Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Ya Koya Daga Kuskurensa
YUNANA zai so da yana da ikon dakatar da mugun iska. Ba iska mai ƙarfi ba ne kawai yake girgiza jirgin, ba kuwa manya manyan raƙuman ruwa ba ne da suke juya jirgin dama da hagu, suke sa katakan da aka yi sa da shi suna ƙara. Amma, abin da ya fi damun Yunana shi ne ihun da ma’aikatan jirgin suke yi, sa’ad da suke ƙoƙari su hana jirgin nitsewa. Yunana ya tabbata cewa waɗannan mutane sun kusa halaka saboda shi!
Menene ya sa Yunana a cikin wannan mugun yanayi? Ya yi mummunan kuskure wajen hulɗarsa da Allahnsa, Jehobah. Menene ya yi? Al’amuran sun wuce a gyara ne? Amsoshin za su koya mana abubuwa da yawa. Alal misali, labarin Yunana ya taimake mu mu fahimci cewa waɗanda suke da bangaskiya ma suna iya yin kuskure, kuma su yi gyara.
Annabi Daga Galili
Sa’ad da mutane suka yi tunanin Yunana, sau da yawa suna mai da hankali ne ga kuskuren da ya yi, kamar rashin biyayyarsa ko kuma taurin kai da ya nuna. Amma akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu sani game da wannan mutumin. Ka tuna, an zaɓi Yunana ya zama annabin Jehobah Allah. Idan da shi mutum ne marar aminci ko kuma marar adalci da Jehobah bai zaɓe shi ya yi wannan babban aiki ba.
A 2 Sarakuna 14:25, mun sami ɗan bayani game da tarihin Yunana. Shi ɗan Gath-hepher ne, birnin da ke da nisan mil biyu da rabi daga birnin Nazareth, inda Yesu Kristi ya yi girma ƙarnuka takwas daga baya.a Yunana annabi ne a lokacin sarautar Sarki Jeroboam na biyu na ƙabila goma na Isra’ila. Zamanin Iliya ya wuce; magajinsa Elisha kuma ya mutu a lokacin sarautar mahaifin Jeroboam. Ko da yake Jehobah ya yi amfani da waɗannan mutanen don kawar da bautar Ba’al, Isra’ila ta fara komawa halinta na dā. Ƙasar tana ƙarƙashin sarki da yake “aika mugunta a gaban Ubangiji.” (2 Sarakuna 14:24) Shi ya sa hidimar Yunana ba zai kasance mai daɗi ba ko kuma mai sauƙi. Duk da haka, ya yi hidimarsa da aminci.
Wata rana, sai rayuwar Yunana ta sami canji matuƙa. Jehobah ya ba shi aiki da ya yi masa wuya ƙwarai da gaske. Menene Jehobah ya ce ya yi?
‘Tashi, ka Tafi Nineveh’
Jehobah ya gaya wa Yunana: “Tashi, ka tafi Nineveh, babban birnin nan, ka tada murya, ka faɗace ta; gama muguntassu ta hau gaba gareni.” (Yunana 1:2) Yanzu mun fahimci abin da ya sa wannan aikin ya kasance mai wuya ƙwarai. Nineveh tana da nisan mil 500 a gabas, ƙila tafiyar wajen wata ɗaya ne da kafa. Amma, wahalar tafiyar itace abu mafi sauƙi a wannan aikin. A Nineveh, Yunana zai sanar da saƙon hukunci na Jehobah ga Assuriyawa, masu nuna ƙarfi da mugun hali. Tun da Yunana bai ga canji sosai daga mutane Allah ba, mai zai gani daga wajen arna? Yaya bawan Jehobah, shi kaɗai zai yi nasara a birnin Nineveh mai girma, wanda za a soma kiransa “birni mai-jini”?—Nahum 3:1, 7.
Ko Yunana ya yi irin wannan tunanin. Ba mu sani ba. Abin da muka sani shi ne ya gudu. Jehobah ya aike shi zuwa gabas; amma Yunana ya yi yamma, ya je da nesa. Ya je bakin teku, zuwa garin da ake kira Joppa, idan ya sami jirgin mai zuwa Tarshish. Wasu masu bincike sun ce Tarshish tana ƙasar Spain. Idan haka ne, Yunana yana tafiya inda ke da nisan mil 2,200 daga Nineveh. Irin wannan tafiya a cikin jirgi zuwa ƙarshen Babbar Teku, wato yadda ake kiran Bahar Rum ke nan a dā zai ɗauki dogon lokaci sosai har shekara ɗaya! Yunana ya ƙuduri ya guje wa aikin da Jehobah ya ba shi!
Hakan yana nufin cewa Yunana matsoraci ne? Kada mu yi saurin hukunta shi. Kamar yadda za mu gani, yana da gaba gaɗi sosai. Kamar kowannenmu, Yunana ajizi ne da yake kokawa da kasawa. (Zabura 51:5) Wanene a cikin mu bai taɓa jin tsoro ba?
A wasu lokatai yana iya kasancewa kamar Allah yana cewa mu yi wani abu mai wuya, ko kuma abin da ba zai yiwu ba. Za mu iya yin sanyin gwiwa a yin wa’azin bisharar Mulkin Allah da aka ce Kiristoci su yi. (Matta 24:14) Ba shi da wuya mu mance da abin da Yesu ya ce: “Ga Allah abu duka ya yiwu.” (Markus 10:27) Idan muka mance da wannan abin da Yesu ya ce, hakan zai sa mu fahimci matsalar da Yunana ya fuskanta. Menene sakamakon gudun da Yunana ya yi?
Jehobah Ya Yi wa Annabinsa Marar Biyayya Horo
Za mu iya yin tunanin Yunana yana zama a cikin jirgin ruwa. Yana kallo sa’ad da shugaban jirgin da mutanensa suna ƙoƙari su sa jirgin a hanya. Sa’ad da suka soma tafiya, wataƙila Yunana ya yi tsammanin ya guje wa haɗarin da yake tsoro. Amma nan da nan sai yanayin ta canja.
Iska mai ƙarfi ta mamaye tekun, da raƙuman ruwa masu girman. Minti nawa ne ya ɗauka wannan jirgin ya gigice a cikin wannan guguwa? A wannan lokaci Yunana ya san abin da ya rubuta daga baya cewa “Ubangiji ya aike da babban iska cikin teku”? Ba mu sani ba. Ya ga waɗanda suke cikin jirgin suna roƙon allolinsu, kuma ya san cewa ba za su sami taimako daga allolin ƙarya ba. Labarin ya ce: “Jirgin yana bakin pashewa.” (Yunana 1:4; Leviticus 19:4) Kuma yaya Yunana zai yi wa Allahn da yake guduwa daga gare sa addu’a?
Da ya kasa taimako, sai Yunana ya nemi waje a can cikin jirgin ya kwanta. A nan ne ya yi barci mai zurfi.b Shugaban jirgin ya ga Yunana yana barci, sai ya tashe shi, ya ce masa ya yi wa Allahnsa addu’a kamar yadda kowa yake yi. Waɗanda suke aiki a cikin jirgin sun tabbata cewa da akwai dalilin wannan haɗari, sai suka jefa ƙuri’a don su ga ko wanene a cikin jirgin sanadin wannan matsalar. Babu shakka zuciyar Yunana ta faɗi sa’ad da ƙuri’a tana cire mutane ɗaiɗai. Nan da nan sai gaskiya ta fito. Jehobah ne yake ja-gorar haɗarin, da kuma ƙuri’ar zuwa kan mutum ɗaya, wato, Yunana.—Yunana 1:5-7.
Yunana ya gaya wa masu aiki a jirgin duk abin da ya faru. Shi bawan Maɗaukakin Allah ne, Jehobah. Shi ne Allahn da yake guje wa kuma shi ne ya sa su cikin wannan haɗarin. Mutanen suka yi mamaki; Yunana ya ga cewa suna cike da tsoro. Suka tambaye shi abin da za su yi don su ceci jirgin da rayukansu. Menene ya ce? Wataƙila Yunana ya yi tunanin yadda zai nitse a cikin wannan teku mai zurfi. Amma me ya sa zai sa waɗannan mutanen su halaka bayan zai iya ceton rayukansu? Sai ya ce: “Ku ɗauke ni, ku jefa ni cikin teku; da hakanan teku za ya yi muku sauƙi ya kwanta; gama na sani saboda ni ne wannan babban hadari ya same ku.”—Yunana 1:12.
Waɗannan kalaman ba na matsoraci ba ne. Hakika waɗannan kalaman sun faranta wa Jehobah rai da ya ga irin saɗaukar da kai da Yunana ya yi a wannan lokaci mai wuya. A nan mun ga bangaskiya mai ƙarfi da Yunana ya ke da shi. Za mu iya yin koyi da wannan ta wurin saka bukatun wasu fiye da na mu. (Yohanna 13:34, 35) Idan muka ga wani yana bukatan taimako, na zahiri, na motsin zuciya, ko kuma na ruhaniya, ya kamata mu ba da kanmu don mu taimake shi? Za mu faranta wa Jehobah rai idan muka yi hakan!
Wataƙila masu aiki a jirgin ma sun damu, shi ya sa da farko ba su yarda da abin da Yunana ya ce su yi ba. Maimakon haka, suka yi iya ƙoƙarinsu don su wuce haɗarin, amma son kasa. Haɗarin sai gaba gaba yake yi. A ƙarshe, sai suka ga cewa ba yadda za su yi. Sai suka yi kira ga Jehobah Allahn Yunana ya yi musu jin ƙai, suka ɗauke shi suka jefa shi cikin tukun.—Yunana 1:13-15.
An Yi wa Yunana Jin ƙai kuma An Cece Shi
Yunana ya faɗa cikin raƙumin ruwa. Wataƙila ya yi ƙoƙari don ya kasance a saman ruwan don ya tabbata cewa jirgin yana tafiya da kyau. Amma sai raƙumin ruwa ta tura shi ƙarƙashin tekun. Ya nitse ƙasa, yana tunanin kwanansa ta kare.
Daga baya Yunana ya kwatanta yadda ya ji a wannan lokaci. Yana ta tunanin abubuwa dabam dabam. Yana baƙin ciki cewa ba zai sake ganin haikali mai kyau na Jehobah a Urushalima ba. Ya yi tunanin yadda ya nitse har ƙasan tukun, kusa da ƙarƙashin dutsuna inda abubuwa da suka tsira a cikin teku suka kakkama shi. Yana ganin wannan ne zai zama kabarinsa.—Yunana 2:2-6.
Amma dakata! Akwai wani abu da yake zuwa kusa, wani babban kifi mai rai. Yana zuwa kusa da shi da sauri. Sai ya buɗe bakinsa ya haɗiye shi.
Ƙarshen rayuwarsa ke nan. Duk da haka, Yunana ya ji wani abu mai ban mamaki. Ya ji cewa yana nan da rai! Bai tauna shi ba, kuma yana nan ba abin da ya same shi. Yana nan da rai, ko da yake yana cikin wurin da ya kamata ya zama kabarinsa. A hankali, Yunana ya cika da tsoro. Babu shakka, Allahnsa Jehobah ne ya “shirya baban kifi wanda za shi hadiye Yunana.”c—Yunana 1:17.
Lokaci na wucewa har ya kai awoyi. A nan cikin irin duhu da bai taɓa gani ba, Yunana ya yi addu’a ga Jehobah Allah. Addu’ar da ya yi tana rubuce a littafin Yunana sura biyu. Hakan ya nuna cewa Yunana yana da ilimin Nassosi sosai, saboda sau da yawa yana ambata Zabura. Ya kuma nuna irin halinsa: wato na yin godiya. Yunana ya kammala: “Amma ni, da muryar godiya zan yi maka hadaya; Zan biya abin da na yi wa’adinsa. Ceto na Ubangiji ne.”—Yunana 2:9.
Yunana ya koyi cewa Jehobah zai iya ceton kowa, a duk inda mutum yake, kuma ko wani lokaci. Har a “cikin cikin kifi,” Jehobah ya ceci bawansa da ke cikin matsala. (Yunana 1:17) Jehobah ne kaɗai zai iya sa mutum ya rayu kwana uku a cikin babban kifi. Yana da kyau a yau mu tuna cewa Jehobah shi ne ‘Allah, . . . wanda lumfashinmu yana hannunsa.’ (Daniel 5:23) Numfashinmu da ranmu suna hannunsa. Muna nuna godiya kuwa? Muna bukata mu yi wa Jehobah biyayya.
Yunana kuma fa? Ya koyi nuna godiya ga Jehobah da yin biyayya? E. Bayan kwana uku, kifin ya zo bakin teku ya “amaitadda Yunana, ya zubasda shi a gaci.” (Yunana 2:10) Ka yi tunani, bayan haka, Yunana bai soma iyo don ya kai bakin teku ba! Amma, daga bakin teku ya soma neman hanya, duk inda take. Amma ba da daɗewa ba, aka gwada halinsa na godiya. Yunana 3:1, 2, ta ce: “Sai maganar Ubangiji ta zo wurin Yunana, zuwa na biyu, cewa, Tashi, ka tafi Nineveh, babban birnin nan, ka faɗace ta da faɗaka wadda na umurce ka.” Menene Yunana zai yi?
Yunana bai yi jinkiri ba. Mun karanta: “Yunana fa ya tashi, ya tafi Nineveh bisa ga maganar Ubangiji. Nineveh babban birni ce ƙwarai, na tafiyar yini uku.” (Yunana 3:3) E, ya yi biyayya. Hakika, ya koya daga kuskurensa. Muna bukatar mu yi koyi da bangaskiyar Yunana. Dukan mu muna yin zunubi; kuma muna yin kuskure. (Romawa 3:23) Amma muna yin sanyin gwiwa, ko kuma muna koya daga kuskurenmu kuma mu yi biyayya ga hidimar Allah?
Jehobah ya albarkaci Yunana don biyayyarsa kuwa? Hakika ya albarkace shi. Abu na farko, Yunana ya sami labarin cewa waɗanda suke cikin jirgin nan sun tsira. Haɗarin ya lafa nan da nan bayan da suka jefa Yunana cikin teku, kuma waɗanda suke cikin jirgin suka “ji tsoron Ubangiji ƙwarai” suka yi hadaya ga Jehobah maimakon allolin su na ƙarya.—Yunana 1:15, 16.
Daga baya ya sami wani sakamako mai girma. Yesu ya yi amfani da lokacin da Yunana yake cikin cikin kifi ya annabta yadda zai kasance a kabari. (Matta 12:38-40) Yunana zai yi farin ciki ya ji wannan albarkar sa’ad da ya tashi daga matattu a duniya. (Yohanna 5:28, 29) Jehobah yana son ya albarkace ka. Kamar Yunana, za ka yi koyi daga kuskurenka kuma ka yi biyayya, ka kasance da halin saɗaukar da kai?
[Hasiya]
a Kasancewar Yunana ɗan asalin Galili abu ne mai muhimmanci saboda Farisawa sun ce game da Yesu: “Ka bi ciki, ka gani, daga cikin Galili babu annabin da ke fitowa.” (Yohanna 7:52) Masu fassara da yawa da kuma masu bincike sun ce wai Farisawa suna nufi cewa ba a taɓa annabi ba daga Galili. Idan haka ne, waɗannan mutanen sun yi watsi da tarihi da kuma annabci.—Ishaya 9:1, 2.
b Don ya nanata irin barcin da Yunana ya yi, wani fassara ya ce ya yi barci har da minshari. Amma, maimakon mu yi tunanin cewa Yunana bai kula da abin da yake faruwa da jirgin ba, za mu iya tuna cewa wani lokaci barci yakan sha kan waɗanda suke da damuwa. A lokacin da Yesu yana cikin azaba a lambun Jathsaimani, Bulus, da Yaƙub da Yohanna suna “barci domin baƙinciki.”—Luka 22:45.
c Da aka fassara wannan kalmar Ibrananci “babban kifi” zuwa Hellenanci yana nufin “dodon teku,” ko kuma “kifi mai girma.” Ko da yake babu yadda za a san kowane irin halitta ne wannan, an lura cewa akwai manyan kifaye da za su iya haɗiye mutum ɗungum a cikin tekun. Akwai wasu manyan kifaye a wasu wuraren; wani babban kifin yana iya kai tsawon kafa 45 wataƙila ma fiye da haka!
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 29]
Yan Suka Sun Soki Littafin Yunana
▪ Abin da aka rubuta a littafin Yunana na Littafi Mai Tsarki da gaskiya ne ya faru? Tun a zamanin dā, ’yan suka suna sukan littafin. A zamanin nan da ake suka da yawa, sau da yawa ana ɗaukan littafin Yunana a kan ƙage ne, ko kuma tatsuniya. Wani mawallafi a ƙarni na 19 ya ba da rahoton yadda wani shugaban addini ya bayyana cewa labarin Yunana da babban kifi tatsuniya ne mai ban mamaki: Ya ce Yunana ya sauka a wani masauki a Joppa mai suna Alamar Babban Kifi. Sa’ad da ba shi da isashen kuɗin da zai biya kuɗin daƙin sai mai gidan ya kore shi. Haka ne aka “shigar” da kuma “fitar” da Yunana daga cikin babban kifi! Hakika, ’yan suka suna ƙoƙari su ƙaryata wanzuwar Yunana fiye da na babban kifin!
Me ya sa mutane da yawa suke shakkar gaskiyar wannan littafi na Littafi Mai Tsarki? Ya kwatanta mu’ujizai. Ga masu suka da yawa, mu’ujiza ba ta taɓa yiwu ba. Amma wannan ra’ayin gaskiya ce? Ka tambayi kanka: ‘Na gaskata da jimla ta farko da ke cikin Littafi Mai Tsarki?’ Ya ce: “A cikin farko Allah ya halitta sama da ƙasa.” (Farawa 1:1) Miliyoyin mutane masu hankali a dukan duniya sun amince da wannan gaskiyar. A wata hanya, wannan jimlar kaɗai ta fi kowace irin mu’ujizai da aka kwatanta daga baya a cikin Littafi Mai Tsarki.
Yi la’akari: Ga wanda ya halicci duka sararin samaniya da duka abubuwa a duniya masu ban mamaki, wane abu ne a littafi Yunana zai gagare shi? Tada guguwa? Sa babban kifi ya haɗiye mutum? Ko kuma ya sa wannan kifin ya yi aman mutumin? Ga wanda yake da iko marar iyaka, waɗannan abubuwa ba za su kasance da wuya ko kaɗan ba.—Ishaya 40:26.
Ko da ma Allah bai sa hannu ba, wani lokaci abubuwa masu ban mamaki suna faruwa. Alal misali, an ce a shekara ta 1758, wani mai tukin jirgi ya faɗi daga cikin jirginsa na ruwa zuwa cikin Bahar Rum kuma babban kifi ya haɗiye shi. Sai, aka harbi kifin da igwa. Ya sami kifin, ya yi aman sa da ransa, kuma ko rauni bai ji ba. Idan hakan gaskiya ce, za mu ɗauki labarin abin ban mamaki, amma ba mu’ujiza ba. Allah ba zai iya yin amfani da ikonsa ya yi abin da ya fi haka ba?
Mutane masu shakka sun ce ba yadda mutum zai kasance da rai a cikin kifi har kwana uku bai mutu ba. Amma, mutane suna da hikima sosai har sun san yadda za su cika tanki da iska su yi amfani da su don su yi numfashi a ƙarƙashin ruwa na dogon lokaci. Allah ba zai iya yin amfani da ikonsa da kuma hikimarsa ya sa Yunana ya kasance da rai kuma ya yi numfashi na kwana uku ba? Kamar yadda wani mala’ikan Jehobah ya ce wa Maryamu, uwar Yesu, “Babu magana daga wurin Allah da za ta rasa iko.”—Luka 1:37.
Menene kuma ya sa littafin Yunana ya zama tarihi na gaskiya? Kwatancin dalla-dalla da Yunana ya yi game da jirgin da kuma ma’aikatan gaskiya ne. A Yunana 1:5, mun ga yadda masu tukin jirgin suna jefar da kaya daga cikin jirgin don su rage masa nauyi. Wasu ’yan tarihi da kuma dokar Yahudawa a dā sun nuna cewa haka ake yi a lokacin mugun yanayi. Kwatancin Nineveh wadda Yunana ya yi daga baya ya yi daidai da na tarihi da kuma binciken tona ƙasa. Bayan haka, Yesu ya kwatanta kwana uku da Yunana ya yi a cikin babban kifi a matsayin annabcin kasancewarsa a cikin kabari. (Matta 12:38-40) Wannan abin da Yesu ya ambata ya nuna cewa labarin Yunana gaskiya ne.
“Babu magana daga wurin Allah da za ta rasa iko.”—Luka 1:37
[Hotunan da ke shafi na 26]
Kamar yadda Yunana ya ba da umurni, masu aiki a jirgin sun jefe shi cikin teku