Ka Daraja Halayen Jehobah Na Karimci Da Sanin Yakamata
“Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane; Jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.”—ZAB. 145:9.
1, 2. Wane zarafi ne abokan Jehobah suke da shi?
WATA ’yar’uwa mai suna Monika ta ce: “Mun yi shekara 35 da aure, kuma ni da mijina mun san juna sosai. Amma har ila, muna kan koyon abubuwa da ba mu taɓa sani game da juna ba.” Babu shakka, abin da yawancin ma’aurata za su faɗa ke nan game da junansu ko kuma abokansu.
2 Muna jin daɗin ƙara sanin waɗanda muke ƙauna. Amma, babu abokantaka da ta kai wadda ke tsakaninmu da Jehobah muhimmanci. Ba zai yiwu mu san kome-da-kome game da shi ba. (Rom. 11:33) Za mu samu zarafin ci gaba da koya game da halayen Jehobah har abada, kuma mu daraja su sosai.—M. Wa. 3:11.
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A talifin da ya gabata, mun tattauna sosai game da halayen Jehobah guda biyu. Mun koyi cewa yana da sauƙi a kusace shi, kuma ba ya son kai. A wannan talifin, za mu koyi wasu halayensa guda biyu kuma, wato karimci da sanin yakamata. Ta hakan za mu san cewa Jehobah “mai-alheri ne ga dukan mutane, jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.”—Zab. 145:9.
JEHOBAH KARIMI NE
4. Mene ne karimci?
4 Mene ne karimci? Kalaman Yesu da ke littafin Ayyukan Manzanni 20:35, sun ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” Mutum mai karimci yana farin cikin ba da lokacinsa da ƙarfinsa da kuma abubuwan da yake da su don ya taimaki wasu. Mutum mai karimci yana bayarwa da zuciya ɗaya, kuma ba sai ya ba da kyauta masu tsada ba. (Karanta 2 Korintiyawa 9:7.) Babu wanda ya kai Allahnmu Jehobah karimci.
5. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake nuna karimci?
5 Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi karimi ne? Yana biyan bukatun ’yan Adam, har da waɗanda ba sa bauta masa. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane.’ Domin “ya kan sa ranatasa ta fito wa miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Mat. 5:45) Shi ya sa manzo Bulus ya gaya wa waɗanda ba Kiristoci ba cewa, Jehobah “yana yin alheri, yana ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi, yana cika zukatanku da abinci da farinciki.” (A. M. 14:17) Hakika, Jehobah yana nuna karimci ga kowa.—Luk 6:35.
6, 7. (a) Su waye ne Jehobah yake farin cikin biyan bukatunsu? (b) Wane misali ne ya nuna cewa Jehobah yana biyan bukatun mutanensa?
6 Jehobah yana farin cikin tanadar wa mutanensa bukatunsu. Sarki Dauda ya ce: “Dā yaro na ke, yanzu kuwa na tsufa, amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.” (Zab. 37:25) Kiristoci masu aminci da yawa sun ga tabbacin hakan. Ga wani misali.
7 A ’yan shekarun da suka shige, wata majagaba mai suna Nancy da take aiki a wurin sayar da abinci ta sami kanta a wani yanayi mai wuya. Ta ce: “Ina bukatar dalla 66 don in biya kuɗin haya washegari, kuma ban san yadda zan samu kuɗin ba. Na yi addu’a game da wannan matsalar, kuma bayan hakan, sai na tafi wurin aiki. Ban yi tsammanin mutane za su ba ni kyauta da yammar ba, domin lokaci ne a mako da ba ma cika yin ciniki. Na yi mamaki sa’ad da muka yi ciniki sosai a daren nan. Sa’ad da na gama aikina na ranar, sai na ƙirga kuɗin da aka ba ni kyauta kuma na ga cewa adadinsa dalla 66 ne.” Nancy ta tabbata cewa Jehobah ne ya biya bukatanta.—Mat. 6:33.
8. Mece ce kyauta mafi tamani da Jehobah ya ba da?
8 Kowane mutum zai iya amfana daga kyauta mai tamani da Jehobah ya bayar. Wace kyauta ce wannan? Hadayar fansa na Ɗansa. Yesu ya ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) “Duniya” da aka ambata a nan tana nufin dukan ’yan Adam. Jehobah ya ba da wannan kyautar mai tamani ga dukan waɗanda suke so. Waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu, za su samu rai madawwami. (Yoh. 10:10) Wannan ne babban tabbaci cewa Jehobah karimi ne.
KA RIƘA YIN KARIMCI KAMAR JEHOBAH
9. Ta yaya za ka riƙa yin karimci kamar Jehobah?
9 Ta yaya za ka riƙa yin karimci kamar Jehobah? Tun da yake Jehobah ya “ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu,” ya kamata mu ma mu kasance da niyyar ba wasu kyauta domin su yi farin ciki. (1 Tim. 6:17-19) Muna farin cikin ba abokanmu da iyalanmu kyauta da kuma taimaka wa mabukata. (Karanta Kubawar Shari’a 15:7.) Mene ne zai taimaka mana mu tuna cewa muna bukatar mu nuna karimci? Waɗansu sun tsai da shawara cewa, a duk lokacin da aka yi musu kyauta, su ma za su nemi zarafin yi wa wani dabam kyauta. Mutanen Jehobah da yawa suna kafa misali wajen nuna karimci.
10. A wace hanya ce za mu iya nuna karimci?
10 Hanya ɗaya da za mu iya nuna karimci ita ce, ta yin amfani da lokacinmu da kuma ƙarfinmu don mu taimaka da kuma ƙarfafa wasu. (Gal. 6:10) Shin kana yin hakan kuwa? Za ka iya tambayar kanka: ‘Ina a shirye in saurari wasu kuwa? Idan wani yana so in taimaka masa ko kuma in taya shi karɓo wani abu, shin ina taimakawa kuwa? Yaushe ne na yaba wa wani a cikin iyalinmu ko kuma wani ɗan’uwa?’ Idan muna ‘bayarwa,’ za mu ƙara kusantar Jehobah da kuma abokanmu sosai.—Luk 6:38; Mis. 19:17.
11. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna karimci ga Jehobah?
11 Za mu kuma iya nuna karimci ga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa mu ‘girmama Ubangiji da wadatarmu.’ (Mis. 3:9) Waɗannan ‘wadatarmu’ sun ƙunshi lokacinmu da ƙarfinmu da kuma kuɗaɗen da za mu iya yin amfani da su a hidimarsa. Yara ƙanana ma za su iya nuna karimci ga Jehobah. Wani mahaifi mai suna Jason ya ce: “Idan muna so mu ba da gudummawa a matsayin iyali a Majami’ar Mulki, mukan ba ’ya’yanmu kuɗin su saka a cikin akwatin gudummawa. Suna farin cikin yin hakan domin sun san cewa suna ba da gudummawar ga Jehobah ne.” Sa’ad da yara suka fahimci cewa za su yi farin ciki idan suka ba Jehobah wani abu, za su ci gaba da yin hakan sa’ad da suka girma.—Mis. 22:6.
JEHOBAH MAI SANIN YAKAMATA NE
12. Mene ne sanin yakamata?
12 Wani halin Jehobah mai kyau shi ne sanin yakamata. Mene ne sanin yakamata? (Tit. 3:1, 2) Mutum mai sanin yakamata ba ya nace wa ra’ayinsa. Ba ya ƙi ƙememe cewa sai an bi wata doka a kowane lokaci. Kuma bai da zafin hali. Yana bi da mutane a hanya mai kyau kuma yana ƙoƙari ya fahimci yanayinsu. Yana a shirye ya saurari wasu, kuma ya bi ra’ayinsu idan hakan ya dace.
13, 14. (a) Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi mai sanin yakamata ne? (b) Mene ne ka koya game da kasancewa da sauƙin hali daga yadda Jehobah ya bi da Lutu?
13 Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi mai sanin yakamata ne? Yana la’akari da yadda bayinsa suke ji, kuma yana yawan ƙyale su su yi abu yadda suke so. Alal misali, ka yi tunani a kan yadda Jehobah ya bi da Lutu, mutum mai aminci. Sa’ad da Jehobah yake so ya halaka birnin Saduma da Gwamrata, ya gaya wa Lutu ya gudu zuwa tuddai. Amma, saboda wasu dalilai, Lutu ya roƙi Jehobah ya ƙyale shi ya je wani wuri dabam. Abin mamaki, Lutu yana so Jehobah ya canja umurninsa!—Karanta Farawa 19:17-20.
14 Wasu za su iya cewa bangaskiyar Lutu ta yi sanyi ko kuma ya yi rashin biyayya. Bai kamata Lutu ya ji tsoro ba, domin Jehobah zai iya rayar da shi. Duk da haka, Lutu ya ji tsoro. Amma, Jehobah ya ƙyale Lutu ya gudu zuwa wani birni dabam, ko da yake Jehobah ya so ya halaka wannan birnin. (Karanta Farawa 19:21, 22.) Hakika, hakan ya nuna cewa Jehobah bai da zafin hali, kuma yana da sanin yakamata a ko yaushe.
15, 16. Ta yaya Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta nuna cewa Jehobah mai sanin yakamata ne? (Ka duba hoton da ke shafi na 12.)
15 Dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa ta kuma nuna cewa shi mai sanin yakamata ne. Alal misali, duk Ba’isra’ile da ba zai iya kawo tunkiya ko kuma akuya don hadaya ba, zai iya kawo kurciya ko kuma tantabara. Amma, idan mutum ya talauce sosai har da ba zai iya kawo waɗannan abubuwan ba, Jehobah ya ƙyale shi ya ba da gari mai-laushi. Ka lura cewa wajibi ne garin ya zama “mai-laushi,” irin wanda ake ba manyan baƙi. (Far. 18:6) Ta yaya waɗannan misalan suka nuna cewa Jehobah yana da sanin yakamata?—Karanta Levitikus 5:7, 11.
16 A ce kai Ba’isra’ile ne kuma talaka talas. Yayin da ka shigo cikin mazauni don ka ba da hadaya da ɗan garinka, sai ka ga wasu Isra’ilawa da suka fi ka kuɗi suna ba da hadaya da dabbobi. Kana iya jin kunya don ɗan hadayar da ka kawo. Amma, ka tuna cewa a gaban Jehobah, hadayar da ka ba da tana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Domin Dokar Jehobah tana bukatar “gari mai-laushi,” wato gari mai kyau sosai. Kamar dai Jehobah yana gaya maka cewa: ‘Na san ba za ka iya ba da irin hadayar da wasu suka ba da ba, amma, ka ba ni abin da za ka iya bayarwa.’ Hakika, wannan misalin ya nuna cewa Jehobah mai sanin yakamata ne. Ba ya bukatar bayinsa su ba da abin da ya fi ƙarfinsu.—Zab. 103:14.
17. Wace irin hidima ce Jehobah yake so?
17 Muna samun ƙarfafa sani cewa Jehobah yana da sanin yakamata, kuma yana amincewa da hidimarmu idan muka yi iya ƙoƙarinmu. (Kol. 3:23) Wata ’yar’uwa tsohuwa ’yar Italiya mai suna Constance ta ce: “Na fi son tattauna da mutane game da Mahaliccina. Shi ya sa na ci gaba da yin wa’azi da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. A wasu lokatai, ina yin nadama don ba zan iya yin hakan da ƙwazo sosai ba sanadiyyar rashin lafiya. Kuma na san cewa Jehobah ya san kasawata, yana ƙaunata kuma yana farin ciki da abin da na iya yi.”
KA ZAMA MAI SANIN YAKAMATA KAMAR JEHOBAH
18. A wace hanya ɗaya ce iyaye za su iya yin koyi da misalin Jehobah?
18 Ta yaya za mu zama masu sanin yakamata kamar Jehobah? Ka sake yin tunani game da yadda Jehobah ya bi da Lutu. Jehobah yana da iko ya gaya wa Lutu wurin da ya kamata ya je. Amma, Jehobah yana da kirki, shi ya sa ya saurari Lutu yayin da yake bayyana yadda yake ji, kuma ya ƙyale Lutu ya tafi inda yake so. Idan kana da yara, shin za ka iya yin koyi da misalin Jehobah? Wataƙila za ka iya sauraron yaranka, kuma ka biya bukatarsu, idan hakan ya dace. Ta yaya za ka yi hakan? Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 2007, ta ce sa’ad da wasu iyaye suke so su kafa doka don iyalin, suna ƙarfafa yaransu su furta ra’ayinsu. Alal misali, iyaye suna iya kafa doka game da lokacin da suke so yaran su dawo gida da yamma. Ko da yake iyaye suna da ikon yin hakan, amma suna iya tattaunawa da yaransu kafin su faɗi lokacin. A wasu yanayi, iyaye suna iya canja lokacin da suke so yaran su kasance a gida, idan hakan ya dace. Idan iyaye suka tattauna da yaransu kafin su kafa dokoki, yaran za su fi fahimtar dokokin kuma su kasance a shirye su bi su.
19. Ta yaya dattawa za su yi ƙoƙari su kasance da sanin yakamata kamar Jehobah?
19 Ya kamata dattawa su yi ƙoƙari su kasance da sanin yakamata kamar Jehobah. Suna iya yin hakan ta wajen yin la’akari da yanayin ’yan’uwansu. Ka tuna cewa Jehobah ya daraja hadayun da Isra’ilawa talakawa suka ba da. Hakazalika, wasu ’yan’uwa ba za su iya daɗewa sosai a hidima ba, wataƙila domin rashin lafiya ko kuma tsufa. Idan sun yi sanyin gwiwa domin kasawarsu kuma fa? Dattawa za su iya taimaka musu su fahimci cewa Jehobah yana ƙaunarsu don suna yin iya ƙoƙarinsu a hidimarsa.—Mar. 12:41-44.
20. Mene ne yake nufi mu kasance da sanin yakamata a hidimar Allah?
20 Hakika, kasancewa da sanin yakamata ba ya nufin ƙin yin hidimarmu ga Jehobah domin muna tausaya wa kanmu ba. (Mat. 16:22) Bai kamata mu ƙi kasancewa da ƙwazo ba, idan za mu iya yin hakan. Maimakon haka, dukanmu muna bukatar mu “yi ƙoƙari” sosai wajen yin hidimar Mulki. (Luk 13:24) Hakika, muna bukatar mu kasance da daidaita. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu a hidimar Jehobah kuma mu tuna cewa ba ya son mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Idan muka yi hakan, muna da tabbaci cewa zai yi farin ciki. Abin ban al’ajabi ne cewa muna bauta wa irin wannan Allah mai sanin yakamata! A talifi na gaba, za mu tattauna wasu halaye biyu na Jehobah masu kyau.—Zab. 73:28.