Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 11/15 pp. 15-19
  • Ka Zama Mai Tawali’u

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Zama Mai Tawali’u
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • BABU IYAKA GA ZURFIN ‘HIKIMAR ALLAH DA SANINSA’
  • ‘ƘANƘANI A CIKINKU, SHI NE BABBA’
  • KA YI ƘOƘARI KA ZAMA MAI TAWALI’U
  • Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ka Koyi Tawali’u Na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Yesu Ya Kafa Misali Na Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Jehovah Ya Bayyana Ɗaukakarsa Ga Masu Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 11/15 pp. 15-19

Ka Zama Mai Tawali’u

“Wanda shi ke ƙanƙani a cikinku duka, shi ne babba.”—LUK 9:48.

MENE NE AMSOSHIN WAƊANNAN TAMBAYOYIN?

Mene ne zai taimaka mana mu zama masu tawali’u?

A wace hanya ce mai tawali’u “babba” ne?

Ta yaya za mu nuna tawali’u a cikin iyali da ikilisiya da kuma a dangantakarmu da mutane?

1, 2. Wane gargaɗi ne Yesu ya ba almajiransa, kuma me ya sa?

A SHEKARA ta 32 sa’ad da Yesu yake Galili, wata gardama ta taso tsakanin almajiransa. Sai suka soma mūsu a kan wanda ya fi girma. Luka ya rubuta abin da ya faru a wannan lokacin. Ya ce: “Gardama fa ya tashi a cikinsu, ko wanene daga cikinsu za ya fi girma. Amma sa’anda Yesu ya ga tunanin zuciyarsu kuma, ya ɗauki ɗan yaro ƙarami, ya sa shi daura da shi, ya ce musu, Dukan wanda ya karɓi ɗan ƙaramin yaron nan a cikin sunana, ni ya ke karɓa: kuma dukan wanda ya karɓe ni, yana karɓan wanda ya aiko ni: gama wanda shi ke ƙanƙani a cikinku duka, shi ne babba.” (Luk 9:46-48) Yesu ya yi haƙuri da almajiransa kuma ya koya musu amfanin tawali’u.

2 Shin nuna tawali’u gama gari ne ga Yahudawa a lokacin? Ko kaɗan. Mutane a zamanin ba su da tawali’u. Wani ƙamus ya bayyana abin da ke faruwa a lokacin. Ya ce: “Yahudawa suna ɗaukan girma da muhimmanci sosai a dukan fannonin rayuwarsu. Suna yawan tunani ko sun ba wani girma, ko kuma an ba su girma.” Yesu yana son almajiransa su yi dabam da mutanen zamaninsu.

3. (a) Mene ne zama ƙanƙani yake nufi, kuma me ya sa yin hakan zai iya kasance mana da wuya? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?

3 Ga yadda aka fassara furucin nan “ƙanƙani” a Helenanci. Mutumin da ke da filako da tawali’u da sauƙin kai, kuma ba ya cika ɗaukan kansa da muhimmanci. Yesu ya koya wa almajiransa cewa ya kamata su zama masu sauƙin kai da tawali’u kamar ƙaramin yaro. Ya kamata Kiristoci ma a yau su bi gargaɗin Yesu. Zai yi mana wuya mu kasance da tawali’u a wasu lokatai. Ajizancinmu zai iya sa mu zama masu fahariya da masu neman girma. Bugu da ƙari, duniyar nan da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan za ta iya sa mu zama masu son kai da masu cin zali. Mene ne zai iya taimaka mana mu zama masu tawali’u? Ta yaya ƙanƙani a cikinmu ne ‘babba’? A waɗanne yanayi ne ya kamata mu zama masu tawali’u?

BABU IYAKA GA ZURFIN ‘HIKIMAR ALLAH DA SANINSA’

4, 5. Mene ne zai taimaka mana mu zama masu tawali’u? Ka ba da misali.

4 Idan mun tuna cewa Jehobah ya fi mu girma, hakan zai taimaka mana mu kasance da tawali’u. Hakika, “fahiminsa ya wuce gaban a bi ciki.” (Isha. 40:28) Manzo Bulus ya bayyana ikon Jehobah. Ya ce: “Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bincika su duka!” (Rom. 11:33) Manzo Bulus ya rubuta waɗannan kalmomin kusan shekara 2,000 da ta shige, kuma tun daga lokacin, ’yan Adam sun ƙara ilimi. Amma, abin da ya faɗa gaskiya ce. Ko yaya yawan iliminmu, ba za mu taɓa daina koyon sababbin abubuwa game da Jehobah da ayyukansa da kuma tunaninsa ba.

5 Alal misali, wani abu da ya taimaki wani matashi mai suna Leoa ya daɗa sauƙin kai shi ne cewa, ba zai taɓa sanin kome game da halittun Allah ba. Leo ya je makarantar kimiyya domin yana son ya yi nazari game da sararin samaniya da kuma duniya. Da shigewar lokaci, sai ya ankara cewa yana bukatar ya zama lauya don ya fahimci kome game da halittu. Daga baya, sai Shaidun Jehobah suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi da matarsa kuma suka yi baftisma. Ko da yake Leo yana da ilimi sosai, mene ne ya taimake shi ya zama mai tawali’u? Ya ce: “Sani cewa ba zan iya taɓa fahimtar kome game da halittun Jehobah ne ya taimake ni.”

6, 7. (a) Wane misali na tawali’u ne Jehobah ya nuna mana? (b) Ta yaya tawali’un Jehobah zai sa mutum ya zama “babba”?

6 Wani abu kuma da zai taimaka mana shi ne sanin cewa Jehobah ma yana da tawali’u. Ka yi la’akari da wannan: “Mu abokan aiki na Allah ne.” (1 Kor. 3:9) Hakan ba abin mamaki ba ne? Jehobah, wanda shi ne mafi iko da girma yana daraja mu ta wajen ba mu zarafin yin amfani da Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki don yi wa mutane wa’azin bishara. Jehobah ne yake sa mutane su samu ci gaba, amma duk da haka, ya ba mu zarafin yin wa’azi da kuma koma ziyara. (1 Kor. 3:6, 7) Hakan ya nuna cewa Jehobah mai tawali’u ne. Hakika, ya kamata yadda Jehobah mai tawali’u ne ya motsa mu mu zama masu tawali’u.

7 Yadda yake nuna tawali’u ya shafi Dauda sosai. Ya ce wa Jehobah: “Ka kuma ba ni garkuwar cetonka: nasiharka [tawali’unka, NW] kuma ta maishe ni mai-girma.” (2 Sam. 22:36) Dauda ya san cewa tawali’un Jehobah ne ya sa yake cim ma abubuwa masu ban al’ajabi. (Zab. 113:5-7) Hakan ma yake da mu a yau. Idan muna da halaye masu kyau, ko iyawa ko kuma gata, Jehobah ne ya ba mu su. (1 Kor. 4:7) Mai tawali’u “babba” ne, domin yana daɗa samun daraja a gaban Jehobah. (Luk 9:48) Yanzu za mu tattauna yadda hakan zai yiwu.

‘ƘANƘANI A CIKINKU, SHI NE BABBA’

8. Me ya sa waɗanda suke ƙungiyar Jehobah suke bukatar su kasance da tawali’u?

8 Masu tawali’u suna farin ciki a ƙungiyar Jehobah kuma suna goyon bayan yadda abubuwa suke tafiya a cikin ikilisiya. Alal misali, ka yi la’akari da misalin wata matashiya mai suna Petra, wadda iyayenta Shaidu ne. Petra tana son ta riƙa yin abin da ta ga dama, sai ta daina tarayya da ikilisiya. Bayan ’yan shekaru, sai ta farfaɗo. Yanzu tana farin ciki domin yin tarayya da ƙungiyar Jehobah kuma tana goyon bayan ayyuka na ikilisiya. Me ya sa ta canja ra’ayinta? Ta ce, “Tawali’u da filako suna da muhimmanci sosai, kuma su ne suka taimaka mini.”

9. Ta yaya mai tawali’u yake ɗaukan Kalmar Allah da littattafanmu, kuma yaya hakan yake sa ya daɗa samun daraja?

9 Mutum mai tawali’u yana godiya don dukan tanadin Jehobah da kuma yadda yake taimaka mana mu san shi sosai. Shi ya sa mutum mai tawali’u yana yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! a kai a kai. Bayin Jehobah da yawa suna karanta sababbin littattafai da aka tanadar mana kafin su saka su a cikin kabat ɗinsu. Idan muka nuna tawali’u ta wajen karanta da kuma yin nazarin littattafanmu, za mu kusaci Allah sosai, kuma zai yi amfani da mu sosai a hidimarsa.—Ibran. 5:13, 14.

10. Ta yaya za mu iya nuna tawali’u a cikin ikilisiya?

10 Akwai wata hanya kuma da mutum mai tawali’u zai iya zama “babba.” Jehobah yana amfani da ruhunsa don ya naɗa maza a matsayin dattawa a dukan ikilisiyoyi. Waɗannan mazan suna shirya taro da yadda za a yi wa’azi, kuma suna ƙarfafa ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Idan muka nuna tawali’u ta wajen goyon bayan dattawa, za mu sa ikilisiyar baki ɗaya ta kasance da farin ciki da salama da kuma haɗin kai. (Karanta Ibraniyawa 13:7, 17.) Idan kai dattijo ne ko kuma bawa mai hidima, kana nuna tawali’u ta wajen daraja gatan da Jehobah ya ba ka?

11, 12. Wane irin hali ne zai sa mu zama masu tamani sosai a ƙungiyar Jehobah, kuma me ya sa?

11 Mai tawali’u yana da amfani a cikin ƙungiyar Jehobah domin tawali’unsa yana sa ya zama mai tamani. Yesu ya aririce almajiransa su zama masu tawali’u domin wasu cikinsu suna fahariya kamar maƙwabtansu. Littafin Luka 9:46 ya ce: “Gardama fa ya tashi a cikinsu, ko wanene daga cikinsu za ya fi girma.” Shin mu ma za mu iya soma tunani cewa mun fi wasu daraja? Bai kamata mu zama kamar mutane da yawa a duniya da suke fahariya da son kai ba. Maimakon haka, ya kamata mu zama masu tawali’u kuma mu sa nufin Jehobah ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Idan muka yi hakan, ’yan’uwanmu maza da mata za su wartsake sa’ad da suke tare da mu.

12 Umurnin da Yesu ya ba mu cewa mu zama masu tawali’u yana da muhimmanci sosai. Ya kamata mu yi hakan a dukan fannoni na rayuwarmu. Bari mu tattauna yanayi guda uku.

KA YI ƘOƘARI KA ZAMA MAI TAWALI’U

13, 14. Ta yaya miji ko mata za su kasance da tawali’u, kuma yaya hakan zai sa su ji daɗin aurensu?

13 A cikin iyali. Mutane da yawa a yau sun fi damuwa da ’yancinsu, kuma na wasu bai dame su ba. Amma, mai tawali’u yana da irin halin da Bulus ya ce mu kasance da shi. A wasiƙarsa ya ce: “Mu bi waɗannan abu fa da ke nufa wajen salama, da abubuwa waɗanda za mu gina junanmu da su.” (Rom. 14:19) Mai tawali’u yana ƙoƙari don ya yi zaman lafiya da mutane, musamman da matarsa ko mijinta.

14 Alal misali, nishaɗin da mai gida yake so zai iya bambanta da na matarsa. Wataƙila, mijin yana son karatu sa’ad da yake hutu, amma matarsa za ta iya so ziyartar ƙawaye. Idan mijin ya kasance da tawali’u kuma ya daraja ra’ayinta, zai yi mata sauƙi ta yi masa biyayya. Idan matar ma ba ta yawan nace wa ra’ayinta, hakan zai sa mijin ya daɗa ƙaunarta sosai. Idan mata da miji suka kasance da tawali’u, za su kusaci juna sosai.—Karanta Filibiyawa 2:1-4.

15, 16. Kamar yadda Zabura ta 131 ta nuna, mene ne Dauda ya ƙarfafa Isra’ilawa su yi, kuma yaya za mu iya yin hakan a cikin ikilisiya?

15 A cikin ikilisiya. Mutanen duniya ba su da haƙuri ko kaɗan. Suna so su samu abin da suke sha’awa nan take. Akasin haka, idan muna da tawali’u, za mu riƙa dogara ga Jehobah. (Karanta Zabura 131:1-3.) Idan mun dogara ga Jehobah, zai saka mana ya kāre mu, kuma za mu yi farin ciki. Shi ya sa Dauda ya ƙarfafa Isra’ilawa su yi haƙuri kuma su dogara ga Jehobah.

16 Za ka samu ƙarfafa idan ka yi haƙuri, kuma ka dogara ga Jehobah kamar yadda Dauda ya yi. (Zab. 42:5) Wataƙila, kana son ka zama dattijo domin ka tallafa wa ikilisiya. (1 Tim. 3:1-7) Ruhu mai tsarki zai taimaka maka ka zama dattijo, idan ka yi ƙoƙari don kasance da halayen da za su sa ka cancanta. Amma, mene ne za ka yi idan ba a naɗa ka da wuri ba? Ya kamata ka kasance da tawali’u kuma ka yi haƙuri don ka samu ƙarin gata. Idan ka yi hakan, za ka ci gaba da bauta wa Jehobah kuma za ka samu ƙarin gata a cikin ikilisiya.

17, 18. (a) Wane sakamako za mu samu idan muka nemi gafara kuma muka gafarta wa mutane? (b) Wace shawara ce ke Misalai 6:1-5?

17 A dangantakarmu da mutane. Yana wa mutane da yawa wuya su nemi gafara. Amma, bayin Jehobah suna da tawali’u kuma suna neman gafara idan suka yi wa wani laifi. Kuma suna gafarta wa mutanen da suka musu laifi. Fahariya tana jawo matsaloli da yawa, amma gafartawa yana sa a kasance da kwanciyar rai a cikin ikilisiya.

18 Akwai wani lokaci da ya kamata mu kasance da tawali’u kuma mu nemi gafara. Alal misali, larura za ta iya sa mu saɓa wani alkawari. Amma idan hakan ya faru, ya kamata mu nemi gafara ko da ba da gangan muka saɓa alkawarin ba.—Karanta Misalai 6:1-5.

19. Me ya sa ya kamata mu yi farin ciki don Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu zama masu tawali’u?

19 Muna farin ciki sosai domin Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu mu kasance da tawali’u. Ba a kowane lokaci ba ne yin hakan yake kamar cin tuwo ba. Amma, idan mun tuna cewa Jehobah ya fi kowannenmu girma, kuma duk da haka, yana da tawali’u, hakan zai ƙarfafa mu mu yi koyi da shi. Idan mun yi haka, Jehobah zai daraja mu sosai. Saboda haka, ya kamata dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu, don mu zama masu tawali’u.

[Hasiya]

a An canja sunan.

[Hoto a shafi na 16]

Jehobah yana daraja mu ta wajen ba mu gatan yin wa’azin bishara

[Hotona a shafi na 19]

A waɗanne yanayi ne za ka iya zama mai tawali’u?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba