“Wane Ne Fa Bawan Nan Mai-aminci, Mai-hikima?”
“Wane ne fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa?”—MAT. 24:45.
1, 2. Ta wace hanya ce Yesu yake ciyar da mu a yau, kuma me ya sa yake da muhimmanci mu san da hakan?
“’YAN’UWA, ba zan iya ƙirga yawan talifofin da kuka wallafa da suka tattauna ainihin abin da nake bukata ba.” Abin da wata ’yar’uwa ta rubuta a wasiƙar da ta aika wa ’yan’uwan da ke hidima a hedkwatarmu ke nan don ta nuna godiyarta. Shin ka taɓa jin hakan kuwa? Da yawa cikinmu mun taɓa jin hakan. Shin ya kamata hakan ya sa mu mamaki ne? A’a.
2 Koyarwar Allah da muke samu a yau tabbaci ne cewa Yesu, Shugaban ikilisiya yana cika alkawarinsa na ciyar da mu. Ta wurin waye ne yake yin hakan? Sa’ad da Yesu yake faɗin alamar bayyanuwarsa, ya ce zai yi amfani da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” don ya ba iyalin gidansa “abincinsu a lotonsa.”a (Karanta Matta 24:45-47.) Yesu yana amfani da wannan bawa mai-aminci don ya ciyar da mabiyansa na gaskiya a wannan kwanaki na ƙarshe. Yana da muhimmanci mu san wannan bawan. Ta wannan hanyar ce muke yin ibada ga Allah kuma muke ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi.—Mat. 4:4; Yoh. 17:3.
3. Mene ne muka bayyana a littattafanmu a dā game da kwatancin bawan nan mai-aminci?
3 Ta yaya za mu fahimci kwatancin da Yesu ya yi game da bawan nan mai-aminci? A dā mun bayyana a littattafanmu cewa, a ranar Fentakos na shekara ta 33 ne Yesu ya naɗa wannan bawan mai-aminci don ya kula da iyalin gidansa. Kuma bawan yana wakiltar dukan Kiristoci shafaffu a matsayin rukuni da ke duniya tun lokacin. Kuma har ila kowane shafaffe yana cikin iyalin gidansa wanda bawan yake ciyar da su. A shekara ta 1919, Yesu ya naɗa bawan nan mai-aminci “bisa dukan abin da ya ke da shi,” wato dukan mallakarsa a duniya. Amma, yin nazari da kuma bimbini sosai ya nuna cewa ya kamata mu yi gyara ga wannan koyarwar. (Mis. 4:18) Bari mu tattauna wannan kwatancin da kuma yadda ya shafe mu, ko da muna da begen kasancewa a sama ko a duniya.
A WANE LOKACI NE ANNABCIN YA CIKA?
4-6. Me ya sa za mu ce kwatancin Yesu na bawan nan mai-aminci ya soma cika bayan shekara ta 1914?
4 Mahallin kwatancin bawan nan mai-aminci ya nuna cewa ya soma cikawa a wannan kwanaki na ƙarshe, ba a ranar Fentakos na shekara ta 33 ba. Bari mu ga yadda Nassosi suka sa muka ce haka.
5 Kwatancin bawan nan mai-aminci yana cikin annabcin da Yesu ya yi game da ‘alamar zuwansa da cikar zamani.’ (Mat. 24:3) Sashe na annabcin da aka ambata a littafin Matta 24:4-22 ya cika sau biyu. Na farko ya cika a shekara ta 33 zuwa ta 70 a zamanin Yesu. Kuma na biyun yana cika sosai a yau. Shin hakan yana nufin cewa kalaman Yesu game da bawan nan mai-aminci zai cika sau biyu ne? A’a.
6 Yesu ya mai da hankali sosai ga abubuwan da za su faru a zamaninmu, sa’ad da ya furta kalmomin da ke littafin Matta 24:29. (Karanta Matta 24:30, 42, 44.) Sa’ad da yake bayyana abin da zai faru a lokacin ƙunci mai girma, ya ce mutane za su ‘ga Ɗan mutum yana zuwa a bisa gizagizai na sama.’ Amma, ya gargaɗi waɗanda suke rayuwa a kwanaki na ƙarshe su kasance a faɗake. Ya ce: ‘Gama ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa,’ kuma a ‘cikin sa’ar da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.’b A wannan mahallin, sa’ad da Yesu yake magana game da abubuwan da za su auku a kwanaki na ƙarshe, sai ya faɗi kwatancin bawan nan mai-aminci. Saboda haka, za mu iya ce kalamansa game da bawan nan mai-aminci ya soma cika bayan an shiga kwanaki na ƙarshe a shekara ta 1914. Hakika, wannan bayanin daidai ne. Me ya sa muka ce hakan?
7. Wace tambaya mai muhimmanci ce aka yi sa’ad da aka soma kaka, kuma me ya sa?
7 Ka ɗan yi tunani a kan tambayar nan: ‘Wane ne fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima?’ A ƙarni na farko, zai yi wuya a yi irin wannan tambayar. Domin kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, manzannin suna iya yin mu’ujizai kuma su ba da baiwar ruhu mai tsarki da taimakon Allah. (A. M. 5:12) Shi ya sa ba wanda zai yi shakkar mutanen da Kristi ya naɗa don su yi ja-gora. Amma, ba haka yanayin yake ba a shekara ta 1914. A shekarar ce aka soma kaka. Wato lokaci ya yi da za a ware ciyayi daga alkama. (Mat. 13:36-43) Sa’ad da aka soma kaka, akwai jabun Kiristoci da yawa da suka yi da’awa cewa su ainihin mabiyan Kristi ne. Amma muhimmiyar tambayar ita ce: Ta yaya za mu san alkamar, wato Kiristoci shafaffu? Kwatancin bawan nan mai-hikima ya amsa tambayar. Shafaffu mabiyan Kristi ne za su zama waɗanda aka ciyar da su sosai da koyarwar Allah.
WANE NE BAWAN NAN MAI-AMINCI, MAI-HIKIMA?
8. Me ya sa ya dace bawan nan mai-aminci ya ƙunshi shafaffu Kiristoci?
8 Wajibi ne bawan nan mai-aminci ya ƙunshi shafaffu Kiristoci da ke duniya. Ana kiransu “zuriyar firist ba-sarauci,” kuma an ba su aikin “gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye [su] daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi.” (1 Bit. 2:9) Kuma ya dace da waɗanda suke cikin “zuriyar firist ba-sarauci” su koya wa ’yan’uwansu masu bi gaskiya.—Mal. 2:7; R. Yoh. 12:17.
9. Shin dukan shafaffu da ke duniya ne suke ciki bawan nan mai-aminci? Ka bayyana.
9 Shin dukan shafaffu da ke duniya ne bawan nan mai-aminci? A’a. Gaskiyar ita ce, ba kowane shafaffe ne yake saka hannu a aikin tanadar wa ’yan’uwa a dukan duniya koyarwar Allah ba. Akwai ’yan’uwa maza shafaffu da ke hidima a ikilisiya a matsayin bayi masu hidima ko kuma dattawa. Suna koyarwa gida gida da kuma a ikilisiyarsu, kuma suna goyon bayan ja-gorar da ake ba da daga hedkwata. Amma, ba sa saka hannu wajen tanadar wa ’yan’uwa a dukan duniya koyarwar Allah. Kuma akwai ’yan’uwa mata shafaffu masu tawali’u da ba sa tunanin ɗaukan hakkin koyarwa a ikilisiya.—1 Kor. 11:3; 14:34.
10. Wane ne bawan nan mai-aminci mai-hikima?
10 To, su waye ne bawan nan mai-aminci, mai-hikima? Ta wajen bin tsarin da Yesu ya yi na koyar da jama’a ta hannun mutane ƙalilan, bawan nan mai-aminci, mai-hikima ƙaramin rukuni ne da ya ƙunshi ’yan’uwa maza shafaffu da ke shirya da kuma tanadar da koyarwar Allah a lokacin bayyanuwar Kristi. A waɗannan kwanaki na ƙarshe, maza shafaffu da bawan nan mai-aminci ne suna hidima tare a hedkwatarmu. Kuma a shekaru baya bayan nan, bawan nan ne Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Amma, ka lura cewa kalmar nan ‘bawa’ a kwatancin Yesu yana nufin abu ne tilo. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana tsai da shawara tare.
SU WAYE NE IYALIN GIDANSA?
11, 12. (a) Waɗanne ayyuka biyu ne aka ce bawa mai-aminci mai-hikima ya yi? (b) A yaushe ne Yesu ya naɗa bawan nan mai-aminci bisa iyalin gidansa, kuma su waye ne ya zaɓa?
11 Ka lura cewa a cikin kwatancin Yesu, an ba bawan nan mai-aminci, mai-hikima ayyuka na musamman guda biyu. Aiki na farko shi ne bisa iyalin gidansa. Na biyu kuma bisa mallakar maigidan. Tun da kwatancin ya cika a kwanaki na ƙarshe, an ɗanka musu waɗannan ayyukan bayan Yesu ya soma mulki a shekara ta 1914.
12 A yaushe ne Yesu ya ce wa bawan nan ya kula da iyalin gidansa? Don mu samu amsar tambayar, bari mu sake duba abin da ya faru a shekara ta 1914, wato somawar lokacin kaka. Kamar yadda muka koya ɗazu, rukuni da yawa suna da’awa cewa su Kiristoci ne a lokacin. To, daga wane rukuni ne Yesu zai zaɓi da kuma naɗa bawan nan mai-aminci? An amsa wannan tambayar bayan da Yesu da kuma Jehobah suka yi bincike a haikalin, wato tsarin bauta wa Allah, hakan ya soma ne daga shekara ta 1914 zuwa farkon 1919.c (Mal. 3:1) Sun yi farin cikin samun wannan ƙaramin rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki masu aminci da suka nuna cewa suna ƙaunar Jehobah da kuma Kalmarsa. Ko da yake suna bukata a tsarkake su, sun ba da haɗin kai a lokacin gwajin da kuma tsarkakewar. (Mal. 3:2-4) Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki masu aminci ne alkamar, wato Kiristoci na gaskiya. Amma a shekara ta 1919, Yesu ya zaɓi ƙwararrun maza shafaffu daga cikin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki don su zama bawan nan mai-aminci mai-hikima, kuma ya naɗa su bisa iyalin gidansa.
13. Su waye ne suke cikin iyalin gidansa, kuma me ya sa?
13 Su waye ne iyalin gidansa? Su ne waɗanda ake ciyar da su. Dukan iyalin gidansa shafaffu ne a farkon waɗannan kwanaki na ƙarshe. Amma daga baya, iyalin gidansa suka ƙunshi taro mai-girma na waɗansu tumaki. A yanzu, waɗansu tumaki ne suka fi yawa a cikin “garke ɗaya” da Yesu yake shugabanci a kansu. (Yoh. 10:16) Dukansu suna amfana daga koyarwar Allah da bawan nan mai-aminci suke tanadarwa. ’Yan Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da a yau su ne bawan nan mai-aminci kuma fa? Su ma suna bukatar su amfana daga wannan tanadin. Yanzu sun fahimci cewa kowanne ɗaya cikinsu na cikin iyalin gidansa kamar sauran mabiyan Yesu.
14. (a) Wane hakki ne aka ɗanka wa bawan nan mai-aminci, kuma mene ne hakan ya ƙunsa? (b) Wane gargaɗi ne Yesu ya yi wa wannan bawan? (Ka duba akwatin nan “Idan Mugun Bawan Nan Ya . . .”)
14 Yesu ya ba bawan nan mai-aminci, mai-hikima gagarumin aiki. A zamanin dā, bawa ne ke kula da gida. (Luk 12:42) Saboda haka, bawan nan mai-aminci, mai-hikima yana da hakkin kula da ƙungiyar Jehobah. Hakan ya ƙunshi kula da dukiyoyin ƙungiyar Jehobah da aikin wa’azi da tsarin ayyuka na manyan taro da taron gunduma da wallafa littattafai da ake amfani da su a wa’azi da kuma taron ikilisiya. Iyalin gidansa suna dogara ne ga dukan koyarwar Allah da bawan nan yake tanadarwa.
A YAUSHE NE UBANGIJIN YA SANYA SHI BISA MALLAKARSA?
15, 16. A yaushe ne Yesu ya sanya bawan nan mai-aminci bisa abin da yake da shi?
15 A yaushe ne Yesu ya sanya bawan nan bisa “dukan abin da ya ke da shi”? Yesu ya ce: “Wannan bawa mai-albarka ne, wanda ubangijinsa sa’anda ya zo za ya iske shi yana yin haka. Hakika, ina ce muku, za ya sanya shi bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Mat. 24:46, 47) Ka lura cewa Yesu ya ba da aiki na biyu sa’ad da ya zo ya iske bawan “yana yin haka,” wato yana tanadar da koyarwar Allah. Sabili da haka, akwai lokacin jira kafin a ba da aiki na biyu. Don mu fahimci yadda Yesu ya sanya bawansa bisa abin da yake da shi da kuma lokacin da ya yi hakan, muna bukatar mu san abubuwa biyu, wato lokacin da ya zo da kuma abin da mallakarsa ta ƙunsa.
16 A yaushe ne Yesu ya zo? Amsar tana cikin ayoyi na farko na littafin Matta sura ta 24. Ka tuna cewa sa’ad da ayoyin da suka gabata suka ce Yesu yana “zuwa,” hakan yana nufin lokaci da zai zo ya hukunta miyagu a ƙarshen wannan zamanin.d (Mat. 24:30, 42, 44) Saboda haka, ‘zuwan’ Yesu da ke kwatancinsa na bawan nan mai-aminci zai auku a lokacin ƙunci mai girma.
17. Mene ne abin da Yesu yake da shi suka ƙunsa?
17 Mene ne “dukan abin da [Yesu] yake da shi” suka ƙunsa? Yesu bai nuna cewa wannan kalmar “dukan” ta ƙunshi abubuwan da yake da su a duniya kaɗai ba. Yesu yana da iko a sama, shi ya sa ya ce: “An mallaka mini dukkan iko a sama da ƙasa.” (Mat. 28:18, Littafi Mai Tsarki; Afis. 1:20-23) Saboda haka, abin da yake da shi ya ƙunshi Mulkin Almasihu wanda aka ɗanka masa tun shekara ta 1914 kuma zai yi mulkin tare da mabiyansa shafaffu.—R. Yoh. 11:15.
18. Me ya sa Yesu zai yi farin cikin sanya bawan bisa dukan abin da yake da shi?
18 Daga abubuwan da muka tattauna, mene ne za mu iya kammalawa? Sa’ad da Yesu ya zo hukunci a lokacin ƙunci mai-girma, zai iske bawan nan mai-aminci yana tanadar wa iyalin gidansa koyarwar Allah. A lokacin ne Yesu zai yi farin cikin sanya shi bisa dukan abin da yake da shi. Za a danƙa wa bawan nan wannan aikin sa’ad da suka je sama kuma suka soma sarauta tare da Yesu.
19. Shin bawan nan mai-aminci zai samu lada fiye da sauran shafaffu a sama? Ka bayyana.
19 Shin bawan nan mai-aminci zai samu lada fiye da sauran shafaffun a sama? A’a. Alkawarin da aka yi wa ƙaramin rukuni zai iya shafan wasu ma. Alal misali, ka yi la’akari da abin da Yesu ya gaya wa manzanninsa guda sha ɗaya masu aminci a dare na ƙarshe kafin ya mutu. (Karanta Luka 22:28-30.) Yesu ya yi wa manzanninsa alkawari cewa akwai ladar da zai ba su domin sun kasance da aminci. Za su yi sarauta tare da shi. Amma, bayan wasu shekaru, ya ce dukan mutane 144,000 za su yi sarautar tare da shi. (R. Yoh. 1:1; 3:21) Hakazalika, kamar yadda aka ambata a Matta 24:47, ya yi alkawari cewa zai sanya ƙaramin rukuni, wato ’yan’uwa maza shafaffu wanda su ne bawan nan mai-aminci bisa abin da yake da shi. Hakika, dukan mutane 144,000 za su yi sarauta tare da Yesu a mulkinsa.—R. Yoh. 20:4, 6.
20. Me ya sa Yesu ya naɗa bawan nan mai-aminci, kuma mene ne ka ƙudura niyyar yi?
20 Bawan nan mai-aminci, mai-hikima ne Yesu yake amfani da shi don ya ciyar da jama’a, kamar yadda ya yi a ƙarni na farko. Yesu ya naɗa bawan nan mai-aminci don ya tabbatar da cewa mabiyansa na gaskiya, ko da shafaffu ne ko kuma waɗansu tumaki, sun samu tanadin koyarwar Allah a kai a kai a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Bari mu ƙudura niyyar ci gaba da nuna godiya ta wajen goyon bayan ’yan’uwa shafaffun da ke cikin bawan nan mai-aminci, mai-hikima.—Ibran. 13:7, 17.
a Sakin layi na 2: A farko, Yesu ya ba da wani kwatanci inda ya kira ‘bawan’ “wakili.”—Luk 12:42-44.
b Sakin layi na 6: Kalmar nan ‘zuwan’ Kristi (a Helenanci, erʹkho·mai) dabam ne da “bayyanuwarsa’ (pa·rou·siʹa). Ya fara sarauta a sama kafin ya zo ya halaka miyagu.
c Sakin layi na 12: Ka duba talifin nan “Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi” a wannan talifin, shafuffuka na 10-12, sakin layi na 5-8.
d Sakin layi na 16: Ka duba talifin nan “Ka Faɗa Mana, Yaushe Waɗannan Abubuwa Za Su Zama?” a wannan mujallar, shafuffuka na 7-8, sakin layi na 14-18.