Ta Hannun Luka
2 A kwanakin nan, Kaisar Augustus ya ba da umurni a yi rajistar mutanen da ke dukan duniya. 2 (Wannan ne lokaci na farko da aka yi rajistar, kuma a lokacin, Kiriniyus ne gwamnan Siriya.) 3 Sai dukan mutane suka koma garuruwansu, domin a yi musu rajista. 4 Yusufu ma ya bar garin Nazaret da ke Galili, ya je garin Dauda, wato Baitalami da ke Yahudiya. Tun da shi daga zuriyar Dauda ne. 5 Ya tafi da Maryamu wadda ta riga ta zama matarsa kamar yadda aka yi masa alkawari, domin a yi musu rajista tare. A lokacin ta kusan haifuwa. 6 Saꞌad da suke wurin, sai lokaci ya kai da za ta haifu. 7 Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zane, kuma ta kwantar da shi a wurin da ake saka wa dabbobi abinci, domin ba su samu ɗaki a wurin da baƙi suke sauka ba.
8 A wannan yankin kuma, akwai makiyaya da ke kwana a waje suna kula da dabbobinsu da dare. 9 Nan da nan, sai malaꞌikan Jehobah* ya tsaya a gabansu, kuma ɗaukakar Jehobah* ta haskaka su, sai suka ji tsoro sosai. 10 Amma malaꞌikan ya ce musu: “Kada ku ji tsoro, domin ina yi muku shelar labari mai daɗi da zai sa dukan mutane farin ciki sosai. 11 A yau, an haifa muku mai ceto a birnin Dauda, wanda shi ne Kristi Ubangiji. 12 Ga alamar da za ku gani: Za ku ga jariri da aka rufe da zane kwance a inda ake saka wa dabbobi abinci.” 13 Nan da nan, sai ga malaꞌiku da yawa, sun bayyana tare da malaꞌika na farkon, suna yabon Allah, suna cewa: 14 “Ɗaukaka ga Allah, a can cikin sammai, a duniya kuma bari salama ta kasance da waɗanda Allah yake farin ciki da su.”*
15 Saꞌad da malaꞌikun suka koma sama, sai makiyayan suka soma ce wa juna: “Mu yi iya ƙoƙarinmu mu je Baitalami don mu ga abin da ya faru da Jehobah* ya bayyana mana.” 16 Sai nan da nan suka tafi, kuma suka sami Maryamu, da Yusufu, da kuma jaririn yana kwance a wurin da ake saka wa dabbobi abinci. 17 Da suka ga hakan, sai suka gaya wa mutane abin da aka gaya musu game da yaron. 18 Kuma dukan mutanen da suka ji abin da makiyayan suka gaya musu, sun yi mamaki sosai. 19 Maryamu kuwa ta riƙe duk abubuwan nan da aka faɗa a zuciyarta, tana tunanin abin da suke nufi. 20 Sai makiyayan suka koma, suna ɗaukaka Allah, da kuma yabon sa, domin sun ji kuma sun ga abubuwa daidai yadda aka gaya musu.
21 Da ya kai kwana takwas, kuma lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, wato sunan da malaꞌikan ya bayar kafin a ɗauki cikin sa.
22 Ƙari ga haka, saꞌad da lokaci ya yi da za a tsarkake su bisa ga Dokar Musa, sai aka kawo shi Urushalima domin a miƙa shi ga Jehobah,* 23 kamar yadda aka rubuta a cikin Dokar Jehobah* cewa: “Dole ne a kira duk wani ɗan fari mai tsarki na Jehobah.”* 24 Sai suka miƙa hadaya bisa ga abin da aka ce a cikin Dokar Jehobah,* wato: “Kurciyoyi biyu ko kuma ƙananan tattabaru biyu.”
25 Akwai wani mutum a Urushalima mai suna Simeyon, shi mutum mai adalci ne da ke bauta wa Allah da dukan zuciyarsa, yana jiran lokacin da Allah zai ceci Israꞌila, kuma ruhu mai tsarki yana tare da shi. 26 Ƙari ga haka, Allah ya bayyana masa ta wurin ruhu mai tsarki cewa ba zai mutu ba har sai ya ga Kristi da Jehobah* ya aiko. 27 Sai ruhu mai tsarki ya sa Simeyon ya shigo cikin haikali, kuma yayin da iyayen Yesu suke kawo shi domin su yi masa abin da Doka* ta ce a yi, 28 sai ya ɗauki yaron a hannu kuma ya yabi Allah yana cewa: 29 “Ya Ubangiji Maɗaukaki, yanzu za ka bar bawanka ya mutu cikin kwanciyar hankali kamar yadda ka faɗa, 30 domin yanzu na ga wanda za ka yi amfani da shi ka ceci mutane, 31 wanda ka aiko don dukan mutane su gan shi, 32 haske ne da zai cire abin da ya rufe idanun alꞌummai kuma zai kawo ɗaukaka ga mutanenka Israꞌila.” 33 Baban yaron da kuma mamarsa sun ci-gaba da yin mamakin abubuwan da ake faɗa game da yaron. 34 Ƙari ga haka, Simeyon ya albarkace su kuma ya ce wa Maryamu mamar yaron: “Ga shi, an zaɓi wannan yaron domin ya zama dalilin faɗuwar waɗansu, da sake tashiwar mutane da yawa a Israꞌila, zai zama abin da mutane za su rena, 35 domin ta haka, asirin zukatan mutane da yawa zai tonu. (Ke kuma za ki yi baƙin ciki kamar wadda aka soke ta da dogon takobi.”)
36 Akwai wata annabiya mai suna Anna, ꞌyar Fanuwel, daga zuriyar Asher. Wannan matar tsohuwa ce, kuma ta yi shekara bakwai ne kawai da mijinta bayan da suka yi aure, 37 sai mijinta ya mutu, yanzu shekarunta tamanin da huɗu. Tana zuwa haikali babu fasawa, kuma tana yi wa Allah hidima mai tsarki dare da rana, tana azumi da yin adduꞌa da dukan zuciyarta. 38 A daidai wannan lokacin, sai ta zo kusa kuma ta soma gode wa Allah, da yin magana game da yaron ga duk waɗanda suke jiran lokacin da Allah zai ceci Urushalima.
39 Bayan da Yusufu da Maryamu suka yi dukan abubuwa da aka faɗa a Dokar Jehobah,* sai suka koma garinsu Nazaret da ke Galili. 40 Sai yaron ya ci-gaba da girma da yin ƙarfi, cike da hikima, kuma Allah ya amince da shi.
41 Iyayensa sun saba zuwa Urushalima don Bikin Ƙetarewa a kowace shekara. 42 Saꞌad da Yesu ya cika shekara goma sha biyu, sun je Urushalima a lokacin bikin kamar yadda suka saba. 43 Saꞌad da aka gama bikin kuma suna dawowa, Yesu wanda yaro ne, ya tsaya a Urushalima kuma iyayensa ba su sani ba. 44 Iyayensa sun yi tsammanin cewa yana cikin jamaꞌar da suke tafiya tare. Bayan da sun yi tafiyar yini guda, sai suka soma neman sa a tsakanin dangi da kuma abokai. 45 Amma da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima, domin su neme shi da kyau. 46 Bayan kwana uku, sai suka gan shi a haikali, yana zaune a tsakanin malamai, yana saurararsu kuma yana yi musu tambayoyi. 47 Amma dukan waɗanda suke saurarar sa suka yi ta mamaki game da yadda yake fahimtar abubuwa da kuma amsoshin da yake bayarwa. 48 Saꞌad da iyayensa suka gan shi, sun yi mamaki, kuma mamarsa ta ce masa: “Ɗana, me ya sa ka yi mana haka? Ga shi ni da babanka mun damu kuma muna ta neman ka a koꞌina.” 49 Sai ya ce musu: “Me ya sa kuke nema na? Ba ku san cewa ya kamata in kasance a gidan Ubana ba?” 50 Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba.
51 Sai ya bi su, suka tafi Nazaret tare, kuma ya ci-gaba da yi musu biyayya. Ƙari ga haka, mamarsa ta ci-gaba da riƙe abubuwan nan, tana tunani a kan su a zuciyarta. 52 Kuma Yesu ya ci-gaba da samun ƙarin hikima, da yin girma. Yana kuma samun farin jini a gaban Allah da kuma mutane.