BABI NA 31
‘Ka Yi Kusa da Allah, Shi Kuwa Zai Yi Kusa da Kai’
1-3. (a) Mene ne za mu iya koya game da mutane ta wajen lura da hulɗa tsakanin iyaye da jaririnsu? (b) Mene ne ainihi yake faruwa sa’ad da wani ya nuna mana ƙauna, kuma wace muhimmiyar tambaya ya kamata mu yi wa kanmu?
IYAYE suna so su ga jaririnsu yana murmushi. Sau da yawa suna kawo fuskokinsu kusa da ta jaririn, su yi raɗa suna murmushi. Suna marmari ganin abin da jaririn zai yi. Ba da daɗewa ba, sai ya zamana—kumatun jaririn su taru, ya ja leɓunansa, sai murmushi ya bayyana. A wannan hanyar, murmushin yana nuna ƙauna, mafarin ƙauna ta jaririn amsa ce ga ƙaunar iyayensa.
2 Murmushin jariri ya tuna mana wani abu mai muhimmanci game da mutane. Amsarmu ga ƙauna, ƙauna ce. Haka aka yi mu. (Zabura 22:9) Sa’ad da muke girma, muna girma a iyawarmu mu amsa ga ƙauna. Wataƙila za ka iya tuna lokacin da kake yarantaka yadda iyayenka, dangi, ko kuma abokane suka nuna maka ƙauna. A zuciyarka murna ta kahu ta yi jijiya, ta yi girma, ta yi fure. Ka mai da ƙauna kai ma. Irin wannan yana faruwa a dangantakarka da Jehobah Allah?
3 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muna ƙauna, gama Allah ya fara ƙaunace mu.” (1 Yohanna 4:19) A Sashe na 1 zuwa 3 na wannan littafin, an tuna maka cewa Jehobah Allah yana amfani da ikonsa, da shari’arsa, da kuma hikimarsa a hanya ta ƙauna da za ta amfane mu. Kuma a Sashe na 4, ka ga yadda yake nuna ƙaunarsa ga ’yan Adam kai tsaye—ga kai kanka—a hanya mai ban sha’awa. Yanzu tambaya ta taso. Ita ce muhimmiyar tambaya da za ka yi wa kanka: ‘Ta yaya zan amsa ga ƙaunar Jehobah?’
Abin da Take Nufi A Yi Ƙaunar Allah
4. A wace hanya ce mutane suka rikice game da abin da yake nufi a yi ƙaunar Allah?
4 Jehobah, Tushen ƙauna, ya sani ƙwarai cewa ƙauna tana da iko ta fito da halaye masu kyau daga wasu. Saboda haka, duk da nacewa ta ’yan Adam wajen yin tawaye, ya tabbata cewa wasu ’yan Adam za su amsa ƙaunarsa. Kuma hakika, miliyoyi sun yi haka. Abin baƙin ciki, addinai na wannan lalatacciyar duniya sun rikita mutane game da abin da take nufi a yi ƙaunar Allah. Mutane babu iyaka suna cewa suna ƙaunar Allah, amma kamar suna tunani ne cewa irin wannan motsin rai za a furta ne da kalmomi kawai. Ƙaunar Allah za ta iya farawa a wannan hanyar, kamar yadda ƙaunar jariri ga iyayensa za ta fara ne ta wajen murmushi. A mutane da suka manyanta kuma, ta ƙunshi fiye da haka.
5. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya bayyana ƙaunar Allah, kuma me ya sa za mu so wannan bayani?
5 Jehobah ya bayyana abin da yake nufi a yi ƙaunarsa. Kalmarsa ta ce: “Ƙaunarmu ga Allah ita ce, mu kiyaye umarnansa.” Saboda haka, ƙaunar Allah ana nuna ta cikin ayyuka. Hakika, batun biyayya ba shi da daɗi ga wasu. Amma kuma wannan ayar ta ƙara cewa: “Umarnan [Allah] ba su da nauyi.” (1 Yohanna 5:3) Dokokin Jehobah da kuma mizanansa ya yi su ne domin su amfane mu, ba domin su yi mana ciwo ba. (Ishaya 48:17, 18) Kalmar Allah tana cike da mizanan da za su taimake mu mu matso kusa da shi. Ta yaya? Bari mu maimaita ɓangarori uku na dangantakarmu da Allah. Waɗannan sun haɗa da magana, bauta da kuma bin misali.
Magana da Jehobah
6-8. (a) Ta wace hanya ce za mu saurari Jehobah? (b) Ta yaya za mu sa Nassosi su kasance kamar yanzu suke faruwa sa’ad da muke karatunsu?
6 Babi na 1 ya fara da wannan tambayar, “Za ka iya tunanin yin magana da Allah?” Mun ga cewa wannan ba sha’awa ba ce kawai. Musa, hakika ya yi magana da shi. Mu kuma fa? Yanzu ba lokaci ba ne Jehobah ya aiko da mala’ikunsa su yi magana da mutane. Jehobah yana da hanya mafi kyau na magana da mu a yau. Ta yaya za mu saurari Jehobah?
7 Domin “duk Rubutacciyar Maganar Allah hurarre ce daga wurinsa,” muna sauraron Jehobah ta wajen karatun Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. (2 Timoti 3:16) Saboda haka, Mai Zabura ya aririci bayin Jehobah su yi irin wannan karatun “dare da rana.” (Zabura 1:1, 2) Yin haka yana bukatar ɗan ƙoƙari a gare mu. Amma dukan irin wannan ƙoƙarin yana da kyau. Kamar yadda muka gani a Babi na 18, Littafi Mai Tsarki kamar wasiƙa ce mai tamani daga Ubanmu na sama. Irin wannan karatun ba aiki ba ne. Dole ne mu mai da Nassosi kamar suna faruwa nan da nan sa’ad da muke karatunsu. Ta yaya za mu yi haka?
8 Ka zana hoton zuci na labarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da kake karatu. Ka yi ƙoƙarin ka ga mutanen cikin Littafi Mai Tsarki da gaske. Ka yi ƙoƙari ka fahimci inda suka fito, yanayinsu, da kuma dalilan da suka sa suke abu. Sai, ka yi tunani mai zurfi game da abin da ka karanta, ka yi wa kanka tambayoyi kamar su: ‘Mene ne wannan labarin ya koya mini game da Jehobah? Wanne cikin halayensa nake gani? Wane mizani Jehobah yake so na koya, kuma ta yaya zan yi amfani da shi a rayuwa ta?’ Ka yi karatu, ka yi bimbini, kuma ka yi amfani da abin da ka koya—sa’ad da ka yi haka, Kalmar Allah za ta kasance da gaskiya a gare ka.—Zabura 77:12; Yakub 1:23-25.
9. Wanene “bawan nan mai aminci, mai hikima,” kuma me ya sa yake da muhimmanci cewa mu saurara da kyau ga “bawan”?
9 Jehobah kuma yana yi mana magana ta wajen “bawan nan mai aminci, mai hikima.” Kamar yadda Yesu ya annabta, an naɗa aji na Kiristoci shafaffu su yi tanadin ‘abinci a kan lokaci’ na ruhaniya a wannan lokaci na bala’i na kwanaki na ƙarshe. (Matiyu 24:45-47) Sa’ad da muka karanta littafi da aka shirya domin ya taimake mu mu samu cikakken sani na Littafi Mai Tsarki da kuma sa’ad da muka halarci taron Kirista a ikilisiya da taron gunduma, ajin bawan ne yake ciyar da mu a ruhaniya. Domin bawan Kristi ne, muna amfani da kalmar Yesu cikin hikima: “Ku yi hankali fa da yadda kuke ji.” (Luka 8:18) Muna sauraro ƙwarai domin mun fahimci cewa ajin bawan hanya ce ɗaya da Jehobah yake magana da mu.
10-12. (a) Me ya sa addu’a kyauta ce mai girma daga wajen Jehobah? (b) Ta yaya za mu yi addu’a a hanyar da za ta faranta wa Jehobah rai, kuma me ya sa za mu tabbata cewa yana ɗaukan addu’armu da tamani?
10 Yin magana da Allah kuma fa? Za mu iya magana da Jehobah ne? Tunani ne mai ban tsoro. Idan kana so ka je gaban wani sarki mai iko na ƙasarku domin ka yi magana da shi game da wasu abubuwa da suka dame ka, za ka samu zarafin yin hakan? A wasu lokaci ƙoƙarin haka ma sai ya kasance da haɗari! A zamanin Esther da Mordecai, za a iya kashe mutum idan ya dumfari sarkin Persiya ba tare da an gayyace shi ba. (Esta 4:10, 11) Yanzu ka yi tunanin zuwa gaban Ubangiji Mamallakin dukan halitta, wanda idan aka gwada mai sarauta mafi iko ma na ’yan Adam yana kama da “ ’yan ƙananan kiyashi.” (Ishaya 40:22) Ya kamata mu ji tsoron zuwa gare shi ne? Ko kaɗan!
11 Jehobah ya buɗe hanya mai sauƙi zuwa gare shi—addu’a. Har yaro ƙarami ma zai iya yi wa Jehobah addu’a cikin bangaskiya, ya yi haka cikin sunan Yesu. (Yohanna 14:6; Ibraniyawa 11:6) Hakika, addu’a ta ba mu daman furta motsin zuciyarmu—har masu ciwo waɗanda suke mana wuya mu faɗe su. (Romawa 8:26) Babu wani amfani mu yi ƙoƙarin mu burge Jehobah a iya magana, ko kuma da doguwar addu’a. (Matiyu 6:7, 8) A wani ɓangare kuma, Jehobah bai kafa iyakar lokaci da za a yi ana magana da shi ba ko kuma iyakan lokaci da za da zo gare shi. Kalmarsa ma ta gayyace mu mu yi “addu’a babu fasawa.”—1 Tasalonikawa 5:17.
12 Ka tuna cewa Jehobah ne kawai aka kira “Mai jin addu’o’i,” kuma yana saurara da juyayi na gaske. (Zabura 65:2) Kawai yana ƙyale addu’o’in bayinsa ne masu aminci? A’a, yana sauraronsu da farin ciki. Kalmarsa ta kwatanta waɗannan addu’o’i da turare, wanda idan aka ƙona ya kai ƙanshi, mai daɗi zuwa sama. (Zabura 141:2; Ru’ya ta Yohanna 5:8; 8:4) Ba abin ƙarfafa ba ne mu sani cewa haka addu’o’inmu suke zuwa sama kuma suke faranta wa Mai Iko duka rai? Idan haka ne za ka so ka matso kusa da Jehobah, cikin tawali’u ka yi masa addu’a sau da yawa, kowacce rana. Ka buɗe masa zuciyarka; kada ka ɓoye masa kome. (Zabura 62:8) Ka gaya wa Ubanka na sama damuwarka, farin cikinka, godiyarka, da yabonka, sakamakon haka, dangantaka da take tsakaninku za ta yi ƙarfi.
Bauta wa Jehobah
13, 14. Me yake nufi mu bauta wa Jehobah, kuma me ya sa ya dace mu yi hakan?
13 Sa’ad da muke magana da Jehobah Allah, ba kawai muna sauraro ba kuma muna magana ba ne kamar yadda muke yi da aboki ko kuma wani dangi. Muna bauta wa Jehobah ne, muna ba shi darajar da ta dace da shi. Bauta ta gaskiya ta shafi dukan rayuwarmu. Yadda muke furta ƙaunarmu ta dukan zuciya ce ga Jehobah da kuma ibada, kuma yana haɗa kan dukan halittu masu aminci na Jehobah, ko a sama ko kuma a duniya. A cikin wahayi, manzo Yohanna ya ji mala’ika yana shelar wannan umurnin: “Ku yi masa sujada, shi wanda ya yi sama, da duniya, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwa!”—Ru’ya ta Yohanna 14:7.
14 Me ya sa za mu bauta wa Jehobah? Ka yi tunanin halaye da muka tattauna, kamar su tsarkaka, iko, kamewa, shari’a, gaba gaɗi, jinƙai, hikima, tawali’u, ƙauna, tausayi, aminci, da kuma nagarta. Mun ga cewa Jehobah shi ne tushen, mizani mai girma, na kowane hali mai tamani. Sa’ad da muka yi ƙoƙari mu fahimci gabaki ɗayan halayensa, mukan fahimci cewa ya fi ƙarfinmu mu yi sha’awarsa kawai. Darajarsa abar ban tsoro ce, girmansa ba a gwada da mu. (Ishaya 55:9) Jehobah shi ne Mamallakinmu da ya dace, babu wata tambaya, kuma babu shakka ya cancanci bautarmu. Amma ta yaya za mu bauta wa Jehobah?
15. Ta yaya za mu bauta wa Jehobah “cikin ruhu da gaskiya,” kuma wane zarafi taron Kirista yake ba mu?
15 Yesu ya ce: “Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuma sai su yi masa sujada cikin ruhu, da cikin gaskiya kuma.” (Yohanna 4:24) Wannan yana nufin a bauta wa Jehobah da zuciya da ta cika da bangaskiya da ƙauna, wadda ruhu yake yi mata ja-gora. Kuma tana nufin a yi bauta cikin jituwa da gaskiya, cikakken sani da ake samu cikin Kalmar Allah. Muna da zarafi mai kyau mu bauta wa Jehobah “cikin ruhu da cikin gaskiya” a duk lokacin da muka taru da ’yan’uwanmu masu bauta. (Ibraniyawa 10:24, 25) Sa’ad da muke waƙa ga Jehobah, muna haɗa kai wajen addu’a a gare shi, kuma muka saurara muka saka baki wajen tattaunawa game da Kalmarsa, muna nuna masa ƙauna a cikin tsarkakkiyar bauta.
Taron Kirista lokatai ne na farin ciki na bauta wa Jehobah
16. Wannene ɗaya cikin umurni masu girma da aka ba Kiristoci, kuma me ya sa muke jin wajibi ne mu yi biyayya?
16 Muna bauta wa Jehobah kuma yayin da muke gaya wa wasu game da shi, muna yabonsa a fili. (Ibraniyawa 13:15) Hakika, wa’azin bisharar Mulkin Jehobah shi ne ɗaya daga cikin umurnai masu girma da aka ba wa Kiristoci na gaskiya. (Matiyu 24:14)Muna biyayya da himma domin muna ƙaunar Jehobah. Sa’ad da muka yi tunanin yadda “allah na zamanin nan,” Shaiɗan Iblis, ‘ya makantar da zuciyar’ marasa ba da gaskiya yana ɗaukaka baƙar ƙarya game da Jehobah, ba ma ɗokin kasancewa Shaidun Allah ne, mu gyara wannan ƙaryar? (2 Korintiyawa 4:4; Ishaya 43:10-12) Kuma sa’ad da muka yi tunanin halayen Jehobah masu ban sha’awa, ba ma jin muradi a cikinmu ya ƙaru mu gaya wa wasu game da shi? Hakika, ba za a kasance da wata gata ba da ta fi wannan mu taimaki wasu su san Ubanmu na sama kuma su yi ƙaunarsa.
17. Mene ne bautarmu ta Jehobah ta ƙunsa, kuma me ya sa za mu yi bauta cikin aminci?
17 Bautarmu ga Jehobah ta ƙunshi fiye ma da haka. Ta taɓa duk ɓangarorin rayuwarmu. (Kolosiyawa 3:23) Idan da gaske mun karɓi Jehobah shi ne Mamallakinmu, za mu nemi mu yi nufinsa a dukan abu—a rayuwar iyali, a wajen aikinmu, a sha’aninmu da wasu, a harkokinmu. Za mu nemi mu bauta wa Jehobah da ‘dukan zuciyarmu’ da kuma aminci. (1 Tarihi 28:9) Irin wannan bautar ba ta da waje wa rababbiyar zuciya ko kuma rayuwa iri biyu—tafarkin riya na nuna cewa ana bauta wa Jehobah sa’ad da ake yin zunubai masu tsanani a ɓoye. Aminci ya sa irin wannan riya ba za ta yiwu ba; ƙauna ta sa za mu guji irin wannan abin. Tsoron Allah zai taimaka mana. Littafi Mai Tsarki ya danganta wannan girmamawa da ci gaba da ƙulla abonkatanta na kud da kud da Jehobah.—Zabura 25:14.
Yin Koyi da Jehobah
18, 19. Me ya sa daidai ne mu yi tunanin cewa mutane ajizai ma za su iya yin koyi da Jehobah Allah?
18 Kowanne sashe na wannan littafin ya ƙare da babi ɗaya ko biyu game da yadda za mu zama “ ’ya’ya waɗanda Allah yake ƙauna.” (Afisawa 5:1) Yana da muhimmanci mu tuna cewa ko da yake mu ajizai ne, da gaske za mu iya yin koyi da kamiltacciyar hanyar yin amfani da iko, yin shari’a, da kuma aikatawa cikin hikima, da nuna ƙauna na Jehobah. Ta yaya muka sani cewa yana yiwuwa mu yi koyi da Mai Iko Duka? Ka tuna, ma’anar sunan Jehobah ya koya mana cewa shi yakan sa kansa ya kasance dukan abin da ake bukata domin ya cika nufinsa. Daidai ne wannan iyawar tana da ban tsoro, amma ya fi ƙarfinmu ne gabaki ɗaya? A’a.
19 An halicce mu cikin surar Allah. (Farawa 1:26) Saboda haka, mutane ba kamar kowacce halitta ba ce a duniya. Ba ilhami ba ne ko kuma abin da muka gada suke yi mana ja-gora, ko kuma yanayin inda muke da zama. Jehobah ya ba mu kyauta mai tamani—’yancin zaɓe. Duk da kasawarmu da kuma ajizancinmu, muna da ’yancin mu zaɓi abin da muke so mu zama. Ƙari ga haka, ka tuna cewa sunan Allah yana kuma nufin zai iya sa bayinsa su zama duk abin da yake so. Saboda haka, kana so ka zama mutum mai ƙauna, mai hikima, adali wanda yake amfani da iko daidai? Da taimakon Jehobah, za ka iya zama haka! Ka yi tunanin abin kirki da za ka cim ma.
20. Wane abin kirki za mu cim ma idan muka yi koyi da Jehobah?
20 Za ka faranta wa Ubanka na sama rai, ka sa zuciyarsa ta yi murna. (Karin Magana 27:11) Za ka iya ka “faranta masa rai” domin Jehobah ya fahimci kasawarka. (Kolosiyawa 1:9, 10) Sa’ad da ka ci gaba da koyon halaye masu kyau ta wajen koyi da Ubanka na sama, zai albarkace ka da gata mai girma. A cikin wannan duniya mai duhu da take a ware daga Allah, za ka zama mai ɗauke da haske. (Matiyu 5:1, 2, 14) Za ka taimaka wajen yaɗa mutuntaka mai daraja na Jehobah a duniya. Lallai daraja ce!
‘Ka Yi Kusa da Allah, Shi Kuwa Zai Yi Kusa da Kai’
Bari ka kusaci Jehobah kullayaumi
21, 22. Wace tafiya ce marar iyaka take gaban waɗanda suke ƙaunar Jehobah?
21 Wannan shawara mai sauƙi da take rubuce a Yakub 4:8, ta wuce maƙasudi kawai. Tafiya ce. Muddin mun kasance da aminci, wannan tafiyar ba za ta ƙare ba. Ba za mu daina matsowa kusa kusa da Jehobah ba. Bayan haka ma, da akwai abubuwa da yawa da za mu ci gaba da koya game da shi. Kada mu yi tunanin cewa wannan littafin ya koya mana dukan abin da muke bukatar mu sani game da Jehobah. Domin ba mu fara ba tukuna mu tattauna dukan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah! Kuma har Littafi Mai Tsarki kansa ba zai gaya mana dukan abin da za mu sani ba game da Jehobah. Manzo Yohanna ya yi tsammanin cewa idan an rubuta dukan abin da Yesu ya yi a lokacin hidimarsa ta duniya, “duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.” (Yohanna 21:25) Idan za a iya cewa haka game da Ɗan, to, ai Uban kuma ba magana!
22 Har rai madawwami ba zai kawo mu ƙarshen koyo game da Jehobah ba. (Mai-Wa’azi 3:11) To, ka yi tunani game da begen da take gabanmu. Bayan mun rayu na shekaru ɗarurruwa, dubbai, miliyoyi, har ma biliyoyi, za mu fahimci Jehobah Allah ƙwarai fiye da yadda muka yi a yanzu. Amma za mu yi tunanin da akwai abubuwa masu ban mamaki marasa iyaka da za mu koya. Za mu yi ɗokin mu samu ƙarin ilimi, domin koyaushe za mu kasance da dalilan ji kamar yadda mai Zabura ya ji, kamar yadda ya rera waƙa: “A gare ni, yana da kyau a yi kusa da Allah.” (Zabura 73:28) Rai madawwami zai kasance da ma’ana sosai—kusantar Jehobah kullum zai kasance ɓangarensa mai albarka.
23. Me aka ƙarfafa ka ka yi?
23 Ka yi na’am ga ƙaunar Jehobah yanzu. Ta wajen ƙaunarsa da dukan zuciyarka, rai, azancinka da kuma ƙarfinka. (Markus 12:29, 30) Ƙaunarka ta kasance mai aminci kuma kafaffiya. Bari kuma dukan shawara da kake yanke kowacce rana, daga ƙanƙani zuwa babba, duka su nuna cewa abin da yake ja-gorarsu ɗaya ne—kuma cewa ko da yaushe za ka zaɓi tafarkin da yake kai wa ga dangantaka mai ƙarfi da Ubanka na sama. Fiye da kome, ka kusaci Jehobah kullayaumi, shi kuma zai kusace ka—cikin dukan dawwama!