Ta Hannun Luka
10 Bayan waɗannan abubuwan, Ubangiji ya zaɓi almajirai sabaꞌin* daga cikin almajiransa kuma ya aike su bibbiyu zuwa kowane gari da wurin da shi kansa zai je daga baya. 2 Sai ya ce musu: “Hakika, girbin yana da yawa, amma maꞌaikatan kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Mai Gonar ya aiko da maꞌaikata su yi masa girbi. 3 Ku je! Ga shi kuwa, ina aikan ku kamar tumaki a tsakanin ƙyarketai.* 4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jakar abinci, ko kuma takalma, kuma kada ku gai da kowa* a kan hanya. 5 A duk inda kuka shiga gida, ku fara da cewa: ‘Salama a gare ku.’ 6 Idan akwai abokin salama a gidan, bari salamarku ta kasance tare da shi. Amma idan babu, bari salamarku ta komo kanku. 7 Ku zauna a gidan da aka karɓe ku, kuna ci da shan abubuwan da aka ba ku, domin maꞌaikaci ya cancanci ya sami hakkinsa. Kada ku bar gidan ku je kuna neman wani gida.
8 “Ƙari ga haka, a duk garin da kuka shiga kuma suka karɓe ku, ku ci duk abin da aka ba ku. 9 Ku warkar da marasa lafiya da ke garin, kuma ku gaya musu cewa: ‘Mulkin Allah ya zo kusa da ku.’ 10 Amma duk garin da kuka shiga kuma ba su karɓe ku ba, ku bi manyan titunan garin kuma ku ce: 11 ‘Mun kakkaɓe muku har ƙurar garinku da ta manne a ƙafafunmu. Duk da haka dai, ku san cewa Mulkin Allah ya zo kusa.’ 12 Ina gaya muku, a ranar zai yi wa Sodom sauƙi ta jimre fiye da garin.
13 “Kaiton ki, Korazin! Kaiton ki, Betsaida! domin da a ce ayyukan ban mamaki da aka yi a cikinku ne aka yi a Taya da Sidon, da sun tuba da daɗewa sun sa tsumma a jikinsu kuma sun zauna a cikin toka. 14 Don haka, a lokacin shariꞌa zai yi wa Taya da Sidon sauƙi su jimre fiye da ku. 15 Ke kuma, Kafarnahum, kina tsammani za a ɗaukaka ki zuwa sama ne? A ina! Ƙasƙantar da ke za a yi zuwa Kabari!*
16 “Duk wanda ya saurare ku, ya saurare ni ma. Kuma duk wanda ya rena ku, ya rena ni ma. Ƙari ga haka, duk wanda ya rena ni, ya rena Wanda ya aiko ni.”
17 Sai almajiransa sabaꞌin suka dawo, suna murna, suka ce masa: “Ubangiji, har aljanu ma sun yi mana biyayya don mun yi amfani da sunanka.” 18 Da jin haka, sai ya ce musu: “Na ga Shaiɗan ya riga ya faɗo daga sama kamar walƙiya. 19 Ga shi! Na ba ku ikon tattaka macizai da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokan gāba, kuma babu abin da zai same ku. 20 Duk da haka, kada ku yi murna don aljanu sun yi muku biyayya, amma ku yi murna don an rubuta sunayenku a sama.” 21 A wannan lokacin, ruhu mai tsarki ya sa Yesu farin ciki sosai kuma ya ce: “Ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, ina yabon ka a gaban kowa, saboda ka ɓoye waɗannan abubuwa da kyau ga masu hikima da ilimi, ka kuma bayyana wa ƙananan yara. Hakika, Ya Uba, wannan ne abin da kake so. 22 Ubana ya ba ni dukan abu, kuma ba wanda ya san Ɗan sai Uban, ba wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma duk wanda Ɗan yake so ya bayyana masa Uban.”
23 Ya juya ya kalli almajiransa kuma ya gaya musu su kaɗai cewa: “Masu farin ciki ne waɗanda suke ganin abubuwan da kuke gani. 24 Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abubuwan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abubuwan da kuke ji, amma ba su ji ba.”
25 Sai wani mutum da ya san Doka* sosai ya tashi don ya gwada shi, kuma ya ce: “Malam, mene ne nake bukatar in yi don in gāji rai na har abada?” 26 Sai Yesu ya ce masa: “Mene ne Doka ta ce? Kuma mene ne ka fahimta daga abin da ka karanta?” 27 Sai mutumin ya amsa masa ya ce: “‘Dole ka ƙaunaci Jehobah* Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan tunaninka’ kuma ‘ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’” 28 Sai Yesu ya ce masa: “Ka amsa daidai; ka ci-gaba da yin hakan kuma za ka sami rai.”
29 Da yake yana so ya nuna shi mai adalci ne, sai mutumin ya ce wa Yesu: “Wane ne maƙwabcina?” 30 Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Akwai wani mutum da ya fito daga Urushalima, yana gangarawa zuwa Jeriko, sai ꞌyan fashi suka tare shi, suka tuɓe masa riga kuma suka ƙwace kayansa, sun yi masa dūka, kuma suka tafi suka bar shi a bakin mutuwa. 31 Ana nan, sai ga wani firist yana gangarowa a kan hanyar, saꞌad da ya gan mutumin, sai ya kauce ya bi ɗayan gefen. 32 Haka ma, saꞌad da wani mutum daga zuriyar Lawi ya iso wurin da mutumin yake kuma ya gan shi, sai ya bi ta ɗayan gefen hanyar. 33 Amma saꞌad da wani mutumin Samariya da ke bin hanyar ya iso wurin kuma ya gan shi, sai ya tausaya masa. 34 Ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa,* ya zuba māi da ruwan inabi a kan su. Sai ya sa shi a kan dabbarsa, ya kai shi wani masauki kuma ya yi masa jinya. 35 Washegari ya ɗauki dinari* biyu, ya ba mai kula da masaukin, kuma ya ce: ‘Ka kula da shi, kuma duk abin da ka kashe fiye da wannan, zan biya ka saꞌad da na dawo.’ 36 A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne ya nuna cewa shi ne maƙwabcin wannan mutumin da ya shiga hannun ꞌyan fashi?” 37 Sai ya ce wa Yesu: “Wanda ya tausaya wa mutumin kuma ya taimaka masa.” Sai Yesu ya ce wa mutumin: “Kai ma ka tafi ka yi hakan.”
38 Yayin da suka kama hanya suna tafiya, sai Yesu ya shiga wani ƙauye. A ƙauyen, wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ꞌyarꞌuwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a kusa da Ubangiji, tana saurarar abin da yake faɗa. 40 Marta kuwa, ayyuka da yawa sun ɗauke mata hankali. Sai ta zo wurin Yesu ta ce masa: “Ubangiji, ba ka damu da yadda ꞌyarꞌuwata ta bar ni ni kaɗai nake yin ayyuka ba? Ka gaya mata ta zo ta taimaka mini.” 41 Sai Ubangiji ya amsa ya ce mata: “Marta, Marta, kin bar ayyuka da yawa suna damun ki kuma sun tayar miki da hankali. 42 Abubuwa kaɗan ne ake bukata, ko kuma ɗaya kawai. Maryamu kuwa, ta zaɓi abu mai kyau* kuma ba za a iya ƙwace mata ba.”