Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 9/15 pp. 13-17
  • ‘Ka Tsaya da Karfi Cikin Imani’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Tsaya da Karfi Cikin Imani’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA BA DA GASKIYA CEWA ALLAH ZAI TAIMAKE KA
  • SHAKKA ZA TA IYA JAWO RASHIN BANGASKIYA
  • KA BI KOYARWAR YESU DON KA KARFAFA BANGASKIYARKA
  • “Ka Kara Mana Bangaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Da Gaske Ka Ba Da Gaskiya Ga Bisharar?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Bangaskiya​—Tana Sa Mu Kasance da Karfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 9/15 pp. 13-17
Yayin da wasu almajirai suke kokari su tuka kwalekwalensu sa’ad da ake iska, Bitrus ya sauka daga kwalekwalen kuma ya soma tafiya a kan ruwa

‘Ka Tsaya da Karfi Cikin Imani’

“Ku tsaya da karfi cikin imani, . . . ku karfafa.” —1 KOR. 16:13.

WAKOKI: 60, 64

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa bangaskiya take da tamani?

  • Ta yaya za mu san cewa mun soma sanyin gwiwa?

  • Me ya sa mai da hankali ga Yesu zai karfafa bangaskiyarmu?

1. (a) Mene ne ya faru da Bitrus sa’ad da ake wata guguwar iska a Tekun Galili? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me ya sa Bitrus ya soma nitsewa?

MANZO BITRUS da wasu almajirai suna kokari su tuka kwalekwalensu zuwa hayin Tekun Galili da daddare yayin da ake wata guguwar iska. Farat ɗaya, sai suka ga Yesu yana tafiya a kan teku. Bitrus ya kira Yesu kuma ya ce yana so ya taka zuwa inda yake. Sa’ad da Yesu ya gaya masa ya zo, sai Bitrus ya fita daga cikin kwalekwalen kuma ya soma takawa zuwa inda Yesu yake. Hakan abin al’ajabi ne. Amma jim kaɗan, sai Bitrus ya soma nitsewa. Me ya sa? Ya mai da hankali ga guguwar iska kuma ya tsorata. Bitrus ya ta da murya don a cece shi. Yesu ya mika hannu ya kama shi kuma ya ce: ‘Kai mai-kankantar bangaskiya, don me ka yi shakka?’—Mat. 14:24-32.

2. Mene ne za mu tattauna yanzu?

2 Bari mu tattauna wasu abubuwa uku game da labarin Bitrus da suka shafi bangaskiya: (1) yadda Bitrus da farko ya ba da gaskiya cewa Allah zai tallafa masa, (2) dalilin da ya sa Bitrus ya soma shakka, da kuma (3) abin da ya taimaka wa Bitrus ya sake kasancewa da bangaskiya. Yin nazarin waɗannan batutuwan zai taimaka mana mu san yadda za mu iya “tsaya da karfi cikin imani.”—1 Kor. 16:13.

KA BA DA GASKIYA CEWA ALLAH ZAI TAIMAKE KA

3. Me ya sa Bitrus ya sauka daga cikin kwalekwale, kuma wane mataki ne muka ɗauka kamar Bitrus?

3 Bitrus yana da bangaskiya sosai don sa’ad da Yesu ya kira shi, Bitrus ya sauka daga cikin kwalekwalen kuma ya soma tafiya a kan ruwa. Ya tabbata cewa ikon Allah zai taimaka masa yadda ya taimaka wa Yesu. Hakazalika, sa’ad da muka ba da kanmu ga Jehobah kuma muka yi baftisma, mun yi imani cewa Allah zai tallafa mana. Yesu ya ce mu zama almajiransa kuma mu bi sawunsa. Mun yi imani cewa Allah da Yesu za su tallafa mana a hanyoyi dabam-dabam.—Yoh. 14:1; karanta 1 Bitrus 2:21.

4, 5. Me ya sa bangaskiya take da tamani sosai?

4 Bangaskiya tana da tamani sosai. Bitrus ya kasance da bangaskiya kuma ya yi tafiya a kan ruwa, abin da ɗan Adam ba zai iya yi ba. Hakazalika, bangaskiya za ta taimaka mana mu yi abin da muke gani ba zai yiwu ba. (Mat. 21:21, 22) Alal misali, da yawa daga cikinmu sun bar halaye da kuma ayyukan banza da suke yi a dā kuma hakan ya sa waɗanda suka san su a dā suna mamaki sosai. Jehobah ne ya taimaka mana mu ɗauki waɗannan matakan don bangaskiya da muka nuna a gare shi. (Karanta Kolosiyawa 3:5-10.) Bangaskiyarmu ce ta sa muka ba da kanmu ga Jehobah kuma muka zama abokansa. In da ba da taimakonsa ba, da ba za mu iya ɗaukan wannan matakin ba.—Afis. 2:8.

5 Bangaskiyarmu tana taimaka mana sosai. Alal misali, tana taimaka mana mu yi tsayayya da babban makiyinmu Iblis. (Afis. 6:16) Kari ga haka, da yake mun dogara ga Jehobah, ba ma yawan damuwa sa’ad da muke fuskanta matsaloli. Jehobah ya ce idan muka kasance da bangaskiya kuma muka saka al’amuran mulki kan gaba a rayuwarmu, zai tanadar mana da abubuwan da muke bukata. (Mat. 6:30-34) Ban da haka, bangaskiyarmu za ta sa Jehobah ya ba mu kyautar rai na har abada.—Yoh. 3:16.

SHAKKA ZA TA IYA JAWO RASHIN BANGASKIYA

6, 7. (a) Da mene ne za mu iya kwatanta guguwar iska da rakuman ruwa da Bitrus ya fuskanta? (b) Me ya sa ya kamata mu fahimci cewa za mu iya rashin bangaskiya?

6 Za mu iya kwatanta rakuman ruwa da guguwar iska da Bitrus ya fuskanta sa’ad da yake tafiya a kan ruwa da matsaloli da kuma gwajin da muke fuskanta a matsayinmu na bayin Allah. Za mu iya kasancewa da karfin zuciya cewa Jehobah zai taimaka mana ko da matsaloli masu tsanani ne. Mu tuna cewa ba guguwar iskar ko kuma rakumin ruwa ne ya sa Bitrus ya nitse ba. Labarin ya ce: “Sa’anda ya ga iska, ya ji tsoro.” (Mat. 14:30) Bitrus ya daina kallon Yesu shi ya sa ya soma shakka. Hakazalika, idan muka soma damuwa ainun saboda matsalolin da muke fuskanta, za mu soma shakka ko Jehobah zai taimaka mana.

7 Wajibi ne mu fahimci cewa za mu iya rashin bangaskiya don Littafi Mai Tsarki ya ce rashin bangaskiya ‘zunubi’ ne da za mu iya yi da sauki. (Ibran. 12:1) Abin da ya faru da Bitrus ya nuna cewa za mu iya soma shakka nan da nan idan mun mai da hankali ga matsaloli da gwaji ko kuma wasu abubuwan da ba su dace ba. Ta yaya za mu iya sanin cewa mun soma shakka? Ka yi la’akari da wasu tambayoyi da za su taimaka mana mu bincika kanmu.

8. Ta yaya za mu iya soma shakkar alkawuran Allah?

8 Shin ina ba da gaskiya ga alkawuran Allah kamar yadda na yi a dā? Alal misali, Allah ya yi alkawari cewa zai halaka wannan mugun zamanin. Duk da haka, idan muka soma barin nishaɗi dabam-dabam na duniya su raba hankalinmu, za mu iya soma shakka ko karshen zai zo. (Hab. 2:3) Ga wani misali kuma. Jehobah ya tanadar da fansa don ya gafarta mana zunubanmu. Amma idan muka soma yawan damuwa game da zunuban da muka yi a dā, hakan zai iya sa mu soma shakka ko Jehobah ya gafarta mana zunubanmu da gaske. (A. M. 3:19) Saboda haka, za mu soma bakin ciki har ma mu daina zuwa taro ko kuma fita wa’azi.

9. Mene ne zai iya faruwa idan muka mai da hankali ga abubuwan da muke so?

9 Ina bauta wa Jehobah da kwazo kamar yadda na yi a dā? Manzo Bulus ya nuna cewa idan muna da kwazo a hidimar Jehobah, za mu kasance da ‘tabbataccen bege har karshe.’ Amma, mene ne zai iya faruwa idan muka soma mai da hankali ga abubuwan da muke so? Alal misali, idan muka soma aiki da ake biyan albashi mai tsoka amma ba ma samun lokacin bauta wa Jehobah, hakan zai sa mu soma shakka kuma mu “yi nauyin jiki” kuma mu daina bauta wa Jehobah da kwazo.—Ibran. 6:10-12.

10. Ta yaya muke nuna cewa mun ba da gaskiya ga Jehobah sa’ad da muka gafarta wa mutane?

10 Gafarta wa waɗanda suka ɓata min rai yana min wuya ne? Sa’ad da wasu suka ɓata mana rai, za mu iya jin haushi sosai har mu yi musu bakar magana ko kuma mu daina musu magana gaba ɗaya. Amma idan muka gafarta musu, muna nuna cewa mun ba da gaskiya ga Jehobah. Ta yaya? Waɗanda suka yi mana zunubi tamkar sun ci bashinmu ne kamar yadda muka ci bashin Jehobah saboda zunubanmu. (Luk. 11:4) Sa’ad da muka gafarta wa wasu zunubansu, Jehobah zai albarkace mu kuma hakan ya fi sa wani ya sha wahala kamar yadda muka sha sa’ad da ya ɓata mana rai. Almajiran Yesu sun san cewa kasancewa da bangaskiya zai taimaka mana mu gafarta wa mutane. Sa’ad da Yesu ya gaya musu cewa su rika gafarta wa waɗanda suke musu zunubi, sai suka ce masa: “Ka kara mana bangaskiya.”—Luk. 17:1-5.

11. Me zai iya hana mu amfana daga gargaɗin Littafi Mai Tsarki?

11 Ina ɓata rai ne idan aka yi min gargaɗi? Za mu iya soma tunani cewa gargaɗin bai dace ba ko kuma mu mai da hankali ga laifuffukan wanda yake ba mu gargaɗin a maimakon yadda gargaɗin zai amfane mu. (Mis. 19:20) Bai kamata mu yi hakan ba don wannan gargaɗin dama ce na daidaita ra’ayinmu da na Allah.

12. Mene ne yawan gunaguni game da waɗanda Allah yake amfani da su don yi wa mutanensa ja-gora yake nuna wa?

12 Shin ina gunaguni da ’yan’uwa da aka naɗa a cikin ikilisiya ne? Sa’ad da Isra’ilawa suka mai da hankali ga rahoto mara daɗi da ’yan leken asiri marasa aminci goma suka bayar, sai suka soma yi wa Musa da Haruna gunaguni. Sai Jehobah ya tambayi Musa cewa: ‘Har yaushe kuma za su ki gaskanta ni’? (Lit. Lis. 14:2-4, 11) Hakika, gunagunin da Isra’ilawa suka yi ya nuna cewa ba su ba da gaskiya ga Allah da ya naɗa Musa da Haruna ba. Hakazalika, idan muna yin gunaguni wa waɗanda Allah yake amfani da su don ya ja-goranci mutanensa, zai nuna cewa bangaskiyarmu ta karaya.

13. Me ya sa bai kamata mu karaya ba idan muka lura cewa muna bukata mu karfafa bangaskiyarmu?

13 Duk da haka, idan binciken da ka yi ya nuna cewa kana bukatar karfafa bangaskiyarka, kada ka karaya. Bitrus manzo ne, amma ya ji tsoro kuma ya yi shakka. A wasu lokatai ma Yesu ya tsauta wa almajiransa don “kankantar bangaskiya” da suka nuna. (Mat. 16:8) Ka lura cewa darasi mai muhimmanci da muka koya game da abin da ya faru da Bitrus shi ne abin da ya yi bayan ya yi shakka kuma ya soma nitsewa cikin teku.

KA BI KOYARWAR YESU DON KA KARFAFA BANGASKIYARKA

14, 15. (a) Mene ne Bitrus ya yi sa’ad da ya soma nitsewa? (b) Ta yaya za mu “zuba ido” ga Yesu da yake ba ma ganin sa?

14 Shin mene ne Bitrus ya yi sa’ad da ya kalli guguwar iska kuma ya soma nitsewa? Da yake Bitrus ya iya ruwa, da ya yi iyo zuwa inda kwalekwalen yake. (Yoh. 21:7) A maimakon ya ceci kansa, ya sake mai da hankali ga Yesu don Yesu ya ceci shi. Idan muka lura cewa mun soma rashin bangaskiya, ya kamata mu yi koyi da Bitrus. Amma ta yaya za mu yi hakan?

15 Kamar yadda Bitrus ya mai da hankali ga Yesu, wajibi ne mu “zuba ido ga Yesu.” (Ibran. 12:2, 3) Ko da yake, ba za mu iya ganin Yesu ido da ido ba kamar yadda Bitrus ya gan shi ba. A maimakon haka, muna “zuba ido” ga Yesu ta wajen yin nazarin koyarwarsa da halayensa da kuma yin koyi da shi. Bari mu tattauna wasu matakai da za mu iya ɗaukawa don mu bi misalinsa. Idan muka bi waɗannan matakan, Allah zai taimaka mana kuma zai karfafa bangaskiyarmu.

Bitrus yana tafiya a kan ruwa; an karfafa bangaskiyar wata mata

Idan muka yi koyi da misalin da Yesu kuma muka bi sawunsa, za mu karfafa bangaskiyarmu (Ka duba sakin layi na 15)

16. Ta yaya za mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki a yadda zai karfafa bangaskiyarmu?

16 Ka karfafa bangaskiyar ka ga Littafi Mai Tsarki. Yesu ya ba da gaskiya cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne kuma yana tanadar da ja-gorar mafi kyau don zaman rayuwa. (Yoh. 17:17) Saboda haka, wajibi ne mu karanta Littafi Mai Tsarki, mu yi nazarinsa kuma mu yi bimbini a kan abin da muka koya. Ka yi bincike sosai don ka sami amsoshin ga wasu tambayoyin da kake da su. Alal misali, za ka iya yin bincike game da dalilan da suka nuna cewa muna rayuwa a kwanaki na karshe don ka kara kasancewa da bangaskiya cewa karshen duniya zai zo nan ba da daɗewa ba. Ka karfafa bangaskiyarka game da alkawuran da aka yi a cikin Littafi Mai Tsarki game da nan gaba ta wajen yin nazari a kan annabcin Littafi Mai Tsarki da suka cika. Ka karanta labaran ’yan’uwa da suka inganta rayuwarsu da taimakon Littafi Mai Tsarki don ka kara tabbatar wa kanka amfanin bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki.a—1 Tas. 2:13.

17. Me ya sa Yesu ya kasance da aminci duk da gwaji masu tsanani da ya fuskanta, kuma ta yaya za ka yi koyi da shi?

17 Ka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi alkawarinsu. Yesu ya kasance da aminci duk da gwaji mai tsanani da ya fuskanta don ya mai da hankali ga abubuwa masu ban ‘farin cikin da aka sa a gabansa.’ (Ibran. 12:2) Bai bar abubuwan duniya su raba hankalinsa ba. (Mat. 4:8-10) Za ka iya yin koyi da Yesu ta wajen yin bimbini a kan alkawura da Jehobah ya yi maka. Za ka iya saka kanka cikin yanayin ta wajen rubuta ko kuma ka zana abubuwan da kake so ka yi muddin Jehobah ya halaka wannan muguwar duniyar. Ka rubuta sunayen mutanen da za ka so ka haɗu da su da kuma abubuwan da za ka tattauna da su sa’ad da aka ta da su daga mutuwa. Ka ɗauka cewa Allah ya yi alkawuran nan don kai ne, ba don dukan mutane ba.

18. Ta yaya addu’a za ta taimaka maka ka karfafa bangaskiyarka?

18 Ka roki Allah ya sa ka kara kasancewa da bangaskiya. Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su roki Jehobah ya ba su ruhu mai tsarki. (Luk. 11:9, 13) Yayin da kake addu’a Allah ya ba ka ruhu mai tsarki, ka roke shi ya sa ka kara kasancewa da bangaskiya. Ka ambaci waɗannan abubuwa a cikin addu’a kuma ka roki Allah ya taimaka maka ka sha kan duk wani hali da zai iya saka bangaskiyarka cikin haɗari, kamar kin gafarta wa mutane.

19. Wane irin mutum ne ya kamata ka yi abota da shi?

19 Ka yi tarayya da masu aminci. Yesu ya mai da hankali wajen zaɓan abokansa. Abokansa na kud da kud, wato manzanninsa sun kasance da aminci ta wajen bin dokokinsa. (Karanta Yohanna 15:14, 15.) Saboda haka, ka yi abota da waɗanda suke nuna bangaskiyarsu ta wajen yin biyayya ga Yesu. Kada ka manta cewa abokan kirki suna faɗa wa juna gaskiya, ko da hakan zai bukaci ba da ko kuma karɓan shawara.—Mis. 27:9.

20. Ta yaya muke amfana idan muka taimaka wa wasu su karfafa bangaskiyarsu?

20 Ka taimaka wa wasu su karfafa bangaskiyarsu. Yesu ya karfafa bangaskiyar almajiransa ta kalamansa da kuma ayyukansa. (Mar. 11:20-24) Hakazalika, ya kamata mu bi misalinsa don idan muka karfafa bangaskiyar wasu muna karfafa namu. (Mis. 11:25) Sa’ad da kake koyarwa da kuma wa’azi, ka ba da hujjoji da suka nuna cewa akwai Allah da ke kaunarmu kuma shi ne ya sa aka rubuta Littafi Mai Tsarki ta ja-gorar ruhu mai tsarki. Ka taimaka wa ’yan’uwanka maza da mata su karfafa bangaskiyarsu. Idan wani daga cikinsu ya soma shakka watakila ta wajen yin gunaguni don waɗanda aka naɗa, kada ka yi saurin watsi da su. Ka taimaka musu su sake karfafa bangaskiyarsu cikin sanin yakamata. (Yahu. 22, 23) Idan kana makaranta kuma ana tattauna juyin halitta a aji, ka ba da hujjoji da suka nuna cewa Allah ne ya halicci abubuwa. Hakan zai iya ba ka damar bayyana bangaskiyarka ga malaminka da abokan makarantarka.

21. Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa kowannenmu game da bangaskiyarmu?

21 Bitrus ya sha kan tsoro da kuma shakka da taimakon Jehobah da kuma Yesu kuma hakan ya sa shi ya zama mai bangaskiya sosai kuma ya karfafa bangaskiyar wasu. Hakazalika, Jehobah yana taimaka mana mu tsaya da karfi cikin imani. (Karanta 1 Bitrus 5:9, 10.) Muna bukata mu dage sosai don mu karfafa bangaskiyarmu kuma idan muka yi hakan za mu sami albarka kwarai.

a Alal misali, ka duba talifofin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” da ke fitowa a Hasumiyar Tsaro na wa’azi.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba