Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 11/1 pp. 4-8
  • Wa Zai Raba Mu Da Ƙaunar Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wa Zai Raba Mu Da Ƙaunar Allah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah
  • Canjin Yanayi Ba Ya Shafan Ƙaunar Allah
  • Ka Daraja Rahamar Allah Har Abada
  • Uban Yana Ƙaunarku
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Kada Ku Bar Ƙaunar da Kuke wa Juna ta yi Sanyi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 11/1 pp. 4-8

Wa Zai Raba Mu Da Ƙaunar Allah?

“Muna ƙauna, domin ya fara ƙaunace mu.”—1 YOHANNA 4:19.

1, 2. (a) Me ya sa sanin cewa ana ƙaunarmu yake da muhimmanci a gare mu? (b) Mun fi bukatar ƙaunar waye?

YANA da muhimmanci ne a gare ka, ka sani cewa ana ƙaunarka? Tun daga jariri zuwa lokacin da suka yi girma, ’yan Adam suna girma ne domin ƙauna. Ka lura da jariri da mamarsa ta riƙe shi cikin ƙauna a damtsenta? Sau da yawa, ko da menene yake faruwa a wurin, yayin da jaririn ya kalli fuskar mamar tana murmushi, sai ya sake, da kwanciyar rai a damtsen mamar wadda take ƙaunarsa. Ka tuna yadda kake lokacin waɗancan shekaru masu wuya na ƙuruciya? (1 Tassalunikawa 2:7) Wasu lokatai, ba za ka san abin da kake bukata ko yadda kake ji ba, amma yana da muhimmanci da ka san cewa babanka da mamarka suna ƙaunarka! Bai taimaka maka ba ka san cewa za ka iya gaya musu damuwarka ko ka yi musu tambaya? Hakika, cikin rayuwa, bukatarmu mafi girma ita ce a ƙaunace mu. Irin wannan ƙaunar tana tabbatar mana cewa muna da daraja.

2 Ƙaunar iyaye mai daɗewa babu shakka tana sa mutum ya yi girma da kyau kuma ya tsaya da ƙarfi. Amma, kasancewa da gaba gaɗi cewa Ubanmu na samaniya, Jehovah yana ƙaunarmu ya fi muhimmanci ga lafiyarmu ta ruhaniya da kuma jiye-jiye. Wasu masu karatun wannan jaridar mai yiwuwa ba su da iyaye da suka kula da su. Idan haka yake a gare ka, ka ƙarfafa. Ko idan babu ƙauna ta iyaye ko idan ta kasa, ƙauna ta gaske ta Allah ta cika wannan.

3. Yaya Jehovah ya sake tabbatar wa mutanensa cewa yana ƙaunarsu?

3 Ta wurin annabinsa Ishaya, Jehovah ya nuna cewa uwa za ta iya “manta” jaririnta mai shan nono, amma shi ba zai manta da mutanensa ba. (Ishaya 49:15) Hakanan ma, Dauda da gaba gaɗi ya ce: “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni.” (Zabura 27:10) Abar ƙarfafa ce! Ko menene yanayinka, idan kana cikin dangantaka ta keɓe kai da Jehovah Allah, ya kamata koyaushe ka tuna cewa ya fi ƙaunarka fiye da ƙaunar da kowanne ɗan taliki zai yi maka!

Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah

4. Ta yaya aka sake tabbatar wa Kiristoci na farko ƙaunar Allah?

4 Yaushe ka fara sani game da ƙaunar Jehovah? Mai yiwuwa, labarinka ɗaya ne da na Kiristoci a ƙarni na farko. Sura ta 5 ta wasiƙar Bulus zuwa ga Romawa ta kwatanta da kyau yadda masu zunubi, da a dā suke a ware daga Allah suka saba da ƙaunar Jehovah. A aya ta 5, mu karanta: “An baza ƙaunar Allah cikin zukatanmu ta wurin Ruhu Mai-tsarki wanda aka bayar a garemu.” A aya 8, Bulus ya daɗa: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da shi ke, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.”

5. Me ya taimake ka ka fahimci yawan ƙaunar Allah?

5 Hakanan ma, lokacin da aka nuna maka gaskiya daga Kalmar Allah kuma ka soma ba da gaskiya, ruhu mai tsarki na Jehovah ya soma aiki cikin zuciyarka. A wannan hanyar ka soma nuna godiya ga girmar aba da Jehovah ya yi wajen aiko ƙaunacaccen Ɗansa ya mutu dominka. Da haka Jehovah ya taimake ka ka san daidai zurfin yadda yake ƙaunar ’yan Adam. Yayin da ka fahimci wannan, ko da an haife ka mai zunubi a ware daga Allah, Jehovah ya buɗe hanya don a ce da mutane masu adalci da zaton rai na har abada, hakan bai taɓa zuciyarka ba? Ba ka ji kana ƙaunar Jehovah ba?—Romawa 5:10.

6. Me ya sa a wani lokaci za mu ji mun yi nisa da Jehovah?

6 Da yake ƙaunar Ubanka na samaniya ta jawo ka kuma ka gyara rayuwarka don ya amince da kai, sai ka keɓe rayuwarka ga Allah. Yanzu kana morar salama da Allah. Duk da haka, a wani lokaci kana jin ka yi nisa da Jehovah? Wannan zai iya faruwa da wani cikinmu. Amma ka tuna ko da yaushe, cewa Allah ba ya canjawa. Ƙaunarsa tana ci gaba kuma tana nan ko da yaushe kamar rana, wadda ba ta daina aikowa da tsirkiyar haske mai ɗumi zuwa duniya. (Malachi 3:6; Yaƙub 1:17) A wata sassa, za mu iya canjawa—ko ma na ɗan lokaci ne. Yayin da duniya take gewayewa, rabinta yana rufe cikin duhu. Hakanan ma, idan muka juya daga Allah, ko ɗan kaɗan ne, za mu ji sanyi a dangantakarmu da shi. Menene za mu yi don mu gyara wannan yanayi?

7. Ta yaya bincika kanmu zai taimake mu mu kasance cikin ƙaunar Allah?

7 Idan mun fahimci cewa ƙaunar Allah ta bar mu, ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Ina ɗaukar ƙaunar Allah da wasa ne? A hankali ina juyawa daga Allah mai rai mai ƙauna ne, ta nuna raunanar bangaskiya a hanyoyi dabam dabam? Na sa zuciya ta a kan “al’amuran jiki” ne, maimakon a kan “al’amuran ruhu”?’ (Romawa 8:5-8; Ibraniyawa 3:12) Idan mun raba kanmu da Jehovah, za mu ɗauki matakai mu daidaita al’amura, mu dawo ga dangantaka ta kud da kud, mai daɗaɗawa da shi. Yaƙub ya aririce mu: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.” (Yaƙub 4:8) Ka yi biyayya ga kalmomin Yahuda: “Ƙaunatattu, cikin gina kanku bisa bangaskiyarku maficin tsarki, kuna addu’a cikin Ruhu Mai-tsarki, ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah.”—Yahuda 20, 21.

Canjin Yanayi Ba Ya Shafan Ƙaunar Allah

8. Waɗanne canje-canje za su iya aukuwa farat ɗaya a rayuwarmu?

8 Rayuwarmu cikin wannan zamanin na canjawa sosai. Sarki Sulemanu ya lura cewa ‘sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannenmu.’ (Mai-Wa’azi 9:11) Farat ɗaya, rayuwarmu tana iya canjawa gabaki ɗaya. Yau muna da lafiya, washegari kuma muna ciwo mai tsanani. Yau kamar aikinmu ba za mu taɓa bari ba, washegari kuma an kore mu a aiki. Wanda muke ƙauna zai iya mutuwa farat ɗaya. Kiristoci a wata ƙasa za su iya morar yanayi na lumana na wasu lokatai, sa’an nan, farat ɗaya muguwar tsanantawa ta ɓarke. Wataƙila an yi mana zargin ƙarya, saboda haka, muna shan wahalar rashin gaskiya. Hakika, rayuwa ba ta tsaya wuri ɗaya ko kuma ba a dogara da ita gabaki ɗaya.—Yaƙub 4:13-15.

9. Me ya sa zai yi kyau a bincika Romawa sura 8?

9 Yayin da abubuwa na baƙin ciki su kan faru mana, za mu iya soma jin an yashe mu, muna tunani ma cewa ƙaunar Allah dominmu ta ragu. Tun da irin waɗannan abubuwa za su iya aukuwa ga dukanmu, zai yi kyau mu bincika a hankali kalmomin ta’aziyya na manzo Bulus da ke rubuce a Romawa sura 8. Shafaffu Kiristoci ne aka rubuta wa waɗannan kalmomi. Duk da haka, a ƙa’ida sun shafi waɗansu tumaki, waɗanda aka ce da su adilai abokanan Allah ne, yadda aka ce da Ibrahim kafin lokacin Kiristoci.—Romawa 4:20-22; Yaƙub 2:21-23.

10, 11. (a) Wane zargi magabta wasu lokatai suke wa mutanen Allah? (b) Me ya sa irin wannan zargi ba ya damun Kiristoci?

10 Karanta Romawa 8:31-34. Bulus ya yi tambaya: “Idan Allah ke wajenmu, wa ke gāba da mu?” Da gaske, Shaiɗan da muguwar duniyarsa suna gāba da mu. Magabta za su iya yi mana zargin ƙarya, har a kotu na ƙasa. An zargi wasu iyaye Kirista cewa sun tsani yaransu domin ba su yarda an yi musu jinya da ta karya dokar Allah ba kuma wai ba su bar su su sa hannu cikin bukukuwa na arna ba. (Ayukan Manzanni 15:28, 29; 2 Korinthiyawa 6:14-16) An yi wa wasu amintattun Kiristoci tuhumar ƙarya wai su masu ta da zaune tsaye ne domin ba za su kashe ’yan’uwansu talikai ba a yaƙi ko su sa hannu cikin siyasa. (Yohanna 17:16) Wasu ’yan hamayya sun baza zargin ƙaryar a hanyar wasa labarai, har ma suna zargin Shaidun Jehovah wai rukuni ne mai haɗari.

11 Amma kada ka manta cewa a zamanin manzanni, an ce: “Ga zancen wannan tarika, sananne ne a garemu ko’ina ana kushenta.” (Ayukan Manzanni 28:22) Zargin ƙarya ya fi muhimmanci ne? Allah ne ya ce da Kiristoci na gaskiya su adalai, domin bangaskiyarsu ga hadayar Kristi. Me ya sa Jehovah zai daina ƙaunar masu bauta masa bayan ya ba su kyauta mafi tamani—ƙaunacaccen Ɗansa? (1 Yohanna 4:10) Yanzu da an ta da Kristi daga matattu kuma an ajiye shi a hannun dama na Allah, yana roƙo koyaushe domin Kiristoci. Wa zai iya musun kāriyar Kristi a kan mabiyansa ko kuma ya yi nasarar tuhumar ɗaukaka da Allah ke yi wa amintattunsa? Babu kowa!—Ishaya 50:8, 9; Ibraniyawa 4:15, 16.

12, 13. (a) Wane yanayi ne ba zai iya raba mu da ƙaunar Allah ba? (b) Menene manufar Iblis a haddasa mana wahala? (c) Me ya sa Kiristoci gabaki ɗaya suke cin nasara?

12 Karanta Romawa 8:35-37. Ban da mu, akwai wanda ko wani abu da zai iya raba mu da ƙaunar Jehovah da Ɗansa Kristi Yesu? Shaiɗan zai iya amfani da wakilansa na duniya ya haddasa wa Kiristoci wahala da yawa. Cikin ƙarni da ya shige, an yi mugun tsananta wa ’yan’uwanmu Kiristoci maza da mata a ƙasashe da yawa. A wasu wurare a yau, ’yan’uwanmu kullum suna fuskantar wahalar tattalin arziki. Wasu suna fuskantar yunwa ko rashin isashen tufafi. Menene manufar Iblis a haddasa waɗannan yanayi masu wuya? Aƙalla, manufarsa ita ce ya sa a daina bautar gaskiya ta Jehovah. Shaiɗan yana son ya sa mu gaskata cewa ƙaunar Allah ta yi sanyi. Amma, haka ne?

13 Kamar Bulus, wadda ya ɗauko a Zabura 44:22, mun yi nazarin rubucacciyar Kalmar Allah. Mun fahimci cewa domin sunan Allah ne waɗannan abubuwa suke faruwa mana, ‘tumakinsa.’ Ya ƙunshi tsarkaka sunan Allah da kunita ikon mallakarsa na dukan halitta. Domin irin wannan batu na musamman ne Allah ya ƙyale gwaji, ba domin ba ya ƙaunarmu ba ne. Ko menene yanayi mai wuya zai zama, mun tabbata cewa ƙaunar Allah domin mutanensa, haɗe da kowannenmu, ba ta canja ba. Kowacce wahala da muke sha za ta zama nasara idan mun riƙe amincinmu. An ƙarfafa mu kuma an kiyaye mu ta tabbacin ƙaunar Allah da ba ta ƙarewa.

14. Me ya sa Bulus ya tabbata da ƙaunar Allah duk da wahala da Kiristoci za su iya sha?

14 Karanta Romawa 8:38, 39. Menene ya tabbatar wa Bulus cewa ba abin da zai iya raba Kiristoci da ƙaunar Allah? Babu shakka abin da Bulus ya fuskanta ne yayin da yake hidima ya ƙarfafa tabbacinsa cewa wahala ba za ta shafi ƙaunar Allah dominmu ba. (2 Korinthiyawa 11:23-27; Filibbiyawa 4:13) Bulus ya sani game da madawwamin ƙudurin Jehovah da sha’aninsa a dā da mutanensa. Mutuwa za ta iya kawar da ƙaunar Allah ce ga waɗanda suka bauta masa da aminci? Ko kaɗan! Irin waɗannan masu aminci da suka mutu sun kasance a tunanin Allah, kuma zai tashe su a lokacin da ya dace.—Luka 20:37, 38; 1 Korinthiyawa 15:22-26.

15, 16. Ka ambata wasu abubuwa da ba za su taɓa sa Allah ya daina ƙaunar bayinsa masu aminci ba.

15 Kowacce masifa rayuwa ta yau za ta kawo mana—ko haɗari da ke raunana mu, ciwon ajali, ko wahalar tattalin arziki—ba abin da zai halaka ƙaunar Allah domin mutanensa. Mala’iku masu iko, kamar mala’ika da ya yi rashin biyayya wanda ya zama Shaiɗan, ba zai iya rinjayar Jehovah ya daina ƙaunar bayinsa ba da suka ba da kansu. (Ayuba 2:3) Gwamnati za ta iya hana aikin bayin Allah, za su iya saka su a fursuna, kuma za su iya kushe su kuma a sa musu suna, “waɗanda ba a son su.” (1 Korinthiyawa 4:13) Irin wannan ƙiyayya da ba daidai ba daga al’ummai za ta iya motsa mutane su yi adawa da mu, amma ba zai sa Mamallakin sararin samaniya ya yasar da mu ba.

16 Kiristoci, ba ma bukatar tsoro cewa abin da Bulus ya kira “al’amuran yanzu”—aukuwan, da yanayi na wannan zamani—ko “al’amura na zuwa” a nan gaba za su iya raba gamin Allah da mutanensa. Ko da iko na duniya da ta sama suna yaƙi da mu, ƙauna ta gaske ta Allah za ta kiyaye mu. Ba “tsawo, ba zurfi” da za su iya hana ƙaunar Allah, yadda Bulus ya nanata. Hakika, babu abin da zai iya sa mu yi sanyin gwiwa, kowanne abu da zai yi iko a kan mu, ba zai iya raba mu da ƙaunar Allah ba; ko kuwa wata halitta ta yanke dangantakar Mahalicci da bayinsa masu aminci. Ƙaunar Allah ba ta ƙarewa daɗai; tana nan har abada.—1 Korinthiyawa 13:8.

Ka Daraja Rahamar Allah Har Abada

17. (a) Me ya sa samun ƙaunar Allah “ta fi gaban rai”? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja rahamar Allah?

17 Yaya ƙaunar Allah take da muhimmanci a gareka? Kana jin yadda Dauda ya ji, wanda ya rubuta: “Gama rahamarka ta fi gaban rai; leɓunana za su yi yabonka. Hakanan zan albarkace ka muddar raina: zan tada hannuwana cikin sunanka.” (Zabura 63:3, 4) Hakika, akwai wani abu ne da rayuwa a wannan duniya za ta bayar da ta fi morar ƙaunar Allah da abuta ta gaske? Alal misali, biɗan sana’a mai kyau ya fi kasancewa da kwanciyar rai da farin ciki da ke zuwa daga dangantaka ta kud da kud da Allah ne? (Luka 12:15) Wasu Kiristoci sun fuskanci zaɓen su ƙi Jehovah ko kuma su mutu. Wannan ya faru da Shaidun Jehovah da yawa a sansanin Nazi a lokacin Yaƙin Duniya na ll. Ban da wasu kalilan, ’yan’uwanmu Kirista sun zaɓi su kasance cikin ƙaunar Allah, suna shirye su fuskanci mutuwa in ya zama haka. Waɗanda suka kasance cikin ƙaunarsa za su iya kasancewa da tabbacin samun madawwamin rai daga Allah, abin da duniya ba za ta ba mu ba. (Markus 8:34-36) Amma ya ƙunshi fiye da rai madawwami.

18. Me ya sa rai madawwami ke da ban sha’awa?

18 Ko da ba za ta yiwu ba a rayu har abada ban da Jehovah, ka yi ƙoƙari ka ƙaga abin da rayuwa ta dogon lokaci za ta zama ba tare da Mahaliccinmu ba. Zai zama wofi, babu ma’ana ta gaske. Jehovah ya ba mutanensa aiki mai gamsarwa da za su yi a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Saboda haka, za mu iya gaskata cewa lokacin da Jehovah, Babban Mai Ƙuduri, zai yi tanadin rai madawwami, zai cika da ban marmari, abubuwa masu kyau da za mu koya kuma mu yi. (Mai-Wa’azi 3:11) Ko da yaya yawan abin da za mu koya a shekara dubu nan gaba yake, ba za mu taɓa bincika gabaki ɗaya, “zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa” ba.—Romawa 11:33.

Uban Yana Ƙaunarku

19. Wane tabbaci ne na rabuwa Yesu Kristi ya ba wa almajiransa?

19 A rana ta 14 ga Nisan, 33 A.Z., a lokacin dina na maraice na ƙarshe da manzanninsa 11 masu aminci, Yesu ya faɗi abubuwa da yawa don ya ƙarfafa su ga abin da yake gaba. Sun lizimci Yesu cikin jarabarsa, kuma sun ga ƙaunarsa dominsu. (Luka 22:28, 30; Yohanna 1:16; 13:1) Sa’an nan Yesu ya sake tabbatar musu: “Uba da kansa yana ƙaunarku.” (Yohanna 16:27) Lallai waɗannan kalmomi sun taimaki almajiran su fahimci juyayin da Ubansu na samaniya yake da shi dominsu!

20. Menene kake niyyar yi, kuma menene za ka tabbata?

20 Mutane da yawa da suke rayuwa yanzu sun bauta wa Jehovah cikin aminci na shekaru da yawa. Babu shakka, kafin ƙarshen wannan mugun zamani, za mu fuskanci ƙarin gwaji da yawa. Kada ka bar irin wannan gwaji ko wahala su sa ka shakkar ƙauna ta gaske ta Allah dominka. Zai yi wuya a nanata wannan gaskiyar: Jehovah yana ƙaunarku. (Yaƙub 5:11) Bari kowannenmu ya ci gaba da iyakar ƙoƙarinsa, cikin aminci muna kiyaye umurnan Allah. (Yohanna 15:8-10) Bari mu yi amfani da kowanne zarafi mu yabi sunansa. Ya kamata mu ƙarfafa aniyarmu na ci gaba da matsawa kusa da Jehovah cikin addu’a da yin nazarin Kalmarsa. Ko menene gobe zai kawo, idan muna iyakacin ƙoƙarinmu mu faranta wa Jehovah rai, za mu kasance da salama, mu tabbata game da ƙaunarsa da ba ta ƙarewa.—2 Bitrus 3:14.

Yaya Za Ka Amsa?

• Don mu daidaita a ruhaniya da jiye-jiye, ƙaunar waye musamman muke bukata?

• Waɗanne abubuwa ne ba za su taɓa sa Jehovah ya daina ƙaunar bayinsa ba?

• Me ya sa samun ƙaunar Jehovah “ta fi gaban rai”?

[Hotuna a shafi na 5]

Idan muna jin muna ware daga ƙaunar Allah, za mu yi aiki don mu daidaita al’amura

[Hoto a shafi na 7]

Bulus ya fahimci abin da ya sa ake tsananta masa

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba