Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 20 pp. 199-208
  • “Mai Zuciyar Hikima”—Amma Kuma Mai Tawali’u

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Mai Zuciyar Hikima”—Amma Kuma Mai Tawali’u
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Jehobah Ya Kasance da Tawali’u
  • Jehobah Yana Ba da Aiki Kuma Yana Sauraro Cikin Tawali’u
  • Jehobah Yana da La’akari
  • Yadda Jehobah Ya Nuna Yin La’akari
  • Ka Koyi Tawali’u Na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Jehovah Ya Bayyana Ɗaukakarsa Ga Masu Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Yesu Ya Kafa Misali Na Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 20 pp. 199-208
Wani mahaifi ya durkusa yana wasa da yaronsa.

BABI NA 20

“Mai Zuciyar Hikima”—Amma Kuma Mai Tawali’u

1-3. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana da tawali’u?

UBA YANA so ya koya wa ɗansa darasi mai muhimmanci. Yana ɗokin ya taɓa zuciyarsa. Yaya zai dumfari yanayin? Zai tsaya ne abin tsoro a kan yaron ya yi masa baƙar magana? Ko kuma zai sunkuya ne zuwa tsayin yaron ya yi masa magana a hankali, a hanya mai kyau? Hakika uba mai hikima zai zaɓi hanyar nan na sauƙin kai.

2 Wane irin Uba ne Jehobah—mai fahariya ne ko mai tawali’u, mai tsanantawa ne ko kuma marar tsanantawa? Jehobah shi ne masanin kome, shi kaɗai ne mai dukan hikima. Amma ka lura cewa, sani da fahimi ba sa mai da mutane masu tawali’u? Yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, “ilimi kuwa yakan kawo ɗaga kai.” (1 Korintiyawa 3:19; 8:1) Amma Jehobah, wanda yake da “zuciyar hikima,” mai tawali’u ne. (Ayuba 9:4) Ka lura cewa wannan ba ya nufin cewa yana da ƙaramin matsayi ko kuma ba shi da iko, amma fahariya ce ba shi da ita. Me ya kawo hakan?

3 Jehobah mai tsarki ne. Saboda haka fahariya, hali da yake ƙazantarwa, babu a gare shi. (Markus 7:20-22) Bugu da ƙari, ka lura da abin da annabi Irmiya ya ce wa Jehobah: “Babu shakka [Jehobah kansa] za ka tuna ka sunkuya a kaina.”a (Makoki 3:20; NW) Ka ji wannan! Jehobah, Ubangiji Mamallakin Dukan halitta, yana shirye ya “sunkuya,” ko kuma ya sauko zuwa matsayin Irmiya, domin ya mai da hankalinsa ga wannan mutumi ajizi. (Zabura 113:7) Hakika, Jehobah mai tawali’u ne. Amma mene ne tawali’u na ibada yake ƙunsa? Ta yaya yake da nasaba da hikima? Kuma me ya sa yake da muhimmanci a gare mu?

Yadda Jehobah Ya Kasance da Tawali’u

4, 5. (a) Mene ne tawali’u, kuma ta yaya yake bayyana, kuma me ya sa bai kamata a rikita shi da kumamanci ko rashin ƙwazo ba? (b) Ta yaya Jehobah ya nuna tawali’u a sha’aninsa da Dauda, kuma yaya muhimmanci tawali’un Jehobah yake a gare mu?

4 Tawali’u ƙasƙantar zuciya ne, rashin taurin kai da fahariya. Hali ne na cikin zuciya, tawali’u yana bayyana a cikin halaye kamar su rashin tsanantawa, haƙuri, da kuma sanin-ya-kamata. (Galatiyawa 5:22, 23) Amma, kada a ɗauki wannan hali na Allah rashin ƙarfi ne ko kuma rashin gaba gaɗi. Suna jituwa da fushi na adalci na Jehobah ko kuma yin amfani da ikonsa na halakarwa. Akasarin haka, ta wajen tawali’unsa da kuma rashin tsanantawa, Jehobah yana nuna ƙarfinsa mai yawa, ikonsa ya kame kansa sarai. (Ishaya 42:14) Ta yaya tawali’u yake da nasaba da hikima? Wani littafin biɗan bayani game da Littafi Mai Tsarki ya lura cewa: “A ƙarshe an ba da ma’anar tawali’u . . . a kan sadaukar da kai kuma cibiya ce mai muhimmanci na dukan hikima.” Saboda haka, hikima ta gaske ba za ta kasance ba ba tare da tawali’u ba. Ta yaya tawali’un Jehobah yake mana amfani?

Uba mai hikima yana bi da ’ya’yansa cikin tawali’u da kuma rashin tsanantawa

5 Sarki Dauda ya rera wa Jehobah waƙa: ‘Ya Yahweh, ka ba ni garkuwar nasara, hannun damanka ya riƙe ni, [tawali’un] ka ya girmama ni.’ (Zabura 18:35) Watau, Jehobah yana sunkuyawa ne domin ya yi sha’ani da wannan mutum ajizi, yana kiyaye shi kuma ya raya shi rana rana. Dauda ya fahimci cewa idan zai samu ceto—kuma idan a ƙarshe zai samu ɗaukaka a zaman sarki—zai kasance ne domin son rai na Jehobah ya sunkuya a wannan hanyar. Hakika, waye a tsakaninmu zai samu begen ceto idan da Jehobah ba mai tawali’u ba ne, wanda yake a shirye ya sunkuya domin ya yi sha’ani da mu na Uba marar tsanantawa mai ƙauna?

6, 7. (a) Me ya sa Littafi Mai Tsarki bai taɓa cewa Jehobah yana da filako ba? (b) Mece ce nasabar da take tsakanin rashin tsanantawa da hikima, kuma wa ya kafa misali mafi girma na wannan?

6 Yana da kyau a lura cewa da akwai bambanci tsakanin tawali’u da filako. Filako hali ne mai kyau da mutane masu aminci za su nema. A ce tawali’u, yana da nasaba da hikima. Alal misali, Karin Magana 11:2, (NW ), ta ce: “Hikima tana ga masu filako.” Amma, Littafi Mai Tsarki bai taɓa yin maganar Jehobah cewa yana da filako ba. Me ya sa? Filako, kamar yadda aka yi amfani da shi a cikin Littafi Mai Tsarki, yana nufin mutum ya sani daidai kasawarsa. Maɗaukaki Duka ba shi da iyaka sai dai waɗanda ya kafa wa kansa domin mizanansa na adalci. (Markus 10:27; Titus 1:2) Bugu da ƙari, tun da shi ne Mafi Girma, ba ya ƙarƙashin kowa. Saboda haka, halin filako bai shafi Jehobah ba.

7 Duk da haka, Jehobah mai tawali’u ne kuma marar tsanantawa. Ya koyar da bayinsa cewa rashin tsanantawa dole ne ga hikima ta gaskiya. Kalmarsa ta yi maganar “sauƙin kai wanda yake fitowa daga cikin hikima.”b (Yakub 3:13) Ka yi la’akari da misalin Irmiya game da wannan.

Jehobah Yana Ba da Aiki Kuma Yana Sauraro Cikin Tawali’u

8-10. (a) Me ya sa abin mamaki ne cewa Jehobah ya nuna son rai wajen ba da aiki da kuma sauraro? (b) Ta yaya Maɗaukaki ya bi da mala’ikunsa da tawali’u?

8 Da akwai tabbacin tawali’un Jehobah a yadda yake ba da aiki ga wasu da son rai kuma ya saurara. Ganin yana haka ma abin mamaki ne; Jehobah ba ya bukatar taimako ko kuma shawara. (Ishaya 40:13, 14; Romawa 11:34, 35) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki a kai a kai ya nuna mana cewa Jehobah yana sauƙowa a hanyoyin nan.

9 Alal misali, ka yi la’akari da abu mai muhimmanci a rayuwar Ibrahim. Ibrahim ya yi baƙi guda uku ya kira ɗaya cikinsu “Jehobah.” Baƙin ainihi mala’iku ne, amma ɗaya cikinsu ya zo cikin sunan Jehobah kuma yana aiki bisa Sunan. Sa’ad da mala’ikan ya yi magana kuma ya yi aiki, hakika, Jehobah ne yake magana kuma yake yin aiki. Ta wannan hanyar, Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa ya ji “kukan mutane game da muguntar Sodom da Gomora ya yi yawa.” Jehobah ya ce: “Zan gangara in gani in bincika ko kukan da ya zo gare ni haka yake.” (Farawa 18:3, 20, 21) Hakika, saƙon Jehobah ba ya nufin cewa shi Maɗaukaki Duka zai “gangara” ko sauka da kansa. Maimakon haka, ya aiko mala’iku su wakilce shi. (Farawa 19:1) Me ya sa? Jehobah mai gani duka ba zai iya “gane” gaskiyar yanayin wannan yankin ba da kansa? Hakika. Amma maimakon haka, Jehobah cikin tawali’u ya bai wa mala’iku aikin bincika wannan yanayi kuma su ziyarci Lutu da iyalinsa a Saduma.

10 Bugu da ƙari, Jehobah yana sauraro. Ya taɓa tambayar mala’ikunsa su ba da shawara game da hanyoyi da za a wulakanta mugun Sarki Ahab. Jehobah ba ya bukatar irin wannan taimakon. Duk da haka, ya yarda da shawarar wani mala’ika kuma ya umurce shi ya yi yadda ya ce. (1 Sarakuna 22:19-22) Wannan ba tawali’u ba ne?

11, 12. Ta yaya Ibrahim ya zo ga fahimtar tawali’un Jehobah?

11 Jehobah yana sauraron mutane ajizai waɗanda suke so su nuna damuwarsu. Alal misali, sa’ad da Jehobah ya gaya wa Ibrahim nufinsa da farko cewa zai halaka Saduma da Gwamarata, wannan mutum mai aminci ya yi mamaki. Ya ce: “Ba zai yiwu ka yi haka ba! Kai da kake mai shari’ar dukan duniya, ba za ka yi shari’a daidai ba?” Ya yi tambaya ko Jehobah zai ƙyale birnin idan da mutane masu adalci guda 150 a cikinsa. Jehobah ya tabbatar masa cewa Zai ƙyale shi. Amma Ibrahim ya sake tambaya, ya rage adadin zuwa 45, zuwa 40, da sauransu. Duk da tabbaci da Jehobah ya bayar, Ibrahim ya ci gaba har sai da ya rage adadin zuwa goma. Wataƙila Ibrahim bai fahimci sosai ba yadda Jehobah yake da jinƙai. Ko da me ya sa, Jehobah ya yi haƙuri da kuma tawali’u ya ƙyale abokinsa kuma bawansa Ibrahim ya furta damuwarsa a wannan hanyar.—Farawa 18:23-33.

12 Mutane masu fahimi guda nawa ne za su iya kasancewa da haƙuri su saurari mutum wanda ba shi da fahimi kamarsu?c Irin wannan ne tawali’un Allahnmu. A lokacin wannan mahawara, Ibrahim ya ga cewa Jehobah ba ya “saurin fushi.” (Fitowa 34:6) Wataƙila fahimtar cewa ba shi da ikon bincika abin da Maɗaukaki yake yi, Ibrahim sau biyu ya yi roƙo: “Kada Ubangiji dai ya yi fushi!” (Farawa 18:30, 32) Hakika, Jehobah bai yi fushi ba. Da gaske, yana da “sauƙin kai mai hikima.”

Jehobah Yana da La’akari

13. Mene ne ma’anar kalmar nan ‘la’akari’ kamar yadda aka yi amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa wannan kalmar ta kwatanta Jehobah daidai?

13 Tawali’un Jehobah ya bayyana har ila cikin wani kyakkyawan hali—la’akari. Abin baƙin ciki wannan halin babu shi a tsakanin mutane ajizai. Ba kawai Jehobah yana so ya saurari halittunsa masu basira ba amma kuma yana shirye ya yarda sa’ad da babu saɓani da mizanai na adalci. Kamar yadda aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki, kalmar nan ‘la’akari’ a zahiri tana nufin “yarda.” Wannan hali ma alama ce ta hikimar Allah. Yakub 3:17 ta ce: “Hikimar da take daga wurin Allah . . . mai sauƙin kai ce.” A wace hanya ce Jehobah mai dukan hikima yake da la’akari? Abu ɗaya shi ne, yana daidaita a kowane yanayi. Ka tuna cewa, sunansa ya koyar da mu cewa Jehobah yana kasance dukan abin da ake bukata domin ya cika nufinsa. (Fitowa 3:14) Wannan bai nuna halin daidaitawa ba da kuma na la’akari?

14, 15. Mene ne wahayin Ezekiyel na keken Jehobah ya koyar da mu game da sashen ƙungiyar Jehobah ta sama, kuma ta yaya ta bambanta da ƙungiyoyin duniya?

14 Da akwai labari na Littafi Mai Tsarki da ya taimake mu muka fara fahimtar daidaita na Jehobah a kowane yanayi. An nuna wa annabi Ezekiyel wahayin sashen ƙungiyar Jehobah ta sama, da ta ƙunshi halittun ruhu. Ya ga keke mai girmar bala’i, “motar” Jehobah da take ƙarƙashin ikonsa kullum. Abin ban mamaki ma yadda take tafiya ne. Manyan ƙafafu huɗu masu kama da zobe sun cika da idanu saboda haka suna iya ganin ko’ina kuma za su iya canja hanya a take, ba tare da sun tsaya ba ko kuma sun juya. Kuma wannan babban keken ba ya bukatar ya yi tafiya da nauyi kamar mota mai nauyi da mutum ya ƙera. Yana iya tafiya kamar walƙiya, kuma ya juya! (Ezekiyel 1:1, 14-28) Hakika, ƙungiyar Jehobah, kamar maɗaukaki Mamallaki da ke riƙe da ita, tana daidaita a kowane yanayi ƙwarai, tana mai da hankali ga yanayi da yake canjawa da kuma bukatu.

15 Mutane sai dai su yi ƙoƙari su yi koyi da irin wannan kamiltacciyar daidaita. Ko da yake, sau da yawa mutane da kuma ƙungiyoyi sun fiye rashin daidaita a yanayi maimakon su daidaita, sun fiye rashin la’akari da yin la’akari. Alal misali: Babban jirgin ruwa ko kuma jirgin ƙasa za su iya kasancewa kyawawa wajen girma kuma da ƙarfi. Amma za su iya canjawa kuwa idan yanayi ya canja farat ɗaya? Idan wani abu ya faɗi a kan hanyar jirgin ƙasa, ba a maganar juyawa. Juyawa a take ba ta yiwuwa da sauƙi. Babban jirgin ƙasa zai yi tafiyar mil guda kafin ya tsaya bayan an taka birki! Hakanan, babban jirgin ruwa zai yi tafiyar mil biyar bayan an kashe inji. Ko ma idan aka saka injin a ribas, jirgin zai ci gaba da tafiya ta mil biyu tukuna! Haka yake da ƙungiyoyi na mutane da ba sa iya canjawa kuma ba sa la’akari. Domin fahariya, mutane sau da yawa suna ƙin daidaitawa da canjin bukatu da kuma yanayi. Irin wannan ya kashe masana’anta har ma ya kifar da gwamnatoci. (Karin Magana 16:18) Muna farin ciki cewa Jehobah da ƙungiyarsa ba haka suke ba!

Yadda Jehobah Ya Nuna Yin La’akari

16. Ta yaya Jehobah ya nuna la’akari a yadda ya yi sha’ani da Lutu kafin a halaka Saduma da Gwamarata?

16 Ka sake yin la’akari da halakar Saduma da Gwamarata. Mala’ikun Jehobah sun ba Lutu da iyalinsa umurni: “Ku gudu zuwa kan tuddai.” Amma, Lutu bai so wannan ba. Ya yi roƙo cewa, ‘A’a ya Jehobah!’ Domin ya tabbata cewa zai mutu idan zai gudu zuwa duwatsu, Lutu ya yi roƙo cewa shi da iyalinsa a ƙyale su su gudu zuwa birni da yake kusa mai suna Zoar. Ka tuna Jehobah ya nufa ya halaka wannan birni. Bugu da ƙari, Lutu ba shi da dalilin gaske na tsorata. Hakika Jehobah zai iya kiyaye ran Lutu a kan duwatsun! Duk da haka, Jehobah ya yarda da roƙon Lutu ya ƙyale Zoar. “To, shi ke nan, na yarda maka, kuma ba zan halaka wannan ƙaramin garin da ka yi magana a kansa tare da sauran wuraren ba,” in ji mala’ikan ga Lutu. (Farawa 19:17-22) Wannan ba yin la’akari ba ne daga Jehobah?

17, 18. Wajen sha’ani da mutanen Nineveh, ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana da la’akari?

17 Jehobah yana amsa tuba ta gaske, kullum yana yin abin da ke jinƙai da kuma daidai. Ka lura da abin da ya faru sa’ad da aka aiki annabi Yunana zuwa mugun birni na Nineveh. Sa’ad da Yunana ya bi cikin birnin Nineveh, huraren saƙo da ya sanar mai sauƙi ne: A cikin kwanaki 40 za a halaka babban birnin. Amma, yanayi ya canja ƙwarai. Mutanen Nineveh suka tuba!—Yona, sura 3.

18 Gwada yadda Jehobah ya ji da yadda Yunana ya ji game da wannan canji zai koyar da mu. A wannan yanayin Jehobah ya daidaita, ya sa kansa ya kasance mai gafarta zunubi maimakon ya zama “gwanin yaƙi.”d (Fitowa 15:3) Yunana kuma, ba shi da daidaita kuma ba shi da jinƙai. Maimakon ya nuna la’akari irin na Jehobah, ya aikata kamar jirgin ƙasa ko kuma babban jirgin ruwa da aka ambata da farko. Ya riga ya sanar da halaka, saboda haka dole halaka ta kasance! Amma cikin haƙuri Jehobah ya koyar da annabinsa marar haƙuri darasi da ba zai manta ba na yin la’akari da kuma jinƙai.—Yona, sura 4.

Wani dan’uwa matashi yana farin cikin taimaka ma wani dan’uwa tsoho a wa’azi.

Jehobah yana da la’akari kuma ya fahimci kasawarmu

19. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana la’akari da abin da yake bukata a gare mu? (b) Ta yaya Karin Magana 19:17 ta nuna cewa Jehobah Shugaba ne na “kirki kuma mai la’akari” kuma da tawali’u mai girma?

19 Na ƙarshe, Jehobah yana la’akari wajen abin da yake bukata a gare mu. Sarki Dauda ya ce: “Ya san abin da aka yi mu da shi, yana kuma tuna cewa mu ƙurar ƙasa ne.” (Zabura 103:14) Jehobah yana fahimtar kasawarmu da kuma ajizancinmu fiye da mu kanmu. Ba ya neman abin da ba za mu iya yi ba a gare mu. Littafi Mai Tsarki ya bambanta waɗannan shugabannai “masu kirki da masu sauƙin kai” da waɗanda su “marasa tausayi” ne. (1 Bitrus 2:18) Jehobah wane irin Shugaba ne? Ka lura da abin da Karin Magana 19:17 ta ce: “Mai yi wa masu talaka kirki, kamar ya ba Yahweh rance ne.” Hakika, sai dai shugaba na kirki ne zai lura da dukan kirki da aka yi wa fakirai. Fiye ma da haka, nassosi sun nuna cewa Mahaliccin dukan halitta, watau, yana ganin mutane da suka yi ayyukan jinƙai suna bin sa bashi! A nan ga tawali’u mai girma ƙwarai.

20. Wane tabbaci ne da akwai cewa Jehobah yana sauraron addu’o’inmu kuma yana amsa su?

20 Jehobah hakanan yana da la’akari kuma ba ya tsanantawa ga bayinsa a yau. Sa’ad da muka yi addu’a cikin bangaskiya yana sauraronmu. Kuma da yake ba ya aika da mala’iku su yi magana da mu, kada mu ce ba ya amsa addu’o’inmu. Ka tuna cewa sa’ad da manzo Bulus ya ce ’yan’uwa mabiya su “yi addu’a” domin a sake shi daga fursuna, ya daɗa cewa: “Domin Allah ya sa in koma gare ku ba da daɗewa ba.” (Ibraniyawa 13:18, 19) Saboda haka, wataƙila addu’o’inmu za su motsa Jehobah ya yi abin da ƙila ba zai yi ba!—Yakub 5:16.

21. Wace kammala ce kada mu taɓa yi game da tawali’un Jehobah, maimakon haka, mene ne ya kamata mu fahimta game da shi?

21 Hakika, babu ɗaya cikin waɗannan nunin tawali’un Jehobah—rashin tsanantawarsa, sauraronsa da son rai, haƙurinsa, da kuma yin la’akarinsa—da yake nufin Jehobah yana barin mizanansa na adalci. Limaman Kiristendam wataƙila suna yin tunanin cewa suna yin la’akari ne sa’ad da suke sosa kunnuwan tumakinsu ta wajen rage muhimmancin mizanan ɗabi’a na Jehobah. (2 Timoti 4:3) Halin mutane na son rage muhimmancin ɗabi’a saboda wata dabara, ba abin da ya haɗa shi da yin la’akari na Allah. Jehobah yana da tsarki; ba zai taɓa ƙazantar da mizanansa masu adalci ba. (Littafin Firistoci 11:44) Saboda haka, bari mu ƙaunace yin la’akari na Jehobah domin yadda yake—tabbacin tawali’unsa. Ba ka farin ciki ka yi tunanin Jehobah Allah, mafi hikima a dukan sararin sama, cewa ya bambanta wajen tawali’u? Abin farin ciki ne mu kusaci wannan Allah mai ban tsoro har ila kuma marar tsanantawa, mai haƙuri, mai la’akari!

a Marubuta na dā, ko kuma Soferim, sun canja wannan ayar ta ce Irmiya ne ba Jehobah ne ya sunkuya ba. Babu shakka suna tunanin cewa bai dace ba a ce Allah ya yi irin wannan tawali’u. Domin wannan, yawancin fassara ba su fahimci batun wannan kyakkyawar aya ba. Amma dai, The New English Bible ya fassara shi daidai Irmiya yana cewa Allah: “Ka tuna, ka tuna, ka sunkuya zuwa gare ni.”

b Wasu fassara suka ce “tawali’u da yake zuwa daga hikima” ne da kuma “sauƙin kai da alamar hikima ce.”

c Littafi Mai Tsarki ya bambanta haƙuri da fahariya. (Mai Wa’azi 7:8) Haƙurin Jehobah ya ba da ƙarin tabbacin tawali’unsa.—2 Bitrus 3:9.

d A Zabura 86:5, an ce Jehobah “mai alheri ne kuma mai yin gafara.” Sa’ad da aka fassara wannan zaburar zuwa Helenanci, furcin nan “mai yin gafara” aka fassara shi e·pi·ei·kesʹ, ko kuma “mai la’akari.”

Tambayoyi don Bimbini

  • Fitowa 32:9-14 Ta yaya Jehobah ya nuna tawali’u wajen amsa roƙon Musa domin Isra’ila?

  • Alƙalai 6:36-40 Ta yaya Jehobah ya nuna haƙuri da la’akari wajen amsa roƙon Gideon?

  • Zabura 113:1-9 Ta yaya Jehobah ya nuna tawali’u wajen yin sha’ani da ’yan Adam?

  • Luka 1:46-55 Maryamu ta yarda cewa Jehobah yana da wane ra’ayi ne game da mutane masu tawali’u da kuma fakirai? Yaya ra’ayinsa ya kamata ya shafe mu?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba