Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w23 Nuwamba pp. 8-13
  • Me Za Mu Yi don Mu Ci-gaba da Ƙaunar Juna Sosai?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Za Mu Yi don Mu Ci-gaba da Ƙaunar Juna Sosai?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ME YA SA MUKE BUKATAR MU ƘAUNACI JUNA?
  • TA YAYA ZA MU NUNA WA JUNA ƘAUNA?
  • ME ZA MU YI DON MU CI-GABA DA ƘAUNAR JUNA SOSAI?
  • ABIN DA YA SA MUKE BUKATAR ƘAUNA SOSAI A YAU
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Fiye Da Kome Kuma, Ku Himmantu Ga Ƙaunar Juna Gaya”
    Ka Zauna A Faɗake!
  • Kada Ku Bar Ƙaunar da Kuke wa Juna ta yi Sanyi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
w23 Nuwamba pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 47

Me Za Mu Yi don Mu Ci-gaba da Ƙaunar Juna Sosai?

“Ya ku waɗanda nake ƙauna, sai mu ƙaunaci juna, gama ƙauna daga wurin Allah take.”—1 YOH. 4:7.

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1-2. (a) Me ya sa manzo Bulus ya ce ƙauna ita ce hali “mafi girma”? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu nemi amsar su?

DA MANZO Bulus yake magana game da bangaskiya da sa zuciya ko bege, da kuma ƙauna, ya kammala da cewa hali “mafi girma duka a cikinsu ita ce ƙauna.” (1 Kor. 13:13) Me ya sa Bulus ya ce hakan? Don a nan gaba ba za mu bukaci mu ba da gaskiya ga alkawuran Allah game da sabuwar duniya ba, kuma ba za mu yi begen su ba, domin a lokacin sun riga sun faru. Amma har abada ba za mu daina ƙaunar Jehobah da mutane ba, sai dai wannan ƙaunar ta ci-gaba da ƙaruwa.

2 Da yake dole ne mu ci-gaba da ƙaunar ꞌyanꞌuwa, bari mu bincika amsar tambayoyi uku. Na ɗaya, me ya sa muke bukatar mu ƙaunaci juna? Na biyu, ta yaya za mu nuna wa juna ƙauna? Na uku, me za mu yi don mu ci-gaba da ƙaunar juna sosai?

ME YA SA MUKE BUKATAR MU ƘAUNACI JUNA?

3. Waɗanne dalilai ne muke da su na ƙaunar juna?

3 Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙaunaci juna? Wani dalili shi ne, yadda muke ƙaunar juna ne zai nuna cewa mu Kiristoci na gaskiya ne. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yoh. 13:35) Ƙari ga haka, za mu zama da haɗin kai idan muna ƙaunar juna. Manzo Bulus ya ce “ƙauna ce take ɗaura dukan kome cikin cikakkiyar ɗayantaka.” (Kol. 3:14) Amma har ila, akwai wani dalili mai muhimmanci da ya sa muke bukatar mu ƙaunaci juna. A wasiƙar da manzo Yohanna ya rubuta wa ꞌyanꞌuwansa Kiristoci, ya ce: “Duk mai ƙaunar Allah, dole ne ya ƙaunaci ɗanꞌuwansa kuma.” (1 Yoh. 4:21) Yadda muke ƙaunar juna ne zai nuna cewa muna ƙaunar Allah da gaske.

4-5. Ka kwatanta yadda ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu zai nuna ko muna ƙaunar Jehobah ko ba ma ƙaunar sa.

4 Idan muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu, ta yaya hakan zai nuna cewa muna ƙaunar Jehobah? Bari mu yi misali da yadda zuciyarmu da sauran gaɓoɓin jikinmu suke aiki tare. Idan likita ya riƙe hannun mutum, ta jijiyoyin jini da ke hannun mutumin ne likitan zai iya sanin ko zuciyarsa tana aiki da kyau. Mene ne wannan misalin ya koya mana?

5 Kamar yadda likita yake iya sanin ko zuciyarmu tana aiki da kyau ta wajen lura da jijiyoyin jini da ke hannunmu, haka ma za mu iya sanin ko muna ƙaunar Jehobah sosai, idan muka lura da ƙaunar da muke nuna wa mutane. Idan muka ga cewa ba ma ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu yadda muke yi a dā, alama ce cewa wataƙila ƙaunarmu ga Jehobah tana raguwa. Amma idan muna nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna kowane lokaci, hakan alama ce cewa muna ƙaunar Jehobah sosai.

6. Me ya sa za mu ce idan ƙaunar da muke yi wa ꞌyanꞌuwanmu ta fara yin sanyi, to akwai babbar matsala? (1 Yohanna 4:​7-9, 11)

6 Idan ƙaunar da muke yi wa ꞌyanꞌuwanmu ta soma yin sanyi, to akwai matsala. Me ya sa muka ce hakan? Domin zai nuna cewa dangantakarmu da Jehobah tana cikin haɗari. Manzo Yohanna ya bayyana wannan gaskiyar saꞌad da ya tuna mana cewa: “Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗanꞌuwansa wanda yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda bai taɓa gani ba.” (1 Yoh. 4:20) Me darasin? Idan har muna so mu faranta ran Jehobah, dole ne “mu ƙaunaci juna.”—Karanta 1 Yohanna 4:​7-9, 11.

TA YAYA ZA MU NUNA WA JUNA ƘAUNA?

7-8. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna wa juna ƙauna?

7 Sau da yawa, Kalmar Allah ta yi ta ba mu umurnin nan cewa: “Ku ƙaunaci juna.” (Yoh. 15:​12, 17; Rom. 13:8; 1 Tas. 4:9; 1 Bit. 1:22; 1 Yoh. 4:11) Amma ba a iya ganin ƙauna da ido domin a zuciya take. Tun da haka ne, ta yaya za mu nuna wa ꞌyanꞌuwanmu cewa muna ƙaunar su? Ta furucinmu da ayyukanmu ne.

8 Akwai hanyoyi dabam-dabam da za mu iya nuna wa ꞌyanꞌuwanmu cewa muna ƙaunar su. Misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowannenku ya dinga faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya.” (Zak. 8:16) “Ku yi zaman lafiya da juna.” (Mar. 9:50) “Kowa ya yi saurin girmama wani fiye da kansa.” (Rom. 12:10) “Ku karɓi juna hannu biyu-biyu.” (Rom. 15:7) Mu dinga “gafarta wa juna.” (Kol. 3:13) “Ku taimaki juna ta wajen ɗaukar wahalar juna.” (Gal. 6:2) “Ku ƙarfafa juna, ku yi ta gina juna.” (1 Tas. 5:11) Ku “yi wa juna adduꞌa.”—Yak. 5:16.

Kananan hotuna: 1. Wata ꞌyarꞌuwa tana adduꞌa. 2. Ta kasa kunne tana saurarar wata ꞌyarꞌuwa. 3. Tana Magana da wata tsohuwa da ke rashin lafiya ta waya. 3. Ta rubuta wasika da za ta aika tare da kyauta. 4. Tana cin abinci tare da wata ꞌyarꞌuwa da ta karya hannu.

Me za mu iya yi don mu taimaka ma ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da take cikin damuwa? (Ka duba sakin layi na 7-9)

9. Me ya sa za mu iya cewa ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu hanya ce ta musamman ta nuna ƙaunarmu gare su? (Ka kuma duba hoton.)

9 Bari mu bincika ɗaya daga cikin hanyoyin nan da za mu iya nuna wa juna ƙauna. Bulus ya ce: “Ku ƙarfafa juna.” Me ya sa ƙarfafa mutane ko yi musu taꞌaziyya, musamman zai nuna cewa muna ƙaunar su? Wani littafin binciken Littafi Mai Tsarki ya ce kalmar nan “ƙarfafa” da Bulus ya yi amfani da ita a nan, tana nufin “mutum ya tsaya a gefen wanda yake cikin damuwa sosai don ya taimake shi ya samu ƙarfin jimre yanayin.” Idan muka ƙarfafa ꞌyarꞌuwa ko ɗanꞌuwa da yake cikin damuwa, za mu taimaka masa ya ci-gaba da bauta ma Jehobah da aminci. A duk lokacin da muka nuna cewa mun damu da ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa, kuma muka ƙarfafa su, ƙauna ce muke nuna musu.—2 Kor. 7:​6, 7, 13.

10. Me ya sa muka ce tausayi da ƙarfafa, tare suke tafiya?

10 Tausayi da ƙarfafa ko taꞌaziya, tare suke tafiya. Me ya sa muka ce hakan? Domin idan har ka tausaya wa mutum, za ka so ka ƙarfafa shi kuma ka yi wani abu don ka taimaka masa. Wato jin tausayin mutane yana sa mu ƙarfafa su. Manzo Bulus ya nuna cewa tausayi yana sa Jehobah ya ƙarfafa mutane. Ya ce da Jehobah: “Uba mai yawan tausayi, Allah wanda yake yi mana kowace irin taꞌaziyya.” (2 Kor. 1:3) Ayar ta ce Jehobah “Uba mai yawan tausayi” ne domin shi ne tushen wannan halin. Kuma tausayin nan ne yake sa ya yi mana taꞌaziyya “a cikin dukan wahalarmu.” (2 Kor. 1:4) Kamar yadda ruwa da ke fitowa daga maɓuɓɓuga ko rafi yake sa duk mai jin ƙishi ya samu wartsakewa, haka ma Jehobah yana sa waɗanda suke cikin damuwa su samu ƙarfafa da kuma wartsakewa. Ta yaya mu ma za mu yi koyi da Jehobah wajen jin tausayin mutane da kuma ƙarfafa su? Wani abin da zai taimaka mana shi ne, koyan halayen da za su motsa mu mu riƙa jin tausayin mutane kuma mu ƙarfafa su. Waɗanne halaye ke nan?

11. Bisa ga Kolosiyawa 3:12 da 1 Bitrus 3:​8, waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu ci-gaba da ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu don mu yi ta ƙarfafa juna?

11 Me zai taimaka mana mu ci-gaba da ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu don mu yi ta “ƙarfafa juna” a koyaushe? Muna bukatar mu koyi halin jin tausayin juna da yin alheri, kuma mu ɗauki ꞌyanꞌuwa a ikilisiya kamar ꞌyan iyalinmu. (Karanta Kolosiyawa 3:12; 1 Bitrus 3:8.) Ta yaya halayen nan za su taimaka mana? Idan muna tausaya wa ꞌyanꞌuwanmu kuma mun damu da su da gaske, da zarar mun ga suna cikin damuwa, za mu ƙarfafa su. Yesu ya kuma ce, “Abin da yake cikin zuciya, shi yake fitowa a baki. Mutumin kirki, daga ajiyarsa na kirki, yakan fitar da abin kirki.” (Mat. 12:​34, 35) Ba shakka, ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu saꞌad da suke cikin damuwa hanya ce ta musamman na nuna musu cewa muna ƙaunar su da gaske.

ME ZA MU YI DON MU CI-GABA DA ƘAUNAR JUNA SOSAI?

12. (a) Me ya sa muke bukatar mu yi hattara? (b) Wace tambaya ce za mu amsa yanzu?

12 Dukanmu muna so mu ci-gaba da ƙaunar juna. (1 Yoh. 4:7) Amma yana da muhimmanci mu tuna cewa Yesu ya ce, “ƙaunar da yawancin mutane suke yi wa juna za ta ragu.” (Mat. 24:12) Yesu bai ce yawancin mabiyansa za su daina ƙaunar juna ba. Amma ya kamata mu yi hattara don kar mu soma bin halin rashin ƙauna da ke duniyar nan da muke ciki. Saboda haka, bari mu amsa wannan tambayar: Ta yaya za mu san ko muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai?

13. Me zai iya sa ya yi mana wuya mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwanmu?

13 Wani abin da zai taimaka mana mu san ko muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai ko aꞌa shi ne, mu bincika abin da muke yi saꞌad da wata matsala ta taso a tsakaninmu. (2 Kor. 8:8) Manzo Bitrus ya gaya mana wani abin da zai iya faruwa, ya ce: “Fiye da kome kuma sai ku ƙaunaci juna da ƙauna ta ainihi, gama ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.” (1 Bit. 4:8) Babu shakka, kasawar ꞌyanꞌuwanmu da kurakuran da suke mana za su iya sa ya yi mana wuya mu ƙaunace su.

14. Bisa ga 1 Bitrus 4:​8, wane irin ƙauna muke bukata? Ka kwatanta.

14 Bari mu bincika abin da Bitrus ya faɗa a ayar nan. A farko-farkon aya ta 8, ya gaya mana irin ƙaunar da ya kamata mu kasance da ita, wato “ƙauna ta ainihi.” (1 Bit. 4:8) A zahiri, kalmar da manzo Bitrus ya yi amfani da ita a nan tana nufin “ƙaunar da aka ja ta don ta ƙara tsayi ko fāɗi.” Saurar ayar ta gaya mana abin da za mu yi idan muna da irin wannan ƙaunar, wato za ta sa mu yafe ko kuma mu rufe laifofin ꞌyanꞌuwanmu. Za mu iya kwatanta shi haka: A ce muna da teburi da wani abu ya ɗiga a kai, ya bushe kuma ba za a iya goge shi ba, za mu iya ɗaukan yadi mu buɗe shi kuma mu ja shi har sai ya rufe dukan teburin. Haka ma, idan muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai, za mu iya rufe laifofinsu, wato za mu iya yafe musu, ko da “laifofi masu ɗumbun yawa” suka yi mana.

15. Idan muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai, me hakan zai sa mu yi? (Kolosiyawa 3:13)

15 Ya kamata mu zama masu ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai, har mu iya yafe laifin da suka yi mana ko saꞌad da yin hakan ya yi mana wuya. (Karanta Kolosiyawa 3:13.) Idan muka yafe ma ꞌyanꞌuwanmu, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar su sosai, kuma muna so mu faranta wa Jehobah rai. Mene ne kuma zai taimaka mana mu iya yafe wa ꞌyanꞌuwanmu kuma kar mu yi saurin fushi saꞌad da suka yi abin da ba ma so?

Wani karamin hoto ya nuna wani danꞌuwa yana goge daya daga cikin hotunan da ya dauka tare da wasu ꞌyanꞌuwa a wayarsa. Ya buga daya daga cikin hotunan kuma ya aje shi a daki.

Idan muka ɗauki hoto, masu kyau ne mukan ajiye sai mu goge sauran, haka ma, abubuwa masu kyau da ꞌyanꞌuwanmu suka yi mana ne zai dace mu ajiye muna tunanin su, saꞌan nan mu cire kurakurensu daga zuciyarmu (Ka duba sakin layi na 16-17)

16-17. Mene ne kuma zai taimaka mana mu yafe ƙananan laifofin da ꞌyanꞌuwanmu suke mana? Ka kwatanta. (Ka kuma duba hoton.)

16 Ka mai da hankali ga halaye masu kyau da ꞌyanꞌuwa suke da shi, ba kurakuransu ba. Misali, a ce kana tare da wasu ꞌyanꞌuwa maza da mata. Kun ci kun sha, kuma bayan liyafar kuka ɗauki hoto. Kun ɗauki hotuna uku don idan ɗaya bai yi kyau ba, sauran za su yi kyau. Da kake duba hotunan, sai ka ga cewa a wani hoton wani ɗanꞌuwa ya ɗaura fuska. Me za ka yi da wannan hoton? Za ka goge shi kuma ka ajiye saura biyun da dukanku kuka yi murmushi har da ɗanꞌuwan, ko ba haka ba?

17 Hotunan da muke ajiyewa a wayoyinmu suna kama da abubuwan da muke ajiyewa a zukatanmu. Mukan tuna lokutan da muka ji daɗin kasancewa da ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Amma a ce akwai lokacin da wata ꞌyarꞌuwa ko wani ɗanꞌuwa ya faɗi ko ya yi abin da ya ɓata mana rai fa? Me ya kamata mu yi idan muka tuna abin da ya faru? Zai dace mu yi ƙoƙari mu goge shi, kamar yadda za mu goge hoton nan da bai yi kyau ba. (K. Mag. 19:11; Afis. 4:32) Za mu iya goge tunanin wannan ƙaramin kuskuren da ɗanꞌuwan ko ꞌyarꞌuwar ta yi mana, wato mu cire shi a zuciyarmu. Domin akwai lokuta da yawa da muka ji daɗin kasancewa tare da wannan ɗanꞌuwan ko ꞌyarꞌuwar. Abin da ya kamata mu ajiye a zuciyarmu ke nan.

ABIN DA YA SA MUKE BUKATAR ƘAUNA SOSAI A YAU

18. Waɗanne abubuwa masu muhimmanci game da ƙauna ne muka tattauna a wannan talifin?

18 Me ya sa muke so mu ci-gaba da ƙaunar juna sosai? Kamar yadda muka tattauna, yadda muke ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu ne zai nuna cewa da gaske muna ƙaunar Allah. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu? Wata hanyar yin hakan ita ce ta wurin ƙarfafa su. Halin tausayi zai sa mu dinga “ƙarfafa juna.” Me za mu yi don mu ci-gaba da ƙaunar juna sosai? Amsar ita ce, mu yi iya ƙoƙarinmu mu gafarta wa ꞌyanꞌuwanmu, ko da hakan yana mana wuya.

19. Me ya sa muke bukatar mu nuna wa juna ƙauna musamman a yau?

19 Me ya sa muke bukatar mu nuna wa juna ƙauna musamman a yau? Manzo Bitrus ya ba mu babban dalili, ya ce: “Ƙarshen dukan abu ya yi kusa. Saboda haka . . . ku ƙaunaci juna da ƙauna ta ainihi.” (1 Bit. 4:​7, 8) Yayin da muguwar duniyar nan take ƙara zuwa ga ƙarshenta, me zai faru da mu? Yesu ya ce: “Duniya duk za ta ƙi ku saboda sunana.” (Mat. 24:9) Sai da haɗin kai za mu iya jimre wannan ƙiyayyar. Idan muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu, Shaiɗan ba zai iya raɓa kanmu ba, ‘gama ƙauna takan ɗaura dukan kome cikin cikakkiyar ɗayantaka.’—Kol. 3:14; Filib. 2:​1, 2.

MECE CE AMSARKA?

  • Waɗanne dalilai ne suka sa muke bukatar mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwanmu?

  • Ta yaya za mu nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna?

  • Me ya sa za mu gafarta wa ꞌyanꞌuwanmu idan muna ƙaunar su da gaske?

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

a A wannan lokaci da muke ciki, nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna yana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Kuma ta yaya za mu ƙara nuna cewa muna ƙaunar juna?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba