Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w23 Yuni pp. 8-13
  • Ku Zauna da Shiri don Ranar Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Zauna da Shiri don Ranar Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TA YAYA RANAR JEHOBAH ZA TA ZO?
  • SU WANE NE BA ZA SU TSIRA A RANAR JEHOBAH BA?
  • MENE NE ZA MU YI DON MU ZAUNA DA SHIRI DON RANAR JEHOBAH?
  • “KU GWADA KOME”
  • Kada Ku Yi Saurin Jijjiguwa Daga Imaninku!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ta Yaya Jehobah Yake Kāre Ka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • “Ku Yi Tsaro”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
w23 Yuni pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 26

Ku Zauna da Shiri don Ranar Jehobah

“Ranar Ubangiji za ta zo kamar zuwan ɓarawo da dare.”​—1 TAS. 5:2.

WAƘA TA 143 Mu Ci Gaba da Ƙwazo da Tsaro da Jira

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1. Mene ne muke bukatar mu yi don mu tsira a ranar Ubangiji?

A DUK lokacin da Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da “ranar Ubangiji,” yana magana ne game da lokacin da Jehobah zai hukunta maƙiyansa kuma ya ceci mutanensa. A zamanin dā, Jehobah ya hukunta wasu alꞌummai. (Isha. 13:​1, 6; Ezek. 13:5; Zaf. 1:8) A zamaninmu, “ranar Ubangiji” za ta soma saꞌad da za a kai wa Babila Babba hari, saꞌan nan ta ƙare a yaƙin Armageddon. Don mu tsira a wannan “ranar,” muna bukatar mu soma shiri tun yanzu. Yesu ya koya mana cewa ba yin shiri kawai za mu yi ba, amma mu ‘zauna da shiri’ don “azaba mai zafi” ko kuma ƙunci mai girma.​—Mat. 24:21; Luk. 12:40.

2. Me ya sa littafin 1 Tasalonikawa yake da amfani a gare mu?

2 A wasiƙa ta farko da manzo Bulus ya rubuta wa Tasalonikawa, ya yi amfani da kwatanci dabam-dabam, don ya taimaka wa Kiristocin su zauna da shiri saboda ranar da Jehobah zai yi hukunci. Bulus ya san cewa ranar Jehobah ba za ta zo a lokacin ba. (2 Tas. 2:​1-3) Duk da haka, ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwan su zauna da shiri kamar washegari ne za ta zo. Mu ma za mu iya bin gargaɗinsa. Bari mu ga yadda ya bayyana: (1) yadda ranar Jehobah za ta zo, (2) waɗanda ba za su tsira a ranar ba, da kuma (3) yadda za mu zauna da shiri don mu tsira.

TA YAYA RANAR JEHOBAH ZA TA ZO?

Hotuna: 1. Manzo Bulus yana rubutu a kan nadadden littafi. 2. Wani mutum yana barci, barawo ya shiga gidansa a hankali.

Saꞌad da Bulus yake rubuta 1 Tasalonikawa, ya yi amfani da kwatanci dabam-dabam da za su amfane mu (Ka duba sakin layi na 3)

3. Ta yaya ranar Jehobah za ta zo kamar zuwan ɓarawo da dare? (Ka kuma duba hoton.)

3 ‘Kamar zuwan ɓarawo da dare.’ (1 Tas. 5:2) A cikin kwatanci guda uku da aka yi game da yadda ranar Jehobah za ta zo, wannan shi ne na farko. Ɓarayi sukan yi sata da dare a lokacin da mutane ba sa tsammanin zuwan su, kuma sukan yi hakan cikin hanzari. Haka ma, ranar Jehobah za ta zo kwasam a lokacin da mutane ba su yi tsammani ba. Mai yiwuwa ko Kiristoci na gaskiya ma za su yi mamakin yadda abubuwa za su faru farat ɗaya. Amma za mu tsira, ba kamar mugayen da za a halaka ba.

4. Ta yaya ranar Jehobah take kama da naƙuda?

4 ‘Kamar yadda zafin haifuwa yakan kama mace mai ciki.’ (1 Tas. 5:3) Macen da take da ciki ba za ta iya sanin ainihin lokacin da za ta soma naƙuda ba. Abin da dai ta sani shi ne ranar za ta zo. Idan lokacin ya yi, naƙudar za ta zo farat ɗaya kuma za ta mata zafi sosai. Amma ba za ta iya dakatar da nakuɗar ba. Haka ma yake da ranar Ubangiji. Ba mu san rana da kuma saꞌar da za ta zo ba. Duk da haka, muna da tabbacin cewa ranar da Jehobah zai hukunta mugaye za ta zo farat ɗaya kuma ba za su iya tsira ba.

5. Ta yaya ƙunci mai girma yake kama da wayewar gari?

5 Kamar wayewar gari. A kwatanci na uku da Bulus ya yi, ya sake ambata ɓarayi da suke sata da dare. Amma a wannan karon, kamar dai Bulus yana kwatanta ranar Jehobah da wayewar gari ne. (1 Tas. 5:4) Abubuwa da yawa sukan ɗauke hankalin ɓarayi saꞌad da suka zo sata da dare har su manta cewa lokaci yana kurewa. Gari zai iya wayewa kwasam kuma ya fallasa asirinsu. Hakazalika, ƙunci mai girma zai fallasa asirin waɗanda suka ci gaba da yin ayyukan da suke ɓata wa Allah rai. Amma mu, muna bukatar mu zauna da shiri ta wajen ƙin halayen da suke ɓata wa Allah rai, kuma mu ci gaba da yin “ayyuka masu kyau, da zaman adalci, da maganar gaskiya.” (Afis. 5:​8-12) Bulus ya kuma yi amfani da kwatanci guda biyu don ya kwatanta waɗanda ba za su tsira ba.

SU WANE NE BA ZA SU TSIRA A RANAR JEHOBAH BA?

6. Me ya sa za mu iya cewa yawancin mutane a yau barci suke yi? (1 Tasalonikawa 5:​6, 7)

6 ‘Waɗanda suke yin barci.’ (Karanta 1 Tasalonikawa 5:​6, 7.) Bulus ya ce waɗanda ba za su tsira a ranar Jehobah ba suna kama da masu barci. Waɗanda suke barci ba sa sanin abin da yake faruwa, kuma ba za su san yadda lokaci yake wucewa ba. Don haka, ba za su san lokacin da wani abu mai muhimmanci yake faruwa ba, balle ma su ɗau mataki. Yawancin mutane a yau suna kama da mutanen da suke barci. (Rom. 11:8) Ba su gaskata da alamun da suke nuna cewa muna “kwanakin ƙarshe” ba, kuma cewa ƙunci mai girma zai zo nan ba daɗewa ba. Idan wani babban abu ya faru a duniya, yakan farkar da wasunsu kuma ya sa su so waꞌazin da muke yi game da Mulkin Allah. Amma daga baya, da yawa sukan koma barci maimakon su ci gaba da koya game da Allah. Ko wasu ma da suka gaskata cewa akwai ranar shariꞌa, suna ganin cewa zai daɗe kafin hakan ya faru. (2 Bit. 3:​3, 4) Amma a kowace rana, mun san cewa ranar tana ƙara matsowa, kuma yana da muhimmanci mu ƙara zama da shiri.

7. Ta yaya waɗanda Allah zai halaka suke kama da masu buguwa?

7 ‘Waɗanda suke buguwa.’ Manzo Bulus ya kwatanta waɗanda Allah zai halaka su da waɗanda suke buguwa. Waɗanda suka bugu ba sa sanin abubuwan da suke faruwa kuma sukan yi abin da bai dace ba. Hakazalika, mugayen mutane ba sa bin gargaɗin da Allah ya bayar. Sun zaɓi salon rayuwar da za ta kai su ga halaka. Amma an gargaɗi Kiristoci su yi zaman tsaro kuma su mai da hankali. (1 Tas. 5:6) Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce hakan yana nufin mutum ya zama mai natsuwa, mai “gwada da kuma kimanta abubuwa yadda ya kamata” don ya iya tsai da shawara mai kyau. Me ya sa muke bukatar mu natsu kuma mu mai da hankali? Don kada mu soma saka hannu a harkokin siyasa ko rikice-rikice da bambamce-bambamce na mutanen duniya. Yayin da ranar Jehobah take gabatowa, za a ƙara matsa mana mu goyi bayan wani ɓangare. Amma ba ma bukatar mu damu game da abin da za mu ce a yanayin nan. Ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu natsu kuma mu yi tunani sosai don mu yi abin da ya dace.​—Luk. 12:​11, 12.

MENE NE ZA MU YI DON MU ZAUNA DA SHIRI DON RANAR JEHOBAH?

Wani sojan Roma sanye da dukan kayan kariyarsa, ya tsaya a kofar tenti yana tsaro. A bayansa kuma ga wasu sojoji da ba su sa kayan kariya ba, suna ci suna sha.

Duk da cewa mutane ba su damu da abubuwan da suke faruwa a duniya ba, muna zama da shiri don ranar Jehobah ta wajen saka rigar ƙarfe ta bangaskiya da hular kwano ta sa zuciya ga samun ceto (Ka duba sakin layi na 8 da 12)

8. Wane kwatanci ne yake 1 Tasalonikawa 5:8 game da halayen da za su taimaka mana mu zauna da shiri? (Ka kuma duba hoton.)

8 Ku ‘sa rigar ƙarfe . . . da kuma hular kwano.’ Bulus ya kwatanta mu da sojojin da suke a shirye don yaƙi. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:8.) Ana bukatar soja ya kasance a shirye a kowane lokaci idan yaƙi ya taso. Haka ma yake da mu. Muna zama da shiri ta wajen saka rigar ƙarfe ta bangaskiya da ƙauna, da kuma hular kwano ta sa zuciya ga samun ceto. Waɗannan halayen za su taimaka mana sosai.

9. Ta yaya bangaskiya take kāre mu?

9 Rigar ƙarfe tana kāre zuciyar soja. Haka ma, bangaskiya da ƙauna suna kāre zuciyarmu. Za su taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah da kuma bin misalin Yesu. Bangaskiya tana sa mu kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ba mu lada don muna bauta masa da dukan zuciyarmu. (Ibran. 11:6) Za ta sa mu riƙe aminci ga Shugabanmu Yesu ko da muna fuskantar matsaloli. Akwai mutane a zamaninmu da suka riƙe aminci duk da tsanantawa da talauci. Idan muna yin tunani a kan labaransu, hakan zai taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu iya jimre matsalolinmu. Ƙari ga haka, za mu iya guje wa son kuɗi da kuma abin duniya idan muna yin koyi da waɗanda suka sauƙaƙa rayuwarsu domin su sa alꞌamuran Mulkin Allah farko.b

10. Ta yaya ƙaunar da muke yi wa Allah da maƙwabtanmu take taimaka mana mu jimre?

10 Ƙauna ma wani abu ne mai muhimmanci da zai taimaka mana mu zauna da shiri. (Mat. 22:​37-39) Ƙaunar da muke yi wa Allah ce take taimaka mana mu ci gaba da yin waꞌazi ko da me hakan zai jawo mana. (2 Tim. 1:​7, 8) Da yake muna ƙaunar kowa har da waɗanda ba Shaidu ba, muna yin waꞌazi har ta waya da rubuta wasiƙu. Muna ci gaba da sa rai cewa mutanen yankinmu za su canja wata rana kuma su yi abin da ya dace.​—Ezek. 18:​27, 28.

11. Ta yaya ƙaunar da muke yi wa ꞌyanꞌuwa za ta taimaka mana? (1 Tasalonikawa 5:11)

11 Ƙari ga haka, muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Muna nuna irin ƙaunar nan ta wajen “ƙarfafa juna” da “gina juna.” (Karanta 1 Tasalonikawa 5:11.) Kamar yadda sojoji suke taimaka wa juna a yaƙi, haka mu ma muna taimaka wa juna. Idan ana yaƙi, wani soja zai iya ji wa ɗanꞌuwansa rauni da kuskure amma ba zai taɓa yin hakan da gangan ba. Mu ma ba za mu taɓa ɓata wa ꞌyanꞌuwanmu rai da gangan ba. In ma sun yi mana kuskure, ba za mu rama ba. (1 Tas. 5:​13, 15) Za mu kuma nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu ta wajen daraja waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya. (1 Tas. 5:12) Saꞌad da Bulus ya rubuta wasiƙar nan, ikilisiyar Tasalonika ba ta kai shekara ɗaya da kafuwa ba. Mai yiwuwa waɗanda aka naɗa su yi ja-goranci ba su ƙware sosai ba, kuma sun yi wasu kurakurai. Duk da haka, sun cancanci a daraja su. Yayin da ƙunci mai girma yake gabatowa, za mu bukaci mu dogara ga dattawan ikilisiyarmu kuma mu bi ja-gorancinsu, fiye ma da yadda muke yi yanzu. Mai yiwuwa ba za mu iya samun umurni daga ꞌyanꞌuwan da ke hedkwatarmu ko reshen ofishinmu ba. Don haka, yana da muhimmanci mu ƙaunaci dattawanmu kuma mu daraja su tun yanzu. Ko da me zai faru, mu zauna da shiri kuma kada mu riƙa mai da hankali a kan kasawarsu. Maimakon haka, mu riƙa tuna cewa Jehobah yana amfani da Kristi don ya ja-goranci dattawanmu.

12. Ta yaya begenmu yake kāre tunaninmu?

12 Kamar yadda hular kwano take kāre kan soja, haka ma begen cewa za mu samu ceto yake kāre tunaninmu. Begen da muke da shi yana sa mu san cewa abin duniyar nan banza ne. (Filib. 3:8) Begenmu yana taimaka mana mu natsu kuma mu zauna da shiri. Abin da ya faru da Wallace da Laurinda ke nan, waɗanda suke hidima a Afrika. A cikin mako uku, kowannensu ya rasa ɗaya daga cikin iyayensa. Kuma saboda annobar korona, ba su iya sun je gida don su kasance tare da iyalinsu ba. Wallace ya ce: “Begen tashin matattu ya sa ba na tuna yadda suke kafin su mutu, amma abin da ke zuwa zuciyata shi ne yadda za su kasance a sabuwar duniya. Idan ina baƙin ciki don rashin, wannan begen yana ba ni kwanciyar hankali.”

13. Mene ne za mu yi don mu samu ruhu mai tsarki?

13 “Kada ku kashe wutar ruhu mai tsarki.” (1 Tas. 5:​19, New World Translation) Bulus ya kwatanta ruhu mai tsarki da wutar da take ci a cikin jikinmu. Idan muna da ruhun Allah, hakan zai sa mu kasance da ƙwazon yin abin da yake da kyau, da kuma ƙarfin yi wa Jehobah hidima. (Rom. 12:11) Mene ne za mu yi don mu samu ruhu mai tsarki? Za mu iya roƙon Allah ya ba mu ruhu mai tsarki, mu yi nazarin Kalmarsa, kuma mu bauta wa Allah tare da mutanensa. Yin hakan zai taimaka mana mu kasance da “halin da ruhun Allah yake haifar.”​—Gal. 5:​22, 23.

Hotuna: 1. Wani danꞌuwa yana karanta Littafi Mai Tsarki. 2. Danꞌuwan yana waꞌazi tare da matarsa.

Ka tambayi kanka, ‘Shin abubuwan da nake yi suna nuna cewa ina son Allah ya ci gaba da ba ni ruhunsa?’ (Ka duba sakin layi na 14)

14. Mene ne za mu guje wa don mu ci gaba da samun ruhu mai tsarki? (Ka kuma duba hoton.)

14 Bayan Allah ya ba mu ruhu mai tsarki, muna bukatar mu yi hattara don “kada mu kashe wutar ruhu mai tsarki.” Waɗanda suke yin abubuwa masu kyau da tunanin abubuwa masu kyau ne kawai Allah yake ba wa ruhunsa. Idan muka ci gaba da yin tunanin abubuwa marasa kyau kuma muna aikata su, zai daina ba mu ruhu mai tsarki. (1 Tas. 4:​7, 8) Ƙari ga haka, idan muna so mu ci gaba da samun ruhu mai tsarki, to, ‘kada mu rena annabci.’ (1 Tas. 5:20) A ayar nan, “annabci” yana nufin saƙon da Allah ya ba mu ta ruhu mai tsarki. Kamar abin da ya ce game da ranar Jehobah da kwanakin ƙarshe da muke ciki. Ba zai dace mu riƙa tunani cewa ranar Jehobah ko Armageddon ba za ta zo a zamaninmu ba. A maimakon haka, mu riƙa ɗaukan cewa za ta zo nan ba da daɗewa ba, ta wajen ci gaba da yin ayyukan ibada da kuma kasancewa da “hali iri na Allah” a kowace rana.​—2 Bit. 3:​11, 12.

“KU GWADA KOME”

15. Me zai taimaka mana kada mu yarda da ƙararrayin da Shaiɗan da aljanunsa suke yaɗawa? (1 Tasalonikawa 5:21)

15 A nan gaba, maƙiyan Allah za su yi wannan sanarwar: “Muna zaman lafiya da salama.” (1 Tas. 5:3) Aljanu za su sa a yaɗa ƙararrayi kuma su ruɗi yawancin mutane. (R. Yar. 16:​13, 14) Mu kuma fa? Ba za a ruɗe mu ba idan muna “gwada kome.” (Karanta 1 Tasalonikawa 5:21.) A Helenanci, furucin da aka yi amfani da shi a ayar nan yana nufin yadda mutane suke gwada zinariya da azurfa don su tabbata cewa ba jabu ba ne. Saboda haka, muna bukatar mu gwada abin da muke ji ko abin da muke karantawa don mu tabbata cewa gaskiya ne. Hakan abu mai muhimmanci ne da Tasalonikawan suke bukatar su yi. Mun ma fi su bukatar yin hakan, musamman yanzu da ƙunci mai girma yake gabatowa. Maimakon mu riƙa gaskata da duka abin da mutane suka ce, zai yi kyau mu riƙa gwada abin da muka karanta ko muka ji, da abin da Littafi Mai Tsarki da ƙungiyar Jehobah suka ce. Ta haka, ba za mu yarda da ƙararrayin da Shaiɗan da aljanunsa suke yaɗawa ba.​—K. Mag. 14:15; 1 Tim. 4:1.

16. Wane bege ne muke da shi, kuma mene ne muka ƙuduri niyyar yi?

16 Mun san cewa bayin Jehobah za su tsira a lokacin ƙunci mai girma. Amma ba mu san abin da zai faru da kowannenmu gobe ba. (Yak. 4:14) Duk da haka, idan mun rayu har lokacin ƙunci mai girma ko mun mutu kafin hakan, muna da tabbaci cewa za mu samu rai na har abada in mun riƙe aminci. Shafaffu za su kasance tare da Yesu a sama, waɗansu tumaki kuma za su kasance a aljanna. Bari dukanmu mu mai da hankali ga begenmu kuma mu zauna da shiri domin ranar Jehobah!

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya ranar Jehobah za ta zo?

  • Su wane ne ba za su tsira a ranar Jehobah ba?

  • Mene ne za mu yi don mu zauna da shiri don ranar Jehobah?

WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto

a A littafin 1 Tasalonikawa sura 5, an yi kwantanci dabam-dabam da suke koya mana game da ranar Jehobah da za ta zo a nan gaba. Me ake nufi da “ranar,” kuma ta yaya za ta zo? Su wane ne za su tsira? Su wane ne ba za su tsira ba? Ta yaya za mu zauna da shiri don wannan ranar? Za mu bincika abin da manzo Bulus ya faɗa kuma mu amsa tambayoyin nan.

b Ka duba jerin talifofin nan mai jigo, “Sun Ba da Kansu da Yardar Rai,” a jw.org. (Don ka same shi, ka rubuta sunan jigon a inda aka ce, “Bincika.”)

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba