RAYUWAR KIRISTA
Yadda Za Ka Yi Kalami Mai Ratsa Zuciya
Kalami mai ratsa zuciya yana ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya. (Ro 14:19) Kuma mutanen da suka yi kalamin suna samun ƙarfafa. (Mis 15:23, 28) Saboda haka, ya kamata mu riƙa kalami a ƙalla sau ɗaya a kowane taro. Hakika, ba a kowane lokaci ba ne za a riƙa kiranmu mu yi kalami ba. Don haka, zai dace mu shirya kalamai da yawa a kowane taro.
Kalami mai ratsa zuciya . . .
gajere ne kuma yana da sauƙin fahimta. A yawancin lokuta, ana iya yinsa a sakan 30 ko ƙasa da hakan
daga zuciya ake yi ba karatu ba
ba maimaita kalamin da wani ya yi ba ne
Idan kai aka fara kira, . . .
ka ba da amsa mai sauƙi kuma kai tsaye
Idan wani ya riga ya ba da amsar, za ka iya . . .
bayyana nassin da ya goyi bayan amsar da aka bayar
faɗin yadda batun ya shafe mu
bayyana yadda za mu yi amfani da darasin
ba da wani labarin da ya bayyana darasin da kyau