Ayyukan Manzanni
12 A lokacin, sai Sarki Hirudus* ya soma tsananta ma wasu ꞌyan ikilisiyar. 2 Ya kashe Yaƙub ɗanꞌuwan Yohanna da takobi. 3 Da ya ga cewa Yahudawa sun ji daɗin hakan, sai ya kama Bitrus ma. (Hakan ya faru ne a lokacin da ake Bikin Burodi Marar Yisti.) 4 Da Hirudus ya kama Bitrus, ya sa shi a kurkuku a hannun sojoji goma sha shida, kuma sojoji huɗu bayan huɗu ne suke gadin sa a kowane lokaci. Ya yi niyyar fito da shi* a gaban jamaꞌa bayan Bikin Ƙetarewa. 5 Saꞌad da Bitrus yake kurkuku, ikilisiyar ta yi ta yin adduꞌa sosai ga Allah a madadinsa.
6 A daren da Hirudus yake tunanin zai fitar da Bitrus idan gari ya waye, Bitrus yana ɗaure da sarƙoƙi biyu, yana barci tsakanin sojoji biyu, masu gadin kurkukun kuma suna bakin ƙofa suna gadi. 7 Amma sai ga wani malaꞌikan Jehobah* yana tsaye a wurin, kuma wani haske ya haskaka ɗakin kurkukun. Sai ya taɓa Bitrus a gefe ya ta da shi, yana cewa: “Ka tashi da wuri!” Sai sarƙoƙin suka faɗi daga hannayensa. 8 Sai malaꞌikan ya ce masa: “Ka saka rigarka, da kuma takalmanka.” Sai ya yi hakan. A ƙarshe malaꞌikan ya ce masa: “Ka saka mayafinka, kuma ka ci-gaba da bi na.” 9 Sai ya fita, ya ci-gaba da bin malaꞌikan, amma bai san cewa abin da malaꞌikan yake yi yana faruwa da gaske ba. Ya ɗauka cewa yana ganin wahayi ne. 10 Da suka wuce masu gadi na farko da na biyu, kuma suka kai ƙofar ƙarfe wadda ake bi a fita daga kurkukun a shiga birni, sai ƙofar ta buɗe musu da kanta. Da suka fita, sai suka gangara a wani titi kuma nan da nan malaꞌikan ya rabu da shi. 11 Da Bitrus ya gane abin da yake faruwa, sai ya ce: “Yanzu ina da tabbaci cewa Jehobah* ya aiko malaꞌikansa, kuma ya cece ni daga hannun Hirudus da dukan abubuwan da Yahudawa suke sa ran zai faru.”
12 Bayan da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu, mamar Yohanna wanda ake kiran sa Markus, wurin da almajirai da yawa suka taru suna adduꞌa. 13 Saꞌad da ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan, sai wata baiwa mai suna Roda ta zo ta duba ko wane ne. 14 Da ta gane muryar Bitrus, ta yi farin ciki sosai, har ba ta buɗe masa ƙofar ba. Sai ta gudu ta shiga ciki, kuma ta gaya musu cewa Bitrus yana tsaye a bakin ƙofa. 15 Sai suka ce mata: “Ba kya cikin hankalinki.” Amma ta yi ta nace cewa Bitrus ne. Sai suka soma cewa: “Malaꞌikansa ne.” 16 Amma Bitrus ya tsaya a wurin, yana ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe masa ƙofa, kuma suka gan shi, sai suka yi mamaki sosai. 17 Amma ya yi musu alama da hannunsa cewa su yi shuru kuma ya bayyana musu dalla-dalla yadda Jehobah* ya fitar da shi daga kurkukun, sai ya ce musu: “Ku gaya wa Yaƙub da sauran ꞌyanꞌuwan abubuwan nan.” Sai ya fita ya tafi wani wuri.
18 Da gari ya waye, sai sojojin suka rikice don ba su san abin da ya faru da Bitrus ba. 19 Da Hirudus ya neme shi a koꞌina bai same shi ba, sai ya yi wa masu gadin tambayoyi kuma ya ba da umurni cewa a hukunta su. Sai Hirudus ya bar Yahudiya ya tafi Kaisariya, kuma ya kasance a wurin na ɗan lokaci.
20 Ana nan, Hirudus yana haushi* da mutanen Taya da Sidon. Sai suka zo wurinsa da nufi ɗaya, kuma bayan da suka sami goyon bayan Balastus, wanda shi ne yake kula da harkokin gidan sarki, sai suka nemi sulhu, domin daga ƙasar sarkin ne ƙasarsu take samun abinci. 21 A ranar da aka shirya, Hirudus ya saka rigar sarki kuma ya zauna a kujerar shariꞌa ya soma jawabi a gaban jamaꞌa. 22 Sai mutanen da suka taru suka soma ihu suna cewa: “Wannan muryar allah ne, ba na mutum ba!” 23 Nan take sai wani malaꞌikan Jehobah* ya buga shi domin bai miƙa ɗaukakar ga Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cin jikinsa har ya mutu.
24 Amma maganar Jehobah* ta ci-gaba da ƙaruwa da kuma yaɗuwa.
25 Bayan da Barnabas da Shawulu suka gama aikin ba da agaji a Urushalima, sai suka dawo kuma suka ɗauki Yohanna, wanda ake kuma kira Markus.