Litinin, 27 ga Oktoba
Maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikinsu.—Afis. 5:28.
Jehobah yana so maigida ya ƙaunaci matarsa, ya biya bukatunta, ya zama abokinta kuma ya taimaka mata ta bauta masa da kyau. Zama mai hankali, da daraja mata, da zama wanda za a iya yarda da shi, za su taimaka maka ka zama miji nagari. Bayan ka yi aure, za ku iya haifan yara. Wane darasi ne za ka iya koya daga wurin Jehobah game da zama uba nagari? (Afis. 6:4) Jehobah ya gaya wa ɗansa Yesu a gaban jamaꞌa cewa yana ƙaunar sa kuma ya amince da shi. (Mat. 3:17) Idan kana da yara, ka riƙa tabbatar musu da cewa kana ƙaunar su. Ka riƙa yaba musu don abubuwa masu kyau da suke yi. Ubanni da suke yin koyi da Jehobah suna taimaka wa yaransu su zama Kiristocin da suka manyanta. Za ka iya yin shirin zama uba nagari ta wajen kula da ꞌyan iyalinku da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ka riƙa gaya musu cewa kana ƙaunar su kuma suna da muhimmanci a gare ka.—Yoh. 15:9. w23.12 28-29 sakin layi na 17-18
Talata, 28 ga Oktoba
[Jehobah] ne tushe a zamaninmu.—Isha. 33:6.
Ko da yake mu bayin Jehobah ne, mu ma muna fuskantar matsaloli kuma muna rashin lafiya kamar yadda sauran mutane suke yi. Ƙari ga haka, muna iya fuskantar hamayya ko kuma tsanantawa daga mutanen da ba sa son ganin mu. Jehobah ba ya hana abubuwan nan faruwa da mu, amma ya yi alkawarin cewa zai taimaka mana. (Isha. 41:10) Da taimakon Jehobah, ko da mun shiga yanayi mai wuya sosai, za mu iya yin farin ciki, mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu riƙe amincinmu. Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba mu “salama.” (Filib. 4:6, 7) Wannan salamar tana nufin kwanciyar hankali da kuma natsuwa da muke samu don muna da dangantaka mai kyau da Allah. Wannan salamar ta “wuce dukan ganewar ɗan Adam,” wato tana taimaka mana a hanya mai ban mamaki. Ka taɓa yin adduꞌa ga Jehobah kuma ka ji hankalinka ya kwanta? Mai yiwuwa abin ya ba ka mamaki. ‘Salamar’ da Jehobah ya ba ka ne ya sa ka ji hakan. w24.01 20 sakin layi na 2; 21 sakin layi na 4
Laraba, 29 ga Oktoba
Yabi Yahweh, ya raina! Dukan abin da ke a cikina, yabi Sunansa mai tsarki!—Zab. 103:1.
Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna so su yabi sunansa da dukan zuciyarsu. Sarki Dauda ya fahimci cewa yabon sunan Jehobah ɗaya yake da yabon Jehobah. Idan muka ji sunan Jehobah, mukan yi tunanin halayensa masu kyau da kuma abubuwan ban mamaki da ya yi. Dauda ya ɗauki sunan Ubansa na sama da tsarki kuma ya yabi sunan. Ya ce zai yi hakan da ‘dukan abin da ke a cikinsa,’ wato da dukan zuciyarsa. Lawiyawa ma sun ja-goranci mutane wajen yabon sunan Jehobah. Sun ce kalmomin bakinsu ba su isa su yabi Jehobah yadda ya dace ba. (Neh. 9:5) Babu shakka, yadda suka yabi Jehobah da dukan zuciyarsu kuma suka yi hakan da sauƙin kai, ya sa Jehobah farin ciki. w24.02 9 sakin layi na 6