TALIFIN NAZARI NA 43
“Zai Ƙarfafa Ka”
“[Jehobah] zai mai da ku cikakku, zai kafa ku, zai kuma ƙarfafa ku.”—1 BIT. 5:10.
WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Ta yaya Jehobah ya ba wa bayinsa ƙarfi a dā?
LITTAFI MAI TSARKI yana yawan cewa masu bangaskiya suna da ƙarfi. Amma ba a ko yaushe ne sukan ji cewa suna da ƙarfi ba. Misali, akwai lokacin da Sarki Dauda ya ce yana da “ƙarfi kamar babban dutse,” amma a wani lokacin kuma, ya ji “tsoro” sosai. (Zab. 30:7) Da Jehobah ya ba wa Samson ruhunsa, shi ma ya samu ƙarfi sosai. Amma ya san cewa idan babu ruhun nan, ‘zai rasa ƙarfinsa, ya zama kamar kowa.’ (Alƙa. 14:5, 6; 16:17) Hakika, Jehobah ne ya ba ma waɗannan bayinsa ƙarfi.
2. Me ya sa Bulus ya ce saꞌad da yake da rashin ƙarfi, lokacin ne yake da ƙarfi? (2 Korintiyawa 12:9, 10)
2 Manzo Bulus shi ma ya dogara ga Jehobah don ya ba shi ƙarfi. (Karanta 2 Korintiyawa 12:9, 10.) Shi ma ya yi fama da rashin lafiya kamar yadda yawancinmu muke fama. (Gal. 4:13, 14) Akwai kuma lokuta da yin abin da ya dace bai yi masa sauƙi ba. (Rom. 7:18, 19) Wasu lokuta kuma, ya yi fama da damuwa da tsoro. (2 Kor. 1:8, 9) Duk da haka, Bulus ya kasance da ƙarfi a lokutan nan. Me ya taimaka masa? Jehobah ne ya ba shi ƙarfin da yake bukata don ya jimre matsalolin nan.
3. Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?
3 Mu ma Jehobah ya ce zai ƙarfafa mu. (1 Bit. 5:10) Amma muna bukatar mu yi namu ƙoƙarin kafin mu samu wannan ƙarfin. Misali, injin mota zai iya sa motar ta yi tafiya. Amma akwai inda direban yake takawa da ƙafarsa don ya ba wa motar wuta. Idan direban bai taka wannan wurin ba, motar ba za ta yi tafiya ba. Mu ma Jehobah yana so ya ba mu ƙarfin da muke bukata, amma akwai wasu abubuwan da muke bukatar mu yi. Me da me Jehobah yake amfani da su don ya ba mu ƙarfi? Kuma me za mu yi don mu samu wannan ƙarfin? Don mu amsa tambayoyin nan, za mu bincika yadda Jehobah ya ƙarfafa mutane uku a Littafi Mai Tsarki, wato annabi Yunana da Maryamu mahaifiyar Yesu da kuma manzo Bulus. Za mu kuma ga yadda Jehobah yake ƙarfafa bayinsa a yau kamar yadda ya yi a dā.
YIN ADDUꞌA DA NAZARI ZA SU BA KA ƘARFIN JIMREWA
4. Me za mu yi don mu samu ƙarfi daga wurin Jehobah?
4 Wata hanyar da za mu samu ƙarfi daga wurin Jehobah ita ce ta yin adduꞌa. Idan muka yi adduꞌa, Jehobah zai ba mu “cikakken ikon da ya fi duka.” (2 Kor. 4:7) Za mu kuma samu ƙarfafa idan muka karanta Kalmarsa, kuma muka yi tunani a kan abin da ta ce. (Zab. 86:11) Kalmar Allah tana da “ƙarfin aiki.” (Ibran. 4:12) Idan ka yi adduꞌa ga Jehobah kuma ka karanta Kalmarsa, za ka samu ƙarfin da kake bukata don ka jimre matsalolinka, za ka ci-gaba da yin farin ciki, kuma ka iya yin aikin da aka ba ka komen wuyar sa. Bari mu ga yadda Jehobah ya ƙarfafa annabi Yunana.
5. Me ya sa annabi Yunana yake bukatar ƙarfafa?
5 Annabi Yunana yana bukatar ƙarfafa. Ya gudu daga aiki mai wuya da Jehobah ya ba shi. Hakan ya sa ya kusan rasa ransa kuma ya sa rayukan waɗanda suke tare da shi a jirgin ruwa cikin haɗari. Da suka jefar da shi a cikin teku, sai wani babban kifi ya haɗiye shi. Yunana ya tsinci kansa a wani wuri mai ban tsoro. A ganinka, yaya Yunana ya ji? Ba mamaki ya ji tsoro. Ƙila ya ɗauka cewa Jehobah ya daina ƙaunar sa. Hakika Yunana ya damu sosai.
Kamar annabi Yunana, me za mu yi don mu samu ƙarfin jimre matsalar da muke ciki? (Ka duba sakin layi na 6-9)
6. Bisa ga Yona 2:1, 2, 7, me ya ƙarfafa Yunana a cikin kifin?
6 Mene ne Yunana ya yi saꞌad da yake cikin kifin? Ya yi adduꞌa ga Jehobah. (Karanta Yona 2:1, 2, 7.) Ko da yake dā bai yi biyayya ba, amma ya tuba kuma ya san cewa Jehobah zai ji adduꞌarsa. Yunana ya kuma yi tunani a kan Nassosi. Me ya nuna hakan? A adduꞌarsa da aka rubuta a littafin Yona sura 2, ya yi amfani da kalmomi da yawa da suke cikin littafin Zabura. (Misali, ka duba alaƙa da ke Yona 2:2, 5 da kuma Zabura 69:1; 86:7.) Yunana ya san Nassosin nan sosai, kuma da ya yi tunani a kan abin da suka ce a wannan lokaci mai wuya, ayoyin sun tabbatar masa cewa Jehobah zai cece shi. Jehobah ya kuwa ceci Yunana, kuma Yunana ya kuɗiri niyyar yin aikin da Jehobah ya ba shi.—Yona 2:10–3:4.
7-8. Me da me suka ba ma wani ɗanꞌuwa ƙarfi saꞌad da yake cikin matsala?
7 Abin da Yunana ya yi zai iya taimaka mana idan muna fama da matsaloli. Misali, akwai wani ɗanꞌuwa mai suna Zhimingb a ƙasar Taiwan da yake rashin lafiya sosai. Ƙari ga haka, ꞌyan iyalinsa sun wulaƙanta shi sosai domin yana bauta wa Jehobah. Abin da ke ba shi ƙarfin jimrewa shi ne yin adduꞌa da nazari. Ya ce: “Wani lokaci idan matsala ta taso, hankalina yakan tashi sosai da har ba na iya yin nazari.” Amma ɗanꞌuwan bai fid da rai ba. Ya ce: “In hakan ya faru, nakan fara da yin adduꞌa ga Jehobah, bayan haka sai in kunna waƙoƙinmu ina ji. Wani lokaci ma sai in dinga bi ina rerawa a hankali har sai na ji hankalina ya kwanta. Bayan hakan, sai in soma nazari.”
8 Yin nazari ya ƙarfafa Ɗanꞌuwa Zhiming sosai. Misali, bayan an yi masa tiyata, ya rasa jini sosai kuma wata nas ta ce masa yana bukatar a ƙara masa jini. Amma ya tuna labarin wata ꞌyarꞌuwa da ya karanta daddare kafin ranar da aka masa tiyatar. An yi mata irin tiyatar da aka masa kuma ta rasa jini fiye da shi. Duk da haka, ba ta yarda a mata ƙarin jini ba kuma ta samu sauƙi. Wannan labarin ya ba wa Zhiming ƙarfin riƙe amincinsa.
9. Idan ƙarfinka ya kasa saboda wata matsala, me za ka iya yi? (Ka kuma duba hotunan.)
9 Wani lokaci kakan kasa yin adduꞌa ga Jehobah saboda tsananin matsalar da kake ciki? Matsalar takan gajiyar da kai har ka kasa yin nazari? Jehobah ya san irin yanayin da kake ciki. Don haka, ko da gajeriyar adduꞌa ce ka yi, Jehobah zai ba ka ƙarfin da kake bukata. (Afis. 3:20) Idan zafin da kake ji a ranka ya sa ka kasa yin karatu ko nazari, za ka iya sauraran karatun Littafi Mai Tsarki ko kuma na littattafanmu. Wani abu kuma da zai iya taimaka maka shi ne jin waƙoƙinmu, ko ka kalli wani bidiyo a dandalinmu. Jehobah yana so ya ba ka ƙarfin jimrewa. Zai ba ka wannan ƙarfin idan ka yi adduꞌa, kuma ka karanta Littafi Mai Tsarki da sauran abubuwa da yake mana tanadin su.
ꞌYANꞌUWA MASU BI ZA SU BA KA ƘARFIN JIMREWA
10. A waɗanne hanyoyi ne ꞌyanꞌuwanmu suke ƙarfafa mu?
10 Jehobah zai iya amfani da ꞌyanꞌuwanmu don ya ba mu ƙarfin jimrewa. Za su iya “zama abin taꞌaziyya a gare” mu idan muna cikin matsala ko an ba mu wani aiki mai wuya. (Kol. 4:10, 11) Muna bukatar abokan kirki sosai musamman ma a “kwanakin masifa.” (K. Mag. 17:17) Idan muna jin cewa ba mu da ƙarfi, ꞌyanꞌuwanmu suna iya ba mu abin da muke bukata, su taꞌazantar da mu, kuma su ƙarfafa mu mu ci-gaba da bauta wa Jehobah. Bari mu ga yadda wasu suka ƙarfafa Maryamu, mahaifiyar Yesu.
11. Me ya sa Maryamu take bukatar ƙarfafa?
11 Maryamu tana bukatar ƙarfafa. Ka yi tunanin irin damuwar da ta ji lokacin da malaꞌika mai suna Jibrailu ya gaya mata abin da zai faru da ita. Ba ta yi aure ba amma malaꞌikan ya ce za ta yi ciki. Ba ta taɓa renon yaro na kanta ba, ga shi yanzu an ce ita ce za ta reni yaron da zai zama Almasihu. Kuma da yake ba ta taɓa kwana da namiji ba, me za ta gaya wa Yusufu wanda yake neman ta da aure?—Luk. 1:26-33.
12. Bisa ga Luka 1:39-45, me Maryamu ta yi don ta samu ƙarfafa?
12 Me Maryamu ta yi don ta samu ƙarfin yin wannan aiki mai wuya da aka ba ta? Ta nemi taimako. Alal misali, ta yi wa malaꞌikan tambayoyi don ya yi mata ƙarin bayani. (Luk. 1:34) Jim kaɗan bayan hakan, sai ta yi doguwar tafiya zuwa wani gari a “tuddan yankin Yahudiya” gun wata danginta mai suna Alisabatu. Kuma tafiyar ta ƙarfafa ta. Jehobah ya sa Alisabatu ta gaya wa Maryamu wani annabci game da ɗan da za ta haifa. (Karanta Luka 1:39-45.) Maryamu ta ce Jehobah ya yi “manyan abubuwa” da hannunsa mai tsarki. (Luk. 1:46-51) Jehobah ya ƙarfafa Maryamu ta wurin malaꞌikan nan Jibrailu da Alisabatu.
13. Ta yaya neman taimakon ꞌyanꞌuwa ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa a Bolibiya?
13 Kamar Maryamu, kai ma za ka iya samun ƙarfafa daga wurin ꞌyanꞌuwa masu bi. Wata ꞌyarꞌuwa daga ƙasar Bolibiya mai suna Dasuri ta bukaci irin wannan ƙarfafar. Mahaifinta ya kamu da rashin lafiya mai tsanani wanda ba shi da magani. Da aka kwantar da shi a asibiti, Dasuri ta yi iya ƙoƙarinta don ta kula da shi. (1 Tim. 5:4) Amma abin bai yi mata sauƙi ba. Ta ce: “Sau da yawa, na ji kamar ba zan iya ci-gaba da jinyar sa ba.” Da farko dai, ba ta so ta gaya wa ꞌyanꞌuwa su taimaka mata ba. Ta ce: “Ban so in dami ꞌyanꞌuwa ba. A ganina, Jehobah zai ba ni ƙarfin da nake bukata. Amma daga baya, na ga cewa idan na ƙi neman taimako, ina ƙoƙarin magance matsalata da kaina ke nan.” (K. Mag. 18:1) Sai Dasuri ta rubuta wa abokanta wasiƙa kuma ta bayyana musu matsalar da take ciki. Ta ce: “Ba zan iya kwatanta irin ƙarfafa da ꞌyanꞌuwa Kiristoci suka yi min ba. Sun kawo mana abinci a asibiti kuma sun karanta mana Nassosi masu ban ƙarfafa. Hakika sanin cewa ꞌyanꞌuwanmu suna tare da mu abin ban ƙarfafa ne. Dukanmu ꞌyan iyalin Jehobah ne. Kuma ꞌyanꞌuwanmu maza da mata suna a shirye su taimaka mana, su yi kuka da mu kuma su taimaka mana mu ci-gaba da bauta wa Jehobah.”
14. Me ya sa ya kamata mu amince da taimakon dattawa?
14 Wata hanya kuma da Jehobah yake ba mu ƙarfi ita ce ta wurin dattawa. Dattawa kyauta ne da Jehobah ya ba mu, yana amfani da su ya ƙarfafa mu kuma ya kwantar mana da hankali. (Isha. 32:1, 2) Don haka, in kana cikin damuwa, ka gaya wa dattawa. Kuma idan suna so su taimaka, ka amince. Jehobah zai iya amfani da su don ya ba ka ƙarfi.
LADAN DA KAKE BEGEN SAMUWA ZAI IYA BA KA ƘARFI
15. Wane bege ne dukan Kiristoci ba sa wasa da shi?
15 Abubuwan da muke begensu za su iya ƙarfafa mu sosai. (Rom. 4:3, 18-20) Mu Kiristoci muna da begen yin rayuwa har abada ko a aljanna a duniya ko kuma a sama. Wannan begen yana ba mu ƙarfin jimre matsaloli da yin waꞌazi da yin ayyuka dabam-dabam a ikilisiya. (1 Tas. 1:3) Kuma wannan begen ne ya ba wa manzo Bulus ƙarfin jimrewa.
16. Me ya sa manzo Bulus yake bukatar ƙarfafa?
16 A wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa Korintiyawa, ya ce shi kamar tulun da aka yi da laƙa ne, wanda bai da wuyar fashewa. An ba shi “wahala ta kowace hanya,” ya yi “shakka,” an “tsananta” masa kuma an ‘buga shi har ƙasa.’ Akwai lokutan da ma ya kusan rasa ransa. Don haka, a lokacin yana bukatar ƙarfafa. (2 Kor. 4:8-10) A ƙaro na uku da Bulus ya je waꞌazi a ƙasar waje ne ya rubuta wasiƙar nan. Kuma bayan haka, ya fuskanci matsaloli da yawa. Wasu mugayen mutane sun kai musu hari, an kama shi, jirgin ruwa ya fashe da shi, kuma an ƙulle shi a kurkuku.
17. Bisa ga 2 Korintiyawa 4:16-18, me ya ba wa Bulus ƙarfin jimre matsalolinsa?
17 Manzo Bulus ya mai da hankali ga ladan da yake begen samuwa kuma hakan ya ba shi ƙarfin jimrewa. (Karanta 2 Korintiyawa 4:16-18.) Ya gaya wa Korintiyawa cewa ko da jikinsa yana “lalacewa” a zahiri, ba zai karaya ba. Begen yin rayuwa a sama da yake yi ɗaukaka ce “mai yawa, wadda ta wuce gaban misali.” Bulus ya ɗauki wannan begen da daraja da har ya yarda ya jimre kowace irin wahala don ya sami ladan. Bulus ya yi ta tunani mai zurfi a kan wannan begen kuma hakan ya sa ya ji kamar ana ‘mai da ruhunsa sabo kullum.’
18. Ta yaya begen da Ɗanꞌuwa Tihomir da iyalinsa suke da shi ya ba su ƙarfi?
18 Wani ɗanꞌuwa mai suna Tihomir a ƙasar Bulgeriya, ya sami ƙarfafa sosai daga ladan da yake begen samuwa. A shekarun baya-bayan nan, ƙaninsa mai suna Zdravko ya yi hatsari kuma ya mutu. Bayan rasuwar ƙaninsa, Ɗanꞌuwa Tihomir ya yi fama da baƙin ciki. Abin da ya taimaka wa shi da iyalinsa su jimre shi ne, yin tunani a kan tashin matattu. Ya ce: “Misali, mun yi magana a kan inda za mu haɗu da Zdravko, da abincin da za mu dafa masa, da mutanen da za mu gayyata su zo fatin da za mu yi masa, da kuma abubuwan da za mu gaya masa game da kwanakin ƙarshe.” Tihomir ya ce, yin tunani a kan abubuwan da suke begen su ya ƙarfafa shi da iyalinsa su ci-gaba da jimrewa, kuma su jira lokacin da Jehobah zai ta da ɗanꞌuwansa.
Ya kake ganin rayuwarka za ta kasance a aljanna? (Ka duba sakin layi na 19)c
19. Me zai taimaka maka ka ƙara kasancewa da bege? (Ka kuma duba hoton.)
19 Me za ka yi don ka ƙara kasancewa da bege? Idan kana begen yin rayuwa a aljanna a duniya, ka karanta Nassosin da suka yi magana a kan aljanna, kuma ka yi tunani a kan su. (Isha. 25:8; 32:16-18) Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta yi daɗi a aljanna. Ka ga kanka a wurin. Wa da wa kake gani a wurin? Ƙarar me kake ji? Kuma ya kake ji? Don ka yi tunanin yadda abin zai kasance, ka kalli hotunan da ke littattafanmu da suka kwatanta rayuwa a aljanna. Ko ka saurari waƙoƙinmu irin su, Rayuwa a Cikin Aljanna, Aljanna Ta Kusa, Ka Ɗauka Muna Aljanna. Idan muka ci-gaba da yin begen rayuwa a aljanna, wahalar da muke sha za ta zama “ꞌyar wahala,” kuma “ba za ta daɗe ba.” (2 Kor. 4:17) Jehobah zai yi amfani da wannan begen ya ƙarfafa ka.
20. Ko a lokacin da ba mu da ƙarfi, me zai taimaka mana mu samu ƙarfi?
20 Ko da muna ji ba mu da ƙarfi, da taimakon Allah za mu ci nasara. (Zab. 108:13) Jehobah ya riga ya yi mana tanadin hanyoyin da za mu sami ƙarfi daga wurinsa. Don haka, idan kana bukatar ƙarfi don ka iya yin wani aiki da aka ba ka, ko ka jimre wata matsala, ko don ka ci-gaba da yin farin ciki, ka nemi taimakon Jehobah ta wurin yin adduꞌa da kuma nazari. Ka yarda ꞌyanꞌuwanka su taimaka maka. Ka dinga samun lokaci kana tunanin ladan da za ka samu. In ka yi hakan, Allah zai ƙarfafa ka da ‘dukan ƙarfin da ya fito daga ƙarfinsa mai ɗaukaka, domin ka jimre a kan kowane abin da ya faru, kana haƙuri cikin farin ciki.’—Kol. 1:11.
WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah
a Wannan talifin zai taimaka ma waɗanda suke ganin matsalar da suke fuskanta ko kuma aikin da aka ba su ya fi ƙarfinsu. Za mu ga yadda Jehobah yake ba mu ƙarfin jimrewa da kuma abin da za mu yi don mu samu wannan ƙarfin.
b An canja wasu sunayen.
c BAYANI A KAN HOTO: Wata ꞌyarꞌuwa da kurma ce tana tunanin alkawuran Allah da ke Littafi Mai Tsarki, kuma tana kallon bidiyon wata waƙa don ta yi tunani a kan yadda rayuwarta za ta kasance a sabuwar duniya.