Zuwa ga Romawa
11 Ina tambaya, Shin Allah ya yi watsi da mutanensa ne? Ko kaɗan! Domin ni ma mutumin Israꞌila ne, daga zuriyar Ibrahim, kuma daga kabilar Benjamin. 2 Allah bai yi watsi da mutanensa da ya zaɓa tun daga farko ba. Ba ku san abin da nassi ya faɗa game da Iliya yayin da yake yin kuka ga Allah a kan Israꞌila ba? 3 Iliya ya ce: “Jehobah,* sun kakkashe annabawanka, sun rurrusa bagadanka, ni kaɗai ne na rage, kuma yanzu suna neman su kashe ni.” 4 Duk da haka, mene ne Allah ya gaya masa? Allah ya ce masa: “Ina da maza dubu bakwai da har yanzu ba su durƙusa don su bauta wa Baꞌal ba.” 5 Haka ma a zamaninmu, akwai raguwar mutane waɗanda Allah ya zaɓa saboda alherinsa. 6 Tun da saboda alherinsa ne Allah ya zaɓe su, hakan yana nufin cewa yanzu ba ayyuka ne suke sa Allah ya zaɓe mutum ba; idan ba haka ba, alherin ba zai zama alheri kuma ba.
7 To, me za mu ce? Israꞌilawa sun kasa samun abin da suke nema, amma waɗanda Allah ya zaɓa sun same shi. Sauran kuma sun yi taurin kai, 8 kamar yadda yake a rubuce: “Allah ya ba su ruhun barci mai zurfi,* da idanun da ba sa gani, da kuma kunnuwan da ba sa ji, har wa yau.” 9 Ƙari ga haka, Dauda ya ce: “Bari teburinsu ya zama abin da ke da haɗari da kuma tarko da abin sa tuntuɓe da kuma hukunci a gare su. 10 Bari idanunsu su yi duhu don kada su iya gani, kuma ka sa su ci-gaba da lanƙwashe bayansu don wahala.”
11 Don haka ina da tambaya, Da Israꞌilawa suka yi tuntuɓe, shin sun faɗi har sun kasa tashiwa ne? Aꞌa, ko kaɗan! Saboda zunubansu, Allah ya ceci mutanen alꞌummai don ya sa su kishi. 12 Idan zunubinsu ya kawo wa duniya albarka, kuma saꞌad da suka ragu hakan ya kawo albarka da yawa ga mutanen alꞌummai, hakika za a samu albarka sosai idan adadinsu ya cika.
13 Yanzu ina magana da ku mutanen alꞌummai. Da yake ni manzo ne ga alꞌummai, ina ɗaukaka hidimata 14 don in ga ko akwai yadda zan iya sa mutanena kishi kuma in ceci wasu daga cikinsu. 15 Idan yashe su da aka yi ya sa mutanen duniya sun yi sulhu da Allah, to me zai faru idan Allah ya amince da su? Ai, zai zama kamar an ta da su daga mutuwa. 16 Ƙari ga haka, idan wani ɓangaren burodi da aka miƙa a matsayin nunan fari yana da tsarki, sauran burodin ma yana da tsarki; idan jijiyar tana da tsarki, rassan ma suna da tsarki ke nan.
17 Amma idan aka sassare wasu daga cikin rassan, kuma aka ɗauke ku duk da cewa ku rassan itacen zaitun na daji ne, aka yi muku aure da rassan itacen zaitun na lambu, kuma kuka soma samun albarku da ke jijiyar itacen zaitun na lambun, 18 kada ku yi taƙama cewa kun fi rassan da aka sassare. Idan kuma kuna taƙama cewa kun fi su, ku tuna cewa, ba jijiyar ce take dogara gare ku ba, amma ku ne kuke dogara ga jijiyar. 19 Za ku ce: “Allah ya sassare wasu rassa domin a yi mana aure.” 20 Hakan gaskiya ne! An sassare su domin ba su da bangaskiya. Amma ku kuna tsaye saboda bangaskiyarku ne. Kada ku yi girman kai, a maimakon haka, ku ji tsoro. 21 Domin idan Allah bai bar ainihin rassan ba, ku ma ba zai bar ku ba. 22 Don haka, ku lura cewa Allah yana yin alheri kuma yana yin horo, ya yi horo ga waɗanda suka faɗi, amma ku, zai ci-gaba da yi muku alheri muddin kun ci-gaba da zama cikin alherinsa; in ba haka ba, ku ma za a sare ku. 23 Kuma su ma, idan ba su ci-gaba da rashin bangaskiyarsu ba, za a yi musu aure da itacen, don Allah zai iya sake yi musu aure da itacen. 24 Gama idan an sassare ku daga itacen zaitun na daji kuma aka yi muku aure da itacen zaitun na lambu, ko da yake bai kamata a yi hakan ba, zai ma fi sauƙi a sake dawo da rassan nan da aka sare a sake yi musu aure da itacen zaitun nasu!
25 Saboda haka ꞌyanꞌuwana, ina so ku san wannan asiri mai tsarki, don kada ku ɗauka cewa kuna da wayo: Wasu daga cikin Israꞌilawa sun yi taurin kai har sai dukan waɗanda aka zaɓa daga cikin alꞌummai sun shigo, 26 ta haka za a ceci dukan Israꞌila. Kamar yadda aka rubuta cewa: “Mai ceto zai fito daga Sihiyona kuma zai kawar da halaye marasa kyau daga Yakubu. 27 Kuma wannan ita ce yarjejeniyata da su, saꞌad da na kawar da zunubansu.” 28 A gaskiya, suna gāba da labari mai daɗi don amfaninku; amma Allah ya zaɓe su kuma yana ƙaunar su, domin kakanninsu. 29 Allah ba zai yi da-na-sani don kyautar da ya bayar, ko don kiran waɗanda ya kira ba. 30 Kamar yadda kuke rashin biyayya ga Allah a dā, amma Allah ya nuna muku jinƙai saboda rashin biyayyar Yahudawa, 31 haka ma, rashin biyayyar Yahudawa ya sa an nuna muku jinƙai, domin su ma a nuna musu jinƙai. 32 Gama Allah ya bar dukan mutane su zama bayi ga rashin biyayya, don ya iya nuna wa dukan mutane jinƙai.
33 Albarkun Allah, da hikimarsa, da kuma iliminsa ba su da iyaka. Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincike, hanyoyinsa sun wuce gaban ganewa. 34 Gama “wane ne ya san tunanin Jehobah?* Kuma wa ya zama mai ba shi shawara?” 35 Ko kuma, “wa ya taɓa ba shi wani abu, har da zai biya mutumin?” 36 Gama daga gare shi, da ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada. Amin.