Zuwa ga Romawa
5 Saboda haka, yanzu da Allah ya ce mu masu adalci ne saboda bangaskiyarmu, bari mu more salama* da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi. 2 Bangaskiyar da muke da ita ga Yesu ce ta buɗe mana hanyar samun alheri da muke morewa yanzu; bari mu yi murna* domin muna da begen samun ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma bari mu yi murna* saꞌad da muke cikin ƙunci, tun da mun san cewa ƙunci yana taimaka mana mu ci-gaba da jimrewa; 4 jimrewa kuma zai sa Allah ya amince da mu; idan Allah ya amince da mu kuma, za mu kasance da bege, 5 kuma begen ba zai zama a banza ba; domin Allah ta wurin ruhu mai tsarkin da ya ba mu, ya saka ƙaunarsa a zukatanmu.
6 Gama, tun muna masu zunubi, Kristi ya mutu don masu mugunta a lokacin da aka tsara. 7 Da kyar wani ya mutu don mai adalci; amma wataƙila wani zai yi ƙarfin hali ya mutu saboda mutumin kirki. 8 Amma Allah ya nuna cewa yana ƙaunar mu, da yake tun muna masu zunubi, Kristi ya mutu saboda mu. 9 Tun da yake mun zama masu adalci a gaban Allah ta wurin jinin Kristi, za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa. 10 Da yake tun muna gāba da Allah an sa mun yi sulhu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, balle ma yanzu da an sulhunta mu da Allah, tabbas za a cece mu ta wurin ran Ɗansa. 11 Ba haka kawai ba, amma muna murna ma da Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda ta wurinsa ne muka yi sulhu da Allah.
12 Shi ya sa, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi, ta haka mutuwa ta shafi dukan mutane da yake kowa ya yi zunubi—. 13 Gama akwai zunubi a duniya kafin a ba da Doka,* amma ba a ce mutum mai zunubi ne a lokacin da babu doka. 14 Duk da haka, mutuwa ta yi mulki a kan dukan mutane, tun daga lokacin Adamu zuwa lokacin Musa, har a kan waɗanda ba su yi zunubi irin wanda Adamu ya yi ba. Adamu ya yi kama da wanda aka ce zai zo.
15 Amma kyautar Allah ba ta kama da zunubin. Idan saboda zunubi na mutum ɗaya mutane da yawa suke mutuwa, a gaskiya mutane da yawa sun amfana sosai saboda alherin Allah, da kuma kyautar da ya bayar ta wurin alherin mutum ɗaya, wato Yesu Kristi! 16 Ƙari ga haka, yadda abubuwa suke faruwa saboda kyautar dabam yake da yadda abubuwa suke faruwa saboda mutum ɗaya da ya yi zunubi. Don zunubin mutum ɗaya, an sami mutane da yawa da laifi, amma kyautar da Allah ya bayar bayan mutane da yawa sun yi zunubi ita ce, ya ɗauke su a matsayin masu adalci. 17 Idan ta wurin zunubin mutum ɗaya mutuwa ta yi mulki, tabbas waɗanda suka sami alherin Allah da kuma kyautar da ya ba su, wato yadda ya ɗauke su a matsayin masu adalci, za su rayu kuma su yi mulki ta wurin mutum ɗaya, wato Yesu Kristi!
18 Kamar yadda ta wurin zunubin mutum ɗaya dukan mutane sun zama masu laifi, haka ma, ta wurin adalcin mutum ɗaya, Allah yana ɗaukan mutane ko da daga ina suka fito a matsayin masu adalci don su sami rai. 19 Kamar yadda ta wurin rashin biyayya na mutum ɗaya mutane da yawa suka zama masu zunubi, haka ma ta wurin biyayyar mutum ɗaya mutane da yawa za su zama masu adalci. 20 Dalilin da ya sa aka ba da Doka shi ne domin zunubi ya fito a fili. Amma saꞌad da zunubi ya ƙaru, sai alherin Allah ya daɗa ƙaruwa. 21 Saboda wane dalili? Domin kamar yadda zunubi ya yi mulki tare da mutuwa, haka ma alheri zai yi mulki ta wurin adalci kuma ya kai ga samun rai na har abada, ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.