Ta Hannun Yohanna
3 Akwai wani shugaban Yahudawa mai suna Nikodimus, kuma shi Bafarisi ne. 2 Mutumin nan ya zo wurin Yesu da dare kuma ya ce masa: “Malam,* mun san cewa kai malami ne da Allah ya aiko, domin ba wanda ya isa ya yi waɗannan alamun ban mamaki da ka yi in ba Allah yana tare da shi ba.” 3 Sai Yesu ya amsa ya ce masa: “A gaskiya ina gaya maka, babu wanda zai iya shiga Mulkin Allah idan ba a sake haifan sa* ba.” 4 Sai Nikodimus ya ce masa: “Ta yaya za a haifi mutum bayan ya tsufa? Zai koma cikin mamarsa kuma a sake haifan sa ne?” 5 Yesu ya amsa ya ce: “A gaskiya ina gaya maka, idan ba a haife mutum ta ruwa da kuma ta ruhu ba, ba zai shiga Mulkin Allah ba. 6 Abin da mutum ya haifa, mutum ne, kuma abin da ruhu ya haifa, ruhu ne. 7 Kada ka yi mamaki domin na ce maka: Dole ne a sake haifan ku. 8 Iska tana busawa inda ta ga dama, kuma kukan ji ƙarar ta, amma ba ku san inda ta fito da inda za ta ba. Haka yake da duk mutumin da aka haife shi ta ruhu.”
9 Sai Nikodimus ya amsa masa ya ce: “Ta yaya abubuwan nan za su faru?” 10 Sai Yesu ya ce masa: “Kai malami ne a Israꞌila, amma ba ka san abubuwan nan ba? 11 A gaskiya ina gaya maka, abin da muka sani ne mukan faɗa, kuma abin da muka gani ne muke shaidar sa, amma kun ƙi ku karɓa shaidar da muka bayar. 12 Idan na gaya muku abubuwa game da duniya kuma ba ku yarda ba, ta yaya za ku yarda idan na gaya muku abubuwa game da sama? 13 Ƙari ga haka, babu mutumin da ya taɓa haura sama, sai dai wanda ya sauko daga sama, wato Ɗan mutum. 14 Kuma kamar yadda Musa ya ɗaga maciji a daji, haka ma dole a ɗaga Ɗan mutum, 15 domin duk wanda ya ba da gaskiya gare shi ya samu damar yin rayuwa har abada.
16 “Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da Ɗansa makaɗaici,* domin duk wanda yake ba da gaskiya gare shi kada ya hallaka, amma ya sami rai na har abada. 17 Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin ya shariꞌanta duniya ba, amma domin duniya ta sami ceto ta wurinsa ne. 18 Duk wanda yake ba da gaskiya gare shi, ba za a yi masa shariꞌa ba. Amma duk wanda ba ya ba da gaskiya gare shi an riga an yi masa shariꞌa, domin bai ba da gaskiya ga sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Ga dalilin da ya sa za a yi wa mutane shariꞌa: wato haske ya zo cikin duniya, amma mutane sun so duhu maimakon hasken, domin ayyukansu na mugunta ne. 20 Duk wanda yake yin abubuwa marasa kyau, yakan ƙi haske kuma ba ya shigowa cikin haske, domin kada a fallasa ayyukansa. 21 Amma duk wanda yake yin abubuwa masu kyau, yakan shigo cikin haske, don mutane su ga abubuwan da yake yi kuma su san cewa abubuwan sun jitu da nufin Allah.”
22 Bayan haka, Yesu da almajiransa sun shiga cikin ƙauyukan Yahudiya, kuma ya ɗan jima a wurin tare da almajiransa yana yi wa mutane baftisma. 23 Yohanna kuma yana yin baftisma a yankin Ainon kusa da Salim domin akwai ruwa mai yawa a wurin. Mutane suna ta zuwa kuma ana yi musu baftisma. 24 A lokacin ba a saka Yohanna a kurkuku ba tukuna.
25 Ana nan, sai almajiran Yohanna suka yi gardama da wani Bayahude a kan alꞌadar tsabtacewa. 26 Sai suka zo wurin Yohanna kuma suka ce masa: “Malam, mutumin nan wanda yake tare da kai a ƙetaren Kogin Jodan, wanda ka ba da shaida game da shi, ga shi yana yi wa mutane baftisma, kuma kowa yana zuwa wurinsa.” 27 Sai Yohanna ya amsa ya ce: “Mutum ba zai iya samun kome idan ba a ba shi daga sama ba. 28 Ku da kanku ma kun shaida abin da na faɗa cewa, ‘Ba ni ba ne Kristi, amma an aiko ni ne don in riga shi zuwa.’ 29 A bikin aure, ango ne mai amarya. Amma saꞌad da abokin ango ya tsaya kuma ya ji muryarsa, yakan yi farin ciki sosai domin ya ji muryar angon. Ta haka ne farin cikina ya cika. 30 Dole ne Kristi ya yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.”
31 Shi wanda ya zo daga sama ya fi kowa duka. Shi wanda ya fito daga duniya kuma, na duniya ne, kuma yakan yi maganar abubuwan duniya ne. Wanda kuma ya zo daga sama ya fi kowa duka. 32 Yakan ba da shaida a kan abubuwan da ya gani da kuma abubuwan da ya ji, amma babu wanda ya yarda da shaidarsa. 33 Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya saka hatiminsa ke nan* cewa Allah mai gaskiya ne. 34 Gama wanda Allah ya aiko yakan faɗi abubuwan da Allah ya faɗa, domin Allah ya ba shi ruhunsa babu iyaka. 35 Uban yana ƙaunar Ɗan kuma ya saka kome a hannunsa. 36 Wanda yake ba da gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada, amma wanda ya ƙi yin biyayya ga Ɗan ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah zai kasance a kansa.