A Waɗanne Hanyoyi ne Jehobah Yake Kaunar Mu?
“Ku dubi irin kaunar da Uba ya nuna mana.” —1 YOH. 3:1, Littafi Mai Tsarki.
WAKOKI: 91, 13
1. Mene ne manzo Yohanna ya karfafa Kiristoci su yi bimbini a kai, kuma me ya sa?
MANZO YOHANNA ya karfafa mu a 1 Yohanna 3:1 cewa mu yi bimbini sosai a kan yadda Jehobah yake matukar kaunar mu. Ya ce: “Ku dubi irin kaunar da Uba ya nuna mana.” Idan muka yi bimbini sosai a kan yadda Jehobah yake kaunar mu da kuma yadda ya nuna hakan, za mu so shi da zuciyar ɗaya kuma za mu karfafa dangantakarmu da shi.
2. Me ya sa wasu mutane sun kasa fahimtar yadda Allah yake kaunar su?
2 Amma wasu mutane ba su fahimci cewa Allah yana kaunar su ba. Suna gani cewa ya kamata a ji tsoron Allah kuma a yi masa biyayya kawai. Ko kuma sun ɗauka cewa Allah bai damu da mutane ba. Watakila suna irin wannan tunanin ne don koyarwar karya da wasu addinai suke yi game da Allah. Wasu kuma suna gani cewa Allah yana kaunar dukan mutane ko da suna yin abubuwan da ba su da kyau. Amma, sa’ad da aka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai, ka fahimci cewa kauna ita ce halin Jehobah ta musamman kuma saboda haka ya ba da Ɗansa fansa a madadin mu. (Yoh. 3:16; 1 Yoh. 4:8) Duk da haka, tarbiyyar da aka yi maka da kuma yanayinka za su iya shafan yadda ka fahimci kaunar Allah a gare ka.
3. Wace dangantaka ce za ta sa mu fahimci yadda Allah yake kaunar mu?
3 Shin a waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake kaunar mu? Wajibi ne mu fahimci ainihin dangantakar da ke tsakanin mu da Jehobah Allah. Jehobah ne mahaliccin dukan ’yan Adam. (Karanta Zabura 100:3-5.) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Adamu “ɗan Allah” ne. (Luk. 3:38, New World Translation; Mat. 6:9) Da yake Jehobah ne ya ba mu rai, shi ne Ubanmu don dangantakar da ke tsakanin mu da shi kamar na uba da ’ya’yansa ne. Saboda haka, Jehobah yana kaunar mu kamar yadda uba mai kauna yake kaunar ’ya’yansa.
4. (a) Ta yaya Jehobah ya bambanta da iyaye maza? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?
4 Da yake iyaye maza ajizai ne, ba za su so ’ya’yansu kamar yadda Jehobah yake kaunar ’yan Adam ba. Wasu ba za su taɓa manta da yadda mahaifinsu ya wulakanta su sa’ad da suke yara ba. Hakan abin bakin ciki ne kwarai. Amma Jehobah ba zai taɓa wulakanta ’ya’yansa ba. (Zab. 27:10) Idan muka fahimci yadda Jehobah yake kaunar mu da kuma yadda yake kula da mu, hakan zai sa mu kusace shi sosai. (Yak. 4:8) Za mu bincika hanyoyi huɗu da Jehobah ya nuna cewa yana kaunar mu a wannan talifin. Za mu tattauna hanyoyi huɗu da za mu iya nuna kaunarmu ga Jehobah a talifi na gaba.
JEHOBAH YANA YI MANA TANADI
5. Mene ne manzo Bulus ya gaya wa mazauna Atina game da Allah?
5 Sa’ad da manzo Bulus ya je Atina da ke Hellas, ya lura cewa birnin tana cike da gumaka kuma mutanen sun gaskata cewa waɗannan allolin ne suka ba su rai da kuma bukatun rayuwa. Saboda haka, Bulus ya gaya musu cewa: “Allah wanda ya yi duniya da abin da ke ciki duka, . . . shi da kansa yana ba kowa rai, da numfashi, da abu duka.” Saboda ikonsa “muke rayuwa, muke motsi, mu ke zamanmu.” (A. M. 17:24, 25, 28) Hakika, saboda yadda Jehobah yake kaunar mu, ya tanadar mana da “abu duka” don mu rayu. Shin za ka iya tuna da wasu abubuwa da Jehobah ya ba mu saboda yana kaunar mu?
6. Ta yaya yadda aka halicci duniya ya nuna cewa Jehobah yana kaunar mu? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)
6 Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah mahalicci “ya ba da duniya ga ’yan Adam.” (Zab. 115:15, 16) Masana kimiyya sun kashe kuɗaɗe da yawa wajen gano wasu duniyoyi da ke kamar wadda muke cikinta. Sun gano ɗarurruwan duniyoyi amma babu wadda aka tsara don mutum ko kuma wani halitta ya rayu a cikinta. Jehobah bai halicci duniyar nan don mu rayu a cikinta kawai ba, amma ya tsara ta da kyau kuma a yadda za mu ji daɗin rayuwa. (Isha. 45:18) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana kaunar mu.—Karanta Ayuba 38:4, 7; Zabura 8:3-5.
7. Ta yaya yadda Jehobah ya halicce mu ya nuna cewa yana kaunar mu?
7 Ko da yake Jehobah ya halicci duniya don mu zauna a cikinta, ya san cewa ba abinci da tufafi da wurin kwana kawai muke bukata don mu ji daɗin rayuwa ba. Alal misali, yaro yakan kasance da kwanciyar hankali idan ya tabbata cewa iyayensa suna kaunarsa. Hakazalika, Jehobah ya halicce mu a cikin kamaninsa, wato a yadda za mu iya kaunar sa kamar yadda ya so mu. (Far. 1:27) Kari ga haka, Yesu ya ce: “Masu albarka ne masu ladabi a ruhu.” (Mat. 5:3) Da yake Jehobah Uba mai kauna ne, yana “ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu,” hakan ya haɗa da abubuwan da zai taimaka mana mu karfafa dangantakarmu da shi.—1 Tim. 6:17; Zab. 145:16.
JEHOBAH YANA KOYA MANA GASKIYA DON YANA KAUNAR MU
8. Me ya sa za mu iya dogara ga “Allah na gaskiya” don ya koyar da mu?
8 Iyaye maza suna kaunar ’ya’yansu kuma suna kāre su don kada a yaudare su. Amma iyaye da yawa ba sa yi wa yaransu tarbiyya mai kyau don su da kansu ba sa bin ka’idodin Allah da ke cikin Kalmarsa kuma hakan yana jawo bakin ciki da ruɗu a iyalin. (Mis. 14:12) Amma Jehobah “Allah na gaskiya” ne. (Zab. 31:5) Yana kaunar ’ya’yansa kuma yana koya mana gaskiya game da shi da kuma yadda za mu bauta masa. Kari ga haka, ya koya yadda za mu yi rayuwa mai ma’ana. (Karanta Zabura 43:3.) Shin wane koyarwar gaskiya ce Jehobah ya bayyana mana, kuma ta yaya hakan ya nuna cewa yana kaunar mu?
Kiristoci iyaye maza suna koyi da Jehobah ta wajen koya wa yaransu gaskiya da kuma taimaka musu su kulla dangantaka da Ubanmu na sama (Ka duba sakin layi na 8-10)
9, 10. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana kaunar mu ta bayyana mana gaskiya (a) game da kansa? (b) game da nufinsa a gare mu?
9 Da farko, Jehobah ya bayyana gaskiya game da kansa. Ya bayyana sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki fiye kowane suna. Hakan ya nuna cewa Jehobah yana so mu san shi. (Yak. 4:8) Kari ga haka, Jehobah ya bayyana mana halayensa. Idan muka lura da abubuwan da ya halitta, za mu san cewa yana da iko da kuma hikima. Idan muka karanta Littafi Mai Tsarki, za mu san cewa shi mai adalci ne da kuma kauna. (Rom. 1:20) Yayin da muke sanin halayensa masu kyau, za mu inganta dangantakarmu da shi.
10 Jehobah ya bayyana mana gaskiya game da nufinsa a gare mu kuma hakan ya sa abubuwa suna tafiya bisa tsari a sama da kuma a tsakanin bayinsa da ke duniya. An bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki cewa ba a halicci ’yan Adam don su mulki kansu ba kuma yin watsi da dokokin Allah zai iya jawo mugun sakamako. (Irm. 10:23) Yana da muhimmanci mu san wannan gaskiyar. Za mu yi rayuwa mai kyau da kuma gamsuwa ne kawai idan muka amince da sarautar Allah. Hakika, wannan gaskiya da Jehobah ya bayyana mana ya nuna cewa yana kaunar mu kwarai!
11. Wane alkawari ne Jehobah ya yi da ya nuna cewa yana kaunar mu?
11 Uba mai kauna ya damu sosai game da yadda ’ya’yansa za su yi rayuwa a nan gaba don yana son rayuwarsu ta kasance da ma’ana sosai. Abin bakin ciki shi ne yawancin mutane a yau ba su san yadda rayuwa za ta kasance a nan gaba ba ko kuma suna ɓata lokacinsu wajen biɗan abubuwan da ba za su dawwama ba. (Zab. 90:10) Muna godiya cewa Ubanmu na sama ya koya mana yadda za mu yi rayuwa mai ma’ana yanzu. Kari ga haka, ya yi mana alkawarin rayuwa mai ban sha’awa a nan gaba.
JEHOBAH YANA YI WA ’YA’YANSA HORO DA KUMA JA-GORA
12. Ta yaya shawarwarin da Jehobah ya ba wa Kayinu da kuma Baruch sun nuna cewa Jehobah yana kaunar su?
12 Sa’ad da Jehobah ya ga cewa Kayinu yana so ya aikata mugunta, sai ya gargaɗe shi cewa: “Don me ka ji haushi? Don me kuma gabanka ya fāɗi? Idan ka kyauta, ba za a amsa ba?” Jehobah ya gaya masa cewa ya guji yin zunubi. (Far. 4:6, 7) Kayinu bai ji shawarar ba kuma ya sha wahala sakamakon haka. (Far. 4:11-13) Amma sa’ad Baruch sakataren Irmiya ya soma tunanin da bai dace ba kuma ya yi sanyin gwiwa a hidimarsa, Jehobah ya ba shi shawara don ya daidaita tunaninsa. Akasin Kayinu, Baruch ya amince da shawarar kuma hakan ya tsira da ransa.—Irm. 45:2-5.
13. Me ya sa Jehobah yake barin amintattun bayinsa sun fuskanci mawuyacin yanayi?
13 Manzo Bulus ya ce: “Gama wanda Ubangiji ke kauna shi yake horo, yana kuwa dūkan kowane ɗan da yake karɓa.” (Ibran. 12:6) Amma ba hukunci ne kawai shi ne horo ba. Mutum yakan sami horo a hanyoyi dabam-dabam. A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai labaran amintattun bayin Jehobah da suka sami kansu a cikin yanayi mai tsanani sosai kuma sun bar yanayin ya horar da su. Alal misali, Yusufu da Musa da kuma Dauda sun sami kansu a cikin mawuyacin yanayi kuma Jehobah ya kasance tare da su. Kari ga haka, darussan da suka koya a waɗannan lokatan sun taimaka musu sosai sa’ad da Jehobah ya ba su karin aiki. Yayin da muka karanta yadda Jehobah ya tallafa wa bayinsa sa’ad da suke fuskantar mawuyacin yanayi da kuma yadda ya yi amfani da su, za mu shaida cewa Jehobah yana kaunar bayinsa kuma yana kula da su.—Karanta Misalai 3:11, 12.
14. Sa’ad da muka yi zunubi, ta yaya Jehobah yake nuna mana kaunarsa?
14 Jehobah yana yi mana horo domin yana kaunar mu. Sa’ad da Jehobah ya yi wa waɗanda suka yi zunubi horo kuma suka tuba, Jehobah zai gafarta musu “a yalwace.” (Isha. 55:7) Mene ne hakan yake nufi? Dauda ya kwatanta yadda Jehobah yake gafartawa sa’ad da ya ce: “Ya gafarta dukan zunubaina, ya kuma warkar da dukan cuce-cucena. Ya cece ni daga kabari, ya sa mini albarka da kauna da jinkai. Kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka nan ne ya nisantar da zunubanmu daga gare mu.” (Zab. 103:3, 4, 12, LMT) Saboda haka, bari mu rika bin shawarwarin da muke samu daga Jehobah nan da nan kuma mu karɓi horon da yake yi mana domin yana kaunar mu.—Zab. 30:5.
JEHOBAH YANA KĀRE MU
15. Mene ne ya nuna cewa bayin Jehobah suna da daraja a gabansa?
15 Uba mai kauna yana kāre iyalinsa daga duk wani abin da zai jefa su cikin haɗari. Jehobah yana nan kamar Uba mai kauna don yana kāre mu. Marubucin zabura ya ce Jehobah yana “kiyaye rayukan jama’arsa, yakan cece su daga ikon mugaye.” (Zab. 97:10, LMT) Alal misali, me za ka yi idan wani kwaro yana so ya shiga idonka? Za ka kāre idon ba tare da ɓata lokaci ba don suna da muhimmanci a gare ka. Hakazalika, Jehobah ba ya jinkirin kāre mutanensa don suna da daraja a gabansa.—Karanta Zakariya 2:8.
16, 17. Ka ba da misalan yadda Jehobah yake kāre mutane a dā da kuma a yau.
16 Jehobah yana amfani da mala’iku wajen kāre mutanensa. (Zab. 91:11) Ya yi amfani da mala’ika wajen halaka sojojin Assuriyawa guda 185,000 a dare ɗaya don ya cece mutanensa da ke Urushalima. (2 Sar. 19:35) Kari ga haka, mala’iku sun taɓa ceton Bitrus da Bulus da kuma wasu daga kurkuku. (A. M. 5:18-20; 12:6-11) A zamaninmu ma, Jehobah yana kāre bayinsa. Wani wakilin hedkwata da ya ziyarci wani ofishin Shaidun Jehobah a Afirka ya ba da rahoto cewa yakin addini da kuma siyasa ya haifar da faɗace-faɗace da sace-sace da fyaɗe da kuma kashe-kashe a kasar. Hakan ya jefa kasar cikin wani yanayi mai wuya sosai. Duk da haka, babu wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa da ta rasa ranta. Amma da yawa daga cikinsu sun yi asarar dukiyoyinsu da kuma sana’o’insu. Sa’ad da aka tambaye su yaya suke, suka yi murmushi kuma suka ce: “Muna lafiya, mun gode wa Jehobah!” Sun shaida cewa Allah yana kaunar su.
17 Ba a kowane lokaci ba ne Jehobah yake kāre mutanensa. Alal misali, bai kāre Istafanus sa’ad da magabta suka yi yunkurin kashe shi ba. Duk da haka, Allah yana kāre mutanensa ta wajen faɗakar da su game da dabarun Shaiɗan. (Afis. 6:10-12) Yana taimaka mana mu san haɗarin da ke tattare da son abin duniya da nishaɗin banza da yin amfani da intane a hanyar da ba ta dace ba, da dai sauransu. Hakika, Jehobah yana kamar Uba mai kauna, yana kula da kuma kāre mutanensa.
KASANCEWA CIKIN WAƊANDA ALLAH YAKE KAUNA BA KARAMIN GATA BA NE
18. Mene ne ra’ayinka game da kaunar Jehobah a gare ka?
18 Sa’ad da Musa ya tuna shekaru da yawa da ya yi yana bauta wa Jehobah, ya ce: “Ka kosar da mu da jinkanka da safe: domin mu yi farin zuciya, mu yi murna kuma dukan kwanakinmu.” (Zab. 90:14) Muna murna cewa Jehobah yana kaunar mu kuma hakan ba karamin gata ba ne. Yanayinmu yana kama da na manzo Yohanna da ya ce: “Ku dubi irin kaunar da Uba ya nuna mana.”—1 Yoh. 3:1, LMT.