Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Satumba p. 11
  • Jehobah Yana Kuɓutar da Waɗanda Suka Fid da Zuciya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Kuɓutar da Waɗanda Suka Fid da Zuciya
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Jehobah “Yakan Warkar da Masu Fid da Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • ‘Yana da Kyau Mu Yi Kusa da Allah!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Jehobah Zai Taimaka Maka Idan Ka Shiga Yanayi Mai Wuya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Satumba p. 11

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Yana Kuɓutar da Waɗanda Suka Fid da Zuciya

A wasu lokuta, mukan yi baƙin ciki. Yin baƙin ciki ba ya nufin cewa ba mu da bangaskiya ga Jehobah. Jehobah ma ya faɗa cewa yakan yi baƙin ciki a wasu lokuta. (Fa 6:5, 6) Idan muna baƙin ciki sosai a kowanne lokaci kuma fa?

Ka nemi taimakon Jehobah. Jehobah ya damu da yadda muke ji. Ya san lokacin da muke farin ciki da baƙin ciki. Ya fahimci dalilin da ya sa muke yin wani tunani da kuma abin da ya sa muke jin wani iri. (Za 7:9b) Abin da ya fi muhimmanci shi ne, Jehobah ya damu da mu kuma zai taimaka mana mu jimre idan muna fama da baƙin ciki ko kuma tsananin damuwa.—Za 34:18.

Ka lura da abin da kake tunani a kai. Yin tunanin da bai dace ba zai iya sa mu baƙin ciki har ma ya shafi dangantakarmu da Jehobah. Saboda haka, zai dace mu kāre tunaninmu.—K. Ma 4:23.

KU KALLI BIDIYON NAN YADDA ꞌYANꞌUWANMU SUKE MORE SALAMA DUK DA TSANANIN DAMUWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne abubuwa ne Nikki ta yi don ta jimre da tsananin damuwa?

  • Me ya sa Nikki ta ga cewa tana bukatar ta nemi taimakon likita?—Mt 9:12

  • A waɗanne hanyoyi ne Nikki ta dogara ga Jehobah ya taimaka mata?

“Hasumiyar Tsaro” Na 1 2023, mai jigo “Lafiyar Kwakwalwa​—Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka?”

Ka san wani ko wata da Hasumiyar Tsaro Na 1 2023 za ta taimaka ma?

Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu rage tsananin damuwa?

(Ka sa maki a akwatin da ke kusa da halayen da za ka so ka kyautata.)

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba