Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Satumba pp. 20-25
  • Ku Yi Saurin Taimaka ma Waɗanda Suke da Zuciyar Kirki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Saurin Taimaka ma Waɗanda Suke da Zuciyar Kirki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ZA MU TAIMAKA MA WAƊANDA SUKE SON WAꞌAZINMU
  • ABIN DA ZA MU YI IDAN MUKA SOMA NAZARI DA MUTUM
  • YADDA ZA MU TAIMAKA WA ƊALIBANMU IDAN SUKA ZO TARO
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Yadda Za Ka Ƙara Jin Daɗin Yin Waꞌazi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Yana da Kyau Mu Kusaci ꞌYanꞌuwa!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Satumba pp. 20-25

TALIFIN NAZARI NA 39

WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

Ku Yi Saurin Taimaka ma Waɗanda Suke da Zuciyar Kirki

“Dukan waɗanda suke marmarin samun rai na har abada, sun zama masu bi.”—A. M. 13:48.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga muhimmancin soma nazari da mutane da kuma gayyatar su zuwa taro.

1. Mene ne mutane suke yi idan muka yi musu waꞌazi? (Ayyukan Manzanni 13:​47, 48; 16:​14, 15)

MUTANE da yawa a ƙarni na farko sun yi farin ciki sosai saꞌad da aka yi musu waꞌazi, kuma sun so su zama Kiristoci nan da nan. (Karanta Ayyukan Manzanni 13:​47, 48; 16:​14, 15.) A yau ma, wasu mutane suna farin ciki sosai a ƙaro na farko da suka ji waꞌazinmu. Wasu kuma da farko ba za su so su ji waꞌazin ba, amma daga baya za su so su yi hakan har ma su zo su bauta wa Jehobah. To, me za mu yi idan muka haɗu da waɗanda suke so su koyi gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki?

2. Me ya sa za a iya kwatanta waꞌazin da muke yi da noma?

2 Za a iya kwatanta waꞌazin da muke yi da noma. Manomi yakan shuka abubuwa dabam-dabam, kuma wasu sukan riga wasu nuna. Don haka, zai girbe waɗanda suka nuna kuma ya ci-gaba da kula da waɗanda ba su nuna ba. Haka ma, idan muka haɗu da waɗanda suke son waꞌazinmu, muna so mu taimaka musu su zama mabiyan Kristi ba tare da ɓata lokaci ba. Kuma muna ci-gaba da taimaka wa waɗanda ba su amince da saƙonmu ba su ga muhimmancin koya game da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. (Yoh. 4:​35, 36) Idan muka gane ko mutum yana so waꞌazinmu ko aꞌa, hakan zai sa mu san yadda za mu taimaka masa. A wannan talifin, za mu koyi abin da ya kamata mu yi a lokaci na farko da muka haɗu da waɗanda da suke son waꞌazinmu. Za mu kuma ga yadda za mu taimaka musu don su ci-gaba da kusantar Jehobah kuma su zo su bauta masa.

YADDA ZA MU TAIMAKA MA WAƊANDA SUKE SON WAꞌAZINMU

3. Idan muka haɗu da waɗanda suke son waꞌazinmu, me muke bukatar mu yi? (1 Korintiyawa 9:26)

3 Idan muka haɗu da waɗanda suke son waꞌazinmu, muna so mu taimaka musu su koya game da Jehobah kuma su soma kusantar sa ba tare da ɓata lokaci ba. Idan muka haɗu da irin waɗannan mutanen, zai dace mu tambaye su ko za su so su yi nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma mu gayyace su zuwa taron ikilisiya a ranar da muka haɗu da su.—Karanta 1 Korintiyawa 9:26.

4. Ka ba da misalin da ya nuna yadda wata mata ta nuna cewa tana son a soma nazari da ita ba tare da ɓata lokaci ba.

4 Soma nazari da mutane. Wasu da muke haɗuwa da su suna son su soma nazarin Littafi Mai Tsarki nan da nan. Alal misali, wata rana ran Alhamis, wata mata a Kanada ta je inda ake waꞌazi da amalanke, kuma ta ɗauki ƙasidar nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! ꞌYarꞌuwar da ke wurin ta gaya mata cewa muna amfani da ƙasidar don yin nazari da mutane kyauta. Sai matar ta ce tana so, kuma suka ba wa juna lambar wayarsu. Daga baya a ranar, matar ta tura wa ꞌyarꞌuwar saƙo, ta tambaye ta lokacin da za su soma yin nazari. Sai ꞌyarꞌuwar ta ce, ko za ta so su zo a ƙarshen mako? Amma matar ta ce: “Gobe fa? Ba inda zan je.” Hakan ya sa sun soma nazari ran Jummaꞌa. A ƙarshen makon, matar ta halarci taro, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta samu ci-gaba.

5. Me muke bukatar mu yi da zai taimaka mana mu san yadda za mu soma nazari da mutum? (Ka kuma duba hotunan.)

5 Gaskiyar ita ce, ba kowa ba ne da muka haɗu da shi zai so a yi nazari da shi kamar yadda matar nan ta yi ba. Wasu za su bukaci lokaci kafin su nuna cewa suna son abin da muke koyarwa. Wataƙila muna bukatar mu soma tattaunawa da mutum daga batutuwan da ya fi so. Idan muka ci-gaba da nuna wa mutum cewa mun damu da shi, mai yiwuwa ba da daɗewa ba za mu soma nazari da shi, kuma a kwana a tashi zai iya son waꞌazinmu. Idan muna so mu tambayi mutum ko zai so a yi nazari da shi, ta yaya za mu yi hakan? Bari mu ga wasu shawarwari da ꞌyanꞌuwan da suka ƙware wajen soma nazari da mutane suka bayar.

Hotuna: Na 1. ꞌYanꞌuwa maza biyu suna yi wa wani tsohon soja da ke zaune a baƙin kofar gidansa waꞌazi. Na 2. ꞌYanꞌuwa mata biyu suna nuna wa wata mata ƙasidar nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, a ƙofar ɗakinta. Matar tana da yara maza biyu, tana ɗauke da ɗaya a hannu, ɗayan kuma yana tsaye kusa da ita.

Me kake ganin za ka iya gaya wa mutanen da aka nuna a hoton nan da zai sa su so yi nazarin Littafi Mai Tsarki? (Ka duba sakin layi na 5)a


6. Idan kana so ka ci-gaba da tattaunawa da wanda yake son saƙonmu, me za ka iya gaya masa?

6 Waɗannan ꞌyanꞌuwan sun ce, a wasu ƙasashe zai fi kyau mu guji gaya wa mutane cewa “muna nazari da su ne,” ko “muna nazarin Littafi Mai Tsarki,” ko kuma “muna koyar da su ne.” Sun ce zai fi dacewa mu gaya wa mutane cewa, “muna tattaunawa ne,” ko “muna hira ne,” ko kuma “muna bincika Littafi Mai Tsarki.” Inda kana so ka ci-gaba da tattaunawa da mutumin wani lokaci, za ka iya gaya masa cewa, “Yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa muhimman tambayoyi game da rayuwa na da ban mamaki,” ko kuma “Littafi Mai Tsarki ba kawai littafin addini ba ne. Yana ɗauke da shawarwari da za su taimaka mana a harkokinmu na yau da kullum.” Za ka iya ƙara da cewa: “A cikin minti 10 ko 15 za ka iya koyan abin da zai taimaka maka a rayuwa.” Ba ka bukatar ka gaya wa mutumin cewa, “za ku yi hakan kowane mako” ko “a daidai wani lokaci,” domin yin hakan zai sa mutumin ya ga kamar yana da wuya ko kuma wajibi ne ku haɗu a daidai wani lokaci.

7. A wane lokaci ne wasu suke gane cewa waꞌazin da muke yi gaskiya ne? (1 Korintiyawa 14:​23-25)

7 Ka gayyaci mutumin zuwa taro. A zamanin su manzo Bulus, da alama cewa, wasu sun gane cewa waꞌazin da suke yi gaskiya ne lokacin da suka halarci taro. (Karanta 1 Korintiyawa 14:​23-25.) Haka ma yake a yau. Yawancin mutanen da suke son saƙonmu suna samun ci-gaba da wuri idan suka soma halartan taronmu. To, tambayar ita ce, a wane lokaci ne za mu gayyace su zuwa taronmu? A darasi na 10 na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, an ƙarfafa ɗalibai su halarci taron Shaidun Jehobah. Amma ba ma bukatar mu jira har sai mun isa wannan darasin kafin mu gayyaci mutumin zuwa taronmu. Za mu iya gayyatar mutum zuwa taron ƙarshen mako a lokaci na farko da muka soma tattaunawa da shi. Za mu iya gaya masa jigon jawabin da za a yi a ranar, ko wasu batutuwa daga Hasumiyar Tsaro da za a yi nazarin sa.

8. Idan muna so mu gayyaci mutum zuwa taronmu, mene ne za mu iya gaya masa? (Ishaya 54:13)

8 Saꞌad da kake gayyatar mutum zuwa taronmu, ka gaya masa bambancin da ke tsakanin yadda muke gudanar da ibadarmu da nasu. A lokacin da wata ɗaliba ta fara halartar taronmu, ta tambayi wadda take nazari da ita cewa, “Sunan kowa da kowa ne mai gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaron nan ya sani?” ꞌYarꞌuwar ta gaya mata cewa, dukanmu muna ƙoƙari mu san sunan kowa da kowa da ke ikilisiya, kamar yadda muka san sunayen ꞌyan iyalinmu. Ɗalibar ta ce, hakan ya bambanta da yadda ake yi a cocinsu, domin yawancin mutane a cocinsu ba su san sunan juna ba. Ban da haka ma, zai kuma dace mu gaya wa mutane wasu abubuwa game da taronmu. (Karanta Ishaya 54:13.) A taronmu muna bauta wa Jehobah, muna koyan abubuwa game da shi, kuma muna ƙarfafa juna. (Ibran. 2:12; 10:​24, 25) Shi ya sa an shirya taronmu yadda za mu iya koyan abubuwa ba tare da bin wasu alꞌadu ba. (1 Kor. 14:40) An shirya wuraren da muke gudanar da taronmu a hanyar da zai yi mana sauƙi mu koyi game da Jehobah. Ba ma tattauna batutuwan siyasa a wurin, kuma ba ma gardama game da raꞌayoyin mutane a wurin. Zai dace mu nuna wa ɗalibinmu wannan bidiyon Me Ake Yi a Majamiꞌar Mulki? Yin hakan zai taimaka masa ya san yadda muke gudanar da taronmu.

9-10. Idan muna gayyatar mutum zuwa taronmu, me za mu iya gaya masa da zai taimaka masa kada ya ji tsoro? (Ka kuma duba hoton.)

9 Wasu suna jinkirin halartan taronmu don suna ganin yin hakan zai sa su zama Shaidun Jehobah nan take. Saboda hakan, idan kana gayyatar mutum zuwa taronmu, ka gaya masa cewa muna son mutane su riƙa kawo mana ziyara. Ba ma tilasta mutane su zama mambobinmu, kuma ba dole ne su yi ko su faɗi wani abu idan suka halarta ba. Mutum zai iya zuwa da iyalinsa har da ƙananan yara. Ba a ware yara a ɓangare dabam. A maimakon haka, iyaye da yara suna zama tare kuma su koyi abubuwa. Hakan yakan sa iyaye su san inda yaransu suke a kowane lokaci, da abin da ake koya musu. (M. Sha. 31:12) Ba ma karɓan baiko a wurin taronmu. A maimakon haka, muna bin abin da Yesu ya faɗa saꞌad da ya ce: “Kyauta aka ba ku, ku kuma bayar kyauta.” (Mat. 10:8) Za ka iya gaya wa mutumin cewa ba ya bukatar ya sa kaya masu tsada kafin ya halarci taronmu. Domin Allah ya fi mai da hankali ga abin da ke zuciyarmu ne, ba kayan da muka saka ba.—1 Sam. 16:7.

10 Idan wani ya zo taro, ka sa ya ji daɗin taron. Ka taimaka masa ya gai da wasu dattawa da kuma ꞌyanꞌuwa. Idan ya saki jiki a wurin, ba mamaki zai so ya sake dawowa. Idan mutumin ya zo taro, kuma bai zo da Littafi Mai Tsarki ba, ku yi amfani da naka. Kuma ka yi ƙoƙari ka taimaka masa ya fahimci abin da mai jawabin yake faɗa, da kuma yadda muke nazari.

Matar da aka ambata ɗazu tana murna don yadda ꞌyanꞌuwa suka marabce ta a Majamiꞌar Mulki. Tana ɗauke da ɗanta ƙarami, ɗayan kuma yana magana da wani yaro.

Idan mutum ya soma halartan taro tun da wuri, hakan zai sa ya kusaci Jehobah da wuri (Ka duba sakin layi na 9-10)


ABIN DA ZA MU YI IDAN MUKA SOMA NAZARI DA MUTUM

11. Ta yaya za mu nuna mun san cewa mutumin da muke nazari da shi yana da wasu harkoki a gabansa?

11 Me ya kamata mu riƙa tunawa saꞌad da muka soma nazari da mutane? Zai dace mu riƙa tuna cewa mutumin da muke nazari da shi yana da wasu harkoki a gabansa. Alal misali, idan kun tsara lokacin da za ku riƙa soma nazari, ka yi ƙoƙari ka je a daidai lokacin, ko da mutane da yawa a yankinku ba su san muhimmancin yin hakan ba. Ƙari ga haka, kada mu ci lokaci a nazari na farko. ꞌYanꞌuwa maza da mata da suka yi nazari da mutane da yawa sun ce yana da kyau mu riƙa gudanar da nazari cikin ƙanƙanin lokaci, ko da mutumin yana so mu ci-gaba. Yana da muhimmanci mu guji dogon bayani, kuma mu ba wa ɗalibin dama ya faɗa raꞌayinsa.—K. Mag. 10:19.

12. Me ya kamata mu yi da zarar mun soma nazari da mutum?

12 Da zarar mun soma nazari da mutum, zai dace mu taimaka masa ya koya game da Jehobah da Yesu, kuma ya ƙaunace su. Za mu iya yin hakan ta wajen, nuna masa abubuwan da muke tattaunawa daga cikin Littafi Mai Tsarki, maimakon raꞌayinmu. (A. M. 10:​25, 26) Manzo Bulus ya kafa mana misali mai kyau a yin hakan. Saꞌad da yake koyar da mutane, yana sa su mai da hankali ga Yesu, wanda Jehobah ya aiko don ya taimaka mana mu san kuma mu kusace Shi. (1 Kor. 2:​1, 2) Bulus ya kuma bayyana cewa yana da muhimmanci a taimaka wa sabbi su kasance da halaye masu kyau. Halayen nan na kama da azurfa, da zinariya da kuma duwatsu masu daraja. (1 Kor. 3:​11-15) Waɗannan halayen sun ƙunshi bangaskiya, da hikima, da fahimta, da kuma tsoron Jehobah. (Zab. 19:​9, 10; K. Mag. 3:​13-15; 1 Bit. 1:7) Saboda haka, zai dace mu yi koyi da Bulus ta wajen taimaka wa ɗalibanmu su kasance da bangaskiya sosai, kuma su ƙulla dangantaka na kud da kud da Ubanmu na sama mai ƙauna.—2 Kor. 1:24.

13. Ta yaya za mu kasance da haƙuri kuma mu nuna sanin ya kamata saꞌad da muke taimaka wa ɗalibanmu? (2 Korintiyawa 10:​4, 5) (Ka kuma duba hoton.)

13 Zai dace mu yi koyi da Yesu ta wajen kasancewa da haƙuri da kuma sanin ya kamata. Kada mu yi wa mutane tambayoyin da za su sa su ji wani iri. Idan akwai wani batu da yake musu wuya su fahimta, za mu iya ci-gaba da wani batu dabam kuma mu dawo kan batu mai wuyar a wani lokaci. Maimakon mu tilasta wa mutum ya amince da wata koyarwa, zai dace mu ba shi lokaci don ya yi tunani kuma ya amince da kansa. (Yoh. 16:12; Kol. 2:​6, 7) Littafi Mai Tsarki ya ce, koyarwar ƙarya na kamar wuri mai ƙarfi da muke bukatar mu rusa. (Karanta 2 Korintiyawa 10:​4, 5.) Mai yiwuwa ba zai yi wa ɗalibanmu sauƙi su daina gaskatawa da abubuwan da suka yi shekaru suna imani da su ba. Saboda haka, muna bukatar mu taimaka musu su ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Hakan zai sa ya yi musu sauƙi su bar koyarwar ƙarya da suka yi imani da su, da suka zama musu jiki.—Zab. 91:9.

ꞌYanꞌuwa maza biyun da aka ambata ɗazu suna nazari da tsohon sojan da littafin nan, “Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!” Kuma akwai hotonsa da lambobin yabon da ya samu a aikin soja kusa da inda suke.

Ka ba wa ɗalibinka lokaci don ya yi tunani a kan abin da yake koya kuma ya amince da kansa (Ka duba sakin layi na 13)


YADDA ZA MU TAIMAKA WA ƊALIBANMU IDAN SUKA ZO TARO

14. Me ya kamata mu yi idan muka ga sabbi sun halarci taronmu?

14 Jehobah yana so mu ƙaunaci dukan mutane ko daga ina ne suka fito, ko alꞌadarsu ta yi dabam da namu, ko kuma su masu kuɗi ne ko talakawa. (Yak. 2:​1-4, 9) To, ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar sabbin da suka halarci taronmu?

15-16. Me ya kamata mu yi da zai taimaka wa sabbi su saki jiki idan suka halarci taronmu?

15 Wasu sukan halarci taronmu don suna so su ga abin da ke faruwa a wurin, ko kuma don wani a wani wuri dabam ya ƙarfafa su su yi hakan. Don haka, idan ka ga wani ya zo taronmu, ka je ka yi masa magana, ka marabce shi. Amma kada ka yi hakan a hanyar da za ta sa ya ji wani iri. Ka gaya masa cewa za ku iya zauna tare. Idan zai yiwu, ka samo masa Littafi Mai Tsarki da kuma littafin da ake nazarin sa, ko kuma ku yi amfani da naka. Ka yi iya ƙoƙarinka don ka sa ya saki jiki. Wani mutum da ya halarci taronmu ya gaya wa ɗanꞌuwan da ya marabce shi cewa, yana jin wani iri don irin rigar da ya saka. Ɗanꞌuwan ya kwantar masa da hankali kuma ya gaya masa cewa ko da yake muna sa kaya masu kyau zuwa taro, hakan ba ya nufin mu dabam ne da sauran mutane. Daga baya mutumin ya yi baftisma, kuma bai manta da yadda ɗanꞌuwan ya kwantar masa da hankali ba. Amma fa, saꞌad da muke tattaunawa da sabbi da suka halarci taronmu, kada mu yi musu tambayoyi da za su sa su ji wani iri ko su ji kunya.—1 Bit. 4:15.

16 Akwai wani abu kuma da za mu iya yi da zai sa sabbi su saki jiki. Saꞌad da muke tattaunawa da ꞌyanꞌuwa, ko ba da amsa, ko gudanar da ayyuka a taro, kada mu yi magana marar kyau game da waɗanda ba Shaidu ba, ko a kan abin da suka yi imani da shi. Kada mu faɗa wani abin da zai dame su, ko kuma su ji kamar an zage su. (Tit. 2:8; 3:2) Alal misali, bai kamata mu yi magana game da imaninsu a hanyar da za ta yi kamar ba su san abin da suke yi ba. (2 Kor. 6:3) Saboda haka, yana da kyau ꞌyanꞌuwa maza da suke ba da jawabi ga jamaꞌa su mai da hankali sosai. Ƙari ga haka, zai dace su riƙa bayyana kalmomi ko batutuwa da kyau, da yake sun san cewa wasu cikin masu sauraro ba Shaidu ba ne.

17. Idan muka haɗu da waɗanda suke “marmarin samun rai” a waꞌazi, me muke bukatar mu yi?

17 Duk wayewar gari, muna bukatar mu ƙara yin waꞌazi da gaggawa, kuma za mu ci-gaba da neman mutanen da “suke marmarin samun rai na har abada.” (A. M. 13:48) Idan muka sami irin mutanen nan, kada mu yi jinkirin nuna musu yadda muke nazari da mutane da kuma gayyatar su zuwa taronmu. Idan muka yi hakan, za mu taimaka musu su soma bin hanyar zuwa rai.—Mat. 7:14.

MECE CE AMSARKA?

  • Me za mu yi a lokaci na farko da muka haɗu da mutumin da yake so ya koyi gaskiya game da Jehobah?

  • Saꞌad da muka soma nazari da wani, me za mu yi don mu taimaka masa?

  • Ta yaya za mu taimaka wa sabbi su saki jiki idan suka halarci taronmu?

WAƘA TA 64 Mu Riƙa Yin Waꞌazi da Farin Ciki

a BAYANI A KAN HOTO: ꞌYanꞌuwa maza biyu suna yi wa wani tsohon soja da ke zaune a baƙin kofar gidansa waꞌazi; ꞌyanꞌuwa mata biyu suna ɗan yi wa wata mata waꞌazi, matar tana da ayyuka da yawa.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba