Ta Hannun Yohanna
4 Da Ubangiji Yesu ya gano cewa Farisiyawa sun ji cewa yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yohanna, 2 ko da yake ba Yesu ne da kansa yake yin baftismar ba, amma almajiransa ne suke yi, 3 ya bar Yahudiya ya sake komawa Galili. 4 Amma ya zama dole ya bi ta cikin Samariya. 5 Sai ya zo wani gari a Samariya mai suna Saika. Garin yana kusa da filin da Yakubu ya ba wa ɗansa Yusufu. 6 A wannan wurin ne rijiyar Yakubu take. Yesu ya gaji da tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Kuma wajen ƙarfe goma sha biyu na rana* ne.
7 Sai ga wata mata ꞌyar Samariya, ta zo don ta ɗibi ruwa. Yesu ya ce mata: “Ki ba ni ruwa in sha.” 8 (A lokacin, almajiransa sun shiga cikin gari domin su saya abinci.) 9 Sai matar ta ce masa: “Yaya aka yi duk da cewa kai Bayahude ne, ka roƙe ni ruwan sha, ko da yake ni ꞌyar Samariya ce?” (Domin Yahudawa ba sa shaꞌani da Samariyawa.) 10 Sai Yesu ya amsa ya ce mata: “Da kin san kyautar da Allah ya bayar da kuma wanda ya ce miki, ‘Ki ba ni ruwa in sha,’ da kin roƙe shi ruwa, shi kuwa zai ba ki ruwa mai ba da rai.” 11 Sai matar ta ce wa Yesu: “Maigirma, ai ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. To, daga ina ne za ka sami wannan ruwa mai ba da rai? 12 Ko ka fi kakanmu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, kuma shi da kansa, da ꞌyaꞌyansa, da kuma dabbobinsa sun sha daga ciki?” 13 Sai Yesu ya amsa ya ce mata: “Duk wanda yake shan ruwa daga rijiyar nan, zai sake jin ƙishi. 14 Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai sake jin ƙishi ba, ruwan zai zama maɓuɓɓugar ruwa a jikinsa, inda ruwa zai riƙa ɓullowa da zai ba shi rai na har abada.” 15 Sai matar ta ce masa: “Maigirma, ka ba ni wannan ruwan domin kada in sake jin ƙishi ko kuma in riƙa zuwa nan domin in ɗibi ruwa.”
16 Sai ya ce mata: “Ki je ki kira mijinki ku zo nan.” 17 Sai matar ta amsa ta ce: “Ba ni da miji.” Sai Yesu ya ce mata: “Kin faɗi gaskiya da kika ce, ‘Ba ni da miji.’ 18 Domin kin taɓa auran mazaje biyar, kuma mutumin da kike tare da shi yanzu ba mijinki ba ne. Abin da kika faɗa gaskiya ne.” 19 Sai matar ta ce masa: “Maigirma, na ga cewa kai annabi ne. 20 Kakanninmu sun yi sujada a kan wannan tudun, amma ku kun ce dole mutane su yi sujada a Urushalima.” 21 Sai Yesu ya ce mata: “Ki ba da gaskiya ga abin da nake faɗa, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uban sujada a kan wannan tudun ko kuma a Urushalima ba. 22 Kuna yin sujada ga abin da ba ku sani ba, amma muna yin sujada ga abin da muka sani, domin ceto ya fara daga wurin Yahudawa ne. 23 Duk da haka dai, lokaci na zuwa, har ma ya riga ya zo, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada cikin ruhu da kuma gaskiya, gama Uban yana neman irin mutanen nan su yi masa sujada. 24 Allah ruhu ne, kuma dole ne waɗanda suke yi masa sujada, su yi masa sujada cikin ruhu da kuma gaskiya.” 25 Sai matar ta ce masa: “Na san cewa Almasihu yana zuwa, wanda ake kira Kristi. Kuma saꞌad da ya zo, zai bayyana mana dukan abubuwa a fili.” 26 Sai Yesu ya ce mata: “Ni ne shi, ni da nake magana da ke.”
27 A lokacin, sai almajiransa suka dawo, kuma suka yi mamaki domin yana magana da mace. Amma babu wanda ya ce masa: “Mene ne kake nema?” ko kuma “Me ya sa kake magana da ita?” 28 Sai matar ta bar tulun ruwanta ta shiga cikin gari, kuma ta gaya wa mutanen garin cewa: 29 “Ku zo ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Anya, ba shi ne Kristi ba kuwa?” 30 Sai mutanen suka bar garin suka soma zuwa wurin Yesu.
31 Ana hakan, almajiransa suna ta roƙon sa cewa: “Malam,* ka ci abinci.” 32 Amma ya ce musu: “Ina da abinci da ba ku san da shi ba.” 33 Sai almajiransa suka ce wa juna: “Ko wani ya kawo masa abinci ne?” 34 Sai Yesu ya ce musu: “Abincina shi ne in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma gama aikinsa. 35 Ba kun ce sauran watanni huɗu kafin a yi girbi ba? Ina gaya muku, ku ɗaga kanku kuma ku dubi gonakin, ai sun nuna kuma sun isa girbi. Ko yanzu ma, 36 mai girbin yana samun lada, kuma yana tara amfanin gona don rai na har abada, domin mai shuki da mai girbi su yi farin ciki tare. 37 Hakan ya yi daidai da karin maganar nan da ta ce: Wani ya yi shuki, wani kuma ya yi girbi. 38 Na aike ku ku girbi abin da ba ku sha wahala a kai ba. Wasu sun sha wahala, ku kuwa kun ci moriyar wahalarsu.”
39 Mutanen Samariya da yawa a garin sun ba da gaskiya gare shi, domin shaidar da matar ta bayar cewa: “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40 Saꞌad da Samariyawan suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi ya kasance da su. Kuma ya kasance a wurin na kwana biyu. 41 Saboda haka, ƙarin mutane sun ba da gaskiya don abin da ya faɗa. 42 Sai suka ce wa matar: “Yanzu ba abin da kika faɗa ne kawai ya sa mun ba da gaskiya ba. Domin mun ji da kanmu kuma mun san cewa, a gaskiya, wannan mutum shi ne mai ceton duniya.”
43 Bayan kwanaki biyun sun ƙare, ya bar wurin ya tafi Galili. 44 Amma Yesu da kansa ya faɗa cewa ba a daraja annabi a garinsu. 45 Don haka, saꞌad da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi, domin sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima a lokacin biki, gama su ma sun halarci bikin.
46 Sai ya sake zuwa Kana da ke Galili, inda ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. Akwai wani mutum da ke aiki a fadar sarki wanda ɗansa yake rashin lafiya a Kafarnahum. 47 Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya zuwa Galili, sai ya je wurin Yesu kuma ya roƙe shi ya zo ya warkar da ɗansa, domin ɗan yana bakin mutuwa. 48 Amma Yesu ya ce masa: “In ba dai kun ga alamu da abubuwan ban mamaki ba, ba za ku taɓa ba da gaskiya ba.” 49 Sai mutumin ya ce masa: “Ubangiji, ka zo kafin ɗana ya mutu.” 50 Sai Yesu ya ce masa: “Ka tafi, domin ɗanka yana raye.” Mutumin ya gaskata da abin da Yesu ya gaya masa, kuma ya tafi. 51 Saꞌad da yake hanyar komawa, sai bayinsa suka same shi kuma suka ce masa ɗansa yana raye.* 52 Sai ya tambaye su lokacin da yaron ya sami sauƙi. Sai suka amsa suka ce masa: “Jiya ne zazzaɓin ya bar shi, wajen ƙarfe ɗaya na rana.”* 53 Sai baban yaron ya tuna cewa, a daidai lokacin ne Yesu ya gaya masa cewa: “Ɗanka yana raye.” Sai shi da dukan mutanen gidansa suka ba da gaskiya. 54 Wannan ne abin ban mamaki na biyu da Yesu ya yi saꞌad da ya dawo Galili daga Yahudiya.