Ta Hanyar Almasihu Ne Allah Zai Kawo Ceto
“Kamar yadda cikin Adamu duka suna mutuwa, haka nan cikin Kristi duka za su rayu.”—1 KOR. 15:22.
1, 2. (a) Yaya Andarawus da Filibbus suka aikata sa’ad da suka sadu da Yesu? (b) Me ya sa muka faɗi cewa muna da ƙarin tabbaci cewa Yesu ne Almasihu fiye da Kiristoci na ƙarni na farko?
DA YAKE yana da tabbaci cewa Yesu Banazare ne Zaɓaɓɓe na Allah, Andarawus ya gaya wa ɗan’uwansa Bitrus, “mun sami Almasihu.” An tabbatar da Filibbus kuma ya nemi abokinsa Natanayilu, ya gaya masa: “Mun same shi wanda Musa a cikin Attaurat, da Annabawa kuma suka rubuta labarinsa, Yesu Ba-nazarat, ɗan Yusufu.”—Yoh. 1:40, 41, 45.
2 Kana da tabbaci sosai cewa Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarinsa, ‘Shugaban ceto’ na Jehobah? (Ibran. 2:10) A yau, muna da tabbaci sosai da suka bayyana cewa shi ne Almasihu fiye da mabiyansa na ƙarni farko. Daga haihuwar Yesu zuwa tashinsa daga matattu, Kalmar Allah ta ba da tabbaci da ba za a iya ƙaryata ba cewa shi ne Kristi. (Karanta Yohanna 20:30, 31.) Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa Yesu zai ci gaba da cika hakkinsa na Almasihu daga sama. (Yoh. 6:40; karanta Korintiyawa 15:22.) Bisa abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki, kai ma za ka iya faɗan cewa ka “sami Almasihu” a yau. Amma ka fara yin la’akari da yadda almajirai na farko suka kammala daidai cewa sun samu Almasihu.
An Bayyana “Asiri” na Almasihu a Hankali
3, 4. (a) Ta yaya almajirai na ƙarni na farko suka ‘sami Almasihu’? (b) Me ya sa za ka faɗi cewa Yesu ne kaɗai zai iya cika dukan annabce-annabce game da Almasihu?
3 Ta yaya mabiyan Yesu na ƙarni na farko suka faɗa da tabbaci cewa shi ne Almasihu? Ta hanyar annabawa, Jehobah ya bayyana a hankali alamun da za su sa a gane Almasihu mai zuwa. Wani masani na Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan tsarin da gina mutum-mutumi da aka yi da dutsen da aka farfasa. A ce mutane da yawa da ba su taɓa tattaunawa da juna ba sun taru a ɗaki ɗaya kowannensu yana riƙe da dutse. Idan aka haɗa waɗannan duwatsun kuma suka zama mutum-mutumin nan, babu shakka, za ka kammala cewa akwai wani da ya yanka duwatsun nan kuma ya aika su ga mutanen nan. Kamar kowane yankan dutsen nan da ya haɗu ya zama mutum-mutumi, kowane annabci na Almasihu zai yi tanadin bayani mai muhimmanci game da Almasihu.
4 Zai yiwu mutum ɗaya kaɗai ya cika dukan annabce-annabcen da aka yi game da Almasihu ba shiri? Wani masani ya faɗi cewa a ce wai wani mutum zai iya cika dukan annabce-annabce game da Almasihu haka kawai, “magana ce mai girma,” hakan ba zai yiwu ba. “Yesu ne kaɗai a cikin dukan tarihi ya yi hakan.”
5, 6. (a) Wane “asiri” ne Yesu ya soma cikawa? (b) Ta yaya Allah a hankali ya bayyana inda “zuriyar” da aka yi alkawarinta za ta fito?
5 Annabce-annabce na Almasihu “asiri” ne mai fannoni da yawa da suke da muhimmanci ga dukan mutanen duniya. (Kol. 1:26, 27; Far. 3:15) Wannan asirin ya haɗa da hukuncin da za a yi wa Shaiɗan Iblis, “tsohon macijin nan,” wanda ya saka ’yan Adam cikin zunubi da mutuwa. (R. Yoh. 12:9) Yaya za a zartar da wannan hukunci? Jehobah ya annabta cewa wata “mace” za ta haifi “zuriya” da zai ƙuje kan Shaiɗan. “Zuriya” da aka annabta zai ƙuje kan macijin, da hakan, zai kawar da abin da ya jawo tawaye, ciwo, da mutuwa. Amma, da izinin Allah, Shaiɗan zai fara ji wa “zuriyar” macen rauni ta alama a dudduge.
6 A hankali Jehobah ya bayyana wanda zai zama wannan “zuriya” da aka yi alkawarinsa. Allah ya yi rantsuwa ga Ibrahim: “Cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka.” (Far. 22:18) Musa ya annabta cewa wannan zai zama “annabi” kuma zai fi shi girma. (K. Sha 18:18, 19) An tabbatar wa Dauda, kuma daga baya annabawa sun ba da tabbaci cewa Almasihun zai fito daga zuriyarsa kuma zai gaji karagar Dauda har abada.—2 Sam. 7:12, 16; Irm. 23:5, 6.
Abubuwa da Suka Sa Yesu Ya Cancanci Zama Almasihu
7. A wace hanya ce Yesu ya zo daga “macen” Allah?
7 Allah ya aiko da Ɗansa, halittarsa na farko daga ƙungiyarsa ta halittun ruhu wadda take sama mai kama da matarsa don ya zama “zuriya” da aka yi alkawarinta. Hakan ya bukaci Ɗan Allah makaɗaici ya “wofinta kansa” ya bar rayuwa a sama kuma a haife shi a matsayin kamiltaccen mutum. (Filib. 2:5-7; Yoh. 1:14) Da yake ruhu mai tsarki ya ‘inuwantar da’ Maryamu, hakan ya tabbatar da cewa abin da za a haifa “za a ce da shi mai-tsarki, Ɗan Allah.”—Luk 1:35.
8. Yaya Yesu ya cika annabci na Almasihu sa’ad da ya miƙa kansa don baftisma na ruwa?
8 Annabce-annabcen Almasihu sun nuna inda Yesu zai bayyana da kuma lokacin da zai yi hakan. An haifi Yesu a Bai’talami kamar yadda aka annabta. (Mi. 5:2) A ƙarni na farko, Yahudawa sun sa rai sosai. Da yake suna sauraron bayyanuwar Almasihu, wasu sun yi tambaya game da Yohanna mai Baftisma: “Ko wataƙila shi Kristi ne”? Amma Yohanna ya amsa: “Wanda ya fi ni iko yana zuwa.” (Luk 3:15, 16) Sa’ad da ya je wajen Yohanna a ƙarshen shekara ta 29 A.Z. don ya yi masa baftisma sa’ad da ya kai ɗan shekara 30, Yesu ya nuna kansa a matsayin Almasihu a kan lokaci. (Dan. 9:25) Sai ya soma hidimarsa, yana cewa: “Zamani ya cika, gashi lokacin bayyanan mulkin Allah ya zo.”—Mar. 1:15.
9. Ko da yake ba su da cikakken bayani, wane tabbaci ne almajiran Yesu suke da shi?
9 Amma, ana bukatan a daidaita ra’ayin mutane. Da dalili mai kyau aka ɗaukaka Yesu a matsayin Sarki, amma mutane a lokacin ba su fahimci cewa sarautarsa za ta zama nan gaba ba kuma daga sama. (Yoh. 12:12-16; 16:12, 13; A. M. 2:32-36) Duk da haka, sa’ad da Yesu ya yi tambaya, “Kuna ce da ni wanene?” Ba tare da ɓata lokaci ba Bitrus ya amsa: “Kai Kristi ne, Ɗan Allah mai-rai.” (Mat. 16:13-16) Bitrus ma ya faɗi hakan sa’ad da mutane da yawa suka daina binsa domin ba su fahimci wata koyarwarsa ba.—Karanta Yohanna 6:68, 69.
Saurarar Almasihu
10. Me ya sa Jehobah ya nanata bukatar yin biyayya ga Ɗansa?
10 A sama, Ɗan Allah makaɗaici ruhu ne mai iko. A duniya, Yesu ne wakilin ‘Uban.’ (Yoh. 16:27, 28) Ya ce: “Koyarwana ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni.” (Yoh. 7:16) Sa’ad da yake tabbatar da cewa Yesu Almasihu ne a lokacin sake kamani, Jehobah ya ba da umurni: “Ku ji shi.” (Luk 9:35) Hakika, ka saurari ko kuma ka yi biyayya ga Wannan Zaɓaɓɓe. Hakan na bukatan bangaskiya da nagargarun ayyuka don suna da muhimmanci wajen faranta wa Allah rai da kuma samun rai madawwami.—Yoh. 3:16, 35, 36.
11, 12. (a) Don waɗanne dalilai ne Yahudawa na ƙarni na farko suka ƙi Yesu a matsayin Almasihu? (b) Su waye ne suka ba da gaskiya ga Yesu?
11 Ko da yake Yesu yana da abubuwa masu yawa da suka tabbatar da cewa shi ne Almasihu, yawancin Yahudawa na ƙarni na farko sun ƙi shi a matsayin Almasihu. Me ya sa? Domin suna da nasu ra’ayoyi a dā game da Almasihu, har da cewa zai zama almasihu na siyasa wanda zai ’yantar da su daga zaluncin Romawa. (Karanta Yohanna 12:34.) Saboda haka, ba su amince da Almasihun da ya cika annabce-annabcen da suka nuna cewa zai zama abin reni, yasashe a wurin mutane, mai baƙin ciki, wanda ya saba da cuta, kuma daga baya za a kashe shi. (Isha. 53:3, 5) Wasu a cikin amintattun almajiran Yesu sun yi sanyin gwiwa domin bai ’yantar da su ba ta hanyar siyasa. Amma sun kasance da aminci, kuma da shigewar lokaci aka ba su cikakken fahimi.—Luk. 24:21.
12 Wani dalilin da ya sa mutane suka ƙi Yesu a matsayin Almasihu da aka yi alkawarinsa shi ne koyarwarsa, wanda ya yi wa mutane da yawa wuya su amince da shi. Kafin mutum ya shiga cikin Mulkin, zai yi “musun kansa” zai “ci” naman Yesu kuma ya sha jininsa, za a “haifi mutum daga bisa,” kuma ya kasance “ba na duniya ba.” (Mar. 8:34; Yoh. 3:3; 6:53; 17:14, 16) Masu fahariya, mawadata, da munafukai suna ganin yana da wuya ainun a cika waɗannan bukatu. Amma, Yahudawa masu tawali’u sun amince da Yesu a matsayin Almasihu, yadda wasu Samariyawa suka yi, waɗanda suka ce: “Wannan Mai-ceton duniya ne lallai.”—Yoh. 4:25, 26, 41, 42; 7:31.
13. Ta yaya Yesu ya sha wahalar rauni na alama a duddugensa?
13 Yesu ya annabta cewa manyan firistoci za su hukunta shi kuma ’yan Al’ummai za su tsire shi, amma a rana ta uku, zai tashi. (Mat. 20:17-19) Sun ce ya yi saɓo saboda tabbacin da ya ba da a gaban ’yan majalisa cewa shi “Kristi ne Ɗan Allah.” (Mat. 26:63-66) Bilatus bai ga “abin da ya yi wanda ya isa mutuwa” ba, amma domin Yahudawa sun tuhume shi da alhakin ta da zaune tsaye, Bilatus “ya bada Yesu ga nufinsu.” (Luk 23:13-15, 25) Da hakan sun yi “musun saninsa” kuma suka ƙulla suka kashe “Sarkin rai,” duk da tabbaci mai yawa da suka nuna cewa Allah ne ya aiko shi. (A. M. 3:13-15) An “datse” Almasihu yadda aka annabta, aka tsire shi a kan gungume a Ranar Idin Ƙetarewa a shekara ta 33 A.Z. (Dan. 9:26, 27; A. M. 2:22, 23) Ta wannan mutuwa ta zalunci, ya sha wahalar rauni a “dudduge” da aka annabta a Farawa 3:15.
Dalilin da Ya Sa Almasihu Ya Mutu
14, 15. (a) Don waɗanne dalilai biyu ne Jehobah ya ƙyale Yesu ya mutu? (b) Menene Yesu ya yi bayan da aka ta da shi daga matattu?
14 Jehobah ya ƙyale Yesu ya mutu don dalilai biyu masu muhimmanci. Na farko, amincin Yesu har mutuwa ya warware fanni mai muhimmanci na “asirin.” Ya nuna sarai cewa kamiltaccen mutum zai iya kasancewa da “ibada” kuma ya ɗaukaka ikon mallaka na Allah duk da gwaji mafi tsanani da Shaiɗan zai kawo. (1 Tim. 3:16) Na biyu, kamar yadda Yesu ya faɗa, “Ɗan mutum ya zo . . . shi bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Mat. 20:28) Wannan daidaitaccen “fansa” ya biya hukuncin zunubi da ’ya’yan Adamu suka gāda kuma hakan ya sa ya yiwu dukan waɗanda suka amince da Yesu a matsayin hanyar ceto na Allah su sami rai madawwami.—1 Tim. 2:5, 6.
15 An ta da Kristi bayan ya yi kwanaki uku cikin kabari, kuma ya bayyana ga almajiransa har tsawon kwanaki 40, ta hakan ya nuna musu cewa yana da rai kuma ya ba su ƙarin umurni. (A. M. 1:3-5) Sai ya haura zuwa sama don ya miƙa amfanin hadayarsa mai tamani ga Jehobah kuma ya jira lokacin da bayyanuwarsa a matsayin Sarki Almasihu zai soma. Kafin lokacin, yana da abubuwa da yawa da zai yi.
Ya Kammala Hakkinsa na Almasihu
16, 17. Ka bayyana matsayin Yesu na Almasihu bayan ya hau sama.
16 A dukan tarihi, tun lokacin da ya tashi daga matattu, Yesu da aminci yana kula da ayyukan ikilisiyar Kirista a matsayin Sarki. (Kol. 1:13) A daidai lokacin da aka ƙayyade, zai soma nuna ikonsa a matsayin Sarkin Mulkin Allah. Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da abubuwan da suke faruwa a duniya sun nuna cewa bayyanuwarsa a matsayin Sarki ya soma a shekara ta 1914, lokacin ne “cikar zamani” ya soma. (Mat. 24:3; R. Yoh. 11:15) Ba da daɗewa ba bayan hakan, ya ja-goranci mala’iku masu tsarki suka jefo Shaiɗan da aljanunsa daga sama.—R. Yoh. 12:7-10.
17 Aikin wa’azi da koyarwa da Yesu ya soma a shekara ta 29 A.Z. ya kusan kai ƙarshensa. Ba da daɗewa ba zai yi wa dukan masu rai shari’a. Sa’an nan zai gaya wa masu kama da tumaki waɗanda suka amince da shi a matsayin wanda ta wurinsa Jehobah zai kawo ceto, su “gaji mulkin da an shirya domin [su] tun kafawar duniya.” (Mat. 25:31-34, 41) Za a halaka waɗanda suka ƙi Yesu a matsayin Sarki sa’ad da ya ja-goranci runduna ta samaniya su kawar da dukan mugunta. Sa’an nan Yesu zai ɗaure Shaiɗan kuma ya tura shi da aljannunsa cikin “rami marar-matuƙa.”—R. Yoh. 19:11-14; 20:1-3.
18, 19. Menene Yesu ya cim ma wajen cika hakkinsa a matsayin Almasihu, wane sakamako ne hakan zai kawo ga ’yan adam masu biyayya?
18 A lokacin Sarautarsa na Shekara Dubu, Yesu zai aikata daidai da laƙabinsa, kamar su “al’ajabi, Mai-shawara, Allah mai-iko duka, Uba madawwami, Sarkin Salama.” (Isha. 9:6, 7) ’Yan adam za su zama kamiltattu saboda sarautar Mulkinsa, har da matattu da zai ta da daga matattu. (Yoh. 5:26-29) Almasihu zai ja-goranci ’yan adam da suke a shirye zuwa “maɓulɓulan ruwaye na rai,” hakan zai taimaka wa ’yan adam masu biyayya su more dangantaka na salama da Jehobah. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 7:16, 17.) Bayan gwaji na ƙarshe, dukan masu tawaye, har da Shaiɗan da aljanunsa za a “jefar da [su] cikin ƙorama ta wuta” hakan zai zama ƙuje kan “macijin” har mutuwa.—R. Yoh. 20:10.
19 Yesu ya cika hakkinsa na Almasihu a hanya mai ban mamaki kuma babu kuskure! Aljanna ta duniya za ta cika da ’yan adam da aka ceto, waɗanda za su yi rayuwa har abada da koshin lafiya da kuma farin ciki. Za a kawar da dukan zargi da aka ɗaura wa suna mai tsarki na Jehobah, kuma za a kunita ikon mallakarsa. Lallai wannan gādo ne mai girma da ke jiran dukan waɗanda suka yi biyayya ga Zaɓaɓɓe na Allah!
Ka Sami Almasihun?
20, 21. Waɗanne dalilai kake da su na gaya wa mutane game da Almasihu?
20 Muna cikin lokacin bayyanuwar Kristi tun shekara ta 1914. Ko da yake bayyanuwarsa a matsayin Sarkin Mulkin Allah marar ganuwa ce, a bayyane yake cewa ya riga ya bayyana domin annabce-annabcen da suke cika. (R. Yoh. 6:2-8) Duk da haka, kamar Yahudawa na ƙarni na farko, yawancin mutane a yau sun ƙi tabbacin bayyanuwar Almasihu. Su ma suna son almasihu na siyasa ko kuma wanda zai cece su daga hannun ’yan siyasa masu mulki. Amma, kai ka san cewa Yesu yanzu yana sarauta a matsayin Sarkin Mulkin Allah. Sanin hakan bai burge ka ba? Kamar almajirai na ƙarni na farko, hakan ya motsa ka ka ce: “Mun sami Almasihu.”
21 A yau, sa’ad da kake magana game da gaskiya, kana nanata hakkin Yesu a matsayin Almasihu? Yin hakan zai sa ka ƙara yin godiya ga abin da ya yi dominka, abin da yake yi a yanzu, da abin da zai cim ma a nan gaba. Kamar Andarawas da Filibus, babu shakka ka yi wa danginka da abokai magana game da Almasihu. Me ya sa ba za ka sake tuntuɓarsu da himma ba kuma ka nuna musu cewa Yesu Kristi ne Almasihu da aka yi alkawarinsa, ta wurinsa ne Allah zai kawo ceto?
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Ta yaya almajirai na ƙarni na farko suka samu Almasihu?
• Don waɗanne dalilai biyu masu muhimmanci ne Yesu ya mutu?
•• Menene Yesu zai yi a nan gaba wajen cika hakkinsa a matsayin Almasihu?
[Hotunan da ke shafi na 21]
Ta yaya mutane a ƙarni na farko suka fahimci cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa?
[Hotunan da ke shafi na 23]
Sa’ad da kake yi wa mutane magana, kana nanata hakkin Yesu a matsayin Almasihu kuwa?