Laraba, 30 ga Yuli
Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.—A. M. 4:20.
Za mu iya yin koyi da almajiran Yesu ta wajen ci-gaba da yin waꞌazi ko da hukuma ta ce mu daina yin hakan. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu iya yin aikin da ya ba mu. Don haka mu roƙi Jehobah ya ba mu ƙarfin zuciya da hikima, kuma ya taimake mu mu iya jimre matsalolinmu. Yawancinmu muna fama da matsaloli dabam-dabam. Ko rashin lafiya, ko rasuwar wani da muke ƙauna, ko wata matsala a iyalinmu, ko tsanantawa da dai sauran su. Annoba da tashe-tashen hankula sun sa jimre wa matsalolin nan ya ƙara yin wuya. Idan kana cikin matsala, ka faɗa wa Jehobah duk abin da ke zuciyarka. Ka bayyana masa abin da ke faruwa da kai kamar yadda za ka gaya wa amininka. Tabbas, Jehobah zai taimake ka, “zai lura da kai.” (Zab. 37:3, 5) Idan muka nace da yin adduꞌa, zai taimaka mana mu “yi haƙuri a cikin azaba.” (Rom. 12:12) Jehobah ya san matsalolin da bayinsa suke fuskanta. “Yakan kuma ji kukansu ya cece su.”—Zab. 145:18, 19. w23.05 5-6 sakin layi na 12-15
Alhamis, 31 ga Yuli
Ku tabbata cewa kun koyi abin da zai gamshi Ubangiji.—Afis. 5:10.
Idan muna so mu tsai da shawara mai muhimmanci, muna bukatar mu fahimci mene ne “nufin Ubangiji,” kuma mu bi shi. (Afis. 5:17) Idan muna neman ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suka dace da yanayin da muke ciki, muna neman sanin raꞌayin Jehobah game da batun ke nan. Kuma idan muka gano ƙaꞌidodin Jehobah kuma muka bi su, za mu iya yin zaɓi mai kyau. “Mugun nan,” wato maƙiyinmu Shaiɗan, zai so ya cika mu da ayyuka da yawa har ma mu rasa lokacin bauta ma Jehobah. (1 Yoh. 5:19) Kirista zai iya sa neman abin duniya, ko makaranta, ko kuma aikin da yake yi, ya zama farko a rayuwarsa, maimakon ya nemi hanyoyin da zai bauta ma Jehobah. Idan ya yi hakan, ya nuna cewa ya soma bin tunanin mutanen duniyar nan ke nan. Hakika, biɗan abubuwan nan ba laifi ba ne. Amma bai kamata a ce su ne muka sa a kan-gaba ba. w24.03 24 sakin layi na 16-17
Jumma’a, 1 ga Agusta
Mai adalci yakan sami wahaloli da yawa, amma Yahweh yakan kuɓutar da shi daga cikinsu duka.—Zab. 34:19.
Ku yi laꞌakari da abubuwa guda biyu daga nassin da ke sama. (1) Masu adalci suna fuskantar matsaloli. (2) Jehobah yana kuɓutar da su daga matsalolin. Ta yaya Jehobah yake kuɓutar da mu? Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta wajen taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da rayuwa a wannan kwanakin ƙarshe. Ko da yake Jehobah ya yi mana alkawari cewa za mu yi farin ciki yayin da muke bauta masa, bai yi mana alkawari cewa za mu yi rayuwa ba tare da matsaloli ba. (Isha. 66:14) Yana dai so mu mai da hankali ga rayuwar da za mu more har abada a nan gaba. (2 Kor. 4:16-18) Kafin lokacin, yana taimaka mana mu ci gaba da jimrewa a kullum. (Mak. 3:22-24) Me za mu iya koya daga bayin Allah a zamanin dā da kuma a zamaninmu? Za mu iya fuskantar matsaloli ba zato. Amma idan muka dogara ga Jehobah, ba zai daina taimaka mana ba.—Zab. 55:22. w23.04 14-15 sakin layi na 3-4