa ce ke tsakanin ƙauna da haɗin kai? (Kolosiyawa 3:​13, 14)

7 Muna cikin mutanen da suke iya ƙoƙarinsu su nuna wa juna ƙauna, don haka muna more albarku da yawa. (1 Yoh. 4:11) Alal misali, ƙauna takan sa mu yi “ta yin haƙuri da juna,” kuma hakan yakan taimaka mana mu zama da haɗin kai. (Karanta Kolosiyawa 3:​13, 14; Afis. 4:​2-6) Shi ya sa muna jin daɗin taronmu fiye da kowace ƙungiya a duniya.

MU GIRMAMA JUNA

8. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu kasance da haɗin kai?

8 Haɗin kai da muke morewa a faɗin duniya abin ban mamaki ne. Jehobah ne yake taimaka mana mu kasance da irin wannan haɗin kai duk da cewa mu ajizai ne. (1 Kor. 12:25) Littafi Mai Tsarki ya ce, “Allah ya koya muku cewa ku ƙaunaci juna.” (1 Tas. 4:9) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana amfani da Littafi Mai Tsarki don ya koya mana ainihin abin da za mu yi don mu kusaci juna. Za mu nuna cewa mu waɗanda Allah yake koyar da su ne ta wajen yin nazarin Kalmarsa da kuma bin abin da ke ciki. (Ibran. 4:12; Yak. 1:25) Abin da Shaidun Jehobah suke iya ƙoƙari su yi ke nan.

9. Mene ne muka koya daga Romawa 12:​9-13 game da yadda za mu girmama juna?

9 Ta yaya Kalmar Allah take koya mana yadda za mu kusaci juna? Ga abin da Bulus ya faɗa game da wannan batun a Romawa 12:​9-13. (Karanta.) Bulus ya ce: “Kowa ya yi saurin girmama wani fiye da kansa.” Mene ne hakan yake nufi? Hakan yana nufin cewa mu nemi zarafin nuna “ƙauna irin ta ꞌyanꞌuwa” ta wajen, gafarta wa juna, da bayarwa hannu sake, da nuna alheri, da dai sauransu. (Afis. 4:32) Bai kamata mu jira sai ꞌyanꞌuwanmu sun kusace mu ba. Zai dace kowannenmu ya yi “saurin” kusantar ꞌyanꞌuwa. Idan mun yi hakan, za mu ga gaskiyar abin da Yesu ya faɗa cewa: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”—A. M. 20:35.

10. Ta yaya za mu kasance da ƙwazo wajen girmama juna? (Ka kuma duba hoton.)

10 Nan da nan bayan Bulus ya gaya mana mu yi saurin girmama juna, ya ƙarfafa mu cewa: “Kada ku taɓa zama da rashin ƙwazo.” Mutum mai ƙwazo yana aiki tuƙuru kuma ba ya ƙiwuya. Idan aka ba shi wani aiki, yana yinsa da kyau. Karin Magana 3:​27, 28 sun ce: “Kada ka janye alheri daga waɗanda sun cancanta a yi musu, saꞌad da ikon yin haka yana hannunka.” Saboda haka, idan muka ga wani da ke da bukata, za mu yi saurin taimaka masa. Ba ma ɓata lokaci ko mu ce ai wani zai yi.—1 Yoh. 3:​17, 18.

Wani matashi ya hau kan tsani, yana ciccire ganyaye daga kan kwanon gidan wani ɗanꞌuwa da ya tsufa.

Ya kamata mu riƙa taimaka wa ꞌyanꞌuwan da suke da bukata (Ka duba sakin layi na 10)


11. Me zai taimaka mana mu ƙara kusantar juna?

11 Wata hanya kuma da za mu girmama ꞌyanꞌuwanmu ita ce yafe musu da wuri idan suka yi mana laifi. Afisawa 4:26 ta ce: “Kada ma fushinku ya daɗe ya kai har rana ta faɗi.” Me ya sa? Aya 27 ta ce yin hakan zai “ba Shaiɗan wata dama.” A cikin Littafi Mai Tsarki Jehobah ya gaya mana sau da sau cewa mu riƙa gafarta wa juna. Kolosiyawa 3:13 ta ce, “Idan . . . wani a cikinku ya yi wa wani laifi, ku gafarta masa.” Babu abin da yake sa mutane su kusaci juna kamar idan suna gafarta wa juna. In muna gafarta wa juna, hakan zai taimaka wajen ‘kiyaye ɗayantakar nan da ruhu ya ba mu, ta wurin salamar da ta ɗaure mu tare.’ (Afis. 4:3) A taƙaice, idan mun gafarta wa juna, hakan zai sa mu kasance da haɗin kai da kuma salama.

12. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu zama masu gafartawa?

12 Gaskiyar ita ce, yana iya zama da wuya mu yafe wa waɗanda suka yi mana laifi. Amma za mu iya yafe musu da taimakon ruhu mai tsarki. Bayan Bulus ya ce mu riƙa nuna “ƙauna irin ta ꞌyanꞌuwa” kuma kada mu taɓa zama da “rashin ƙwazo,” sai ya ce: ‘mu ɗauki niyya sosai a zukatanmu.’ Juyin Littafi Mai Tsarki Mai Makamantu[n] Ayoyi ya ce: “ku himmantu a ruhu,” hakan yana nufin cewa ruhu mai tsarki ne zai taimaka mana mu kasance da niyyar yin abin da ya dace. (Rom. 12:11) Ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu iya nuna ƙauna irin ta ꞌyanꞌuwa kuma mu riƙa gafarta wa juna. Don haka, zai dace mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki.—Luk. 11:13.

“KADA KU ZAUNA A RABE”

13. Mene ne zai iya raba kanmu?

13 Mutanen da suke ikilisiya sun zo daga wurare dabam-dabam kuma alꞌadun su ba iri ɗaya ba ne. (1 Tim. 2:​3, 4) Saboda haka, mukan kasance da raꞌayi dabam-dabam game da irin kayan da muke sakawa, da ado, da nishaɗin, da kuma irin jinyar da muke so. Idan ba mu mai da hankali ba, abubuwan nan za su iya raba kanmu. (Rom. 14:4; 1 Kor. 1:10) Da yake ‘Allah ya koya mana cewa mu ƙaunaci juna,’ wajibi ne mu yi hattara don kada mu nace cewa raꞌayinmu ya fi na waɗansu.—Filib. 2:3.

14. Me ya kamata mu riƙa yi kowane lokaci, kuma me ya sa?

14 Wata hanya kuma da za mu iya guje wa abubuwan da za su raba kanmu ita ce, ta wajen ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da kuma kwantar musu da hankali a kowane lokaci. (1 Tas. 5:11) A kwana-kwanan nan, ꞌyanꞌuwan da suka daina zuwa taro da kuma fita waꞌazi da kuma waɗanda aka cire daga ikilisiya suna dawowa. Kuma muna karɓan su da hannu bibbiyu! (2 Kor. 2:8) Ga abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa da ta halarci taro, bayan ta yi shekaru goma da daina zuwa. Ta ce, “Kowa ya yi farin ciki da ganina kuma sun gaishe ni sosai.” (A. M. 3:19) Ta yaya yadda suka bi da ita ya taimake ta? Ta ce, “Abin da suka yi ya sa na gane cewa Jehobah ne yake so ya taimaka min in sake yin farin ciki.” Idan muna ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, Yesu zai iya sa mu taimaka ma waɗanda suka ‘gaji, kuma suna fama da kaya masu nauyi.’—Mat. 11:​28, 29.

15. Ta wace hanya ce kuma za mu sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai? (Ka kuma duba hoton.)

15 Wata hanya kuma da za mu sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai ita ce, ta wajen abin da muke faɗa. Ayuba 12:11 ta ce: “Yadda harshe yakan ɗanɗana daɗin abinci, haka nan kunne yakan auna kalmomin da yake ji.” Kamar yadda mai girki yakan ɗanɗana abin da yake dafawa don ya tabbata cewa kome ya yi daidai kafin ya ba wa mutane, zai dace mu yi tunani a kan abin da muke so mu faɗa kafin mu faɗe shi. (Zab. 141:3) Burinmu a kullum shi ne, abin da muke so mu faɗa ya zama abin ban ƙarfafa, da “amfani,” kuma ya zama abin da zai kwantar da hankalin mutane.—Afis. 4:29.

Wani ɗanꞌuwa yana ɗanɗana abincin da yake dafawa kafin ya ba wa bakinsa.

Zai dace mu riƙa yin tunani a kan abin da muke so mu faɗa kafin mu faɗe shi (Ka duba sakin layi na 15)


16. Su waye ne musamman suke bukata su ƙarfafa mutane da abin da suke faɗa?

16 Magidanta da kuma iyaye musamman suna bukatar su riƙa faɗin abin da zai ƙarfafa mutane. (Kol. 3:​19, 21; Tit. 2:4) Dattawa ma suna bukata su riƙa ƙarfafa bayin Jehobah, kuma su faɗi abin da zai kwantar musu da hankali. (Isha. 32:​1, 2; Gal. 6:1) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abu mai kyau ne magana ta fita a daidai lokaci.”—K. Mag. 15:23.

“KU NUNA ƘAUNARKU TA WURIN AIKATAWA DA KUMA GASKIYA”

17. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu da dukan zuciyarmu?

17 Manzo Yohanna ya ƙarfafa Kiristoci cewa: “Kada ku nuna ƙaunarku ta wurin surutun baki kawai, amma ku nuna ƙaunarku ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.” (1 Yoh. 3:18) Ya kamata mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwanmu da dukan zuciya. Ta yaya za mu yi hakan? Idan muna yawan cuɗanya da ꞌyanꞌuwanmu, hakan zai sa mu kusace su kuma ƙaunarmu gare su za ta ƙaru. Saboda haka, ka nemi hanyoyin yin cuɗanya da su a taro ko a waꞌazi. Ka riƙa ziyartar su. Yin hakan zai nuna cewa Allah ya koya mana mu “ƙaunaci juna.” (1 Tas. 4:9) Kuma za mu ci gaba da gani cewa: “Hakika, abu mai kyau ne, mai daɗi kuma ꞌyanꞌuwa su zauna tare kamar ɗaya!”—Zab. 133:1.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa yake da kyau mu kusaci ꞌyanꞌuwanmu?

  • Ta yaya za mu yi saurin girmama wani fiye da kanmu?

  • Ta yaya za mu sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai?

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba