TALIFIN NAZARI NA 33
WAƘA TA 4 “Jehobah Makiyayina Ne”
Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Yana Ƙaunar Ka
‘Na jawo ka wurina da ƙauna marar canjawa.’—IRM. 31:3.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga dalilin da ya sa ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, da kuma abin da za mu yi don mu ƙara tabbatawa da hakan.
1. Me ya sa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)
KA TUNA lokacin da ka yi wa Jehobah alkawari cewa za ka bauta masa da dukan zuciyarka? Ka yi hakan ne domin kana ƙaunar sa, kuma ka koyi abubuwa da yawa game da shi. Ka yi masa alkawari cewa za ka sa yin nufin sa farko a rayuwarka. Ka kuma ce za ka ci-gaba da ƙaunar sa da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka. (Mar. 12:30) Babu shakka, tun daga lokacin, ƙaunarka ga Jehobah sai daɗa ƙaruwa take yi. To, me za ka ce idan wani ya tambaye ka cewa, “Da gaske kana ƙaunar Jehobah?” Mun san cewa ba tare da ɓata lokaci ba, za ka ce masa, “E, ina ƙaunar sa fiye da kome da kowa!”
Shin, ka tuna da yadda ka ƙaunaci Jehobah lokacin da ka yi alkawarin bauta masa da kuma baftisma? (Ka duba sakin layi na 1)
2-3. Wane tabbaci ne Jehobah yake so mu kasance da shi, kuma mene ne za mu tattauna a wannan talifin? (Irmiya 31:3)
2 Mene ne za ka ce idan wani ya tambaye ka, “Kana da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuwa?” Mai yiwuwa za ka yi jinkiri kafin ka amsa, domin wataƙila, kana ganin ba ka cancanci Jehobah ya ƙaunace ka ba. Wata ꞌyarꞌuwa da tana ganin babu wanda ya ƙaunace ta a lokacin da take ƙarama ta ce: “Na san cewa ina ƙaunar Jehobah. Ban yi shakkar hakan ba. Amma sau da yawa ina shakka ko Jehobah yana ƙauna ta.” To, mene ne zai taimaka maka ka san ko Jehobah yana ƙaunar ka?
3 Jehobah yana so ka kasance da tabbaci cewa yana ƙaunar ka. (Karanta Irmiya 31:3.) Gaskiyar ita ce, Jehobah ne da kansa ya jawo ka wurinsa. Ƙari ga haka, saꞌad da ka yi alkawarin bauta masa kuma ka yi baftisma, ya ba ka wani abu mai daraja, wato, ƙaunarsa marar canjawa. Hakan yana nufin cewa yana ƙaunar ka sosai, kuma ba zai taɓa barin ka ba. Jehobah yana nuna wa dukan bayinsa masu aminci ƙauna marar canjawa. Yana ɗaukan su da daraja sosai. Saboda haka, kai ma kana da “daraja” a wurinsa. (Mal. 3:17) Jehobah yana so ka kasance da tabbaci cewa yana ƙaunar ka, kamar yadda manzo Bulus ya yi saꞌad da ya ce: “Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko malaꞌiku ko aljanu, ko halin yanzu ko na nan gaba, ko ikoki iri-iri, ko tsawo ko zurfi, ko wani abu dabam a dukan halitta, duk ba su isa ba sam su raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana.” (Rom. 8:38, 39) A wannan talifin, za mu ga dalilin da ya sa ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, da kuma abin za mu yi don mu ƙara tabbatawa da hakan.
ME YA SA MUKE BUKATAR MU TABBATA CEWA JEHOBAH YANA ƘAUNAR MU?
4. Wace ƙarya ce Shaiɗan yake yaɗawa, kuma ta yaya za mu yi tsayayya da wannan dabararsa?
4 Idan muna da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, hakan zai taimaka mana mu yi tsayayya da “dabarun Shaiɗan.” (Afis. 6:11) Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Wani mugun dabara da Shaiɗan yake amfani da shi shi ne, yaɗa ƙarya cewa Jehobah ba ya ƙaunar mu. Kada mu manta cewa Shaiɗan yana son amfani da kowace damar da ya samu. A yawancin lokuta, yana kawo mana hari ne a lokacin da ba mu da ƙarfi. Alal misali, zai iya yin hakan lokacin da muke sanyin gwiwa don abubuwan da suka faru da mu a dā, ko lokacin da muke fama da matsaloli, ko kuma lokacin da muke cikin damuwa don abubuwan da za su iya faruwa a nan gaba. (K. Mag. 24:10) Shaiɗan yana kama da zaki da yake neman dabbobin da suna nan su kaɗai, ko waɗanda ba su da ƙarfi. Saboda haka, idan Shaiɗan ya ga cewa muna cikin damuwa, zai so ya yi amfani da wannan damar don ya sa mu fid da rai. Amma idan mun ci-gaba da kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, hakan zai taimaka mana mu iya yin tsayayya da dabarun Shaiɗan.—1 Bit. 5:8, 9; Yak. 4:7.
5. Me ya sa sanin cewa Jehobah yana ƙauna da kuma daraja mu yake da muhimmanci?
5 Idan muna da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, hakan zai sa mu ƙara kusantar sa. Me ya sa muka ce hakan? Jehobah ya halicce mu yadda za mu ƙaunaci waɗanda suke ƙaunar mu. Shi ya sa idan mutane suka nuna mana cewa suna ƙaunar mu, mu ma muna nuna musu cewa muna ƙaunar su. Saboda haka, sanin cewa Jehobah yana ƙauna da kuma daraja mu, zai sa mu ƙara ƙaunar sa. (1 Yoh. 4:19) Kuma yayin da muke ƙara ƙaunar sa, shi ma zai ƙara ƙaunar mu. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.” (Yak. 4:8) Amma, me za mu yi don mu ƙara kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu?
ME ZAI TAIMAKA MANA MU KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH YANA ƘAUNAR MU?
6. Me muke bukatar mu yi idan muna shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu?
6 Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka fahimci dalilin da ya sa yake ƙaunar ka. (Luk. 18:1; Rom. 12:12) Mai yiwuwa, za ka bukaci ka roƙi Jehobah sau da yawa kowace rana, ya taimaka maka ka fahimci yadda yake ɗaukan ka. A wasu lokuta, zuciyarka za ta iya damun ka har ka ga kamar Jehobah ba ya ƙaunar ka. Amma, ka tuna cewa Jehobah ya fi zuciyarka, kuma ya san kome da kome. (1 Yoh. 3:19, 20) Ya san ka fiye da yadda ka san kanka, kuma yana ganin halaye masu kyau da kake da su da mai yiwuwa ba ka san kana da su ba. (1 Sam. 16:7; 2 Tar. 6:30) Saboda haka, ka gaya masa duk abin da ke zuciyarka, kuma ka roƙe shi ya taimaka maka ka yarda cewa yana ƙaunar ka. (Zab. 62:8) Bayan ka yi adduꞌa ga Jehobah, yana da muhimmanci ka yi abubuwan da za a ambata a gaba.
7-8. Ta yaya littafin Zabura ya taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu?
7 Ka yarda da abin da Jehobah ya faɗa. Jehobah ya ba wa waɗanda suka rubuta Kalmarsa ruhu mai tsarki. Saboda haka, abubuwan da suka faɗa game da Jehobah gaskiya ne. A littafin Zabura Dauda ya bayyana yadda Jehobah yake kula da mu a wata hanya mai kyau sosai. Ya ce: “Ga waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa, Yahweh yana kusa da su, yakan kuɓutar da masu fid da zuciya.” (Zab. 34:18) Idan kana cikin damuwa, za ka iya ga kamar babu wanda zai iya fahimtar ka, ko ya taimake ka. Amma a irin wannan lokacin, Jehobah ya yi alkawari cewa yana kusa da kai domin ya san cewa kana bukatar taimako. A wata aya kuma a littafin Zabura Dauda ya ce: “Ka sa hawayena cikin goranka.” (Zab. 56:8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.) Jehobah yana ganin lokacin da kake fama kuma kana zub da hawaye. Ya damu da kai sosai, kuma ba ya so ya ga kana fama da wahala. Kamar yadda mai tafiya a hamada yake daraja ruwan da ke cikin gorarsa, haka Jehobah yake daraja hawayenka. Kuma yana tuna kowane lokaci da kake cikin damuwa kuma ka zub da hawaye. A Zabura 139:3, Dauda ya ce: “Ka saba da dukan alꞌamurana.” Duk da cewa Jehobah yana ganin dukan alꞌamuranmu, yana mai da hankali ga abubuwa masu kyau da muke yi. (Ibran. 6:10) Me ya sa? Domin yana daraja duk ƙoƙarin da muke yi don mu faranta masa rai.a
8 Jehobah yana amfani da irin Nassosin nan masu ban ƙarfafa don ya nuna mana cewa ya damu da mu, kuma yana ƙaunar mu sosai. Amma kamar yadda muka gani ɗazu, Shaiɗan yana yaɗa ƙarya cewa Jehobah ba ya ƙaunar mu. Saboda haka, idan a wasu lokuta ka soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar ka, ka ɗan dakata, kuma ka tambayi kanka, ‘Waye ne zan yarda da shi, “uban ƙarya” ko “Allah mai aminci”?’—Yoh. 8:44; Zab. 31:5.
9. Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa duk waɗanda suke ƙaunar sa? (Fitowa 20:5, 6)
9 Ka yi tunani a kan yadda Jehobah yake ɗaukan waɗanda suke ƙaunar sa. Ka yi laꞌakari da abin da Jehobah ya gaya wa Musa da kuma Israꞌilawa. (Karanta Fitowa 20:5, 6.) Jehobah ya yi alkawari cewa zai ci-gaba da nuna wa masu ƙaunar sa ƙauna marar canjawa. Hakan ya tabbatar mana cewa, idan mun ƙaunaci Jehobah, tabbas zai ƙaunace mu, domin shi Allah mai aminci ne. (Neh. 1:5) Saboda haka, idan ka soma ji kamar Jehobah ba ya ƙaunar ka, ka ɗan dakata, kuma ka tambayi kanka, ‘Ina ƙaunar Jehobah?’ Idan kana ƙaunar Jehobah, kuma kana iya ƙoƙarinka don ka faranta masa rai, ka kasance da tabbaci cewa yana ƙaunar ka sosai. (Dan. 9:4; 1 Kor. 8:3) A taƙaice, idan ka tabbata cewa kana ƙaunar Jehobah, ba ka bukatar ka yi shakka cewa yana ƙaunar ka. Ka kasance da tabbaci cewa zai ci-gaba da ƙaunar ka, kuma ba zai taɓa barin ka ba.
10-11. Ta yaya Jehobah yake so ka ɗauki fansar Yesu? (Galatiyawa 2:20)
10 Ka yi tunani game da fansar Yesu. Fansar Yesu ce kyauta mafi girma da Jehobah ya ba wa ꞌyanꞌadam. (Yoh. 3:16) Amma kai ma za ka iya amfana daga wannan kyautar. Ka yi laꞌakari da labarin manzo Bulus. Ya yi munanan abubuwa sosai kafin ya zama Kirista, kuma bayan da ya zama Kirista, ya ci-gaba da fama da nashi ajizanci. (Rom. 7:24, 25; 1 Tim. 1:12-14) Duk da haka, ya rubuta cewa fansar Yesu kyauta ce da Jehobah ya ba shi. (Karanta Galatiyawa 2:20.b) Ka tuna cewa Jehobah ne ya sa manzo Bulus ya rubuta hakan a cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma duk abin da ke Littafi Mai Tsarki don amfaninmu ne. (Rom. 15:4) Abin da Bulus ya faɗa ya nuna yadda Jehobah yake so ka riƙa ɗaukan fansar Yesu. Yana so ka ɗauka a matsayin kyauta daga wurinsa. Yin hakan zai sa ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar ka.
11 Muna godiya ga Jehobah don yadda ya turo Yesu ya zo ya mutu a madadinmu. Amma, wani dalilin da ya sa Yesu ya zo duniya shi ne don ya gaya mana gaskiya game da Allah. (Yoh. 18:37) Ɗaya daga cikinsu shi ne cewa Jehobah yana ƙaunar mu.
YESU YA CE JEHOBAH YANA ƘAUNAR MU
12. Me ya sa muke da tabbaci cewa duk abin da Yesu ya faɗa game da Jehobah gaskiya ne?
12 Saꞌad da Yesu yake duniya, ya ji daɗin gaya wa mutane game da halayen Jehobah. (Luk. 10:22) Muna da tabbaci cewa duk abin da Yesu ya faɗa game da Jehobah gaskiya ne. Me ya sa? Domin Yesu ya yi shekaru aru-aru da Jehobah a sama kafin ya zo duniya. (Kol. 1:15) Yesu ya san cewa Jehobah yana ƙaunar sa, kuma ya ga yadda Jehobah yake ƙaunar malaꞌiku da mutane sosai. To, ta yaya Yesu ya taimaka wa mutane su kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar su?
13. Mene ne Yesu yake so mu gane game da Jehobah?
13 Yesu yana so mu fahimci yadda Jehobah yake ɗaukan mu. A cikin littafin Matiyu, da Markus, da Luka, da kuma Yohanna, Yesu ya kira Jehobah “Uba” fiye da sau 160. Ya gaya wa mabiyansa cewa Jehobah ‘Ubansu’ ne. (Mat. 5:16; 6:26) Ƙarin bayani a Matiyu 5:16 da ke juyin New World Translation na Turanci ya ce: “Kafin Yesu ya zo duniya, bayin Jehobah masu aminci sun kira Jehobah da laƙabi dabam-dabam, kamar ‘Mai Iko Duka,’ da ‘Maɗaukaki,’ da kuma ‘Mahalicci.’ Amma a yawancin lokuta, Yesu ya kira Jehobah ‘Uba.’ Hakan ya nuna cewa, Jehobah yana so mu kasance da dagantaka da shi kamar yadda uba yake da ɗansa.” Saboda haka, Yesu yana so mu gane cewa Jehobah yana ƙaunar mu, kamar yadda uba mai ƙauna yake ƙaunar yaransa. Bari mu yi laꞌakari da wurare biyu da Yesu ya kira Jehobah “Uba.”
14. Ta yaya Yesu ya nuna cewa kowannenmu yana da daraja a gun Ubanmu Jehobah? (Matiyu 10:29-31) (Ka kuma duba hoton.)
14 Da farko, bari mu ga abin da Yesu ya faɗa a Matiyu 10:29-31. (Karanta.) Ƙananan tsuntsaye da Yesu ya ambata a ayoyin nan, ba za su taɓa ƙauna ko kuma su bauta wa Jehobah ba. Duk da haka, Yesu ya ce Ubanmu ya san inda kowannensu yake a kowane lokaci. Idan Jehobah ya damu da ƙananan tsuntsaye haka, muna da tabbaci cewa ya damu da kowannenmu. Domin muna ƙaunar sa, kuma muna bauta masa. Yesu ya kuma ƙara da cewa: “Ko gashin kanku ma ya san adadinsu.” Da yake Jehobah ya san ƙananan abubuwa game da mu, muna da tabbaci cewa ya damu da mu sosai. Babu shakka, Yesu yana so kowannenmu ya kasance da tabbaci cewa yana da daraja a gun Jehobah.
Jehobah yana daraja ƙaramin tsuntsu sosai har yana sanin inda yake a kowane lokaci. Idan Jehobah ya damu da ƙaramin tsuntsu haka, ka kasance da tabbaci cewa ya damu da kai sosai da yake kana ƙaunar sa kuma kana bauta masa! (Ka duba sakin layi na 14)
15. Mene ne abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:44 yake koya mana game da Ubanmu na sama?
15 Ka yi laꞌakari da wani wuri da Yesu ya kira Jehobah “Uba.” (Karanta Yohanna 6:44.) Ubanmu na sama ne ya taimaka maka ka koya game da shi, kuma ka ƙaunace shi. Me ya sa ya yi hakan? Domin ya ga cewa kai mutumin kirki ne, kuma kana da halaye masu kyau. (A. M. 13:48) Saꞌad da Yesu ya faɗi abin da ke Yohanna 6:44, wataƙila yana ƙaulin abin da ke Irmiya 31:3 ne. A wurin, Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa: ‘Na jawo ku wurina da ƙauna marar canjawa.’ (Irm. 31:3; ka kuma duba Hosiya 11:4.) Ka yi tunanin abin da hakan yake nufi. Ubanmu na sama yana ganin halayenka masu kyau da wataƙila ba ka ma san cewa kana da su ba.
16. (a) Mene ne Yesu ya koya mana, kuma me ya sa zai dace mu amince da abin da ya faɗa? (b) Me zai taimaka maka ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ne Uba da dukanmu muke bukata? (Ka duba akwatin nan “Uba da Dukanmu Muke Bukata.”)
16 Yadda Yesu ya kira Jehobah Ubanmu ya nuna cewa, Jehobah ba Ubansa ne kaɗai ba, amma Uban kowannenmu ne. Yesu yana so kowannenmu ya kasance da tabbaci cewa Jehobah ya damu kuma yana ƙaunar sa sosai. Saboda haka, idan a wasu lokuta ka soma ji kamar Jehobah ba ya ƙaunar ka, ka tuna da abin da Yesu ya faɗa kuma ka aminci da shi. Domin ba ya ƙarya kuma ya san Jehobah fiya da kowa.—1 Bit. 2:22.
KA YI IYA ƘOƘARINKA DON KA KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH YANA ƘAUNAR KA
17. Me ya sa muke bukatar mu ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu wajen tabbatar wa kanmu cewa Jehobah yana ƙaunar mu?
17 Muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci-gaba da kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Kamar yadda muka gani ɗazu, Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Don ya iya cim ma hakan, zai ci-gaba da sa mu ɗauka cewa Jehobah ba ya ƙaunar mu. Amma mun san hakan ba gaskiya ba ne. Saboda haka, ba za mu yarda da ƙaryar nan ba!—Ayu. 27:5.
18. Me muke bukatar mu yi don mu ci-gaba da kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu?
18 A wannan talifin, mun koyi abubuwan da za mu iya yi da za su sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Saboda haka, mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa yake ƙaunar mu. Mu yi tunani a kan Nassosin da suka bayyana yadda Jehobah yake kula da masu ƙaunar sa. Mu tuna cewa Jehobah yana ƙaunar masu ƙaunar sa, kuma ya ba da ɗansa fansa don kowannenmu. Ƙari ga haka, mu yarda cewa Jehobah Ubanmu ne kamar yadda Yesu ya faɗa. Yin hakan zai sa idan wani ya tambaye ka: “Kana da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuwa?” Ba tare da shakka ba za ka ce masa: “E, yana ƙauna ta! Kuma ina yin iya ƙoƙarina kowace rana in nuna masa cewa ina ƙaunar sa!”
WAƘA TA 154 Ƙauna Ba Ta Ƙarewa
a Don samun ƙarin Nassosi da suka tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu, ka duba jigon nan “Doubts” wato Shakka, da ke littafin Scriptures for Christian Living.
b Galatiyawa 2:20 (NWT): “An rataye ni a kan gungume tare da Kristi. Yanzu ba ni ne nake rayuwa ba, amma Kristi ne yake rayuwa a zuciyata. Wannan rayuwa ta jiki da nake yi, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni har ya ba da ransa domina.”