WAƘA TA 114
Ku Kasance Masu “Haƙuri”
Hoto
(Yaƙub 5:8)
1. Jehobah Allah ne da
Yake son sunansa sosai.
Kuma burinsa shi ne
Ya tsarkake sunansa fa.
Ya jima yana nuna
Haƙuri har da ƙauna,
Amma ba ya jinkiri
Don shi mai ƙauna ne.
Yana son duk mu tsira
Shi ya sa yake haƙuri.
Yana ba wa mutane
Damar canja hanyoyinsu.
2. Halinmu na haƙuri
Zai sa mu riƙe aminci.
Zai sa mu farin ciki,
Zai sa mu daina yin fushi.
Zai sa mu riƙa nuna
Ƙauna ga duk mutane,
Idan muna wahala
Zai taimaka mana.
Allahnmu yana so mu
Kasance da halayensa.
In muna yin haƙuri
Muna bin misalin Allah.
(Ka kuma duba Fit. 34:14; Isha. 40:28; 1 Kor. 13:4, 7; 1 Tim. 2:4.)