Ta Hannun Yohanna
6 Bayan wannan sai Yesu ya ƙetare Tekun Galili, ko kuma Tibariya. 2 Kuma mutane da yawa suna ta bin sa domin suna ganin yadda yake warkar da marasa lafiya ta wurin yin abubuwan ban mamaki. 3 Sai Yesu ya haura kan tudu ya zauna a wurin tare da almajiransa. 4 A lokacin, Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa. 5 Saꞌad da Yesu ya ɗaga kai kuma ya ga mutane da yawa suna zuwa wurinsa, sai ya ce wa Filibus: “Ina ne za mu sayo burodi don mutanen nan su ci?” 6 Amma Yesu ya faɗi hakan ne domin ya gwada Filibus, gama Yesu ya riga ya san abin da zai yi. 7 Filibus ya amsa masa ya ce: “Ko burodin dinari* ɗari biyu ma ba zai isa kowannensu ya sami ɗan kaɗan ba.” 8 Ɗaya daga cikin almajiransa mai suna Andarawus, ɗanꞌuwan Siman Bitrus ya ce masa: 9 “Ga wani ɗan yaro nan da burodi biyar na garin hatsin bali da kuma ƙananan kifaye guda biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”
10 Sai Yesu ya ce: “Ku gaya wa mutanen su zauna.” Da yake akwai ciyayi sosai a wurin, sai mazan suka zauna, kuma su wajen dubu biyar ne. 11 Sai Yesu ya ɗauki burodin, kuma bayan ya yi godiya, sai ya rarraba shi ga waɗanda suke zaune a wurin. Ya yi hakan ma da ƙananan kifayen, kuma sun ci su ƙoshi. 12 Amma bayan da suka ci suka ƙoshi, sai Yesu ya ce wa almajiransa: “Ku tattara burbuɗin da suka rage, domin kada kome ya lalace.” 13 Sai suka tattara burbuɗin da suka rage daga burodi biyar na garin hatsin bali da mutanen suka ci, kuma sun cika kwanduna goma sha biyu.
14 Da mutanen suka ga abin ban mamaki da ya yi, sai suka soma cewa: “Babu shakka, wannan ne Annabin da aka ce zai zo duniya.” 15 Da Yesu ya gano cewa mutanen suna shirin zuwa su kama shi ƙarfi da yaji kuma su naɗa shi sarki, sai ya sake komawa kan tudun shi kaɗai.
16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa teku. 17 Sai suka shiga jirgin ruwa za su ƙetare tekun zuwa Kafarnahum. A lokacin, dare ya yi kuma Yesu bai dawo wurinsu ba tukuna. 18 Ƙari ga haka, tekun ta soma hauka, saboda iska mai ƙarfi tana busawa. 19 Amma saꞌad da suka tuƙa jirgin ruwan wajen kilomita biyar zuwa shida,* sai suka ga Yesu yana tafiya a kan ruwa, kuma ya zo kusa da jirgin ruwan. Sai tsoro ya kama su sosai. 20 Amma ya ce musu: “Ni ne; kada ku ji tsoro!” 21 Saꞌan nan suka yarda suka karɓe shi cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai wurin da za su.
22 Washegari, jamaꞌa da suke ɗayan gefen tekun sun lura cewa babu jirgin ruwa a wurin. Akwai wani ƙaramin jirgin ruwa da ke wurin, amma Yesu bai shiga wannan jirgin ruwan tare da almajiransa ba, gama almajiran sun tafi su kaɗai. 23 Sai jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da suka ci burodin bayan da Ubangiji ya yi godiya. 24 Da jamaꞌa suka ga cewa Yesu da almajiransa ba sa wurin, sai suka shiga nasu jirgin suka je Kafarnahum don su nemi Yesu.
25 Da suka ga Yesu a ƙetaren tekun, sai suka ce masa: “Malam,* yaushe ka isa nan?” 26 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “A gaskiya ina gaya muku, ba alamun da kuka gani ne ya sa kuke nema na ba, amma domin kun ci burodi kuma kun ƙoshi ne. 27 Kada ku yi aiki don abincin da zai lalace, amma ku yi aiki don abincin da zai kasance har abada, wanda Ɗan mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uban, wato Allah da kansa ya saka hatiminsa a kansa don ya nuna cewa ya amince da shi.”
28 Sai suka ce masa: “Mene ne ya kamata mu yi don mu iya yin ayyukan Allah?” 29 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Wannan shi ne aikin Allah, wato ku ba da gaskiya ga wanda ya aiko.” 30 Sai suka ce masa: “Wace alama ce za ka yi don mu gani kuma mu ba da gaskiya gare ka? Wane aiki ne kake yi? 31 Kakanninmu sun ci manna a daji, kamar yadda yake a rubuce cewa: ‘Ya ba su burodi daga sama don su ci.’” 32 Sai Yesu ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, Musa bai ba ku burodi daga sama ba. Amma Ubana ne ya ba ku burodi na gaske daga sama. 33 Domin burodin Allah shi ne wanda ya sauko daga sama kuma ya ba da rai ga duniya.” 34 Sai suka ce masa: “Ubangiji, ka riƙa ba mu wannan burodin kullum.”
35 Sai Yesu ya ce musu: “Ni ne burodin da ke ba da rai. Duk wanda ya zo wurina, ba zai sake jin yunwa ba, kuma duk wanda yake ba da gaskiya a gare ni, ba zai taɓa jin ƙishi ba. 36 Amma ina gaya muku, kun ma gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37 Dukan waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma ba zan taɓa korin wanda ya zo wurina ba; 38 na sauko daga sama ba domin in yi nufina ba, amma domin in yi nufin wanda ya aiko ni ne. 39 Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, wato kada in rasa ko ɗaya daga cikin dukan waɗanda ya ba ni. Amma in ta da su daga mutuwa a ranar ƙarshe. 40 Wannan shi ne nufin Ubana, wato duk wanda ya yarda da Ɗan kuma yake ba da gaskiya a gare shi, ya sami rai na har abada, kuma zan ta da shi daga mutuwa a ranar ƙarshe.”
41 Sai Yahudawan suka soma gunaguni a kan Yesu domin ya ce: “Ni ne burodin da ya sauko daga sama.” 42 Sai suka soma cewa: “Wannan ba shi ne Yesu ɗan Yusufu ba, wanda mun san babansa da mamarsa? To, me ya sa yanzu yake cewa, ‘Na sauko ne daga sama’?” 43 Sai Yesu ya amsa ya ce musu: “Ku daina gunaguni a tsakaninku. 44 Babu wanda zai iya zuwa wurina, sai dai in Uba, wanda ya aiko ni, ya jawo shi wurina. Kuma zan ta da shi daga mutuwa a ranar ƙarshe. 45 An rubuta a cikin littattafan annabawa cewa: ‘Jehobah* zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uban kuma ya koya, yakan zo wurina. 46 Babu wanda ya taɓa ganin Uban, sai dai wanda ya fito daga wurin Allah; shi ne wanda ya ga Uban. 47 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda ya ba da gaskiya, yana da rai na har abada.
48 Ni ne burodi mai ba da rai. 49 Kakanninku sun ci manna a daji, duk da haka sun mutu. 50 Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama domin kowa ya iya ci kuma kada ya mutu. 51 Ni ne burodi mai ba da rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodin zai rayu har abada. Kuma gaskiyar ita ce, burodin naman jikina ne, wanda zan bayar a madadin mutane a duniya domin su sami rai.”
52 Sai Yahudawan suka soma gardama a tsakaninsu, suna cewa: “Ta yaya mutumin nan zai ba mu naman jikinsa don mu ci?” 53 Sai Yesu ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, in ba kun ci naman jikin Ɗan mutum kuma kun sha jininsa ba, ba za ku sami rai ba.* 54 Duk wanda ya ci naman jikina, kuma ya sha jinina, yana da rai na har abada, kuma zan ta da shi daga mutuwa a ranar ƙarshe; 55 domin naman jikina abinci ne na gaske, kuma jinina abin sha ne na gaske. 56 Duk wanda ya ci naman jikina, kuma ya sha jinina, zai kasance da haɗin kai da ni, ni ma zan kasance da haɗin kai da shi. 57 Kamar yadda Uba mai rai ya aiko ni, saboda shi kuma nake rayuwa, haka ma wanda ya mai da ni abincinsa zai rayu saboda ni. 58 Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Ba kamar burodin da kakanninku suka ci, duk da haka sun mutu ba. Duk wanda ya ci burodin nan, zai rayu har abada. 59 Ya faɗi abubuwan nan ne saꞌad da yake koyarwa a wata majamiꞌa a Kafarnahum.
60 Saꞌad da suka ji hakan, da yawa daga cikin almajiransa suka ce: “Wannan maganar banza ce, wa zai saurare ta?” 61 Amma da Yesu ya gane cewa almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai ya ce musu: “Wannan ya sa ku tuntuɓe ne? 62 To, me zai faru idan kun ga Ɗan mutum yana haurawa zuwa inda yake a dā? 63 Ruhun ne yake ba da rai, jikin kuma ba shi da wani amfani. Abubuwan da na gaya muku daga ruhun ne, kuma suna ba da rai. 64 Amma akwai wasu a cikinku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun daga farko, Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai ci amanarsa. 65 Sai Yesu ya ƙara cewa: “Shi ya sa nake gaya muku, ba wanda zai iya zuwa wurina, sai in Uban ya yarda.”
66 Saboda haka, da yawa daga cikin almajiransa sun koma ga abubuwan da suke yi a dā, kuma suka daina bin sa. 67 Sai Yesu ya ce wa almajiransa goma sha biyun: “Ku ma kuna so ku tafi ne?” 68 Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce masa: “Ubangiji, wurin wa za mu je? Kai ne kake magana mai ba da rai na har abada. 69 Mun gaskata kuma mun sani cewa, kai ne Mai Tsarki na Allah.” 70 Sai Yesu ya amsa ya ce musu: “Ni ne na zaɓe ku, ku goma sha biyu, ko ba haka ba? Duk da haka, ɗaya daga cikinku, mai ɓata suna* ne.” 71 Hakika, Yesu yana magana ne game da Yahuda ɗan Siman Iskariyoti, shi ne zai ci amanar Yesu duk da cewa yana cikin almajiransa goma sha biyu.