TALIFIN NAZARI NA 46
Yadda Jehobah Ya Tabbatar Mana Cewa Zai Kawo Aljanna
“Duk wanda ya roƙi albarka a ƙasar zai [sami] albarka da Sunan Allah Mai Aminci.”—ISHA. 65:16.
WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Wane saƙo ne annabi Ishaya ya sanar wa Israꞌilawa?
ANNABI Ishaya ya ce Jehobah “Allah Mai Aminci” ne ko kuma gaskiya. A Ibrananci, kalmar nan “aminci” tana iya nufin amin. (Isha. 65:16) Amin kuma tana nufin “hakan ya tabbata” ko kuma “tabbas.” Don haka, idan ana magana game da Jehobah ko kuma Yesu a Littafi Mai Tsarki kuma aka ce “amin,” tabbaci ne cewa abin da aka faɗa gaskiya ne. Saƙon da Ishaya yake sanar wa Israꞌilawan shi ne cewa, za su iya gaskata duk wani alkawarin da Jehobah ya yi. Hakan gaskiya ne domin Jehobah bai taɓa faɗan abu kuma ya kasa cika shi ba.
2. Me ya sa za mu iya gaskata cewa alkawuran Jehobah za su cika a nan gaba, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
2 Mu ma za mu iya gaskata cewa alkawuran da Jehobah ya yi mana za su faru a nan gaba kuwa? Wajen shekaru 800 bayan mutuwar Ishaya, manzon Bulus ya ba mu dalilin kasancewa da tabbaci cewa alkawuran Allah za su cika. Bulus ya ce: “Ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.” (Ibran. 6:18, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Kamar yadda bishiyar mangoro ba za ta iya ba da ꞌyaꞌyan lemu ba, Jehobah Allah mai gaskiya ne, ba zai iya yin ƙarya ba. Don haka, za mu iya gaskata duk wani abin da Jehobah ya ce, har da alkawuran da ya yi mana da za su faru a nan gaba. A wannan talifin, za mu samu amsar tambayoyin nan: Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya ce zai yi mana a nan gaba? Kuma wane tabbaci ne Jehobah ya ba mu cewa alkawuransa za su cika?
WANE ALKAWARI NE JEHOBAH YA YI MANA?
3. (a) Wane alkawari ne bayin Jehobah suke so sosai? (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4) (b) Yaya wasu mutane suke ji idan muka gaya musu wannan alkawarin?
3 Za mu tattauna wani alkawarin da bayin Jehobah a duk duniya suke so sosai. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4.) Jehobah ya yi mana alkawari cewa a nan gaba, ba za a sake “mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba. Yawancinmu mukan yi amfani da ayoyin nan saꞌad da muke waꞌazi don mu nuna wa mutane yadda rayuwa za ta kasance a aljanna. Yaya mutane suke ji idan muka gaya musu wannan alkawarin? Wasu sukan ce, “Alkawarin yana da ban shaꞌawa amma zai yiwu kuwa?”
4. (a) Da Jehobah ya yi alkawarin kawo aljanna, mene ne ya san zai faru a zamaninmu? (b) Ban da yin alkawari, me kuma Jehobah ya yi?
4 A lokacin da Jehobah ya sa manzo Yohanna ya rubuta wannan alkawarin, ya san cewa a zamaninmu za mu yi waꞌazi kuma mu gaya wa mutane wannan alkawarin. Kuma Jehobah ya san cewa zai yi ma wasu mutane wuya su yarda cewa zai kawo wannan canjin a nan gaba. (Isha. 42:9; 60:2; 2 Kor. 4:3, 4) Me zai taimaka mana mu iya tabbatar wa mutane cewa alkawarin nan da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4 zai cika? Kuma ta yaya mu ma za mu ƙara kasancewa da tabbaci? Ba alkawari ne kawai Jehobah ya yi mana ba, ya kuma ba mu dalilai masu kyau na gaskata cewa abubuwan nan za su faru. Waɗanne dalilai ne ya bayar?
JEHOBAH YA TABBATAR MANA DA CIKAR ALKAWARINSA
5. Waɗanne ayoyi ne suka ba mu dalilan gaskatawa da alkawarin Jehobah game da aljanna, kuma mene ne ayoyin suka ce?
5 Ayoyin da suka bi bayan alkawarin Jehobah game da aljanna sun ba mu dalilan gaskata cewa alkawarin zai cika. Wurin ya ce: “Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce, ‘Duba, sabonta dukan abu ni ke yi.’ Ya ce kuma, ‘Ka rubuta: gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.’ Ya kuma ce mani, ‘Sun tabbata. Ni ne Alpha da Omega, farko da ƙarshe.’”—R. Yar. 21:5, 6a, Mai Makamantu[n] Ayoyi.
6. Me ya sa abin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:5, 6 yake ƙara tabbatar mana da cewa Jehobah zai cika alkawarinsa?
6 Ta yaya ayoyin nan suke ƙara tabbatar mana cewa alkawarin Allah zai cika? Da Jehobah ya furta kalmomin da ke ayoyin nan, kamar ya sa hannu ne a kan takardar mallaka don ya tabbatar mana da cewa, zai cika alkawuran nan. A Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4 ne Jehobah ya yi wannan alkawarin. Saꞌan nan a ayoyi 5 da 6, mun ga yadda Jehobah ya sa hannu a kan alkawarin, wato ya ba mu tabbacin cewa abin da ya faɗa zai cika. Bari mu bincika abubuwan da Jehobah ya faɗa a ayoyin nan don mu ga tabbacin.
7. Wane ne ya faɗi abin da ke aya 5, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?
7 Aya ta biyar ta soma da cewa: “Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce.” (R. Yar. 21:5a, MMA) Waɗannan kalaman suna da muhimmanci, domin a littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, sau uku ne kaɗai Jehobah da kansa ya yi magana. Jehobah bai ba da wannan tabbacin ta bakin wani malaꞌika mai iko ko ta bakin Yesu ba, a maimako ya faɗe shi da kansa! Wannan babban dalili ne na gaskata kalmomin da ke Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21 ayoyi 5 da 6. Me ya sa? Domin Jehobah “ba ya ƙarya.” (Tit. 1:2) Ba shakka abin da ayoyin nan suka ce zai faru.
“DUBA, SABONTA DUKAN ABU NI KE YI”
8. Mene ne Jehobah ya ce don ya nuna cewa ba abin da zai hana shi cika alkawarinsa? (Ishaya 46:10)
8 Jehobah ya soma da cewa: “Duba.” (R. Yar. 21:5) An yi ta amfani da kalmar nan “duba” sau da yawa a littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna. Wani littafin bincike ya ce, “a Helenanci, ana amfani da kalmar nan ne don a jawo hankalin wanda yake karatu ya lura da abin da za a faɗa.” Mene ne Jehobah ya faɗa bayan haka? Allah ya ce: “Sabonta dukan abu ni ke yi.” Jehobah yana magana ne a kan abin da zai faru a nan gaba, amma ya san cewa ba abin da zai hana wannan abin faruwa. Shi ya sa a ayar nan, ya yi magana kamar ya riga ya soma yin su.—Karanta Ishaya 46:10.
9. (a) Waɗanne abubuwa biyu ne Jehobah zai yi da ya ce, “sabonta dukan abu ni ke yi”? (b) Me zai faru da “sama” da kuma “ƙasa” da muke da su a yau?
9 Jehobah ya ce: “Sabonta dukan abu ni ke yi,” a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:5. Me hakan yake nufi? A wannan surar, kalmomin nan suna nufin abubuwa kashi biyu da Jehobah zai yi, wato canji da kuma gyara. Mu soma da na farkon, mene ne Jehobah zai canja? Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:1 ta ce: “Sama na farko da ƙasa ta farko duk sun ɓace.” “Sama na farko” yana nufin mulkokin duniya waɗanda Shaiɗan da aljanunsa ne suke iko a kan su. (Mat. 4:8, 9; 1 Yoh. 5:19) A Littafi Mai Tsarki, akan yi amfani da kalmar nan ƙasa, wato “duniya” idan ana zancen mutanen da suke rayuwa a duniya. (Zab. 96:1) Don haka, mugayen mutane da suke a duniya su ne “ƙasa ta farko.” Jehobah ba zai gyara “sama na farko” da “ƙasa ta farko” ba, a maimako zai canja su ne, wato zai kawar da su gabaki ɗaya. Bayan haka, zai kawo “sabon sama da sabuwar ƙasa,” wato zai kawo sabon gwamnati ko kuma mulki da zai yi sarauta a kan mutane masu adalci.
10. Su mene ne Jehobah zai mai da su sabo?
10 Me kuma Jehobah zai yi don ya mai da dukan kome sabo? (R. Yar. 21:5) Jehobah zai gyara duniya kuma ya warkar da mazaunanta don kome ya zama marar aibi. Kamar yadda annabi Ishaya ya annabta, Jehobah zai mai da dukan duniya ta zama wuri mai kyau kamar lambun Adnin. Mu ma Jehobah zai mai da mu sabo, ta wurin warkar da kowannenmu. Guragu da makafi da kurame, duka za su warke. Waɗanda suka mutu ma za a ta da su.—Isha. 25:8; 35:1-7.
“GAMA WAƊANNAN ZANTATTUKA MASU-AMINCI NE MASU-GASKIYA. . . . SUN TABBATA”
11. Wane umurni ne Jehobah ya ba wa Yohanna kuma me ya sa ya ce ya yi hakan?
11 Wane ƙarin tabbaci ne kuma Jehobah ya ba mu? Ya gaya wa Yohanna cewa: “Ka rubuta: gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.” (R. Yar. 21:5, MMA) Jehobah ya ce a “rubuta,” amma bai tsaya a nan ba. Ya kuma ba da dalili. Ya ce: “Gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya,” wato za mu iya gaskata abin da ya faɗa. Mun gode wa Yohanna sosai da ya yi biyayya kuma ya “rubuta” kalmomin nan. Shi ya sa za mu iya karanta alkawarin aljanna da Jehobah ya yi mana, kuma mu yi tunani a kan albarkun da za mu samu a nan gaba.
12. Me ya sa Jehobah ya ce: “Sun tabbata”?
12 Me Jehobah ya faɗa bayan hakan? Ya ce: “Sun tabbata.” (R. Yar. 21:6) Me ya sa Jehobah ya ce “sun tabbata”? Domin ba abin da zai iya hana shi cika nufinsa. Bayan haka, Jehobah ya faɗi wani abu kuma da ya ba mu babban dalilin gaskata alkawarinsa. Me ya ce?
“NI NE ALPHA DA OMEGA”
13. Me ya sa Jehobah ya ce: “Ni ne Alpha da Omega”?
13 Sau uku ne Jehobah da kansa ya yi magana da Yohanna a wannan ruꞌuyar. (R. Yar. 1:8; 21:5, 6; 22:13) Kuma a dukan lokutan nan Jehobah ya yi ta maimaita cewa: “Ni ne Alpha da Omega.” Alpha shi ne harafi na farko a rubutun Helenanci kuma omega shi ne na ƙarshe. Jehobah ya ce Shi ne “Alpha da Omega” don ya nuna cewa idan har ya soma yin abu, tabbas zai yi nasara wajen ƙarasa shi.
Idan Jehobah ya soma yin abu, ba ya dainawa har sai ya gama shi (Ka duba sakin layi na 14, 17)
14. (a) Wane lokaci ne “Alpha,” kuma wane lokaci ne zai zama “Omega”? (b) Wane tabbaci ne Jehobah ya ba mu a Farawa 2:1-3?
14 Da Jehobah ya halicci Adamu da Hauwaꞌu, Ya gaya musu dalilin da ya sa ya halicci mutane da kuma duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ya sa musu albarka ya ce, ‘Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta.’” (Far. 1:28) A wannan lokacin ne Jehobah ya bayyana nufinsa, “Alpha” ke nan, wato ‘farkon.’ Idan Jehobah ya cika nufin nan kuma ꞌyan Adam masu aminci sun cika duniya sun kuma mai da ita aljanna, wannan lokacin ne zai zama “Omega,” wato ‘ƙarshen.’ Da Jehobah ya gama halittar “sama da duniya, da dukan tulin abubuwan da suke cikinsu,” ya faɗi wani abin da ya nuna cewa tabbas nufinsa zai cika. Wannan tabbacin yana Farawa 2:1-3. (Karanta.) Jehobah ya ce rana ta bakwai rana mai tsarki ce. Mene ne hakan yake nufi? Yana nufin cewa ya keɓe rana ta bakwai musamman don ya cika nufinsa ga ꞌyan Adam da kuma duniya. Ta haka, Jehobah yana ba da tabbaci ne cewa zai cika dukan nufinsa a ƙarshen rana ta bakwai.
15. Me ya sa Shaiɗan ya ɗauka cewa abin da ya yi zai hana Jehobah cika nufinsa?
15 Da Adamu da Hauwaꞌu suka yi tawaye, sun zama masu zunubi kuma sun ba ma ꞌyaꞌyansu gādon zunubi da mutuwa. (Rom. 5:12) Hakan ya sa ya zama kamar duniyar nan ba za ta taɓa cika da kamiltattun mutane masu biyayya kamar yadda Jehobah ya nufa ba. Amma Shaiɗan ya hana Jehobah cika nufinsa ne? Mai yiwuwa Shaiɗan ya zata Jehobah zai kasa cika alkawarinsa. Wataƙila ma ya zata cewa Jehobah zai kashe Adamu da Hauwaꞌu kuma ya halicci wasu mutane don su cika duniya. Da hakan zai sa Allah ya cika nufinsa. Sai dai kuma Shaiɗan zai ce, Allah ya yi ƙarya. Me ya sa? Domin kamar yadda Farawa 1:28 ta ce, Jehobah ya gaya wa Adamu da Hauwaꞌu cewa ꞌyaꞌyansu ne za su cika duniya.
16. Mene ne zai iya sa Shaiɗan ya yi wa Allah dariya cewa ya kasa cika nufinsa?
16 Mene ne kuma wataƙila Shaiɗan ya zata Jehobah zai yi? Mai yiwuwa Shaiɗan ya ɗauka cewa Jehobah zai bar Adamu da Hauwaꞌu su haifi ꞌyaꞌya amma ꞌyaꞌyan ba za su taɓa zama kamiltattu ba. (M. Wa. 7:20; Rom. 3:23) Idan hakan ya faru, ba shakka Shaiɗan zai yi wa Jehobah dariya don ya kasa cika nufinsa. Me ya sa? Domin ba za a samu kamiltattun ꞌyaꞌyan Adamu da za su cika duniya kuma su mai da ita aljanna kamar yadda Allah ya nufa ba.
17. Mene ne Jehobah ya yi don ya warware matsalar da Shaiɗan da Adamu da Hauwaꞌu suka jawo saꞌad da suka yi tawaye, kuma mene ne zai faru a ƙarshe? (Ka kuma duba hoton.)
17 Ba shakka, yadda Jehobah ya warware wannan matsalar ya ba Shaiɗan mamaki. (Zab. 92:5) Jehobah ya bar Adamu da Hauwaꞌu su haifi ꞌyaꞌya. Ta hakan, ya cika alkawarin da ya yi musu kuma ya nuna cewa ba ya ƙarya. Jehobah ya nuna cewa in har ya ce zai yi wani abu, ba abin da ya isa ya hana shi. Ya buɗe hanyar cika nufinsa ta wurin tanadar da wani zuriya wanda zai ceci ꞌyaꞌyan Adamu da Hauwaꞌu masu aminci. Wannan zuriyar zai ba da ransa don ya ceci ꞌyan Adam. (Far. 3:15; 22:18) Hakika, hakan ya ba Shaiɗan mamaki. Me ya sa? Domin ƙauna da rashin son kai ne suka sa Jehobah da Yesu suka yi tanadin wannan fansar. (Mat. 20:28; Yoh. 3:16) Shaiɗan ba haka yake ba, shi mai son kai ne. Wane amfani ne wannan fansar za ta kawo? A ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu, ꞌyaꞌyan Adamu da Hauwaꞌu kamiltattu masu biyayya su ne za su kasance a duniyar nan, kuma za su mai da ita aljanna kamar yadda Jehobah ya so tun farko. A lokacin nan ne zai zama Omega, wato ‘ƙarshen.’
YADDA ZA MU ƘARA ZAMA DA TABBACIN CEWA JEHOBAH ZAI KAWO ALJANNA
18. Waɗanne dalilai uku ne Jehobah ya ba mu da suka tabbatar mana cewa zai cika alkawarinsa? (Ka kuma duba akwatin nan “Dalilai Uku da Suka Tabbatar Mana Cewa Jehobah Zai Cika Alkawarinsa.”)
18 Bisa ga abin da muka tattauna, me za mu iya gaya wa mutanen da suke shakkar cewa aljanna za ta zo kamar yadda Allah ya yi alkawari? Na ɗaya, Jehobah da kansa ne ya yi alkawarin. Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna ya ce: “Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce, ‘Duba, sabonta dukan abu ni ke yi.’” Jehobah yana da hikima, da iko, da kuma niyyar cika wannan alkawarin. Na biyu, Jehobah ya san cewa tabbas abin da ya faɗa zai faru, don haka a gunsa, kamar ya riga ya faru ne. Shi ya sa ya ce: “Waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya. . . . Sun tabbata.” Na uku, idan Jehobah ya soma yin abu, ba abin da ya isa ya hana shi kammalawa. Shi ya sa ya ce, “Ni ne Alpha da Omega.” Jehobah zai nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne da bai isa ya hana shi cika nufinsa ba.
19. Idan mutane suna shakkar cewa Allah zai kawo aljanna kamar yadda ya ce, me za ka yi?
19 Ka tuna cewa a duk lokacin da kake waꞌazi kuma ka gaya wa mutum dalilan da suka tabbatar mana cewa Jehobah zai cika alkawarinsa, kai ma za ka ƙara samun wannan tabbacin. Don haka, idan ka karanta wa mutum alkawarin nan mai ban ƙarfafa cewa aljanna za ta zo, kamar yadda Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4 ta ce, kuma mutumin ya ce, “Anya! Wannan abin zai faru kuwa?” Me za ka yi? Za ka iya karanta masa ayoyi 5 da 6 kuma ka bayyana masa abin da ke wurin. Ka nuna masa yadda Jehobah ya sa hannu don ya tabbatar mana cewa zai cika alkawarinsa.—Isha. 65:16.
WAƘA TA 145 Allah Ya Yi Mana Alkawarin Aljanna
a A wannan talifin, za mu ga tabbacin da Jehobah ya ba mu cewa zai cika alkawarin da ya yi na kawo aljanna. A duk lokacin da muka gaya wa mutane dalilan da suka tabbatar mana cewa Jehobah zai cika alkawuransa, mu kanmu za mu ƙara samun tabbaci.