Ta Hannun Matiyu
25 “Za a iya kwatanta Mulkin sama da budurwai guda goma da suka ɗauki fitilunsu suka fita don su haɗu da ango. 2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima ne. 3 Domin wawayen sun ɗauki fitilunsu amma ba su ɗauki māi ba. 4 Masu hikimar kuma sun ɗauki māi a cikin kwalabe tare da fitilunsu. 5 Da yake angon bai zo da wuri ba, sai dukansu suka soma jin barci har barci ya kwashe su. 6 Da tsakar dare sai aka ji ihu cewa: ‘Ga angon! Ku fito ku haɗu da shi.’ 7 Sai dukansu suka tashi, suka kunna fitilunsu. 8 Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan ba mu mānku kaɗan, domin fitilunmu sun kusan mutuwa.’ 9 Sai masu hikimar suka amsa suka ce: ‘Kamar dai mān ba zai ishe mu da ku ba. Ku je wurin waɗanda suke sayarwa don ku saya.’ 10 Da suka je su saya mān, sai angon ya zo, kuma budurwai da suke a shirye suka shiga bikin auren tare da shi, sai aka kulle ƙofa. 11 Bayan haka, sai sauran budurwai ɗin suka dawo, suna cewa, ‘Mai Girma, Mai Girma, ka buɗe mana ƙofa!’ 12 Sai ya amsa musu ya ce, ‘A gaskiya ina gaya muku, ban san ku ba.’
13 “Saboda haka, ku ci-gaba da yin tsaro, domin ba ku san rana ko kuma lokacin da hakan zai faru ba.
14 “Yana kamar mutum ne da zai yi tafiya zuwa wata ƙasa, sai ya kira bayinsa kuma ya danƙa musu dukiyarsa. 15 Ya ba wa ɗaya talenti* biyar, ya ba wa ɗaya kuma talenti biyu. Har ila, ya ba da talenti ɗaya ga wani, ya ba kowannensu daidai da ƙarfinsa, saꞌan nan ya tafi wata ƙasa. 16 Nan da nan wanda aka ba shi talenti biyar, ya je ya yi kasuwanci da kuɗin, har ya sami ribar talenti biyar. 17 Haka ma, wanda aka ba shi biyu, ya samo ribar biyu. 18 Amma bawan da aka ba shi talenti ɗaya, ya tafi ya je ya tona ƙasa, ya binne kuɗin* maigidansa.
19 “Bayan dogon lokaci, sai maigidan waɗannan bayin ya dawo don ya bincika abin da suka yi da kuɗinsa. 20 Sai wanda aka ba shi talenti biyar, ya zo ya ba da ƙarin talenti biyar, yana cewa, ‘Maigida, ka ba ni talenti biyar; ga shi, na samo ƙarin talenti biyar.’ 21 Sai maigidansa ya ce masa: ‘Sannu da ƙoƙari bawan kirki, mai aminci! Ka nuna aminci a kan ƙananan abubuwa, zan danƙa maka abubuwa masu yawa. Ka zo ka yi farin ciki tare da maigidanka.’ 22 Sai bawan da ya karɓi talenti biyu, ya zo ya ce, ‘Maigida, ka ba ni talenti biyu; ga shi, na samo ƙarin talenti biyu.’ 23 Sai maigidansa ya ce masa: ‘Sannu da ƙoƙari bawan kirki, mai aminci! Ka nuna aminci a kan ƙananan abubuwa, zan danƙa maka abubuwa masu yawa. Ka zo ka yi farin ciki tare da maigidanka.’
24 “A ƙarshe, bawan da aka ba shi talenti ɗaya ya zo ya ce: ‘Maigida, na san kai mai wuyar shaꞌani ne, kana girbi a inda ba ka yi shuki ba, kuma kana kwashe hatsi da ba ka sha wahala a kai ba. 25 Don haka na ji tsoro kuma na je na binne kuɗinka a ƙasa. Ga kuɗinka.’ 26 Sai maigidan ya ce masa: ‘Mugun bawa, mai ƙiwuya, ashe ka san cewa ina girbi a inda ban yi shuki ba, kuma ina kwasan hatsi da ban sha wuya a kai ba? 27 To, ai da ka sa kuɗin* a banki don in na dawo in karɓi kuɗin har da riba.
28 “‘Don haka, ku karɓi talentin daga wurinsa kuma ku ba ma wanda yake da talenti goma. 29 Domin duk wanda yake da abu, za a ƙara masa, har a sa ya yi yawa sosai. Amma duk wanda ba shi da abu, za a ɗauke har abin da yake da shi. 30 Ku kuma jefa bawan banzan nan waje cikin duhu. A wurin ne zai yi ta kuka da cizon haƙora.’
31 “Saꞌad da Ɗan mutum ya zo a cikin ɗaukakarsa, tare da dukan malaꞌiku, zai zauna a kujerar mulkinsa mai ɗaukaka. 32 Dukan alꞌummai za su taru a gabansa, kuma zai ware mutane daga junansu, kamar yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki. 33 Zai sa tumaki a hannun damansa, awaki kuma a hannun hagunsa.
34 “Saꞌan nan Sarkin zai ce ma waɗanda suke hannun damansa: ‘Ku zo, ku waɗanda Ubana ya albarkace ku, ku gāji Mulkin da aka shirya muku tun farkon duniya.* 35 Domin saꞌad da nake jin yunwa, kun ba ni abinci. Saꞌad da nake ƙishin ruwa kun ba ni abin sha. Saꞌad da na zo a matsayin baƙo, kun karɓe ni hannu bibbiyu. 36 Saꞌad da ba ni da riga, kun ba ni riga. Saꞌad da nake rashin lafiya, kun kula da ni. Saꞌad da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’ 37 Sai masu adalcin za su amsa masa su ce: ‘Ubangiji, yaushe ne muka gan ka kana jin yunwa, muka ba ka abinci, ko kuma kana ƙishin ruwa, muka ba ka abin sha? 38 Yaushe ne muka gan ka a matsayin baƙo, muka karɓe ka hannu bibbiyu, ko kuma muka gan ka ba riga, muka ba ka riga? 39 Yaushe ne muka ga kana rashin lafiya ko kana kurkuku har muka ziyarce ka?’ 40 Sarkin zai amsa musu cewa, ‘A gaskiya ina gaya muku, tun da yake kun yi wa mafi ƙanƙanta daga cikin waɗannan ꞌyanꞌuwana, kun yi mini ke nan.’
41 “Saꞌan nan zai gaya ma waɗanda suke hannun hagunsa cewa: ‘Ku rabu da ni, ku laꞌantattu, ku shiga cikin wuta ta har abada wadda aka shirya wa Ibilis da malaꞌikunsa. 42 Domin na ji yunwa, amma ba ku ba ni abinci ba. Na ji ƙishin ruwa, amma ba ku ba ni abin sha ba. 43 Saꞌad da na zo a matsayin baƙo, ba ku karɓe ni hannu bibbiyu ba; ba ni da riga, amma ba ku ba ni riga ba; na yi rashin lafiya kuma ina kurkuku, amma ba ku kula da ni ba.’ 44 Saꞌan nan su ma za su amsa masa su ce: ‘Ubangiji, yaushe ne muka gan ka kana jin yunwa, ko kana ƙishin ruwa, ko ka zo a matsayin baƙo, ko ba ka da riga, ko kana rashin lafiya, ko kana kurkuku kuma ba mu yi maka hidima ba?’ 45 Zai amsa musu cewa: ‘A gaskiya ina gaya muku, tun da yake ba ku yi ma ɗaya daga cikin mafi ƙanƙantan nan ba, ba ku yi mini ba ke nan.’ 46 Waɗannan za su hallaka har abada,* amma masu adalci za su rayu har abada.”