Zuwa ga Romawa
2 Saboda haka ɗanꞌuwana, ba ka da wata hujjar shariꞌanta wani ko da kai wane ne; idan ka shariꞌanta wani, ka yanke wa kanka hukunci ke nan, domin kai ma kana yin abubuwan da yake yi. 2 Mun san cewa Allah zai yi shariꞌar gaskiya a kan waɗanda suka ci-gaba da yin irin waɗannan abubuwan.
3 Amma kai ɗanꞌuwana, kana tsammanin za ka iya guje wa hukuncin Allah idan ka ci-gaba da shariꞌanta waɗanda suke yin abubuwan nan kuma kai da kanka kana yin su? 4 Ko dai kana rena yawan alherinsa, da jimrewarsa, da haƙurinsa, domin ba ka san cewa Allah cikin alherinsa yana ƙoƙari ya taimaka maka ka tuba ba? 5 Amma saboda taurin kanka da kuma zuciyarka da ta ƙi tuba, kana tara wa kanka fushi da za ka fuskanta a ranar fushin Allah, da kuma ranar bayyana hukuncin adalci na Allah. 6 Kuma zai sāka wa kowa daidai da ayyukansa: 7 wato rai na har abada ga waɗanda suke neman ɗaukaka, da daraja, da jiki marar mutuwa, ta wurin ci-gaba da yin aiki mai kyau; 8 amma masu son rikici, da masu ƙin gaskiya da suke rashin adalci, Allah zai yi fushi da su kuma ya hukunta su. 9 Duk mutumin da yake yin ayyukan mugunta zai sha wahala da azaba, somawa da Bayahude saꞌan nan mutumin Girka; 10 amma duk wanda yake yin ayyuka masu kyau zai samu ɗaukaka, da daraja, da kuma salama, somawa da Bayahude saꞌan nan mutumin Girka. 11 Domin Allah ba ya nuna bambanci.
12 Duk masu yin zunubi ba tare da sanin doka ba, za su mutu ba tare da sanin doka ba; amma duk masu yin zunubi duk da cewa sun san doka, za a yi musu hukunci bisa ga doka. 13 Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma za a ce da masu bin doka masu adalci. 14 Ko da yake mutanen alꞌummai ba su san doka ba, suna yin abin da ke cikin doka da kansu, duk da cewa ba su da doka, su doka ne ga kansu. 15 Su ne suka nuna cewa abin da dokar ta ce a yi yana nan a rubuce a cikin zukatansu, kuma lamirinsu yana taimaka musu su san ko abin da suka yi daidai ne ko ba daidai ba ne. 16 Wannan zai faru a ranar da Allah, ta wurin Kristi Yesu zai shariꞌanta mutane don abubuwan da suke yi a ɓoye, kamar yadda labari mai daɗi da nake shelar sa ya faɗa.
17 To, idan ka ce kai Bayahude ne, ka dogara ga doka kuma kana taƙama da dangantakarka da Allah, 18 ka san nufinsa kuma ka amince da abubuwan da suke da muhimmanci, domin da Doka* ce aka koyar da kai, 19 kuma kana da tabbaci cewa, kai ne ja-gorar makaho, da haske ga waɗanda suke cikin duhu, 20 mai koyar da marasa wayo, malamin yara, da kuma mai ilimin muhimman koyarwa da gaskiyar da ke cikin Dokar, 21 amma kai da kake koyar da wani, ba ka koyar da kanka ne? Kai da kake waꞌazi kana cewa, “Kada a yi sata,” kana sata? 22 Kai da kake cewa, “Kada a yi zina,” kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana sata a haikali? 23 Kai da kake taƙama da doka, kana ɓata sunan Allah ta wurin taka Dokar? 24 Gama “ana saɓo ga sunan Allah tsakanin alꞌummai saboda ku,” kamar yadda yake a rubuce.
25 A gaskiya, yin kaciya yana da amfani, idan dai kana bin doka; amma idan ba ka bin doka, kaciyar da ka yi ba ta da amfani. 26 saboda haka, idan wanda bai yi kaciya ba yana yin abubuwan adalci da ke cikin Doka, Allah zai ɗauke shi a matsayin wanda ya yi kaciya ko da yake bai yi kaciya ba, ko ba haka ba? 27 Kuma yayin da wanda ba a yi masa kaciya ta jiki ba yake bin Doka, zai shariꞌanta kai da ba ka bin doka duk da cewa kana da dokar kuma an yi maka kaciya. 28 Gama zama Bayahude na gaske ba a siffar jiki ba ne kuma kaciyarsa ba ta jiki ba ce. 29 Amma Bayahude na gaske Bayahude ne a zuciya, kuma kaciyarsa ta zuciya ce ta wurin ruhu, ba bisa doka ba. Irin mutumin nan yana samun yabo daga wurin Allah ba daga wurin mutane ba.