Alhamis, 31 ga Yuli
Ku tabbata cewa kun koyi abin da zai gamshi Ubangiji.—Afis. 5:10.
Idan muna so mu tsai da shawara mai muhimmanci, muna bukatar mu fahimci mene ne “nufin Ubangiji,” kuma mu bi shi. (Afis. 5:17) Idan muna neman ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suka dace da yanayin da muke ciki, muna neman sanin raꞌayin Jehobah game da batun ke nan. Kuma idan muka gano ƙaꞌidodin Jehobah kuma muka bi su, za mu iya yin zaɓi mai kyau. “Mugun nan,” wato maƙiyinmu Shaiɗan, zai so ya cika mu da ayyuka da yawa har ma mu rasa lokacin bauta ma Jehobah. (1 Yoh. 5:19) Kirista zai iya sa neman abin duniya, ko makaranta, ko kuma aikin da yake yi, ya zama farko a rayuwarsa, maimakon ya nemi hanyoyin da zai bauta ma Jehobah. Idan ya yi hakan, ya nuna cewa ya soma bin tunanin mutanen duniyar nan ke nan. Hakika, biɗan abubuwan nan ba laifi ba ne. Amma bai kamata a ce su ne muka sa a kan-gaba ba. w24.03 24 sakin layi na 16-17
Jumma’a, 1 ga Agusta
Mai adalci yakan sami wahaloli da yawa, amma Yahweh yakan kuɓutar da shi daga cikinsu duka.—Zab. 34:19.
Ku yi laꞌakari da abubuwa guda biyu daga nassin da ke sama. (1) Masu adalci suna fuskantar matsaloli. (2) Jehobah yana kuɓutar da su daga matsalolin. Ta yaya Jehobah yake kuɓutar da mu? Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta wajen taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da rayuwa a wannan kwanakin ƙarshe. Ko da yake Jehobah ya yi mana alkawari cewa za mu yi farin ciki yayin da muke bauta masa, bai yi mana alkawari cewa za mu yi rayuwa ba tare da matsaloli ba. (Isha. 66:14) Yana dai so mu mai da hankali ga rayuwar da za mu more har abada a nan gaba. (2 Kor. 4:16-18) Kafin lokacin, yana taimaka mana mu ci gaba da jimrewa a kullum. (Mak. 3:22-24) Me za mu iya koya daga bayin Allah a zamanin dā da kuma a zamaninmu? Za mu iya fuskantar matsaloli ba zato. Amma idan muka dogara ga Jehobah, ba zai daina taimaka mana ba.—Zab. 55:22. w23.04 14-15 sakin layi na 3-4
Asabar, 2 ga Agusta
Kowa ya yi biyayya ga shugabannin gwamnati.—Rom. 13:1.
Za mu iya koyan darasi daga gun Yusufu da Maryamu, domin sun yi biyayya ga hukumomin gwamnati duk da cewa hakan bai yi musu sauƙi ba. (Luk. 2:1-6) Saꞌad da Maryamu ta yi wata tara da juna biyu, gwamnati ta umurce su su yi wani abu mai wuya sosai. A lokacin, Augustus ne yake mulkin Daular Roma kuma ya ba da umurni cewa a ƙirga mutanen da ke Daular. Don haka, ya zama dole Yusufu da Maryamu su je Baiꞌtalami, kuma tafiyar ta kai kilomita 150. Ban da haka, za su yi ta hawa a kan tuddai da yawa. Hakika, tafiyar za ta yi musu wuya sosai, musamman ma Maryamu. Wataƙila sun damu da yadda tafiyar za ta shafi lafiyar Maryamu da kuma ɗanta. Me zai faru idan ta soma nakuɗa a hanya? Jaririn da ke cikinta shi ne Almasihu da aka yi alkawarin sa. Shin dalilan nan sun sa sun ƙi yin biyayya ga shugabannin gwamnati ne? Yusufu da Maryamu ba su bar dalilan nan su hana su bin umurnin ba. Jehobah ya yi musu albarka don sun yi biyayya. Maryamu ta isa Baiꞌtalami cikin ƙoshin lafiya kuma babu abin da ya samu ɗan da ta haifa!—Mik. 5:2. w23.10 8 sakin layi na 9; 9 sakin layi na 11-12